shafi na biyu

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
 
MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

0⃣2⃣

Qasimu ya karisa shago ya tsince abinda zai yi amfani dashi
Ya dawo gidan ya share shi tsab
  Yana gamawa yaji kiran sallar  la'asar daga masallaci da yake  can kasar layi
Suna ida wa ya mika hannu sukai musabaha da wadanda suke sahu daya kamar yadda musulunci ya tanada
Suka fito daga masallacin yasa kai yayi gaba
Da niyyar shi taلا wucewa kasuwa   ya sayo katifa da zanin gado da zai jefa a dakinshi,

  Lawiza ce take  cewa maigidanta '' baban daddy munyi bako fa''

   Ke ya akayi kika sani ?

'' dazu na raka maman  salima  na ganshi  ya fito  nan nake tambayar shi ina matar shi........
Bata karisa ba ya katse ta
'' wai  maman daddy ban hanaki mu'amalan nan da su maman salima ba?
Ah a  ai ba ni naje ba,
Ina zaune ta isko ne
  har gida kuma kasan  bazan kore ta ba':
   Ke kenan  babu dama na hanaki abu ki hanu sai kin aikata,

Wato kinfi zabar kawaye akai na,

Kai baban daddy nacce maka isko ne suke ,

To ki sani wallahi da mutunci na bazaki zubar min da mutunci ba koyaushe  a cikin hada daba kike a gidanan , kice uwar daba baku da aiki sai yi da wannan kuyi da wannan kuyi da  wancan, Allah ya yaye mike,
Ya raba ki da wannan dabia''
Amin
Ai kuwa maman daddy ta amsa tace ''
.
Ta cigaba da kunkuni ta wuce daki,
Tsoki yaja '' mtwssss
Saboda idan akwai abinda ya tsana a rayuwar shi to ba yaga dabi'ar matar shi ta hada   daba da  take yi idan ya  tafi wurin aiki,

Yayi iya bakin kokarinsa
Don ya hanata   amma abun  ya gagara,

Kai har karar ta yakai wurin magabatan su sunyi sunyi  abin yaci  tura,

Wai tsabar rainin hankali ma ce mishi take ita Allah ya bata farin jinin mutane ne

mi zai  sa ya takura mata,
Babban abinda yake  daga mishi hankali shine yadda mata suke kin kula da hakkin da ya ratayu a wuyansu
Mace zata bar gidanta babu shara babu wanke wanke kai abinci ma basu damu dashi ba idan akwai mai aiki to za'a bar musu sallahu suyi yadda suke so
Bai manta ba kwanakin  baya hakan sanda  yayi  sanadin   mutuwar  auren  daya daga cikin makwabtan su  kai harda rasa rai ma,
  amma duk bai ishe su EZNAH   ba
Maimakon sauran su koyi darasi da abinda ya faru akan maman ihsaan

Wata rana mijinta ya mata gargadi akan ta daina zuwa gidan maman daddyn nan da suke yi  ranshi baya so har ce mata yayi zai dauki kwakkwaran mataki idan bata daina ba,

Da farko kamar taji ashe likimo tayi,
Ta cigaba da fitarta tanasa lantana mai aikinta yin abinci,
Wata rana maigidan yayi dawowar bazata ya tsaida motar shi can nesa ya karisa gidan bata nan

Kusan minti goma yayi bata dawo ba ,

Bayan dawowarshi ne a wurin aiki ya mata magana ina taje?

'' tace ba inda najee baban ihsaan,
Ko?
Eh,
Bai ci mata kala ba,
Washe gari ta kira mai aikinta lantana ta bar mata sallahu,
'' zan fita amma ba dadewa zanyi ba,
Idan kin gama shara  ki dau nama a fridge ki sulala  ki soya min kafin na dawo''
  To Aunty,
Da manja za'a soya ko mangyada?
Manja mana,
Kinsan baban ihsaan baya cin mangyada ai,

Har ta fita ta dawo
'' ki kula Ihsaan tana bacci idan ta tashi ki dama mata Golden morn dinta,

To Aunty,

Lantana ko data kammala share share tayi goge goge ta dauko nama ta zuba a tukunya ta daura,
Ta duba manja sai taga a daskare yake ta fito dashi ta ajiyi  galan din a kusa da tukunyar naman a nata tunanin ya narke kafin nama ya dahu,

Gaba daya hankalinta yana kan T.V Arewa 24 sun hasko shirin ~DADIN KOWA~
Sam ta manta da abinda take yi,

Madafi kuwa  nama ya dahu har ya  tsotse tukunyar tayi baki can galan din manja ya narke shike nan wuta ta hadu da manja sai wuta tayi sama shiken madafi ya turnike da hayaki  gaba daya madafin ya kama da wuta har ya shiga silin kan kace kwabo wutar ta tsallaka dakin kwanansu
Can lantana ta hango bakin hayaki,
Tana dosar madafi taga wuta har ta kama dakin kwanansu maman ihsaan gaba daya ma ta manta da anbar mata ihsaan ,

Da gudu ta tafi gidan maman daddy ta samu basu nan sai kanwar maman daddy  take ce mata
'' sun tafi barka layin kasa ta kwatanta mata  da gudu ta isa gidan tana shiga ba sallama maman ihsaan ta mike
'' kaddai ya dawo?
A'a
Wu... Wu..  Wuta ne..... Tat ta takama
Wayyyo Allah nah ina ihsaan?
Nan lantana tasa hannu a ka ta zunduma ihu tana chan,

TASHIN HANKALI DA BA'A SA MASHI RANA!!!

Basu tsaya daukan takalmansu ba suna isowa suka tadda gidan makil da yan kaiwa dauki,
Duk kokarinsu da sukayi ina!
Wutar ta riga da ta mamaye ko ina,

Maman ihsaan gadan gadan cikin wutar zata shiga aka kamota ,
Sai kiran ihsaan take yi

Wani mai shagon da suke sayyaya ne ma ya kira number baban ihsaan ya sanar dashi abinda ya faru,
Ko ta kan motar shi Bai biba
Ya haye babur ya fada mishi inda zai je,
Yana isa ya tadda gidan ya gama konewa kurmus
Can gefe ya hango maman daddy da sauran yan kungiyarta rike da maman ihsaan suna rirrike ta abarta ta shiga zata dauko ihsan dinta

Bai san lokacin da ya tsinka mata mari ba,

''Wallahi kar ki kuskura kice min ihsaan tana ciki
Sai ji yayi maman daddy tana ce mishi

''Baban ihsaan sai dai hakuri ihsaan kam tana ciki,''
Dan ubanki rufa min baki

Ya kutsa kai zai shiga gidan wani makocinsu ya kama shi

'' kayi hakuri kar ayi HAIHUWAR GUZUMA 'YA KWANCE UWA KWANCE

''Na tabbata yadda gidan nan ya kone babu mai ran da zai fita daga ciki ka dau hakuri''
Ya juya ya tunkari matar tashi,

Nan aka fara tsegumi

''Allah ya isa tsakani na dake kuma ki sani bazan cigaba da zama dake ba,
Na sake ki sake biyu,
Bazan taba yafe miki ba,
Sanda na hanaki fitar gulman nan kika ki ko shekaran jiya sanda na dawo baki nan kika min musu,
To gashi Allah ya kamaki kin tafi yawon shashanci yar da kika haifa da cikin ki kin rasata!

Mai shagonsu dai rarrashin shi ya hau yi,
ya kama hannunshi suka nufi kofar shagun

''Ayya oga da bakai saurin sakin nan  ba,
Ba'a saki cikin hushi, saboda DANA SANI

haba malam sada wani Dana sani zanyi akan wannan mata  wallahi naja mata kunni akan yawon makotan nan amma fir taki saboda ta raina ni,

Ita ko da kuka  su maman daddy suka kamata suka shiga da ita  gidan maman daddyn

Sai cewa take yi ''wayyo na banu na lalace,
Nayi asara,
Na rabu da 'yata na rabu da mijina wayyo ina zan sa kaina?

Maman daddy tace mata
'' kin bani mamaki akan wannan mugun kike cewa kin rasa mijinki mutum da bashi da tausayi bashi da imani bai tausaya  miki na rashin 'yarki ba ya hada miki  har da saki,
ina sam !!

Allah ya raba ku,

Daina kuka don Allah kika san irin wanda zaki samu nan gaba,

Can wata yar gulma da ta biyo su tace haba ke kuwa barta mana taji da mutuwar yarta ai mutuwa ba wasa ba,

Hakane cewar maman daddy
Sukai ta bata baki bayan sa'o'i suka ce ta tashi su rakata gida,

Isarsu kenan suka tarad da mahaifiyarta a madafi tana fama da hayaki zata daura taliya yar murji itanma da kyar aka samu
Ta isko su tace
'' lafiya?
Mi ke hwaruwa haka nan na gaane ku wujiga wujiga,
Da zawalin rannan nan

Shugaba maman daddy itace mai bayani,

''Mun tahi barkatu nan kasanmu mai aiki ta tadda  mu take sanar mana da kamawar wuta a gidan yanzu haka ihsaan ma ta toye,

Subhanallahi !!!

Maman ihsaan ta kara fashewa da kuka,

Yanzu ina shi mahaihin ihsaan din?

Inna sakinta yayi hwa,
Saki kuma?
Baki hwadi mishi bane kinga tai
Ta hwadi mai inna dama ba mutunci ne dashi ba, kullum na cikin tsangwaminta,
Ya hanata rawar gaban hantsi,

'' kai yar nan hwada min gaskiya ,

Walle inna da miyan shi na hita
Inna saki biyu yammin
Sukai sallama da mamansu daddy suka tai
  
Dalili kenan da baban daddy baya son wannan muganyar Al'ada ta matar shi,

TANGAZA
UNAIZA juyi take kawai akan  gado ta gagara runtsawa saboda kewar mijinta tunda suke basu taba raba shimfidi ba sai yanzu,
Tai ta sake sake ashe inna tana hankalce da ita,
'' yar nan lahiyarki dai ko?

Eh inna ban jin dadi ne,
Hala haihuwarce?
a'a
Kinga tashi ki hwadi min kar kiji kunya
Walla ba ita bace  inna,

~~~~~~~~~~~~~~
Kwance tashi asarar mai rai
Yau satin  Qasimu biyu a cikin sokoto ya nemi izini zai tafi dubo mai dakinshi sun hanashi sunka ce mai  yaushe ma kazo?

Ranshi bai mishi dadi ba domin har ya sanar dasu yana hanya,
Sai bugawa yayi yace da mahaifiyar shi oganshi na wurin aiki bai bashi damar tahowa ba,

''Ba damuwa dan nan,
kai dai saurara har lokacin da zasu barka ,
Kaga kai bako ne a wurin bai kamata ka fara kin bin doka ba,

Bin nagaba bin Allah,
Ka zamu mai biyayya a duk inda kake ,
Insha Allahu inna na gode,

Ta mikawa UNAIZA wayar tsam ta mike ta kewaya bayan dakin innar tana mishi shagwaba da kyar ya kashe wayar.

Ta zagaya dakinta ta hada kayan tafiya asibiti domin yau kam alamar take ji,

SOKOTO

  Ya lura da matan unguwar suna da matsala sosai har ya fara tunanin dauko UNAIZA sai dai yasan idan ya sa mata doka dole ne tabi domin yasan bai taba sa mata doka ta kitare ba,
Yau safiyar Asabar ya tashi da niyyar yin wanki sai ya fita shago sayan omo,
Yana dawowa ne ya hangi  wani da alama maigidan ne da matar shi zasu fita abin mamaki  sai yaga FAROUK ne da sukai jami'ar  AHAMADU BELLO UNIVERSITY  ZARIA ba kokonto ya karisa,

FAROUK

Ya waigo
'' a'aha QASEEM  kaine yau a quater's dinmu?

Eh

FAROUK ai kusan sati na uku kenan anan
ya nuna mishi gidanshi
Kai kana nufin kai ne ka shiga gidan can?
Eh nine,
Ikon Allah,
UBAIDA hito ku gaisa  abo kina da neke baki labarin munyi A.B.U dashi  nake ce miki dan TANGAZA ne
Oh
QASEEM ko?
Eh shine,
Ayyah
Sannu,
Sannu kadai,
  Ai mu shiga kawai na hwasa hitan,
Ai kuwa lalle yau akwai hiran yaushe gamo cewar UBAIDA,

FAROUK  ya kamo hanunshi suka shiga cikin falon,

Sukai sabon gaisuwa
Nan UBAIDA
Ta kawo mishi flaks da kayan tea sai ragowar doya da kwai  ya karya,
Nan KASEEM yace wai ya akayi ka baro DAURA ka dawo nan
Hmmm kasan bayan nagama ne ina ta laluben aiki sai aka fara diban custom kamar bazan cikaba,
da yake ina da rabo  sai nayi sa'a  nasamu sukai posting dina ILELLAH tanan sokoto  border tsakanin nigeria da niger
bayan shekaru hudu ne suka mai so ni nan Headquater'  kaga iyalina na aurota daga kaduna Allah ya Albarkace mu da 'ya'ya biyu HANIFA DA HUMAIRA,
itama malamar makaranta ce tayi karatunta na jami'a a jami'a  mallakin jihar  kaduna
KADUNA STATE UNIVERSITY

QASEEM  yace
'' Allah yassa musu Albarka''
Farouk yace
'' amin
Yaya iyali hwa kayi ko har yanzu gauro ne?
QASEEM  ya bigi kafadar shi yace''
kaima kayi bare  ni,
Nima bayan rabuwar  ina komawa gida nasamu aiki na malunta a makarantar gaba da firamare ta TANGAZA,
  a haka nayi aure UNAIZA da 'yarmu UMAIMA sai kuma ciki na biyu yau ko gobe''

Allah ya raba lafiya ya sauke ta lafiya,

Nima sauyin aiki ne ya kawo ni nan domin sati uku da ya wuce
Na samu takardar sauyin aiki zuwa ma'aikatar INFORMATION & TECHNOLOGY,
kai Alhamdulillah ina tayaka murna sukayi musabaha,
Na hanaku hita unguwa,
Kar ka damu
Yanzu yaushe zaka kawo mai dakin naka,
Eh ina tunanin sai ta sauka tukunnan,
Saboda nafison ta haihu a can gida idan ta yi Arba'in sai su taho,
Allah ya raba lafiya,
Amin
UBAIDA kinji zaki samu kawa kwanannan ,
Kai baban hanifa.
Eh
Ai kuwa zanfi kowa murna saboda dama a takure nake a unguwar nan,
Kai ,
Miyasa?
  Tace mai'' wai ce min suke mai girman kai tunda naki shiga cikin su,QASEEM yace '' na lura da matan unguwar kamar suna da damuwa ya kwashe musu yadda sukayi da makotanshi randa yazo ,
Hmmm kasan kuwa itama mijinta dan TANGAZA ne kai,
Har yau ban san shiba,
FAROUK yace''
Bawan Allah kenan matar ce kamar tafi karfinshi domin itace shugabar daba ta unguwan nan sai ka ga mata sun tsallake gidajensu sun taru suna hira to da yake mamansu hanifa bata biye musu ba shiya sa suke zaginta,
To itakam ma ba hayaniya ta iya ba,
Farkon dawowar mu ne idan sun hada mata Gurmi har kuka take,
Daga baya da ta gane inda suka dosa ta rabu dasu,
Tana samun aiki shike nan ta fara fita  nan kuma  sabon tsegumi ya tashi ta hita hanyarsu sai ta samu sa'ida.
  Mtwsssssss
QASEEMU yaja tsoki ni ELFAH ( haka suke kiranshi a A.B.U)
Ni miyasa mata suke da haka ne?
Wallahi inaga kamar da rashin aikin yi sai naga idan suna da abinyi misali suna aiki ko sana'ar hannu basu da lokacin taruwa suyi ta tsitsitsi,
Hakane,

Amma inaga UNAIZA bazata kyalesuba,

Ko?

Eh,

Allah yasa,
bari na tashi zanje nayi wanki ne,
La akwai wanda yake min mizai hana ka bashi kawai,
To Almajiri ne ko ko?
Eh Almajiri ne,
zan turo maka shi,

TANGAZA

UNAIZA ta sauka lahiya ta santalo 'ya'yanta  namiji da mace,namijin  sak mahaihinshi,
Macen  kuma tayi kama da indo yar dakin mama, jini kenan,

Tun dare akai  waya gidan su  aka sanar musu da haihuwar

Washe gari  sai ga abiyyan zaman mahaifiyarta sun zo ,

Musa ne ya kira QASEEM ya sanar dashi,
Cike da murna,
Yace
'' dole na baka goron Albishir,
To yaya nagode,

Ya kira inna ta gasgata mishi,
Yace insha Allah zai nemi izini yau dinnan idan ya shiga office,
Yana son ya tambayi UNAIZAN ya kasa,
Maman tace ka kirata ta layinta mana
To inna
Ya kira lokacin tayi dumu dumu da naman kayi da aka taho mata daga gidansu ,

Maman biyu ashe nauyin da kike ji kenan,
Tace '' hmmmmmm
Ka bari wallah nasha wuya hwa ,
Allah ya saka miki da Aljanna''
Amin,
Sai nazo,
Yaushe zaka taho?

Insha Allah yau zanyi report a office,
Zan dai sanar dake idan zan taho,
To Allah ya taimaka,
Ya kashe wayar

Almajirin gidan UBAIDA ya kawo mishi abin karin kumallo,
Yake sanar mishi ka shaidawa maman Hanifa UNAIZA ta haihi TAWAYE,

to
Insha Allah zan shaida mata,

bayan isarsa da sa'a guda ne ya samu oganshi ya shaida mai  an mishi haihuwa mai dakin shi ta sauka ,
Abin mamaki sai ogan yake cewa,

'' mi anka samu ne?

Tawaye anka samu,

Masha Allah Allah ya dayyaba su yasa cikon musulmai ne,

  '' kace sai shirin tahiya gida,

Eh oga ina neman izini, ya lankwasa murya ya risina,

'Ai kuwa ya kamata ka tai ka dibo kyautar da Allah yab-baka

to ranka ya dade,

''yaushe kake ganin zan tahi, inji QASEEM
Oga ya dan juya kujerarsa

Ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu,
To Ranka ya dade nagode,
Allah ya tsare ya kare ka,

Yace
''Amin''
Yasa hannu  aljihu ya fiddo da dubu goma ya mika mishi
Gashi asai musu riguna,
Nan ya sunkaya
yayi ta zuba mishi Addu'o'ie

Ya mata waya yace sun hanani tahowa wai sai ana gobe suna ,
''Kai baban umaima'' tace

''Kai amma wasu irin mutane ne masu son kansu,
Kai kuma ka yarda?
Eh ya zanyi?
Sune gaba dani ai,
Fushi tayi ta kashe wayar,
Yasa dariya
Zan miki bazata,

~~~~~~~~~~~~~~

Washe gari ya hito kenan sai ga ELFAH da ledoji a hannun shi kuma QASEEM da warmer's din abinci akan tray
,
Sukai kicibus a kofa dama gidanka zan shiga yanzu,
Ayya
Kayi shiri kenan ?
Eh,
To ya kira lawandi Almajiri ya karbi kwanukan ,
Shi kuma ya mika wa QASEEM din leda shake da kayan jarirai kala bibbiyu,sai Atampah ta UNAIXA

kai harda wahala haka.

Allah ya biyaku  nagode a isar min da gaisuwa wa maman su Hanifah,
Ah ba komai bari na dauko mota sai na sauke ka a tasha,

Ya isa dab da Azahar
Musa ne ya fara hango shi yayi maza ya karbo kayan hannunshi jakar kaya sai ledojin kayan jarirai,
Suka shige cikin gida ya saukar da kayan a sashin shi,,
Ya mika wa musa dubu daya ga goron Albishir ,
Ya rusuna ya karba yace nagode yaya,
Yauwa zo ya miko mishi dubu uku je ka sayo min zabbi a yanka a gyara a wajen .
Ya amsa ya tafi
Shi kuma ya shiga dakin inna

Kamar wanda aka jeho shi a sama,

Har ka iso cewar inna
Hankalinshi nakan yaran domin bai hango uwar ba ashe ta zagaya kewaye ne,

Suka gaisa da inna yayi mata barka,
Can sai ga UNAIZA  tayi jifa da butar nufinta
kanshi ta nufa zata rungumeshi sai ta tuna ashe   dakin surkai ne,...............

Ta'aliki
Zaba
Watsa

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

Comment