shafi na sha tara

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ πŸ‘ŒπŸ»

Na sadaukar da wannan shafin ga HARUNA Admin na beneficial writers ngde sosai,

1⃣9⃣

HASBUNALLAHU WA NI'EMAL WAKIL,
Maryama ta ambata jin haka mustapha ya fito daga daki yace

''Maryama lafya?
Miya faru?

Ka ga zo kaga abinda na gani?

SUBHANALLAH!!
Jini kuma maryama?
Eh
Dama kina jin ciwo ne ko ko?

','ni dai lafiya klau na fito zan sha ruwa fitar da zanyi kawai sai naji mara ta ta murda da kyar na zauna akan kujera shine naji abu na biyowa kafata,,

Shiga ki cire kayan baccin nan muje Asibiti,

Baban Auwal lafiya kuke tsaye chirko chirko?

Lafiya klau maryama ce jini ya balle mata shine nake shirin kaita Asibiti,

Asibiti kuma a wannan talatinin daren bazaka bare gari ya waye ba?

Baka tsoron wani abu ya same ku a hanya?

Maryama kuwa har ta fito sanye da hijabinta da jallabiyar shi hannunta ya karbi rigar yace '' ta koma ta dauko mashi dan makullin shi,

Amma dai maman Asiya kinsan bazan barta haka jini yana zuba ba'asan miye dalilin ba

' to ni dama baban Auwal ina jiye maka fitar dare ne,
da hakurin kayi idan yaso gari na wayewa sai ku tafi,

Ke maryama zo mu tafi,

Ya wuce ya fita maryama tasa kai kenan sai taji maman Auwal tana cewa

Ai wannan cikin sai dai yabi shadda ba dai ya zama mutum ba
Ta fashe da dariya

Maryama ta jiyo ta kalleta,

Bata ce mata kala ba ta wuce suka tafi,

Sun isa Asibitin sunyi sa'a akwai likita ON CALL maza maza ya karbesu yana jin bayanin ya ce ta kwanta ayi scanning a duba aga miye matsaallar,

Likita yace ranka ya dade sakamakon ya nuna ba komai sai dai zai iya kasancewa ko rashin hutu ne,

Ya rubuta magani,
Ya mika mishi

ga wannan ka saya amma da sharudda ka dan nisanceta na kwana biyu,sannan banda aiki mai wahala ,kamar daukar abu mai nauyi, a kiyaye insha Allahu babu abinda zai taba cikin,

Suka koma gida abin mamaki maman Auwal idonta biyu

Yace mata ya naganki a zaune ne?

Eh wallahi dama jiranku nake yi ka dawo nasan ita zasu rike ta,

'' basu riketa ba gata nan mun dawo,
Kuma mi suka ce?

Gata nan tambyeta?

Umm mi suka ce??

Take dabara ta fadowa maryama'' Sunce ya zube gobe naje ayi wankin ciki,

Nan da nan farin ciki da murna suka bayyana mata,

ba maryama ba har mustapha sanda ya gane,

Maryama ta wuce daki ta barta a tsaye daga baya shima ya bita dakin ,

amma maryama idan ba ido naba gani nayi kamar Asiya murna take da abinda kika fada,
Kuma kema nayi mamakin da kika fada mata akasin abinda likita yace,

Lah kar ka damu ya za'ayi tayi farin ciki?

Baka lura bane,

Ke nifa ba yaro bane,
Yayana ka bar maganar don Allah sai da safe,

Ta juya ta kwanta shima dai haka ya hadiye damuwarsa ya kwanta da niyyar idan gari ya waye zai sayo magani,

Asubar fari kuwa inna dije ta kwankwasa musu kofa,

Ya bude kofar da zata sada ka da tsakar gidan,

Inna lafiya da Asuban nan?

Lafiya klau, ina maryama?

Tana ciki tana bacci
Jiya nayi mummunan mafarki da ita, an mata ajiya akan hanya ta zallaka jini ya balle mata,

( Yasan halin mahaifiyarshi ta kasance idan tayi mafarki to da ikon Allah yana zama gaskiya ko kuma sai makamancin hakan ya auko,

Kai ta kasance ko hasashe tayi yakan yi kusan zama gaskiya,
Baiwar ta kenan ita shiyasa bata faye son yawan magana akan abu ba)

Inna shiga dakin tana ciki ai,

tana zuwa dai dai wurin ta ja baya ta karanto addu'o'inta ta shiga ta samu ta tashi kenan

Maryama abinda nayi mafarki haka ne?

Inna ban fahimci mi kikai mafarkin ba,

Inna ta leka wurin da maryama ta taso taga jini yadan bata zanin gadon,

Hmmmmmm,

Kuna da jar kanwa a gidan nan ?.

Eh inna ba'a rasa ba inaga akwai don kwanaki na saya lokacin da za'an dafa MADOBIYA

''Dauko min akwai tsintsiyar laushi sabuwa?

.eh akwai to jiko min

Ta jika ta kawo mata

Inna dija ta tofah addu'ointa a ciki tazo ta fara yarfa wannan ruwan jan kanawar da Adduo'e

Maryama kinyi wasa da Addu'a ko?

Idan ba haka ba ba abinda zai same ki,

Inna sunce fah wai ba komai basu ga komai ba amma sun ce na daina aiki ina kwanciya banda aiki,

Hmmmm!
Maryama kenan dama mi zasu gani ke dai ki dage da Addu'a

ANIYAR MODA TABI RANDA,

inna sun rubuta magani ma zamu sayo anjima,

To ban yarda kuyi na Asibiti ba idan kun fita ku tafi irin chemist dinnan na Addini ku samu kuyi musu bayani zasu hada miki magani,

To inna sai dai ki fadawa baban Auwal kinsan su sunfi yarda da Asibiti,

Kyale ni dashi.

Maman samha tana kwance tana baccin safenta da ta saba
Mai aiki tana hada abin karyawa a madafi,

Sai ga baban samha da samha a hannun shi ,

Jamila karbeta inaga bayan gida tayi a pampers yake damunta,

To ta rusuna ta karbeta tace inaga
shine yake damunta,
Ta wuce ya bita da kallo a zuciyarshi ta ayyana mishi kyawun jamilar ga iya girki ga juriya da kula da yara domin kullum ya dawo daga wurin aiki zai sameta dauke da samha tana bata abinci a baki ko tana mata wasa, wani sa'in/kuma tana goye a bayanta,

Abinda uwar ta gagara kenan ya rasa yaushe zata daina lalaci da son jiki,

Bari dai zaiyi shawara,

Tuni harta wanketa ta karisa abin karyawa tana jera akan teburin cin abinci,

Baban samha a tsaye akan maman samha,

Ki tashi nace mu karya zan tafi office ,
ta juya haba baban samha nace maka bazan ci ba,

Ta ja fulo ta toshe kunenta,

To hungo kudin cefane,

Ka bawa jamila don Allah sai ka dawo,

Ranshi a bace ya fice ya zauna yaci abincin yana lura yadda jamila take lallaba samha tana bata kununta a baki,

Ya gama ya mika mata kudin cefane
Ranka ya dade mi za'a girka?

Tuwo miyar ogbono nake so, akwai busashen kifin nan ko ya kare?

a'a akwai,
yauwa baban samha babu naman ragon nan ya kare, sai sauran na kaza na kazar ma bata da yawa,

Pampers din samha ma sauran guda biyu,

''To kunun ta fah akwai?

Eh amma bazai wuce shan gobe ba,

Owk to ki shiga dakina ki bude durowar gado ki debi dubu Ashirin ina zai ishe ku?

ai yayi yawa ma

To kema kisai su turare da kayan kwalliya mana,

Ta durkusa ta mishi godia,

Ya fice,

Jamila ta kasance matashiya ce mai nutsuwa baka ce,amma ba chan ba a takaice dai kyakykyawa ce amma farat daya baza'a gane hakan ba saboda kananan kyau ne da ita,

Taje ta musu shopping ta debo kayan gyara iri iri,
suka dawo sannan ta daura musu abincin ranar,

Sai lokacin Ladeefah ta fito bayan tayi wanka tayi feshe feshenta,

Akwaita da son gayu amma miji kam bai samun kulawa ba.

Hello T.J ya ne kam?

Lafiya klau don Allah arxiki nake son roka matatace take da ciki ko zaki bani aron mubaraka ta rakani kasuwa sayayya kinsan matar tawa bata waye ba,

To ba damuwa wace kasuwa zaku don nima ina son anjima na shiga kasuwar na dubo mayafai,

a'a basai kin shiga ba fada min kala kawai sai na sayo miki,

Owk dama purple ne sai Ash da kuma brown,

Ba damuwa,
Taji bulus karfe nawa zaka zo sai ta shirya kar kazo kana jiranta?

Misalin karfe hudu idan an tashi daga wurin aiki,

Ki tanada min abinci ma,

Toh ba damuwa sai ka zo kenan,

Yauwa don Allah maman daddy kafin nazo ko zaki min list din da ake bukata na baby dana uwar?

Kar ka damu, indai wannan ne,

MUBARAKA taho,
kiyi sauri ki gama sanwar dare yayanki T.J zai zo zaku je kasuwa sayayya,

Nace mishi nima zanje sayan gyale yace na bari zai sayo min,

Kinsan mi nake son ki min?

a'a
Ki zaba min irin gyalen da maman hanipan nan take yafawa, kin gane ko?

Eh Aunty

Yauwa je ki kintsa.

TANGAZA

Mama ce zaune da indo a daki suna shawara lalle itama indo zata tarkata nata ya nata ta koma birni da zama gidan yayanta QaSEEMU,
saboda itama ynzu so take ta zama yar birni irin kannenta su BELLO da MUSA
,
Tunda auren ya gagara mama ai gwanda nakoma ta birni,,
mama tace''
gaskiyar ki indo gwanda kam kije kema ki ci abinda suke ci uwata,

Sha kurumin ki mama,

Amma baki san abinda nake tunani ba,

Miye kike tunane?

Kina ganin baba zai yarda kuwa na tafi birni ?
Eh toh,
Ki jarraba tambayarshi mana idan yaso sai muji abinda zai ce,

ai karya QASIMU yake yace zai tara arziki su BILYAMINU basu tara ba,
gwanda kuje ku cinye abinda yake samu a abinci kinga idan kun mishi yawa ai bazai tara komai ba sai abinci,

Allah ya tabbatar da tafiyar nan mama wannan matar tashi mai gulu gulun idon sai na ringa hada su rigima da gangan,

''dai dai ne uwata''

Ana idar da sallar magariba kenan inna ta kawo mishi abinci,
ta xAuna a gefenshi bayan yaci ne yake cewa dazu munyi waya da matata tace ina inna da mama mai fadan nan?

Kai!

Tayi wayo sosai bakin ta ya bude
Har karatun makarantarta sanda ta min,

Hmmmmmm ina ruwan umaima baki ya bude kasan yaran yanzu kamar wahayin magana ake musu,

Indo tai sallama,

Ta gaishesu taacigaba da cewa

'' baba dama so nake na tambaye ka ina son bin yaya QASEEMU idan ya zo hutun karshen mako,

a'a indo wani irin hauka ne wannan ace duk kun tattara kun koma mishi miye yake dashi?
ko don kunga yana karfin hali,
a'a bana son wannan rashin hankalin,

a'a malam ka barta mana ai iya bakinta kam ba zai rasa ba,

Ke salamatu bani son shirme ku mata duk hankalinku baku da hangen nesa,

Mi yake dashi da duk za'a rore gidan shi?

Ta'aliki
Watsa
Zaba

Ummu iman ce!
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

Comment