shafi na sittin

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
  
6️⃣0️⃣

النهاية
FINAL

🔚🔚🔚
 
الحمد لله الذي بنعمته تتم الصالحات
  Larabawa   suka ce"

*"مهما  طال الليل سيظهر الفجر !! !"*
"  *_WAI KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE_ "*

Daga wajen taron gidan Alhaji BAGUDO aka wuce gaba dayansu Bello ne kawai  ba shi a wajen,

Bayan kammala liyafar cin Abinci ne ALH SULAIMAN BARKINDO  ya mika wa Kasimu key din motoci guda uku: biyu iri daya dayan kuma daban
Mai daban din naka ne biyun kuma na matanka ne,
   Tukwicin gaskiya da rokon Amana da kayi kenan,
Ban taba tsammanin akwai sauran irinku a rayuwa nan ba,
Na fid-da tsammani gaskiya ashe har yanzu kuna da saura to!
Allah ya dorar da kai alan halinka na kwarai!!!
        Kuma ina fatan Allah ya kara datar da kai akan gaskiyar ka,
Sannan ga takardar aiki wa kanin ka musa ina son ya zame min ma'aji  sannan ina son na hadaka da yaro na kanin mai daki nane gashi  nan sunan shi Fadeel ya zama shine manager kai kuma M.D saboda haka don Allah asa shi a hanya sosai kwanan nan ya dawo daga karatu to shima ina son ya koyi dogaro da kai ya san neman na kan shi,

ALH BAGUDO yace " to gaskiya ka min shigar sauri na so ace MUSA ya maye gurbin Kasimu A PRINTING PRESS din mu amma duk daya ne Allah ya sanya Alheri,
Ke kuma zubaida ina son ki mikawa musa dan makullin motar ki,

  Musa yace "

  " YAA SALAAM,!!!

   gaba  dayansu sukai musu godia rabo kenan haka yake
Unaiza tai musu kyakyawar Addu'a cikin harshen larabci sukai ta binta da Ameem Ameen,
  Daga nan suka fita harabar gidan ganin sabbin motocin sun,
  Kasimu yayi mamaki da yaga irin motar da aka mallaka mishi irinta ce ake cewa ONE IN TOWN fara ce  kal samfurin MERCEDES 4MATIC new model dinta kamar a satin nan ma aka fidda ta

Bai tsinke da Al'amarin mutanen ba sai da yaga motar zUbaida iri daya ce da ta unaiza kuma tsabar kara sanda aka ce unaiza ce zata fara zaba kafin zubaidan ta dauka ta ta.

  Da yake itama akwai dattako tace " a'a ai nice babba karama ce take zaba tukunna"
   Barkindo yace haka ne kam to ki zaba my daughter

Ta zabi kalan ROYAL BLUE,

unaiza ta samu golden kuma dama itace ta mata tun farko amma kuma baza tayi
azarbabin zaba ba,
To da yake Allah ya nufa itace rabon nata aka bar mata ita,
Unaiza a take ta kira mahaifinta ta fada mishi Alherin da aka mata yace 
" Basu wayar to nayi masu godia"
Mikawa Alh Bagudo  wayan tayi ya karba suka gaisa yayi mishi godiar jinyar zubaida
" Allah ya saka da Aalheri "

Ya mikawa Barkindo suka gaisa cikin mutunci da mutuntawa,

    Bayan komawarsu gida ne Sai ga Bello

  kasimu ya kira shi
" Bello lafiya kuwa naka  halarci wurin taron ba?

   " Lafiya kalau kawai cewa nayi gwanda na kwanta nayi bacci yafi min Zuwan naje na sha rana da zafi,

( Wai ya fadi hakan ne don ya kunta ta mishi ya nuna shifa bai damu bama irin ko ohon nan )

Owk rana da zafin ne ya hana zuwa ka taya ni murnaa ?
  "  To yaya ai ba sai naje ba,"

   To gashi dan uwanka yaje ya kuma samu kyautar mota da aikin yi ka ga kaima da kaje ai da an dauke ka aikin ka huta da wahalar neman aikin,

   a'a dama shi kam ai an saba mishi hanyoyin Alheri da yake ni dinnba maman mu daya ba.........

Bai gama fada ba ya kwashe shi da mari,
Don tsabar baka da kunya ni ne zaka fadawa haka na taba nuna banbanci tsakaninka da musa to bari kaji ba zan dauki rashin kunyar nan ba .
   To gashi ai ka yiwa kanka dama idan mutum yana yin bakin ciki ko bakin hali wata rana zai wa kanshi,
  Duk rashin kunya da rashin mutunci da kake yiwa 'ya'yana da matana ba wanda ban sani ba

Wai tsabar lalacewa kai ne zaka hada baki da bare don a wulakantani a ci mun mutunci
Domin idan kayiwa iyalai na ai ba wasu kayi  wa ba,

Nine dan uwanka ka walakanta,
  kyale ka nayi kawai saboda ba na son yawaita yi maka magana ka kulllaci abun a ranka,

  Baka daraja ni ba
Baka daraja mata na ba
Baka daraja 'ya'yana ba,
Haka kaga musa yana yi?
Yanzu musa da ya zama mai biyayya baka  ga yadda rayuwar shi take cigaba ba, kafa girme shi,
   Ya warware shi tas
  Idan kaga dama ka gyara idan ka sa nunkufurci a ranka kai ka sani,

    Bakin cikin aikin musa da motar nan ya dame shi uwa uba ma wai an bashi mata
Matar ma irinsu beeba ma'aikaciya yar masu hannu da shuni,

Ni wallahi ban san miyasa MUSA yake ta cin nasara a rayuwarsa ba ni kuwa kullum baya nake komawa

Yayi kwafa ya fara tattare kayan shi gwanda ya koma kauye kawai yafi mishi Alheri,

   ( Bello kenan Hassada ce ke sa kake komawa baya,
Shi kuma musa bashi da hassada ga ladabi ga kwantar da kai,
Sannan kuma wannan hassadar da kake yiwa musan shi yasa kullum yake cigaba yake daukaka,
Dama ance mai hassada da yasan Alherin yin hassada ma wani to da bazai yiwa kowa ba,
Wa kan shi zai yiwa hassadar don ya bunkasa kanshi,)
   
Ya fara tattara kwamutsan shi yana durawa a ghana must go

A can falo kuma kasimu ne da matan shi,
An baje zanin gidan da za'a fara gina musu yana nuna musu  kowa na fadan Albarkancin  bakin shi,
    Amma matan nan kun fiye son kanku ina ta nuna muku wannan plat din amma kunce wai da nayi gwanda muyi wurin kiwo to kanwar taku fah??

   Wacce kanwa kuma cewar zubaida?.

Ehh Amaryar da zan yi mana ina nan na samu wata kanuriya ta makalkale min yanzu ma tace zuwa karahen watan nan na turo magabata na,

  Kai baban umaima ina zaka kai mace kuma ai inaga mun isa gani baka  ga zubaida fara ni doguwa ita gajeriya
   Ah don Allah ka rufawa kanka asiri wallahi mun isheka
Ita dai zubaida shiru tayi ta bar su suna ta yi da unaiza,

Memories din abinda ya faru ne yake dawo mata,
   Ta dan yi murmushi,
  To Aunty unaiza ki barshi mana ya auro indai kanuriya ce,

   Yauwa sannan gidansu habeeba sun sa auren musa nan da wata biyu,

" Wata biyu?!!!!!?
Ta firfito da idanuwa

Unaiza ta zabura
Wata biyu uwardaki bata shirya ba
To Allah ya kaimu amma ya sani kuwa,?

Zubaida tace tab ai inaga ya sani kinsan habeeba da surutu kuwa?
  Unaiza ki kwantar da hankalinki yanzu kam ba ga B..S.M

" Haka fah komai cikin sauki in sha Allah
Yanzu ki maganantu dashi ya kawo abinda ke hanun shi sai mu gani kinsan yana da kyau yasan wahalar abin,

   "  Kar ka damu,
Zamu yi magana unaiza tacewa . Zubaida " ki tambaya mana beeban size din inners wears da takalmi da kalar da tafi so,
" In sha Allahu,
Zan kirata"

Maman salima kam  laure ta tafi ta barta da kewa kullum tana tuno ta, ga saliman ma ta koma gidansu din din din saboda rashin Auntynta
wani abu mamaki ita da kanta tace "
Nikam baban salima kadaice yana damuna da zaka yarda da ka kara aure kaga ni haihuwar dama likita yace ba yinta zanyi sosai ba saboda raunin mahaifata,

"  Lalle ma maman salima da kanki kike cewa nayi aure baki tsoro?
" Tsoron me zanji zanyi ta Addua'a Allah ya hada mu da irin lauratu,

    Hmmmm naso ace lauratu na  da kanwa wallahi da mun auro ta
Yace

" Idan bana son ta fah?

" Ai in dai halin lauratu  ne da ita zaka so ta,"

  " Kuma itama ba lalle ne halinsu ya zamu daya  da lauren ba ba saboda zaki ga mutum cikinsu daya amma hali ya banbanta

   "Haka ne kam,
  Allah yasa mu dace ki sa cikiya idan kin gano mai nutsuwwa ki taya ni zance na bada sadaki ni kuma
Biki yayi biki kam an kashe kudi iya kudi abin burgewan ba bidia kawayenta sunyi kokarin su tilasta mata yin bidiar amma taki tace auren Albarka take so,
Suna ta gulmanta a gefe wai kanin bayanta ta aura daga gani ta girme mishi,
Kunsan hali irin na dan Adam komai kayi ba fita zaka yi ba
  Alhamdulillah an kawo Amarya ARKILLAH KWATAS gidan dasu maman inti suka tashi suka bari,
Ya sha kwaskwarima duk da cewa na dan lokaci ne zaman kafin kasimu ya gama ginin shi .
Don harda side din musa yake yi  ginawa amma shi gate din shi a ta baya yake,

  Mutanen TANGAZA sun zo kaca kaca amma tsabar hassada Bello bai zo ba
(wai auren cikin umanshi idan ba damuwa ba)
Masha Allahu Allah ya bawa ango da Amarya zaman lafiyaa,
     Ana gama biki unaiza ta haifo danta namiji sak kasimu inna tace
"lalle wannan yaro SODANGI  ne

( Wai duk dan da aka haifa a lokacin taro akan ce mashi sodangi saboda sanda ya tattaro yan uwa(   kunsan Allah ya yiwa malam bahaushe hikima da basira komai na yinshi cikin ilimi)

Kai yan Tangaza sun tsorata da budin da suka ga kasimu ya samu abin ya basu mamaki yadda suka ga yaje ya gyara fasalin gidansu ya mai dashi na zamani ba laifi haka zalika dakin Baba malam ma ya kwaskware shi   tas dashi

Mama fa abin ya motsa sai habaici sai kyashi a filin Allah,
    Basu koma ba sanda akai suna yaro yaci sunan mahifin zubaida  gwanin sha'awa matan Arkilla sunyi kara sun hade kawu nansu babu wani sauran tsegumi ko mita,
Maman hanifa daga lagos tazo sunan Aminiyarta itama tayi mamaki yadda taga Maman daddy ta nutsu da ita ake komai a gidan unaizan
Duk da suma ba'a bar su a baya ba  suna taimaka musu sosai don ko da Mubaraka tazo yin aure sun tsaya mata sosai tana chan ibadan aka kaita a can wajen shan maganin su na masu cutar kanjamau  suka hadu da gayen bai taba haihuwa ba dama,
ya rungumeta da yarta mace mai kama da baban daddy sak,
    Zubaida ma da dan cikinta  da yake mai dauriyace haka tai ta taimakawa unaiza har akai Arbain ita da Aunty fauziyya,
Yayar unaiza da mijinta ya rasu,
Tsabar kyawun halin Aunty fauziyyan zubaida ta hada ta aure da uncle dinta a zamfara saboda mutum ne mai son tsafta  sai bai dace ba,

Ita kuma Aunty fauziyya aakwai tsafta ga kwalliya,
  
Bayan shekaru 5 zubaida dai gwarnai tayi don yanzu 'yayanta uku unaiza ta ce  " ta bar mata haihuwar tunda ta kara mace "
tace da ma da mace ake auta
Umaima kuwa ta koma hanun Baba musa ta zama gwanin sha'awa tsabar luran da take samu a wajen beebalo itama ta dan yi jinkirin samun nata rabon Abinka da mai ilimi tace
"tunda an bata umaimish bata da matsala idan Allah yayi zata samu nata rabon"

Allah maji kiran bawansa kuwa ta samu danta ya ci sunan ya kasimu,
   Kasimu ya zama babban mutum yana zaune cikin rufin asirin  shi da matan shi biyu kowa tana kokuwar kyautata mishi,
kishi suke yi amma mai tsafta ba kyashi, ba hassada ba munafurci unaiza ce mai dan zafin ma tana ganin abinda ba dai dai ba zata amayar
Ita ko zubaidatu ta kanyi dariya ne kawai tayi mata bayani sai magana ta wuce"

Xuby kullum tana addu'a. Da Allah yasa ta dace da aure gashi ta zama gwana wajen shimfidar mijinta,
     Ko tsakar rana yazo nemanta takan bashi hadin kai tunda ta gane lakonsa
Abinka da yar boko ko bai neme ta ba zata lakato shi,
Ita kuma unaiza kunya,
Tana ganin hakan kamar zai ce bata da kunyaa!!!
Abin ba daga nan bane mata ( HALALIYAR KI CE KUMA MAZA NA SON HAKAN)
  

Masha Allah la kuwwata illa billah
الحمد لله الذي بنعمته تتم الصالحات
لكل بداية لها نهاية
Duk abinda yayi farko yana da karshe!!!
  
DARUSSA :

HAKURI IRIN NA INNA MAHAIFIYAR SU KASIMU DA YI MUSU ADDU'A SHI YA KAI SU GA SAMUN NASARA DA DAUKAKA
HAUSAWA SUKA CE " KA SO NAGA DUNIA TA KI SHI "
KA KI NAGA DUNIA TA SO SHI"
 
RIKON AMANA DA GASKIYA YA KAN KAI MUTUM ZUWA GA TUBALIN NASARA A RAYUWA

ABINDA KA SHUKA SHI KAKE GIRBA ( LAWIZA) MAMAN DADDY TA ZAMA MAI SA IDO GULMA TSUGUDIDI SHIGA HIDIMAR DA BA TA TABA
UWA UBA CIN AMANAR ZUMUNCI

DAUKAR KISHIA DA SAUKE YAFI KOMAI SAUKI DA SAMUN NUTSUWA A RAYUWA GA MISALIN MAMAN SALIMA DA UNAIZA.
 
HANGEN DALA, KAMAR YADDA MAMAN INTI TA SA GASA DA KARYA A RANTA ITA DOLE SAI TA YI ABINDA BA TA ISA YI BA,
KARSHE DAI ABINDA BATA SO NE YA AFKO AN AURO MATA WACCE TA FI KARFINTA

HASSADA TAKI CE MUSA YA SAMU DAUKAKA BELLO YA KWAMMACE YA ZAUNA A KAUYE DA ZAMA YANA GANIN DAN UWANSA YA CI GABA.

ALLAH YA DATAR DA MU YASA MU AMFANA.
CIKIN RUBUTUN NAN IDAN AKWAI KUSKURE ALLAH YA YAFE MIN.
NAGODE

TAKU A KULLUM

اختكم فى الاسلام
*_UMMUKULSUM BAPPAH AZARE*_
 
KU TA RA A SABON RUBUTU NA
 
*ZAMANTAKEWAR MU A YAU*

NAGODE

Comment