Shafi na talatin da uku

๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

MATAN QUATERS

โœ๐Ÿผโœ๐Ÿผโœ๐Ÿผโœ๐Ÿผ
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธBAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
( BAHWA ๐Ÿ“)

_(Matattarar zaฦ™aฦ™urai, haziฦ™ai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)๐Ÿ‘Œ๐Ÿป

3๏ธโƒฃ3๏ธโƒฃ

Suka hada baki
gaba dayan su Daya biyu uku aka da ga BILKISU daga gadon da aka mata aikin zuwa gadob da ake tura marassa lafiya,
Daki ne na musamman aka ware mata
Da taimakon majin yatan AKa ciccibeta aka kwantar da ita
akan gadon majin yata,
Suka gargade ta da kada ta motsa kanta kuma kar tA yawaita magana sai bayan awanni shida,
Yin hakan zai iya sabbaba miki ciwon kai mai tsanani
Cewar likitiyar,
yayinda haseena take mata tafinta,
Likitar ta zaro wayarta ta dauki yaran a hoto domin yauce rana ta farko a tarihin kafuwar asibitin da aka cire 'yan uku rus,
Yanzu haka ofishinta zata wuce zatai rubuce rubuce zata tura wa gwabnatin kasar don akwai " HIDAYA " kyauta ta musamman da gwabnatin kasar saudiyya take warewa wa mahaifan da su kansu iyayen baki daya.
Har likitan ta fita sai ta juyo ta sanarwa
HASEENA baban yan ukun ya zama cikin shiri a ko yaushe wakilan gwabnativ za'asu iya neman shi domin tattaunawa, dashi.
HASEENA ta rakata har ofishinta, tana mata godiar kulawa ta musamman tare da taya ta murnan samun nasaran aikin da akayi.

Yauwa inna zaku iya shigowa ku da maijegon amma banda hayaniya,Aunty ki shigo kema,
Nan take sanar da baban 'yan uku sakon likitar.
To wai miye hakan yake nufi ? So suke yi su san yaya na kwanta da ita har aka same su ko yaya???

HASEENA ta kyalkyalce da dariya kai zaka kashe mutum wallahi

Yoo to miye suke son sani??
Kaga saurara kwantar da hankalinka.
Mu kasan gwabnatin mu mai adalci ce da tausayin talakawa,
Ka gane gwabnati ce zata turo wakilan ta zasu maka tambayoyi.

To akan mi kenan?

Eh suna so su san zaka iya rike 'ya'yan ne?
Kana da sana'ar da zaaka iya daukar al'alarsu, na game da ci da sha, da sutura tare da nema musu lfy idan hakan ta taso?
Kai hatta da muhallinka fa sai sunje sun gani,
Idan kana da hali to
Idan babu kuma za'a gina maka gida da wadatattun dakuna
Cike da kayan more rayuwa,
Dadin daadawa suturarsu da kayan sa wansu duk su zasu dauke maka,
Idan kuwa baka aiki ka tabbata zasu baka aiki........

To da aiki na ma nikam,
Ekuma nasan ina da wadatar da in sha Allah zan wadatar dasu na ciyar dasu,

Kai dai ka saurare su kawai,
SUBHANALLAHI!!!
Aunty B mi nake gani?
Ta ina jinin nan yake zubowa?
Tai maza ta dannan na'uran da aka tanada a kowani daki yayin neman taimakon gaggawa nan da nan ta hau tsuwa tana cewa " AN-NAJDA AN NAJDA""
kafin kiftawar ido likitoci sun cika gadon balkisu,
sun fara bata dauki na gaggauwa.
Yara kuma suna cikin gadajensu na jarirai da aka tanadar musu.

A gida nigeria kuwa mata ne sukai dandazo a cikin jerin gidajen zama na kananan ma'aikata na ARKILLA,

Maman DADDY ce akan gaba ita da tawagarta tana jiran isowar mai girma gwabna don tace ba makawa ba wanda ya isa ya hanata ganawa da mai girma!
gefen ta kuwa MUBARAKA CE tana ta wani taunar jin kam,
Ga wani makeken tabarau da ya cika mata rabin fuska
Irin na rikakkun 'yan Bariki,
Rashin hankali cutar mai rayi,!!

Wai hakan MAMAN DADDY ce ta sa ta tayi wannan shigar ko zata ja hankalin gwabnan ko wani na kusa da shi a cewarta kakarsu ta yanke saka,
Tun suna marmarin tsayuwar har suka fara gajiya can sai ga dan sako,
Ya sanar da rashin damar hallatan mai girma gwabna saboda wasu baki da suka halar ce shi.
Tab nan hantar cikin MAMAN HYDAR ta kada
Karfe hudu na rana ake nema ko abin karyawa ba ta yiwa maigidan ba. gashi shi mutum ne mai zuciya,
Kuma ya washi alakarsu da su maman Daddy,
Gaba daya hankalin ta ya tashi gashi gwabnan bai zo ba bare ta sa ran abin zai zo mata da sauki, tunda maman Daddy ta musu Alkawarin kudi mai myawa zasu samu daga wurin shi,
Hankalinta a tashe yake amma da ta ga fuskar MUBARAKA yadda su fandishin da eye shado suka chakube mata a fuska zuffa duk ta jika mata hammata bata san sanda ta dara ba.
Maman Auwal da yake muguwa ce tace
"Aunty Mubaraka gaskiya adon nan bai kamata ya tashi a iska ba ya kamata ki biya ta shagon hoton a baki flAsher don tarihi,"
Ita kuwa M Daddy tsabar ranta ya baci bala'ei ta fara surfawa ga yunwa ga gajiya ga kuma rashin biyar bukata, ke kira mana (T.J ) ki dan rage mana zafi don yau na sa a raina sai naci Dankwaleliyar kaza,
Amma gaskiya unty sai na je gida nayi wanka na ci abinci,
To Allah yasa Daddy ya yi girkin da kyau,

Ummm maman Hydar ya dai naga kamar baki cikin nutsuwa???
Hmmmmm bari dai kawai yau kam sai ta Allah ni da maigidan,
Hmmmmm.
Kar ki bada mata don Allah,
Mu fa isassun mata ne masu 'yanci idan yace zai bude miki ido ba sai ki tsats-tsayar mishi ba,
Ko dama ke baiwa ce??
Ni matan hausawa kuna bani mamaki kun kallafawa ranku tsoron maaza idan zaku canza gwanda ku canza nan tai ta musu famfo da zuga har maman hydar ta ke jin komai ta fanjama fanjam. Domin maganganun shugabarsu yayi mata tasiri.

Haka dai har suka karisa shiyarsu kowa ta kama gabanta,
zuciyar maman hydar ce ta tsinke ganinshi a tsaye a kofar gida.
Fuskar nan kamar wanda akai hatsarin jirgi sama dashi tsabar rashin annuri,

Duk da haka ta matse ta cije kamar Ba komai ta wuce shi zata shige cikin gida, wata irin firgitarciyar tsawa ya daka mata sanda hantar cikinta ta kaada,
Jikinta ya fara rawa,
Ya nuna mata inda ta fito,
Ki koma inda kika fito,
Mi na rage ki dashi da zaki fara yawon siyasa.
Wa yace maka yawon siyasa naje?

wai ita tana son ta baasaar, haka dai rigima ta kara habbaka har ta kai ga ya furta abin da ba'a son,
Kai mata kennan ga rauni ga shagala,
Nan da nan ta zama abin tausayi ta zube gwiwoyi tana mishi magiya

"Don Allah ka rufa min asiri,
Ina kake so naje?
Iyayena basu da karfi inda zan tsuguna ma kasan basu dashi tunda su ma ta kansu suke yi,,,,,
Yanzu kika san haka?
bani da damuwa duk inda zaki je kije ya shiga ya banko kofa,
Kuka take wiwi, taki barin wajen,

Har ya fito zuwa masallacin sallar magariba tana wajen a rakube,
Nan duk wanda yazo wuciwa sai ya gane akwai matSala
A haka aka je aka tseguntawa shugaba sai gata tazo,
abin nema ya samu,yar masu tsegumi tayi cikin ershege
Tai ta mata farfaganda har akai sallan isha ya dawo,
Wai don tsabar iyayi itace mai tsara baban hydar tana bashi hakuri,

An fada miki ni solobiyo ne irin mijinki gantalalle da yasa miki ido kike rashin mutunci da rashin hankalinki don da ace yasan ciwon kanshi ya san hakkin da Allah ya dora mishi akanki da bai barki kin zama annoba wa Matan ARKILLAH ba,

Kaga kar ka kuskura ka zagen
Karyar ka tasha karya, akan mi zaka aibata ni da mijina, kulll!!

nan suka fara musayar kalamai masu zafi,
Maman hydar ta rasa yadda zata yi,
Maganar shi ta karshe ne ya firgita su
Ki tashi ki bi uwar taki ba dai gidana ba!
Ya shige gidanshi tana jin 'yaranta suna kuka.
Nan ta fara bin Mamman Daddy ito ko ba kunya ta juyo
" ko da wasa ina zan saki? dama kinsan mijin ki bashi da mutunci kika bini; ke nemi inda dare ya miki
Nikam bani da inda zan saki,
Tab lalle maman daddy haka zaki min ? ina zaman zamana kika biyo ne har gidana sanda abu ya kwabe min zaki min haka!??
To wallahi baki isaba kinyi kadan yadda kika raba ni da nawa gidan in sha Allahu sai kinyi da na sanin sanina a rayuwar ki,
Kinga ki rufawa kanki asiri ki san inda dare ya miki a koma chan a cigaba da cin datsa da koko,
Kai ramin karya kurarre ne a kofar gidan UNAIZA sukai ta tone tonen asirin su
B umaima ya jiyo haya niya ya fito fara basu baki,
da kyar maman haidar ta saurare shi da yake itan da sauran mutuncinta,

Ta fara koro mishi bayani ,
Ya katseta kinga dare yayi kiyi hakuri ki karisa gida ki kyaleta,
Nan ta rushe mishi da kuka ta labarta mishi abinda ya faru.

Ya tausaya mata,

Idan ba zaki damu ba ko za ki iya kwana wurin mu,
Idan yaso zuwa wayewar gari in sha Allah zan same shi
Wuya mai sa nadamar dole nan ta hau zuba godia.
A kunyace ta shiga,
ya ma unaiza bayani " ki gyara mata dakinki zuwa safiya"
To baban umaima.

Cikin kudirar ubAngiji Imran ya angwance da amaryar shi lAURAT
Amarya ta tare an sha wuni an watse yan uwan amarya sunyi kokarin bada amana wa uwargida amma sam basu samu fuska ba,
haka suka hakura,
Kashe gari IMRAN ya shiga gaida uwar gida sarautar mata ta kare shi da kallo tana son ta gane da gaske yayi auren nan??
sannan kuma har ya fara cin amarci? da gaske yanzu sun zama su biyu?

Shi ko Sai fara'a yake da annashuwa
""
ban gane ba ban ganki a madafi ba?

Ai ya kamata war haka kin mana abin karin kummalo ko?,

Ta zabga mishi harara har zatai magana ta tuna nasihar da mahaifanta sukai mata,
Shiyasa taki yarda da rainin hankalin kawowa amanar dangin amarya da kuma kin amsa gayyatar imraan ya hada su ya musu fada da kuma zAncen raba kwana.
Don zuciyarta na ayyano mata rashin mutunci da cin zarafin da zatai musu,
To anata tunanin maganin ayi kar a fara,
Oh. Matata ta kaina ba ko gaisuwa to ina kwana??
Yaya kika kwana?:
a hasale ta bashi amsa
Yadda ka kwana mana a
ya dan saki murmushi idan kuwa kika kwana yadda na kwana gaskiya na miki murna.
Malam don Allah ka bani wuri nasha iskaa "
Idan naki fah?
wai ina Salima ce bata dawo banee,?
Auntyn ta tAce sam bata ji hayaniyarta ba,har karfe kusan goma fah
Tana gidan mu.
To ya batun abin karyawar?

Ta fito ta girka muku mana.

a haba ba neman shawarar ki nake ba,. ai nasan da itan na same ki,
Ba girman ki bane kar ta raina ki mana ki danyi mata kara mana,
Ta rainan nace ta rainan, dama kana ganin wani mutunci zamuyi? to ka Canza tunanin ka, kayi kuskure.
Ya mike sassauta murya kar ta jiyo ki don Allah,

Ta kara sauti yo taji yo mana sai mi ni da gidana ???
Ya yi murmushi ya fice,

Don Allah kiyi waya a kawo min rabin raina,

Idan anki fah??

Murmushi yayi ya fice

Auntyn salima inaga tashi za kiyi ki mana kalacen nan dama kin sabaa...
Kai baban salima Kawai sai ta ganni a madafi......?
Kar ki damu jihadi kika dama kuma ki shirya kalu balen da zaki fuskanta kafin Allah ya dai dai ta lamarin,
Kusan karfe biyu na rana Maman salima ta fito yinwa ta gama kwaakwale mata ciki,
Tai turusss!!
yanzu laure ki shigo gidan ko nema na baza kiyi ba,
Sai ki shigo ki daura musu abinci wato shiyasa ake cewa " da dangin miji da musu aiki na kowa ne a gida,"
ai ina ganin ko naman ki nake yanka baza ki juya min baya lokacin da kowa ya gujen ba hatta iyaye na laifi na suke gani sun ce ni ce na jawo aka min kishiya,

Tsabar takaice umman mu fah hana kuwa zuwa wurinaa tayi,
Baban saliman ne ya kira ki???
Ana kiran waya ta laure dauko min ita a daki tana kan gado na gefen filo,
ba gardama laure ta shiga cikin dakin ta dauko mata mata wayar a sanyaye ta mika mata,
MA'U tabi hannunta da kallo wanda suka sha kunshi da gyara cikin nan luwai luwai,
Ta cigaba da amsa wayarta daga nan tayi daki don ta samu ta sake da kawartata.
tana cewa oho ni ban ganta ba ma ban san na ya take ba,don bani da damuwa da ita.
Tana ta daukan darasi a waya ana ta daurata akan karkatac-ciyar hanya daa bata da ma bulla sai da nasani.

Tana fitowa taga laure na zubawa IMRAN abinci ta mika mishi,
Malam kasan wannan kam tawa ce ko?
Sai ka bari amaryar taka tazo ta baka,
laure zo ki daura min ruwan Shayi,

To Aunty Bari na gama da aikin lada tukun,

Akwai wani aikin da ba na lada ba ne? naga biyan ki ake ko?
Ko kin taba yafe mana Albashin ki kince don lada kike yi??.
Yace" Kinga
ce miki tayi za tayi aikin lada tana nufin aikin aure za tayi"
Ina ita amaryar taka da bazata fito tayi aikin auren ba???
Gata nan a gabanki.............
Saitin hanunshi tabi da kallo cikin firgici da razana ta hau kak-karwa tana nuna LAURE
Ke ke ke ce dama.........!!?!.

A dai dai nan Alkamin maman Iman ya fadi tsabar razana da kidima da taga ASMA'U ta shiga

โœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ

Comment