shafi na Ashirin da takwas

🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘🏘🏘
 
MATAN QUATERS


✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman


Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com


🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻


2️⃣8️⃣


HASBINALLAHU WA NIE'MAL WAKEEL!!!


Allah ka bani mafita!


Yanzu ni dai Alkawari ne tsakanina da  UNAIZA ba boye boye ba rufah rufah tsakanin mu,
Amma kuwa anya zan iya fada mata wannan kuwa?


Sai ya tuno girman Alkawari, da hukunci da Allah ya tanada wa mai saba Alkawari,


Yayi dogon ajiyar zuciya ya tura babur dinshi ya shiga gida,


Yar halak ya gani zaune tana ma KHALEEDA kitso  da yake rikitacciya ce bata son a taba mata kai sai ta kwanta bacci ake mata,


Ta yi zubur ta mike ta karbi abin hanun shi ,
Baban umaima yau baka dawo da wuri ba,.inata tunanin ko lafiya?
Har na daga waya da zummar zan kira ka sai naga ashe kati na ya kare,


Amma nai tunanin tunda oga na gari hala kuna tare,


Bari na dumama maka miya don gaskiya na dade da yinta yau ina gama sanwar rana. Na daura,


UNAIZA ki hakura da dumamen nan kar ki damu zanci haka,


Ah haba kar ka damu nasan bazaka ci abincin yadda kake so ba idan da sanyi haba minti nawa ne,
Kafin ya ankara har ta zari ashana ta fita madafi,


Jikin shi ya kara sanyi,


Duk abinda zatayi don ta faranta mishi rai  shi take yi,


Hmmmmm Ta mayar dani tamkar dan lili, ko dan sarki,


Yana ta sake sake a zuciyar shi,
Har ta kawo ta zuba ta kawo mishi ruwan wanke hannu,sai ta tuno bata kawo mishi yajin haihuwa ba, don shi mutum ne mai matukar son gargajiya,
A hanyarta ta komawa madafi ne, ta lura da sauye sauyen da QASEEM ya shigo dashi jikinta ya bata mijinta tattare yake da damuwa,
   amma bari dai yaci abinci, ta tambaye shi,


Hadiyar abincin yake amma zuciyar shi na tsaro mishi yadda zai tunkari UNAIZA kan wannan batun,
  don gaskiya bazai fara rufarta da wannan maganar ba,
   idan bai manta ba abinda ya jawo gagarumin matsala kenan gidan  yayan shi kasancewar ya boye wa  uwargidan  labarin  auren shiyasa har yanzu zaman lafiya ya gagara tana ganin anci amanarta ne,
  shiyasa " take cewa zaman daduru suke yi; -- *WA IYAZU BILLAH* ---
ko da yake bazai hada jahilcin matan yaya da UNAIZA ba domin yanayin  halin su sam ba daya ba ne, kuma Tarbiyar da UNAIZA ta samu kwatankwacin sa basu samu ba,
  shiyasa suke zuba jahilcin su da rashin hankalinsu idan suna hira fah kai kace MAGUZAWAN KANO ne tsabar Ashariya,
  
Baban umaima abincin dai ya kare,
   Naga kamar yau baka walwala inji dai lafiya ????


   Don yanayinka ya nuna akwai abinda ke damunka,
 


Ki dai bari,,


    Haka abin yake amma  dama ina da niyyar yanzu idan naci abinci zan sanar dake,
    
  To ubangiji Allah yasa dai lafiya,,


     Wato dama Alhaji  ne ya dora min wani nauyi mai wuyar dauka,


  Wanda anawa tunanin wuya na kamar bazai iya dauka ba,
   
  A haba baban umaima ban katse ka ba; yanzu har akwai abinda Alhaji zai nema a gare ka ka gagara mishi,  irin kauna da yarda da aminci da ya baka,
   Inaga gaskiya a shawarce ko abin yafi karfin ka,
    ya kamata kayi ta maza ka daure ka jajirce ka karbi wannan abin hannu bibbiyu, iya kacin sakayyar da zaka mishi kenan don baka da abinda zaka biya shi dashi,,


  " *RASHIN SANI YAFI DARE DUHI* "


Abinda ya fada kenan a zuciyar shi,


   Ya wani langwabe


" Maman umaima abin ya wuce yadda kike tsammani fah,
    
    Baban umaima na tabbata bazai saka a hanyar da ba dai dai ba ko hanyar da zata cutar da kai ba,
    
  Idon shi ya kura mata yayi ta maza yace "  Auren 'yar shi ZUBAIDA ya bani wai yasan tunda na rike mishi dukiya tsakani da Allah zan iya rike mishi ita Amana,      
    saboda tausayinta yake ji a halin mazan zamanin.......
       UNAIZA taji ya ambaci aure amma  gaskiya daga nan kwakwalwarta ta dauke DIF don  ma bata ji mi yake cigaba da fadi ba,


  Don batasan ma ta sau tsolon kalabar da take wa KHALEEDA ba,,
  Zuciyarta kamar zata tsage ta fito,
  Numfashin ta ya nemi ya dauke,
   AURE QASEEMU???
    Yadda QASEEMU yaga cikin kankanin lokaci ta fita hayyacinta sai ya cire tsammani  sassauci daga gareta
" *ASHE KOWACE GAUTA JA CE"*
  Ta saukar da numfashi a hankali da taimakon SALATIN ANNABI da yazo bakinta ta yi yakee, wanda hausawa suke cewa " *YAFI KUKA CIWO*
  Ta kakalo wani busashen murmushi ta shafa wuyan shi,


haba baban umaima wannnan wuyan bazai gaza daukar nauyin Mata hudu ba balle kuma karin daya,


Allah ya Tabbatar mana da Alheri,
   ya baka ikon yin Adalci,
   yasa ta zama abokiyar Ar-ziki-n m-u 
- da kyar ta iya karesa furucinta na karshi saboda rawar da muryar ta take yi ,
    Ta sungumi yarta cikin zafin nama tai daki bata iya  Ganin mi ye a gabanta hakan ya jan yo kan  KHALEEDA ya  kuskuri jikin kofar dakin; ta dan sa kuka,
     abinka da TSARGAGGE a sukwane yazo duba miya faru,


  Ta dan kakalo murmushi lah ba komai baban umaima,


Tayi maza ta rufo daki,
    Shi kuwa sa'kare yayi a bakin kofar zuciyar shi na bugawa,


  " ALLAH YA BANI DA SAUKI"
   Kwana sukai basuyi bacci ba kowa da abinda yake sakawa
  Shi QASEEMU fargaba ne, abinda kaaje ka zoo
    Ita kuma tunaninta biyu ne: itace zatai kishi da yar masu kudi tana 'yar gidan malam shehu,
   taso ace  ko  QASEEMU zai kara aure sai sun  warware.


********************


Yanzu dai maman INTI ta gama sadaukarwa ummi yar Benue ta cuceta ne,
  Domin  ta kira lambar wayar ta  yafi sau dari sai ace LINE BUSY,
  Mai gidanta yayi ta mata fadan ta rage rawar kai da yawan  hulda da mutane,,
   Bakin cikin maman inti ya karo ga asara ga rashin lafazi mai dadi daga bakin baban inti, balle tasa  ran zai rage mata zafi,


  Da sassafe ta nufi gidan Balkisu tana kuka ta mayar mata abinda ya faru,


Balki kamar zatai dariya idan ta tuno da STATUS din maman inti, to dai asara bata da dadi sai ta kintse,


   Haba makociyata kar ki damu da wannnan jarabawa ce kowa da yadda Allah zai jarabce shi;
     Yanzu tashi muje MA'AJIYATA ki debe zannuna da lesuka da kayan yara yadda kike so ki cigaba da daurawa a STATUS,.


    Amma kinsan bani da kudin da zan biya su yanzu kam, cewar maman intisar,


     Wallahi kyauta na baki ba rance ba kuma tsakanina dake ne kar ki yarda wani ma yaji Allah ya dafa miki,


Wallahi maman intisar bata taba jin kunya da dana sanin rashin mutunci da maganganun da ta ringa watsa su a dandalin sada zumunta na WHATSAPP Ba  sai yau, ta kwantar da murya tai ta godia,
    Maman inti cikin zuciyarta tace"  *NA YARDA *WUTSIYAR* *RAKUMI TAYI NESA DA KASA* "*


      Innan mustapha ko ta kasa ta tsare ta hana ASIYA sakat a cikin gidan nan;  duk da cewa ranar girkin maman hydar dinne amma haka tasa MARYAMA ta shirya musu dambun zogale da yasha man kuli da gyada, ala tilas inna  so  take ta  hukunta Asiyar na son zubar da cikin maryama da ta tunkari yi,
 
Kuma fah  ba komai zata aikata ba,  barazana ce kawai tana " *TAUNA TSAKUWA CE DON AYA TAJI TSORO"*
  Tunda Maryaman ta mata wa'azi ta hakura,
    Ita ko abin dunia duk ya ishe ta,
    saboda an hanata girkin ma balle ta samu hanyar da zata surfe mustyn,
Ga kuma kiran maman daddy da tace mata ta ga Maryama gidan  UNAIZA,


GEMU  da GEMU sun hadu an tsai da ranar auren LAURE da IMRAAN,
   Watan SALLAR MA'DEBI,


  Sun fara shirye shiryen su ba wani bidiar da zasu yi iyaka zai bata kudi tayi sayayya kayan lefenta,
Nan ta  bugawa Auntynta da take Abuja ta fada mata kan ta turo lambar ajiyarta ta banki zata turo mata kudin lefe,


  BUDURI wai duk wannan waina da ake toyawa maman salima bata sani ba,


  Tana zaune ranar tana kallon mutanen nata Laure ta shigo rike  da salima a hannunta,


Salima ta nufi uwar amma tsabar kallo ne a gabanta ko ta kulata, yarinyar na ta mata suruta amma ina!


  Karshe ma tsawa ta daka mata,
ta umurci laure da ta dauketa su koma daki don ta raba mata hankali biyu bata fahimtar komai,
     Aunty dama kayn ciye ciyenta ne suka  kare, kuma inaga.......
 
      Don Allah barni haka, idan babanta ya dawo kunyi maganar dama jibi ladi sai kuje ku saya, amma na roke  ko don Allah ku tafi dakinku,
   SAKARYA MARAR WAYO INJI ( BARMANI CHOGE)


     Shigarta ke da wuya ta kulle kofar, IMRAAN ya kirata don yanzu ko gidan bai fiye shigowa da wuri ba,
Ya kuwa tsara  maman salima kan cewa  karatu yake dauka a masallacin kasan su  idan yake sallah ,
kai namiji makiri ne, tsabar makirci har littafai ya sayo na musulunci,
  Zama yake a can nesa da gidan sun,
Su  sha hirar su a waya.
 


TOFAH  ko wace wainar za'a toya a gidan mal Qasimu na Unaiza da zubaida?


shin Unaiza zata canza ne, ko kuma zata rungumi kaddara??


   wani farin ciki Bello dasu maman daddy  zasu ji idan suka samu labarin auren Qasimu!!!
   
Maman IMAN
 

Comment