shafi na Talatin

🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
 
MATAN QUATERS


✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman


Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com


🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)


_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
  
Dukkan yabo da godia sun tabbata ga  Allah madaukakin sarki,
Cikin ikon shi da kudirar shi ya bani ikon cigaba da rubutun littafin MATAN QUARTER'S
    Allah ka karawa Annabi Daraja tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi,
 
Wannan shafin sadaukarwa ce ta musamman ga kyautar da Allah ya bani na haihuwar IBRAHEEM ( FARHAAAN )
Allah ya raya min shi,
Ya Albarkace shi da sauran Al'umma gaba daya.


بسم الله الرحمن الرحيم


3️⃣0️⃣


Bayan tafiyar QASEEMU wajen aiki  Allah Allah UNAIZA take yi ta  kammala  aika ce aikacen cikin gida
Ta doshi  Aminiyarta Maman Hanifah ta sanar da ita damuwarta,


  Domin tasan ita kadai ce zata tausashe ta,


Ta ja doguwar TSAKI


" Mtwssss"


  Tabbasss duk wanda yace kalmar kishiya akwai dadi to babu shakka ya fada ne kawai,
  Ita kanta UNAIZAR mamakin kanta take yi,


Yadda ta iya danne damuwarta,


   Ko da yake tasan da taimakon Addu'o'e da ta  ambata ne zuciyar ta samu nutsuwa,
  Uwa uba ma bata son ta tayarwa QASEEMU hankali, ita kanta tasan abin bagatataan yazo mishi.


  Yana isa ma'aikatarsu ya tarad - da sako, oga kuma surki yana son ganin shi,
Bai yi kasa a gwiwa ba ya karisa,,
  Kamar kullum ya rusuna ya gayar dashi cikin girmama  wa da mutuntawa,
  Alhaji ya mishi izini zama
  Ba bata lokaci Alhaji ya numfasa ya fara ayyano mishi dalilin kiran,
Ya mishi maganganu masu ratsa zuciya gameda zancen auren shi,
da yadda zai tafiyar da matanshi cikin Adalci da mutuntawa,


" da fatan ka sanar wa mai dakinka ???


  Don kar ka zama irin  sakar karun  mazaje masu boyewa matayen su lamuransu,


" Ko kadan Ranka ya dade, yanzu haka ban fito ba sanda ta shawarce ne da zuwa TANGAZA na sanar dasu batun,
   
" Tabbass tayi tunani QASEEMU"


Eh ranka ya dade, da kanta tace zata rakani ta musu bayani domin nassan mahaifiyata
Bazata Amince da
Karin aure na a yanxu ba,kasancewar ban mallaki muhallin kaina ba,
  To amma da yake akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu in sha Allahu ba damuwa,
Zuwa karshen makon nan zamu tafi,
 
Eh tana da gaskiya amma zancen muhalli ba damuwa bace
Inaga zan nemi Alfarmar masu kula da fannin gidaje su musanya wa makotanku masu lamba ta ashirin a sama musu wani gidan a cikin jerin gidajen ARKILLAN,
  Ka ga baki da hanci kenan,
      QASEEMU ina da muhallai a cikin garin nan da zan iya baka amma sanin halin mata yasa bazan baka ba
Abu daya ne ina neman Alfarma a wajenka da ka boye wannan sirrin;
  Baya da ku kadan wajen FLY OVER da BAFARAWA yayi ina da fili xan baka,
ba za'a fara ginawa ba sai
Nan da shekara daya da rabi haka,


bana son kowa  ya san da maganar nan,
  In sha Allah,
  Allah ya saka da Alheri,
ubangiji yasa a mizani,
Allah ya jikan magabata,
ya musu Rahama""
.
  Aunty inason ki bani izini zani gida gobe idan Allah ya yarda,


Hankalinta na ga Talabijin
  " LAURE mi zaki je kiyi ???
Kinsan ban fiye son kiye nisa ba, saboda,SALIMA da Babanta;
Kin riga da kin sangarta ne,
To Allah ya kaimu kwana nawa zakiyi ??


   ""Inaga zanyi sati daya "


   Haba LAURATU har sati guda?
  Kice kawai na nemo BAHIJJA tazo mu zauna kafin ki dawo,
  Idan IMRAAN yazo kya karbi kudin mota,
  


IMRAAN kuwa na chan anata penti a gidan da ya gina mai kunshe da dakuna 4 a talauce da falo guda biyu,
Daya nashi ne wanda yake hade da  dakin kwanan shi,


  Sai babban falo wanda zai dauki kujeru A kalla seti biyu,
Da dakuna 3 uku a ciki, biyu daga ciki na matan shi, sai daya na yara wanda bai kai na iyayen girma ba,


   Madafi kuwa; kowa da nashi gudun fitina,
   Ba laife wuri yayi kyau dai dai gwargwado,
Yanzu kawai abinda ya rage share share da goge goge,
sai kuma zuba kaya,
  " Inama ace kwangilar da na nema ta fito da gaba daya zan zuba dukiya a gidan maman salima da laure ko tsinke ba za su zo dasu ba,
Amma lokaci ne.


Assalamu Alaikum
 
" a'a  UNAIZA ce?


   Eh maman Hanifah nice"


  Bismillah kariso ciki ina jera kayan wanki ne a wardrobe,
  
Ayya sannu da aiki cewar UNAIZA,
 
Sun gaisa cikin mutuntawa tare da taMbayar yan makaranta,,


Shiru ya ratso dakin da yake maman Hanifah mace ce da yawar magana bata dameta ba

Chan UNAIZA ta ce
Hmmmmm nazo ki taya ni ja je ne,
Baban su umaima zai kara aure,


A sittin ta bar jikin wardrove din tace,
  Aure !!
  Zama tayi akan durowar madobi da kaya a hannunta


" Wani irin aure UNAIZA??


  Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo
  Nan ta labarta mata komai.


" UNAIZA kowa da kaddarar sa a rayuwa ina son ki rungumi taki kaddarar hannu bibbiyu,


Kar ki tada hankalinki, da zafi kam;  amma kib dauki
Lamarin tamkar ruwan sanyi zai zo miki da sauki,


UNAIZA tace

"IN SHA ALLAHU
"
kuma ko tazo ki kama kanki ba ruwn ki da shishshigi da sa ido akan abinda bai shafe ki ba,
   " In sha Allahu"


Abu na gaba ya zama wajibi ki kama sana'a UNAIZA;


To maman Hanifa wace san'a?


  Ba sai da jari ba?
  
" Kwantar da hankalinki in dan wannan ne,


    Zan sa a saro miki zannuwan gado da takalma da yan kunnaye, sai ki fara gwadawa,


Idan ya karbe ki, Alhamdulillah,


   Har TANGAZA zaki na turawa,


   Yanzu bari babansu Hanifa ya dawo zamuje  mu ciro kudin Allah yasa ki fara a sa'a,
 
Allah sarki!
maman hanifa, Allah ya biya ki,
Allah ya shiryar miki da zuria ,
Ya sa ki gama lafiya


Amin


BILKISU ce zaune tana ta fama da tsotsar magarya,
don har yanzu bata iya cin wani abincin kirki sai karume karumen su magarya , goruba Atile, Asillen zogale, gidido, su yadiya da sauransu, dan gwanda su Bula ( Tuwon Ruwa ) takan sa a kwada mata da yajin daudawa,
 
Hannunta rike da waya  tana duba status din mutane,


domin ta kasance mai sha'awar duba status din mutane,
ba don komai ba sai don tasha Dariya, da masu azanci da masu Habaici,
bata ji shigowar hubbynta ba,
sai tsinkayar maganar shi taji


Habibty  EDD  din  ki na ta kusantowa,
sauran kwana sha bakwai  inaga ya kamata mu fara shirin tafiya,


    Ni kuwa sai naga kamar zan iya haihuwar anan ma, domin akwai zakakuran likitoci fah,


   Hmmmmmm,
BILKISU kenan  Alkawari ne in sha Allahu yadda aka samu cikin acan gari mai tsarki   in Allah ya yarda acan za'a haifeshi ,


  Yanzu ki kira Aunty
( mahaifiyar Bilkisu ) ki tmbayeta  da wa zamu tafi.
   "To hubby
    Inaga bata kusa amma nasan zata kira idan tazo ta riski an kira"



Hmmmmmmm,
Allah ya raba lafiya Habibty yasa mafarki na ya tabbata na Tagwaye....


Kai rufah min asiri don Allah
BILKISU ta katse shi,


Ya kyalkyale da
dariya Allah Amin.


Mustapha ko ka ki ko ka so  maryama  tafiya zanyi da ita idan ta sauka lafiya tai Arbain sai ta dawo,
  ( INNO akwai fitina )

To  ba yadda zanyi amma gaskiya zan cutu idan maryama ta tafi,
saboda kinsan ko abinda zanci gagara ta yake yi,


Eyyi  ba dole ya gagare ka ba, tunda ka zama lusari kasawa matarka ido bata da aiki sai shegen yawun Gantali ga kazanta, kai uwa uba bata san hakkin dake kanta ba balle tasan. Hanyar da zata sauke hakkin wani,


abin kunya wai Auwal mai shekara 11 shi zai na daura girki uwa ta tafi yawun ta zubar, yawon zagayen gidan makota,


Kaga yau Al laraba ko?
to ka shirya ran Asabar zaka kaimu


Ba don yaso ba ya amsa,
   Yana kallon maryama yasan cewa ita kanta ba a son ran ta inna ta yanke hukunci ba,
  
Hmmmm


Allah ya kaiku lafiya ya sauketa lafiya,


Aminnn


[ TANGAZA


Kai da kyar INNA  ta Amince mishi da kara auren sanda aka hau sama aka sauko tukunna da Albarkacin kalamai masu tausar da zuciya da UNAIZA da ELFAH sukai  amfani dasu,


   Ba INNA   ba har MAMA abin ya burgeta don dai  bazata iya fitowa ta yabi UNAIZAR bace domin ta tabbata da matan Babban yaya ne kam; to,
Hala jeji zasu shiga sai an kamo su
Tsabar Bala'e da masifa da Tijara,
,
Nan taje ta labartawa INDO,

INDO kuwa tuni ta nemi layin BELLO don ta ji gaskiyar lamarin,
Tana murna tana bakin ciki :


Murnar za'ayi wa shalele kishiya,
  Bakin cikin kuma ance yar manya zai aura
Ubanta mai arziki ne,,


( Ban yarda gulma ta bar wajen mata ta koma wurin maza ba sai yau,)
  
BELLO kamar ya kifu da bakin shi tsabar sauri yana son ya isar wa MAMAN DADDY

"  Da gaske kake BELLO?


barin kujerar da take kwance tayi,
ta dawo kan hannun  kujerar da BELLO yake,


  Wai da gaske kake yi??


Haba Aunty ai ba wannan wasan yanzun nan INDO take sanar da ni'
  
" To ina ita uwar iyayin uwar yarda da namiji??
 
ance tare suka tafi TANGAZAN ma,


   kila ma yaji tayi cewar MUBARAKA

Baka taba bani labarin da yamin dadi irin wannan ba MUBARAKA, bashi dubu uku yasa kati,
 
Kai Aunty har dubu uku??
   " Eyyi  bari kaga ;
zama bai kama ni ba
   Nayi gidan maman Hydar don nasan shegiyar uwar mijin maman Auwal tana nan,
  Nayi mata waya,


Biyar dai dai suka shigo ARKILLAH,


ELFAH  ya sauke su ya shige gidan shi,


Hakan yayi dai dai da fitowar su MAMAN DADDY da tawagarta,
  
Suka sheke da dariya
 
Jira suke QASEEM ya shiga


    TAttabara uwar soyayya,


Uwar yarda da miji,


   To yau kin yarda da  maganarmu da muka ce namiji ba dan goyo bane,


   Gashi zai dan karo miki kishiya,
  
UNAIZA kwatsam taji maganar,


  amma da yake  tasan dunia sai tace


" Ai Alhamdulillahi tunda  auran sunna zai yi,
  
  Gwanda yayi auren da wanda zai yi kwance kwance  yana lalata da fasikanci da  'yar rikon gidanshi ,
   Yayin da  matar gidan  ta  tafi yawun gantali yawon ta zubar  !!! !!! !!!


UNAIZA........
  QASEEMU ya kirata.


Ummin FARHAAN

Comment