shafi na Ashirin da daya

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ πŸ‘ŒπŸ»

ALHAMDULILLAH muna godia ga Allah madaukakin sarki,sarki da bashi da abokin tarayya cikin mulkinshi,Allah ya karbi ibadunmu da muka aiwatar na ramadana,
Inai muku barka da Allah,Allah ya maimaita mana,
Ina neman Afuwa na jina shiru da akayi.

Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…

2⃣1⃣

Maman Auwal hankalinta ya tashi,
Iyakar tashi,
Tashin hankali wanda hausawa suke cewa ba'a sa masa rana!

Da na sani qeya ce,

'' yanzu ya zanyi ni 'yaasu
Haka ne fah mugunta fitsarin fago ne gashi zai gangaro min abina,

kai nima dai da fitina nake,
Koda yake Allah ya nuna min isharar shi ne,
na hana miji kar ya sadu da ita, sai ga ciki Allah ya nuna min,

to amma dama maman daddy yaudarata tayi kenan ta kaini gidan wannan mata?

Kai inah na yarda da bayanin ta domin naga Alamon rashin nutsuwa a tare dasu,

To ni anya ma cikin baban Auwal ne a jikinya?.
Saboda bokanya bazata min karya ba tace zata toro mata bakin Aljani ya shige ta idan yazo zai kusanceta ya sabbaba musu fitina yaji ya washe ta,

Kai dole na samu baban Auwal ma na fahimtat dashi,
ba cikin shi bane maryama take dauke daashi,
Zumbur ta miki, haka za'ayi
Ta kira wayar MUSTAPHAN
Ina da magana da kai idan ka dawo,

Lafiya ko?

Eh lafiya amma yana da muhimmanci,

To sai ki jira sai na dawon,

Ya kashe wayar yasan fitinarta,

Yaja tsuka yace'' ke kenan kullum sababi da fita Allah yasa ki gane maman Auwal!

kai ina zuwa maman intisar?

Barni baban inti zanje na sanar da ita namu kujerun sun iso ?

Ba kya bari ta shigo da kanta ta gani ba?

Ina bazan bari ba! ina so tasan muhimmancin ka tasan cewa mijina ba rago bane, ba mijinta bane kawai ya iya sayayya wa iyalan shiba,

Sai na dawo yayi dariya ya bita da kallo
Hoo
BILKI! BILKI !
KO sallama
babu tsabar zumudi

Sannun da zuwa'' mai mai aikinta ta amsa ai bata nan sun tahi federal sectreteriat,

To da wuri haka,
Eh kamar wai sunje canza ko E.passport,

saboda jiya ina yan share share na naji uncle na cewa za su tafi umrah sai da tasani na dauko mata abin cikin durowa ashe yayi expire shine suka tafi canza shi,

Nan da nan fuskar maman inti ya canza,

Ita ko mai aiki ta lura
da hakan hasalima da gangan ta koro mata bayani domin abin takaice yake bata ace mutum bashi da aiki sai ganin kai,

Kin tafi ne maman inti,
oh eh ban miki sallama sauri nake baban inti zai fita,

Miya faru kuma naga kin dawo jikin ki a sanyaye?

Ba komai. Ban sameta bane wai umrah zasu taje canza pasfo,

Nan da nan baban inti ya sha jinin jikin shi,
Owk kwarai kuwa dazu na muka je sallar Asuba yana cewa liman ya taya shi da Addu'a zai kai matar shi ganin likita saudi germany
Domin juya ce,

Kinga tafiyar ta neman lafiya ce,
gaskiya maman inti nayi dace,
ba karamin dace bane Allah ya baka mace mai haihuwa ba juya ba,

Wacce sai anyi ta dawainiyyar neman haihuwa,

Nan ya saki ranta ashe ma asibiti zata amma da har tana tunanin yanzu zata karo wulakanci,

( namiji kenan dan babanshi kunji karyar da ya shera saboda kar a janyo mishi zuwa. Umrah ba shiri )

QASEEMU ne zauni cikin office dinshi,
Sai ga kiran maigidanshi cikin biyayya da girmamawa ya rusuna ya dauka suka gaisa cikin girmamawa yake amsawa don Allah idan an tashi wurin aiki ina so ka biya gidana ka kai musu kudi dubu hamsin haka sukai min waya wai na hannunsu ya kusan karewa,

Bana son lokaci daya a basu mai yawa sai suyita kashewa tunda sun san za'a turo,

Insha Allahu za'a kai
Bai zarce ko inaa ba sai kasuwa inda ake saida kayan miya yadan saya musu kamar na dubu daya da zummar ya kai musu wannan daga cikin Aljihun shine don kyautatawa,.

Bai ko mance gidan ba yayi sallama wa maigadi ya bude mashi gate kasancewar ya taba ganinshi da maigidan nashi ,

Suka gaisa don Allah amin iso wurin hajia,
To dan tsimaye ni anan ?

Tace ka karisa,

Ya shiga ya sameta a falo zaune da counter na casbaha,
Faram faram ta karbeshi suka gaisa ya mika mata sakon ta tmbyeshi ya iyalan nashi,

Ta dau waya ta kira yarta ta kawo wa bako ruwa

Pure wata ni sai maltina kanshi duke a kasa amma yadda yarinyar ta gaidashi cikin nutsuwa yasa ya daa go fuskar shi a nutse sukayi arbaa
Zuciyar ZUBAIDATU ce ta yanke da kyar ta nutsu,

Yace mata ga kayan miya ta shiga dashi ciki, ta dauka tana waiwayen shi hajiya kuwa idonsu na kanta
Ayya harda dawainiya haka mungode Allah Ya kai lada MIZANI,

Oh mama wai kyauta ya kawo mana,

Eh zubAidatu,

Ashe hajia dama ana samun irin wadannan naga tunda baba ya tafi saudi ba wanda yazo gidan nan don duba lafiyar mu balle ayi tunanin ko muna da wata damuwa,

'' To banda abinki ai ba'a taro an zama daya ''

Nan dai ya mikE bayan ya dauki ledar ruwan sanyi ya musu sallama
ah bazaka tsaya kaci abinci ba nasan daga office kake
Cewar zubaida,

Hajia tace to babbar magana wata sabuwa yau zubaida ce da kanta take tayin wani yaci abinci kasancewar yawanci mutanen da suke rabe da mahaifinta duk makwadaita ne ba tarayyar Allah da annabi suke mishi ba sai don Abin dunia,

Amma ta lura wannan kyakkyawan daban yake duba da yadda taga ya zauna a kasan kafet tasan cewa dan mutunci ne wanda ya gaji mutunci yasan darajar na gaba dashi,
Kar ki damu

nagode, zan karisa gida nace
aiko da ya ka tsaya kacin,

Hajia ta amsa mata
Ke zubaida barshi ya tafi yaci na matar shi ai yana da gaskiya alama ce ta mutunta iyali,

ai mama dama yana da iyali
Ke mi kika daukeshi ne?

Nada iyalanshi kamar harda yan biyu ko?
Eh harda su su uku ne? Umaima khaleeda sai khaleed

Kai don Allah yan biyu, yaushe zaka zo ka kaini wurinsu

To uwar son 'ya'ya

Hajiya kyaleta yana da kyau hakan ai
Amma sai dai bani da mota sai machine,

Eyyah zakayi wataran ai gashi Abba yaki barina na koyi mota amma ba damuwa zan ma driver magana sai muje,

Ta rakashi har bakin gate to baban twins a shafa min kansu sai anjima.

Ta jiyo gida abinta farat daya taji ya kwanta mata 😳😳😳😳

Haka dai ranar maman Auwal ta yini a takure.

Yana dawowa bayan ya gaida inna dija ya karisa dakin gani lafiya kike nema na?

Ta hau kame kame
Fito ki fada min abinda ke ranki sai kumbiya kumbiya kike yi,
Dama naji ana cewa maryama nada ciki ne shine nake tunanin anyah naka ne kuwa?

Subhanallah ta inda kika fito kenan,
To wani dalili kike dashi da zaki jefi matata da wannan masifar?
wani kika ga ta kawo gidan?
ko kuma na kirata yanzu naji daga bakinta tunda kin ganta,

A'a nidai bance maka ba,
Jikina ne kawai ya bani saboda naga yanzu andan yi dari dari da juna ban fayi jiyowa haya niyarku ba,
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun
Anya kina tsoron Allah kuwa kice dama labe kike yi

Ya ringa mata balai yadda yake shiga ba ta nan yake fita ba,

Don Allah ka rufan
Asiri kar inna taji kasan ba so na take yi ba''

Yoo wa zai soki da wannan halin naki.

Ya fita
Ya samu inna a falo ta kasa ta tsare yanayin fuskar dan nata ta tabbatar akwai wani abu,

Zauna nan kaji na kira nace ayi kaikayi koma kan masheqiya,
saboda nasan akwai hannun mahassada a cikin lamarin maryama,

Inna mi nene kuma kaikayi kuma kan masheqiya?

a'ah ah yaro kenan,

Maryama ta fito
Ta durkusa gefen inna tace
'' inna don Allah ina neman Alfarma,

Fadi inji,

Ina wai dama cewa nayi da kin hakura annbar azzalumi da zaluncin shi zai fi ai,

tunda Allah ya kiyaye sai mu bar mishi komai a hannun shi saboda yanzu ma ba wayonmu bane ba dabarmu bace tasa Allahn ya gare cikin ba,

Ta cigaba da nusar da ita cikin lumana da ruwan sanyi har ta fahimta,

Shekenan Allah ya cigaba da karewa kuma nagode da tunasarwa,

Tashi kaje kaci abinci,

Zuciyar shi nata hararo mishi abubuwa wato dama wannan dan rashin kusantar akwai dalili kenan Allah dai yasan dai dai kar ya tsawaita zargi.

UNAIZA taga shiru shiru bai isoba kuma ba baba musa ma,

Can taji machine tai maza ta fita tace har hankalina ya kwanta naji shiru yau

Wallahi sako na Kai gidan ogana kinsan ya. Tafi Japan daga nan zai wuce saudiyya,

to kudin cefane ya ce na kai wa iyalan shi

Kawo min abinci yar gusau nake ji.

Yana cikin cin abincin ne yake ce mata ''
Zamuyi baki fah?
To daga ina?
Daga gidan ogana wai zasu zo ganin yan biyu kinsan farin jini ne dasu,

Haka ne yaushe zasu zo don a shirya ?

Wallahi ban sani ba,
Allah ya kawo su lafiya

Amin

Zuciyar shi ta buga dammmm da ya tuno kwayar idon zubaidatu kamar yadda yaji maman ta ambata mata,

Nikam ina Bello ne?

anya yana zuwa makaranta?
jiya naga ya shiga makotanmun nan,
Kinsan kema ban so kiyi mua'amala da maman daddyn nan bare shi mai karamin shekaru,

Kai anya kuwa Bello ka gani banyi tsammanin shi bane gaskiya saboda nasan ba abinda ya hada shi da ita,

To gaskiya kisa mishi ido,

Haba baban umaima Bello fah ba yaro bane? Balle nace duk inda zai shiga sai na tambaye shi

Hmmmm to ina marabar shi da yaron duk yara ne shida musa fah
Hmmm baban umaima insha Allahu za'a kiyaye,
Wai ban tambaye ka musa ba,
baku dawo tare ba,

Hmmn yana da aiki akwai commisioner na youth yarta tana birthday ya wuce can zai musu hotuna,

Kai Allah ya taimaka,

Amin harka tana ta kankama

amma ni kuma baban umaima ina da shawara,
Bismillah
Miyasa idan Bello ya dawo daga makaranta baza'a nema mishi wurin koyan sana'ar ba
kaga shike nan an huta da tunanin shige shigen,
Eh tabbas kince wani abu bari to zan nema mishi abinyi kinsan kwanaki na mishi magana sai yake nuna min bazai iya aikin wahala ba dama irin nasu musa ne da sauki tunda su ba wahala ake sha ba,

Eh baban umaima ai bazaka biye shi ba nake gani,

Hmmmm UNAIZA bazaki gane ba kinsan fah matukar akace akwai banbancin haifayya to zai ga kamar ko ina ware shi da musan ne,

Haka ne amma ina ganin kayi da zuciya daya dan adam ba'a iyar masa

Haka ne

Ina mama na ne kam?

Suna bacci tana yiwa kannen wasa har itama barcin ya sace ta

Cikin ikon Allah kwanaki suka shudi komai ya cigaba da tafiya dai dai ba yabo ba fallasa domin yanzu Bello ya dan tsorata da hidimar yan biyun nan amma yana nan yana ta kulle kullen yadda zai bullu musu yana ganin shawarar maman daddy zai bi ya rabu da yaran kawai idan yaso ya cigaba da matsanta wa uwar tayi mishi Alkawarin insha Allahu zata taimaka mishi da hikimomi yadda yayanshi bazai gane ba,
Shifa bakin cikin hadin kan musa da unaiza yake ji,
Yayi kwafa
'' Shege kanin kanin bayana amma sai cigaba yake samu ya ja tsuka.

Mubaraka dai tasha gori iri iri a wurin yaya T.J amma da yake bukatar ta kudi bata damuwa da damuwarshi bacin rai ko na miskala zaratan bata ji

Idonta ya kara budewa a F.C.E.T ta koma ruwa musamman da ta gamu da yar corner ta da suke less tare shikenan baban daddy kuwa yanxu aikin shi rabi da rabi ne ta ciko ainin iskancinta bai tsaya ba har lecturers dinta fah,

ta zama kamar Akuya amma duk da haka maman daddy taki ankarewa suturunta ya canza ga wani bleaching da takeyi amma da yake laifi tudu ne ka gan boye naka ka hango na wani,
Ga kuma kwadayi.

ZUBAIDATU kuwa raba dari tai tana tunanin dan mutan Tangaza
Ta tashi tayi sallah ta kai kukanta ga ubangiji,
Haka kawai take jin nutsuwa a cikin zuciyarta,
Wayarta ta dauko ta kira Abbanta tasan yana harami yanzu domin idan yaje saudiyya kwana yake a harami yana ibada musamman da yake official tafiya ne ya saba duk kasar da yaje idan ya gama da ita a saudiyya zai yada zango ya roke uban giji nasars kafin ya dawo, haka wannan ma ya kasance yana gamawa da Japan saudiyyan ya wuce,
''
Ummina idonki biyu lafiya ko?

Ta kwantar da murya ta gaidashi,

Nan
Yake tambayarta mutanen gida kamar su maigadi da sauran hidimomin gidan
Ba bata lokaci ta sanar da ita Abba ina son ka kara kaimi wajen yimin Addu'a zuciyata ta samu nutsuwa da wani bawan Allah,

Alhamdulillah uwata yau ke da bakinki kike fadin haka Allahu Akbar,
Allah mai amsa Addu'ar bawa
Insha Allahu yanxu ma Dawafi zan shiga na chanza niyya,
Yaya sunan shi?

Tab bansan sunan shiba Abba,

Kawai kayi
Niyya Abba shikenan ya wadatar.

TO FAH ABIN YAZO UP UP QASEEM ANGON ZUBAIDAT

Ta'aliki
Zaba
Yada

Kaltum Bappah

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

Comment