shafi na hamsin da takwas

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

5️⃣8️⃣

Indo na cikin daki a zaune ta ringa jiyowa kaurin hayaki yana tashi ta fito ta bi inda take jin kaurin sai ta lura a dakin zubaida ne,
Ta karisa har cikin falon don ta tabbatar ai kuwa a dakin ne;  zubaida take ta turara su habba mai hadin tafarnuwa da hulba da jan miski,
  Ta leka
" ki ce  ?
to sannu da aiki ta fita cikin sassarfa  ta nufi wajen unaiza da hanzarinta tai ta kwada mata  sallama To ki fito na fada miki kin karyatani har kina neman ki ci mun mutunci to fito ki ga zubaida hayake hayake take ta bangawa a gidan nan,
A hakan kike kokarin tura yaranki gidansu su shanye su da asiri da tsafi,
    Baki ji wari yana ta tashi ba,
     Wallahi zo muje ki gani???
   Yaya kasimu ya aurowa kanshi bala'i a masifar son kudin shi, da rana a tsaka ake hayake hayake
  Sai ganin kasimu tayi ya fito daga dakin unaiza a tsammaninta ya dade da ficewa wajen aiki tunda sha daya ake nema,

  Ta kideme ta hau kame kame ya.. ya... Ina... Kw...ina kwana????
   Ashe kana ciki??
  "  Ina nan indoo, zuciyar shi na azalzala sai ya boye damuwarshi,
Muje wurin zubaidan ashe yanzu har ta samu wurin da zata fara min banke banken hayaki a gidana,
Unaiza muje domin ki zama. Shaidaa,
   
Rashin hankali cutar mai rayi
Jikinta na rawa tai hanyar dakin zubaidan harda  hanzarintaa,
 
  Ita kuwa hankalinta a kwance
  Ta fito daga dakin
  Ta amsa musu sallama,
A can gefe kuwa ga burner hayaki na tashi.

"  Indo ce tazo mana da labari wai kina ta hayaki zaki mallake mu,
     Indo maimata mana bayaninki,
   Dama ina daki ne na jiyo kaurin nayi tsammanin ko abu ne yake konewa ashe  magani ne???
   
To maganin miye indo zayyane mana??

A'a mu ai bakon Al'amari ka zo har cikin gida kana irin wannan hayake hayaken,

  " To indo bude kunnuwanki kiji,

  Wannan maganin da hayaki da kike gani ni ne na kawo mata da hannuna kuma Alhamdulillah;
Ke wai ma ina ruwanki a ciki idan ma mallakar mun zata yi,?

   Naji kina zancen 'ya,'ya na to ahir din ki ba zaki zo ki tayar min da hankali yadda kika hana matan yaya Bilyaminu zaman lafiya ba,
Kun zama bakin ganga duk inda aka buga zaki,
   To ki shirya ya fito da kudin mota ya mika mata,
Mun gode da zumunci Allah ya saka da Alheri dama baba tun wancan satin ya min waya ya umurci ne da na baki kudin mota ki koma saboda gudun irin haka ashe ya fini gaskiya

   " Yaya don Allah kayi hakuri sharrin shaidan ne  yace " sharrin shaidan ne ko??
Wai miyasa mutanen dunia sai kun gama yin damuwarku sai kuce aikin shaidan ne?

  a'a ke gane indo matsayin ki daban a waje na haka zalika matsayinsu daban : ke jini na ce kanwata ce babu ruwan da zai wanke wannan zumuncin,
Su kuma na auro su ina sonsu, na rabo su da gatan su wato iyayensu Allah ya dora min nauyin kula dasu dawainiyya dasu, kinga kuwa suma ba abin walakantawa bane,
Wai don Allah na tambaye ki mana

" Mi yake sa kullum tsakin kannen miji da matan yayyensu basu da zaman lafiya ne kam?

     Sai sharrance sharrance idan kuka hadu da marrasa hankali ayi ta iye ana kai ruwa rana,
  To ina gargadinki ba nan bama ko matan yaya bilyaminu da kika mai dasu tamkar karnuka ki ka hana su zaman lafiya a tsakani ki kiyaye saboda kinsan dai dole ne mu yi aure mu zauna dasu ba zamu aure ku ba,
Don Allah bai halasta hakan ba kinga kuwa ya zama wajibi ku kau da idonku akan matayen mu ,

Kuma matayen mu abin girmamawa ne a gare ku,
Idan ma banda abinku da ire iren masu irin halayyarku ai banga abinda zaku sa matan yan uwanku a gaba ba,
ai kwa basu girma ko don domin yan uwan naku amma ina??
   kishi da rashin hankali yakan rufe muku idanu.
 
Unaiza tace " baban umaima da ka rabu da ita,  daga ni har zubaida da hankalin mu ba za mu bari su gurbata mana zaman mu ba,

  " A'a unaiza umurnin baba na bi idan ann kwana biyu ta zo muku ziyara ko idan munje.kwa gaisa.

Sun rakashi har kofar gida  kenan ya dawo unaiza kice wa musa ya sanar dasu zuwa yamman zamu je
Ke kuma zubaida ki tambaye habeeban  ko akwai wani abin Al'ada da zamu tafi dashi.

   " Yauwa baban umaima zamu asibiti dubo makociyar mu anjima,"

   Oh haka fah amma da kun bari sai na dawo na kai ku ,
   Ah haba kai da zaku tambayar aure ga dai zubaida ta kaimu idan yara sun tafi islamiyya kafin ku dawo
   " To ba matsala ya ciro dubu biyar ya mika wa unaiza to ga kudin mai sauran kuma ko sai kayan dubiyaa.
Allah ya tsare.

Suka Amsaa

" Ameen."


Abinda ya saka kuka wataran shi zai sa ka dariya,
Maman daddy ne zaune tana ta mamakin yadda aka ce jinin musa ake saka mata duk da cewa ance mata yazo lokacin tana bacci
Kaicho ! kaicho nah!! kaicho na !!!
babban daddy dunia kenan mutanen  dana tsana na wasa wai su ne farkon wadanda suka zo suka duba  ni;  ita wacce tai dalilin fadawa ta cikin wannan halin ko keyarta ban gani ba,
Don Allah baban daddy idan ka koma gida ka karba min number musa mana na mishi godia,
 
Wallahi baban daddy dunia ba komai bace wai ace Bello ne yake gudu na yau,
 
Ke maman daddy dama fah haka dunia take ba lalle bane wanda ya more ka ace shine zai kyautata maka ba,
Shiyasa ake son ka zauna da kowa lafiya saboda wata rana masoyinka zai rikida ya koma makiyi,
Haka zalika makiyin zai iya komawa masoyi to yaya za'ayi a lokacin??

Ka  Zauna da kowa lafiya

Butulci kuma ai abinda dan adam kenan yafi iyawa yo kar kisha mamaki ma zaiyi miki abinda yafi haka,

   Ubangiji da kanshi fa yace " innal insana lirabbihi lakanuddd"  ( lalle dan adam mai butulcewa ubangijinsa )
To inaga wani Bello da dama ba. Amincin gaskiya da gaskiya aka kulla ba,
Dama dole haka zata kasance,
Allah yasa mu dace ya bamu lafiya
    Ki yi godia wa ubangijin ki ma da ya baki damar gane kurakuranki hakan ma ni'ema ce idan bai so ba zai iya kashe ki da kukai hatsarin
  Allah ya yafe mu ...........

Shigowar maman hanifa ce ta katse shi

Hanifa na biye da ita da basket,
Suka gaisa tare da tambayar jiki

  " Alhamdulillah da sauki,
Kinga yau ma har anyi aikin,
Dazu su unaiza suka bar nan suma,

" Ehh mun gamu a bakin gate "

Allah sarki ai nagode muku da zumunci Allah ya saka da Alheri, nasan Albarkacin zumuncin makotaka kuka zo ba wai don Hali na ba,
  A haba maman daddy kar  ki damu ai ko kafiri ne idan makotaka ta hada ku idan ya shiga wani hali ai zaka ziyarce shi balle ke, musulma yar uwar mu,
Allah ya baki lafiya,

Maman inti kam aure ba fashi duk da yasan cewa dole sai an kai ruwa rana da ita,
  Sukai da bilkisu ma balle kishiya,
Kishiyar ma wacce tayi mata nisa da fintikau

  Ba laifi ya mata kayan uwargidancin amma taki karba karshe dai gidansu ya kai mata,
Amarya tazo cikin kasaita da Alfarma,
Abinda bata so kenan ace wata ta fita,

Ita kuwa Amarya sadeeya masters take dashi kuma ma'aikaciya ce tana da kudinta ga kuma kudin ubanta,

Ko dan girkin Amarcin nan ma bata mata ba;  taki ta basu ko ruwa,
Ita kuwa  Amarya tasa aka kawo mata mai aiki.
Daga gidansu

     
Imraan ya kamata kai hanzarin zuwa mu kai laure  asibiti abin kamar nakuda amma kuma cikin bai kai haihuwa ba ,

To gani a hanyaa in sha Allahu,
   Kai tsaye maternity suka nufah aka fara a'aunata
Aka dubata tabbas haihuwa ce amma bakwai ni ne,
Ga B.Pnta ya hau sosai

Aka nufi labour room da ita likitoci sun rufu a kanta kowa na gwada kwarewarsu don jinin yayi sama sosai suna tsoron shigar cutar taune taune,
    Likitan ne ya kira nurse
" yace ku kira min mijintaa inaga tunda jinin ya sauka ya kamata ayi booking ayi mata c section kawai,

   " Waye mijin  lauratu ???
    "  Gani nan "

" Bismillah ka shigo likita yana son ganinka,
   
Ba tare da bata lokaci ba imraan ya amince da ayiwa lauratu c.s din don a tseratar da ita da abinda yake cikinta,

       Haka ne maman salima  ina ganin ya kamata mu kira yan uwantan ,
  
Bari na kira Auntyn nata,
    Nan da Awa biyu suka ce zasu mata aikin suna bukatar jini,
Leda daya da za'a ajiye incase sunce tana da isash- shen jini kam,

    Bari naje a dauka,
Ke kuma ki shiga ki same ta
 
" Maman salima bakwai ni zan haifa ni kuma, kinga abinda nake fada miki ko?
Lauratu ki kwantar da hankalinki in sha Allahu lafiya zaki haihu na fada miki ki daina sa damuwa a ranki, yawan damuwar shi sai sa jinin yayi ta hawa,
    
     Suna zaune nurse ta zo take cewa ina kayan haihuwar nan da awa daya da rabi za'a shiga aikin,
  Laure ta zabura " aiki kuma??
A wa za'ayiwa aikin??
 
Maman salima ta kwantar da muryaa tace lah aikin ma ba komai bane yafi sauki yanzu ,saboda yanzu haka matan yan gayun nan da kansu suke booking ayi musu saboda su huta da zafin nakuda,.
   Nan da nan hankalinta ya tashi,
  Ta fara rikicewa tana nuna kanta, kanta zai fashe kafin a ankara harshe ya sarke,
  Ta fara tattauna shi,
   Nan da nan likitoci sukai kanta,
Aka maidata dakin yan taune taune,
 
  Sunfi awa a kanta amma ina basu ga alamar sauki ba,
Haka dai Allah yake ikon shi,
  Kowa da hanyar tafiyar shi,
Lauratu ta Amsa kiran ubangijinta
  
Yadda Aunty da maman salima

Yadda suka ga imraan ya fito jikin shi a sanyayye suka  san akwai matsalaa,
  
" Aunty sai hakuri lauratu tayi shahada"

Auntyn ta zabura ""
    Ban fahimci tayi shahada ba??
  
" Eh ta amsa kiran ubangijinta,

Inna lillahi wa inna ilaihir-rajiun,
 
Hankula sun tashi gaba daya
Musamman maman salima da ko yaushe idan suna tare   maganganunta kenan.
Allahu Akbar.

   Akai cuku cuku aka bada gawarta
   Wai gawa ma sai an biya  mata kudi.
  
Dare yayi kowa ya watse maman salima da imran suna tare
To kaga dunia fah da yanzu na biye munyi ta kishi irin na jahilci da tashin hankali da sai dai naji kunyaa, gashi ta tafi ta barmu

"" Hmmmmm ni salima ma nake ji wallahi sun shaku sosai,
  ai  Shiyasa nace ta tafi da su mama Allah yasa ta iya barci.........
   Kai Rayuww kenan
  
U.k.B

Comment