shafi na sha uku

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ πŸ‘ŒπŸ»

SHAFIN NAN SADAUKARWA NE GA SAMEENA ALIYU FAN'S NOVELS GROUP
ina matukar jinjina muku bisa ga yawan TA'ALIKI da kuke yi
Nagode

Ω„Ψ§ فى Ψ§Ω„Ψ·ΩŠΨ± ΩˆΩ„Ψ§ فى Ψ§Ω„Ω†ΩΩŠΨ±

BASHI SA TSUTSU BASHI DA TARKO

1⃣3⃣

Dariya maman Hanifah tayi ,
Ta gyada kanta
'' mutanen nan baza su daina hali ba,
Allah ya yaye musu,

TANGAZA

ALQASEEM ne zaune gaban mahaifinshi don isowar shi kenan ya gaishe shi cikin kwantar da murya da lankwasa harce,

ina ka baro min Amaryar da yan biyu?

Suna can

Yaya ita mahaifiyar tasu da makwabtanku,?

Lafiyansu klau

kaje wurin mahaifiyarta ka idan kun gaisa zan kara so muyi magana idan ka huta,
.Baba wacc irin magana ce wannan da sai na huta zaka min ita?
ai ba damuwa muyi ta kawai,

'' to dama dan uwanka Bello ne ya same ni akan yana son ya koma makaranta,
Shine nace to ya bari idan kazo sai na fada maka muji yadda Za'ayi:

Ah to Alhamdulillah ai gwanda da yayi nazarin hakan,

Mi za'ayi da zaman banzan nan da yake yi,

Eh da din so yake yabi sahun yayunshi su bilya,

To yanzu Baba inaga abinda nake gani kawai ya tattaro ya dawo cikin sokoto don akwai makarantu na gwabnati masu kyau sosai ,

Yauwa dama shima hasashen da yake yi kenan,''

To Allah ya yi maka Albarka ya kara maka zumunci da son yan uwanka,

Amin Baba nima nagode da Addu'o'inku

KASIMU idan bamu muku Addu'ar ba mi zamu yi muku?

Hakane Baba Allah ya kara lafiya to!

Amin summa Amin

Ya mike ya dauki takalmanshi sanda yayi nisa da tabarmar mahaifinshi kafin ya saka,

QASIMU mutum ne mai taantsar ladabi da girmama nagaba dashi musamman iyayenshi,
Yana bala' in
Kaskantar da kanshi a wajensu,
bai taba yadda da wayewar zamani ba da zaka ga babba zai wuce yaro ba zai iya jinkirtawa babba ba,

Da girman shi nan
idan yaga wani dattijo ya dauki kaya sai ya kai mishi har gida,

shiyasa tsakanin s
hi da mutane sai son barka!
Haka zalika ko zai rasa kwabo a hannunshi idan zai ga wanda ya fishi bukata zai bashi
Wannan itace nasara a rayuwarshi

ah aha! Mutanen sokoto tun dazu aka kawo jaka akace kana wurin malam

Eh inna

Ina can wurin Baba ne,
Ya rusunar da kanshi,
Inna mun same ku lafiya?

Yaya kewar musa?

Ka jika da tsiya ko ?
Gododo dashi zanyi kewar shi,

Ina ma laifin kace takwarata umaima, inasu Maimunatu da ibrahimu
,
Suna can lafiyar su klau,
To yaya matar abokin naga da makwabtanka?

kowa lafiya inna
Ta kawo mishi ruwa da abinci

Ya mike bari naje na gaida mama tukunna '

a'a KASIMU ka sauka?
Eh mama,
Mun same ku lafiya?
Yaya zafi ?
ai lokacinshi ne kam ana fama

kunyi magana da baban ka ko?

Eh mama yanzu yake fada min ai mama gwanda hakan yanzu karatun shine gatan kowa ai duk wani dan talaka kam mama karatun shine rufin asirin shi wata rana

Tabbas haka ne ?

Yanzu dama insha Allahu idan na koma zan duba mishi makaranta mai kyau acan,
acan birnin ?
Kai kace Bello zai zama dan birni to ai yafi kam Allah ya bashi sa'a dai

Amin mama

Bari naje na sha ruwa
To

Wai ina takwarata ne kam ?
tana chan lafiyarta klau sai girma take yi

' shi kuma wannan Al'adar mama tana bashi mamaki, duk Alheri da za'ai mata indai ba danta bane baza ta taba cewa Allah yayi Albarka ba

( TO fah! Idan taki addu'ar Albarka ma ai Allah ya rigada yayi)

Bayan ya gama cin abincin ne
Ya fuskanci inna,

Inna don Allah ki yafe ni na zartas da hukunci ban shawarce kiva;

Ina jinka,

Ya kwashe komai tsakaninshi da mahaifinshi da kuma mama ya fada mata,

Haba QASIMU wannan ai abin Alfahari na ne, ace dana yana bin maganar mahaifinshi,
Ba komai Allah ya baka bayaan da zaka iya daukar dawainiyar mu gaba daya,

Amin

mama amma kinsan mi yake damuna?

Sai ka fadi,

Zamantakewar Bello nake dubawa da UNAIZA kinga yana da rashin kunya,
ko matan yaya Bilya da suka girme wa UNAIZA bai bar suba,
Balle ita,

Ka kwantar da hankalinka, kar ka yadda ka bashi kofar rainata a gabansu,
Misali idan tai maka wani abu da ranka bai so ba kar ka hau mata bambami a gabansu,

Sannan kayi matukar sa musu ido akan zamantakewar ko lokacin musa na fada maka balle Bello da ba shayin kowa yake yiba ,

Allah ya rufa asiri ya kara bude ya baka ladan zumunci,

Yauwa ga sako inji UNAIZA

Mi na samu ?

Kinsan ta fara zobo da kunun ayya su kankarar yara kuma ba laifi tana samu,

ayyah kaga takalmi ne na roba Allah sarki UNAIZA
Allah ya mata Albarka ya dayyaba mata 'iyalanta,

to ka ga dai yadda take kyautatamin
Kayi iya iyawarka akan ta da ma makusantantaa, ai tana da uwa,amma bata mata ba ta fara min

a'haba inna ai ina tunanin zan mata Amarya ma

Ungo naka,

Kai haba inna
akan UNAIZAN inna?

Eh itan

Inna ko dama cin hanci take baki ne?

Ba wani cin hanci neman Albarka take yi,

Yau zaka koma ne

a'a innah sai gobe Asabar zan koma,

Yauwa anjima kaje ka dubo baffanka Garba bai ji dadi ba,

Kai inna miya same shi?
Kasan nada ciwon sugari kuma bai bin kaidar shi komai labta yake yi shiyasa abin ya tashi mishi kmar bazai yi ba,
amma dai da sauki yanzu

Bari anjima idan zani Gabasawa na biya na dubashi,

Idan da hali a saya mishi kayan dubiya akai mishi,

Insha Allahu

Yanzu inna mi zan kaiwa mutan gabasawa ne?

Eh toh bansan yanayin Aljihunka ba,
Da sai nace ka sai ko da galan din manja ne ka kai musu, ba don babu ba don ace Allah yayi Albarka,

to mahaifiyar kuma ka sai mata sabulu da omo zai mata amfani sosai,

To inna insha Allahu haka za'ayi

bayan fitar shi ne mama ta shigo fada mata batun tafiyar Bello birni gobe,

eh dazu yake fada min ai Allah ya bashi sa'a yasa a dace,
.Amin

WASHE GARI

Bello ya karade abokanshi da sallama zai koma birni da zama,

Zai tafi gidan yayanshi ma'aikacin gwamnatin tarayya,

Abokinshi Rabe yake ce mishi.
'' Abokina kai kam ka haye wallahi ina ma ace nine nake da gatanka,

Kaga dai na gama makarantar sakandare tuntuni ga takarduna sunyi kyau amma bani da gatan wanda zai sama min wata ,
Shiyasa kaga na dage da wanki da guga na biya da kaina,
Don Allah abokina ka maida hankali kar kayi wasa da damanka'=

Kai nifa ba wani muradin karatun nake ba,

Kawai dai nima so nake na fasa maraya nima naga rayuwar da ake ciki,

Mtwsssss

'' wallahi bansan ranar da zaka daina shirirta ba ''
To Rabe kasan dai kwakwalwata ba ja take ba KAMAR TA KIFI take shiyasa tunda mu kazo canjin Aji aka ki wutar dani na daina ,

Allah ya shiryeka

Ameen.

SOKOTO

Bayan magariba suka isa gida
Musa yana masallaci ya saba idan suka tafi sallar magariba sai anyi isha su dawo,

UNAIZA murnan tarban maigida ya isheta,

Ga kuma bakonta sai haba haba take yi dashi tare da tambayan mutanen gida,

QASIMU ya shiga dakin shi kenan,
sai
BELLO yake ce mata
Ina ne dakin nawa?

dakin ka k0 dakin ku?
Dawa kenan?

kai da musa mana

Owo nayi tsammanin kowa da dakinshi ai?

to tare kuke!
Ta mishi kwatance ya dauki kayan shi ya kai dakin,

ko kallon inda su umaima suke bai yiba,

UNAIZA ashe kinsan dakin a rufe yake kika barni na wuce da niki nikin kaya,

Ga can makullin aacan ta nuna mai,
Ya wani fisga ya wuce tace
'' to
Kai kuma da haka kazo
dai dai nake da kai ai idan kai baka canza ba nima bazan canza ba,
Yan gadarar tsiya kawai,

Baban umaima ne ya fito da Alwala

ina Bello yake mu tafi masallaci?

Ya wuce daki,

ai ka umaima ta kirashi mu tafi masallaci,
To
Umaima ta mike tayi sallama

Waye?

Abban mu ne yace kazo zaku masallaci,

Ya watsa mata tsawa da sanda ta firgita je kice sai naci abinci tukunna,

Jikinta na rawa ta koma uban ya riga da ya fita yana jiranshi a waje,

Maman ta lura da yanayin yartan lafiya kuwa?
Tana maganar cikin tsoro ya ya ce nace abinci zai ci,
To miye na tsoron kuma ?
Mama da abin tsoro ya fada min

Ta kamota tasa ta a cinyarta taji yadda kirjinta yake bugawa fat fat fat da sauri da sauri

QASIM ne ya dawo a'a yaya na ayki yarinya kin rikita a cinya,

''Faduwa tayi ,

A gudun nata ko?
dan nan da nan sai tayi gudu ba dole ki fadi ba,
Mamana ki daina ko?
Baba nifa ba faduwa nayi ba tsawa yamin !

Kafin ta karisa uwar ta harareta
Ki min shiru nace,

QASIMU da kanshi ya shiga ya same shi yana kwance yayi bake bake a katifar musa

Jiranka nake fah
Bello yanzu za'a shiga sallan,

To yaya
Ya tashi ya shiga bayin waje yayi alolar suka wuce masallaci,

Bayan dawowar sune QASIMU yace wa musa
'' ya bashi katifar shi zuwa gobe za'a sayo mishi wata

To ba komai yaya,

Suka wuce daki
QASEEM ya dauko tsaraba
'' uwata gashi angon ki yace a kawo miki,

Ta karba su yalon Bello ne da Aduwa
Ke kuma ga naki inji inna kin wani saye ta sai wani barazana take min,

Ta bude
a'a Allah sarki inna
Nagani
Ina ruwanka,
uwa tayi aike wa yarta sai kace dole sai ka duba
Zubur ta mike tayi daki

To ga sauran nan

Ina zuwa

Ina sauran?

wannan naki ne wannan na UBAIDA

TO mungode Allah ya saka mata da Aljanna ta tattare

wallahi bacci nake ji na gaji sosai a hanya
Gashi yunwa nake ji

Haba duk abincin da kaci?

Kinsan yunwar iri iri ce:
akwai na abinci Alhamdulillah na koshi,
akwai kuma na bukata ,

Kai baban umaima baka da dama wallahi,

Gaskiya ne ai je ki kwantar da yara kizo ina jira amma ki dafa min tea,

Tsumin da inna ta aiko mata tasha,

Taje madafi ta daura ruwan shayin,
Sannan ta fada wanka,

Tayi ta kal kale jikinta
Tafi minti talatin tana shafe shafen su roll on ne humra, humra tasu ta mata,
Ta dauko wata rigar bacci mai kyau da taushi wanda suka saya a kasuwa randa suka fita da maman hanipah,

Madafin ta shiga ta tace mishi shayin ta zuba zuma ta dauki tray din ta kai mishi,

Zata juya yace '' ina zuwa?
Zan musu addu'a ne,
Kar ki dadi mana sai wani jan aji kike yi, kwantar da hankalinki ni din nake ne,

Tace ummmmm ,

Ita kuwa zuwa tayi ta samu waje tayi kwanciyarta shirun yaji yayi yawa,

Haba maman yan biyu miye hakan?

Mi ya faru,

Babu,

Taso ko nazo na dauke ki,

Ta kara juyi yarana nake ji shiyasa bazan iya zuwa ba, bana son na barsu na tafi zuwa wajen abin dadi ba kowa,

Oho yanzu na gane ramawa kike yi, to kiyi hakuri my BABY kinsan wasa nake miki,

Cakkk ya dagata sai dakin shi,

Da dina dake bakya mantuwa ai wasa nake miki ranar ,

Ya fara playing da ita.

Kin shirya ne my only,

Maryama ta amsa
Eh durlin kaya nake sawa,

Bari nazo na karisa mike bana son muyi rana,

Aikin bur inji tusa a bazawarar dai ?

Cewar maman Auwal
Dawowarta kenan daga gidan mutanen ta
(Domin tunda aka kawo maryama maman Auwal ta kudiri a niyar rashin zama,

A cewarta rashin zama yanzU ta fara tunda akai ne aka mata kishia)

Ko ya saurareta
Yana shiga ya ganta daga ita sai Bra ya fara mata cakulkuli

''durlin ka bari don Allah tana wata shagaltacciyar dariya mai tunzura zuciyar abokin gaba,

Kai abu ya kai sun fara zagaye dakin but tayi waje sai bayan Asiya
Don Allah ki hana shi Aunty

Kutumar uba !
Ranku zaiyi mummunan baci akuyoyi,

Ke waye akuyoyi?
Inji baban Auwal kenan

Waye kuwa wanda ya wuce ku bunsuraye kawai,

Asiya ki iyawa bakinki ki ka kara danganta mu da dabba ranki idan dubu ne zai lalace,

Ya lalacen nace ya lalacen,

Idan banda sallamamme baka da aiki sai saduwa

Baban Auwal har yayi shiru sai yace

'' ke ba'a saduwan ne dake kike jin haushi''

Haushin mi zanji naga kafin a sadu da ita sanda akai dani,
Abinda saura ta samu,
duk jarabarki bazaki kamo ni ba saboda nice matar shi ta fari sauran so di na kika samu,

Ayya Aunty sodin ma nagode da kika bar min shi

Baban Auwal kuwa don ya bata mata rai sungumar maryama yayi

'' kanwata zo kema ki samu sodin mursii ta rufe ido ya dauketa sukai daki

Wata zuciyar tana ce mata ta debo fetur ta watsa musu,
Su kone ta huta

Sai ta tuno hukuncin da za'ayi mata,

Ta kulla ta saka har lokaci ya tafi
Suka fito tsab gashi dai ba komai sukayi ba amma sun barta da bakin ciki,

To Aunty Asiya mun tafi,
mun barki lafiya!

Ta kawo harara ta watsa mata,

Ubangiji yasa kar ku dawo lafiyan
Ku dawo kuna yaki!!

Suka manna mata hauka suka wuce

Washe gari ya kama ranar da maman daddy zata koma Asibiti a cirewa Abdul hakori
,
Kamar kullum ta bar sallahu wa mubaraka amma fah bana son kibar CHINYERE ta taya ki aiki kinsan Baban su na gida bana zargin shi da komai amma idan yaga farar fatar ta da dirin ta sai a hankali,

''Haba Aunty Babban daddy da wanda ya zame mishi dole ma bai daga ido ya gansu ba balle wata Arniya,

To zanyi latti kamar abin jiya don Allah ruwan wanka idan ya tafi gyaran daki,

To Adawo lafiya Aunty Abdul Allah ya kara sauki ko

Tana tafiya ta rufe kofar taje tayi wanka har chinyere na ce mata
'= baza kiyi aiki bane yau na tayaki?

Kar ki damu

Zanyi naga kinyi wanka ne kamar zaki je wani wuri,
Ina nan kinsan zafi ake yi,
Bari naje kitchen

To

Kafin fitarta ta bude akwati ta dauko wasu magunguna a sachet mai hoton wata da sicket ta hadiyi uku madadin tasha daya,

Ta shiga kicin akwai tsumin maman Auwal na kwakwa a fridge ta dauka tasha,

Ta faraa shara kafin ya tashi tasan ya gama ratsata har ta gama wanki wanke bai fito ba ga shi ta fara jin idan batai harka nan ba mararta tana iya fashewa tsabar ciwo,
Taji ta fara yoyo sai kullewar mara ta biyo baya
Da kyar take daga kafarta ai a sittin ta shiga dakin ta same shi yana duba laptop,

Kayi hakuri bokitin wanka zan dauka,

Har ta shiga sai taji yace mata'

hungo shigar min da wannan
Ya mika mata boxer dinshi,

Wayyo tukur dinshi haihuwar gyatumarshi

Amma kafin nan zo nan kiyi aikin lada,

Shauki ya kara lillbeta

Yau kam bansan adadin da aka yiba domin kwayoyi sun
birkita ta ainun , saukar nunfashinsu kawai ake ji.

Yanzu idan ki ga Auntynki fah
Yaya zakiyi?

Wai yadda take da kishin nan na tabbata kashe ni ne kawai ba zata yiba

Kawo min ruwan kar ta dawo kinsan ana cirewa zasu dawo,

Haka ne

Ya gama tsiyarshi ya fice

Ba dadewa sai gata sun dawo Allah ya so ta gama abincin rana kenan,

Tayi mata sannu ta kawo mata ruwa tana ta shafa kan Abdul sannu Abdul sannu yaro na koh.

Kin gama aikin ne duka?

a'a bai fita da wuri ba sanda har ruwan ma ya salince kafin ya fito y ya karba,

Kodai baki ce mishi kin gama ba?

ah toh Aunty yana daki yaya zanyi na shiga,
a'a ai bai dace ba,

Haka ne,

Je ki gyara toh. Sannu

Ta bi ta da kallo idan ba idonta ba sai taga kamar tana tafiya agwame irin na wacce ta kwanta da na namiji nan,
Zatai magana kenan sai ga chinyere ta fito mata sannu da zuwa
To abinda ya mantar da ita kenan....

Ta'aliki
Watsa
Zaba

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

Comment