shafi na arbain da takwas

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣8️⃣

Isa sulaiman ne zaune gaban Alh sadau suna jiran isowar Lectureeern su shiru shiru,

Alh sadau ya gaji da shirunn ya kira shi a waya har yayi kusan  katsewa sannan ya dauka,

" Ranka ya dade don Allah amin afuwa mata tace bata ji dadi ba muka tai asibiti,

  Allah bata lafiya!
Amma ka tuntubi yaron kuwa?

  " Ehh to na kira mahaifin yaron ya nunamin sun fi son ya cigaba da karatun a nan danfodio, kuma sunce na kara mika godi'arsu a gareka;
Don har nace musu ma ya kamata su zo da kansu ma suyi  maka godia,
Yayi ta maganganu wanda in ba mutum yasan TA YAU  da HALIN YAU ba bazai gane ba,

   Beeba ta numfasa tace ikon Allah haka rayuwar mu ta koma
RASHIN GASKIYA
CIN AMANA
HAINCI
UWA UBA FUSKA BIYU
Marassa gaskiya sukan shiga rigar arxiki da mutunci su yita cin amana da ha'inci ,
wanda ba kowa ke gane wa ba sai mai tsananin wayo da basira saboda tsabar yadda suka iya  bad-da kama duniya takan dauka cewa su mutanen kirki ne na gari ne........
Alh sadau ya amsa da cewa" FUSKAR AKUYA CE DA FATAR KURA

  Aminu yace haka zamanin yazo, kuma ma ranka ya dade anfi yiwa masu kudi irin wannan abun ayi ta mishi dadin baki akan fuskar shi amma ta bayan shi kuwa ana cin amanar shi

Alh sadau ya juya wajen
Isa miko min takardunka,
Akwai passport a ciki?

  Ranka ya dade bani da   passport,

To hungo kaje ka dauka, amma dan dakata bari na kira kanina IMMIGRATION ne ya fada mana kalan backround din da suke amfani dashi,

   Bayan sun gaisa da tambayar iyali

   " Ina son kazo zuwa gobe da safe kafin ka wuce office kazo ka karbi fasfo ka nema mana VISA   sannan kuma wani irin backround kuke bukata??.

To sai kazo.

  Isa zuwa yamma nake son ka kawo min in sha Allahu nan da sati biyu nake son a gama shirye shirye, ka bar kasan,

Banji dadin yadda ka jefa rayuwarka cikin garari  ba,
kuma ina son naja maka kunne ka kiyaye,
Ka  zama mai rungumar kaddara a duk yanayin da ka tsinci kanka a ciki,
Ba hujja bace kace bacin rai ne ya maka jagoranci ya sauya maka rayuwa ba, ka kiyaye ka kiyaye jefa kanka ga halaka da sabawa ubangiji babu turban da zai kaika sai turban DA NA SANI DA NADAMA,

Ya juya kan Aminu kai kuma nagode bisa hallacin da kayi mini don hallaci ne wannan idan wani ne yadda rayuwa ta sauya da kai za'a hadu a gari ana yamuɗiɗi dani ,

Aminu ya nisa yace"
Alh bani daga cikin mutane  masu manta Alheri,

Nan nazo bani da kudin da zan zana WAEC ka taimaka mani baka tsaya anan ba sanda ka hada min da kudin JAMB ka cigaba da tallafa min har na kai ga cimma gaci
To,
Ta yaya zanji abu na   faru wa da kai nayi shiru?

ai sai inda karfina ya kare in sha Allahu,

Sukai mai  godia suka mike.

Bilkisu ce zaune tana ma wafeeya mita da korafi kanta ya dameta da ciwo ga rashin bacci idan gari ya waye kamar kanta zai tsince, su kuma lokacin zasu koma suyi ta barcin su,

   Wafeeya tai dariya tace  " LAISA BI-SAHAL KAUNIKIL UMMM,
( Ba. Sauke kasancewar ki uwaaa)
  Baba tai dariya tace "
WASA FARIN GIRKI"
ai haka iyaye sukai fama ku gode Allah ma da zamAni yazo muku da chanje chanje komai a saukake yake;
a zamanin da idan akayi aikin haihuwa akan kai sati biyu a asibiti koma fiye,
Yanzu fah?
Kwana uku  Ne,
sannan akan dauka muku masu reno, gasu taimakon injin wanki  ga pampers a zamanin da fah?
Kullun sai kayi wanki
Ku dai gode Allah,

   Wafeeya tace kinsan ciwon kan nan fa dole ne,
Saboda wannan Alluran da aka miki lokacin tiyata dole za ki sha fama da ciwon kai ciwon kafa ke harda baya ma,

Yau ni na banu,

Baba tace dai na fadin hakan ki ce Alhamdulillah

Mijin ya shigo ta hau zumɓure zumɓuren  baki wai ita sakaliya,

  Maman 'yan uku naga bakinki da magana,

  Baba ce ta tashi, ta basu wuri,

Wafeeya kam dirshan ta zauna diramar su tana bata dariya,

   Ta nuna TRIPLE ba sune suke hana ni bacci ba,

  Kawai sai hawaye
   Lahhhh.........

   Ya sa hannun shi ya share mata hawayen  ya rarrashinta ya kwantar mata da hankali,
Ya dauki yaran ya sumbace su yana musu huduba ku daina hana mamanku bacci ko, yan Albarka,,
   Ya ajiye su   yace mata ina bukatar Addu'arki yau zan fara shiga office,
Ya kwararo mishi addu'a sukai sallama ya tafi,

Wafeeya tace,
Aunty B ki gode Allah da kikai dacen masoyi ya damu da damuwarki,
da yawa mata sukan faɗa cikin ciwon damuwa wato ( DEPRESSION KO SCHIZOPHRENIA ) bayan haihuwa jijiyoyin kwakwalwarsu kan samu rauni, hormones dinsu yayi rauni shiyasa idan kin lura masu ciki suke yawan samun sauye sauye a halayyarsu kamar su CANJIN YANAYI ( MOOD CHANGES ) mata komai hakurin ta  takan xama mai faɗa, korafi saurin tunzura da sauransu,

Jijiya ce da ta taso tun daga kwakwalwa taa hadu da spinal cord take karkacewa, idan mace  ta haihu ta samu nutsuwa zata iya mike wa ta koma yadda take da,
amma idan aka samu akasin hakan ko tsananin zafin nakuda mai kamar kai zai buɗe to zai iya bada gudumawa ta  fada wancan tarkon,
To sai anyi ta fama da magunguna  irinsu ANTI DEPRESSANT don ya samu ya dai dai ta mata CENTRAL NERVOUS din ta da suka illata,
  Shiyasa idan son samu ne mace idan ta haihu a kyaleta ta samu isashen bacci, to amma naga hausawa kam abin ya banbanta maijegon bata ma da lokacin da zata huta saboda yan zuwa BARKATU, su hanata hutu su hanata barci gashi idan dare yayi yaro ya hanaka barci,

Haka ne kam wafeeya an ringa maka tururuwa kenan,
Allah yasa mudace.

Suna komawa gida tsabar kitifi indo suka tarar  tana zaune tana jiransu,

   Suka shigar da ita daki ta kwanta tai wa zubaida godia,
" sannu da kokari na hanaku bar barci"

Allah ya saka da Alheri,

Ameen ai yiwa kai ne tunda ciwo kam yau gare ka ne gobe ga wanin ka cewar zubaida
   Ta ajiye mata ledar magunguna ta juya kenan kasimu ya tsayar da ita,

Zo ki zauna ya kamata tun jiya ace na hadaku munyi magana kamar yadda Al'ada ta tanada
Maganganu ne game da zaman lafiya,. ,rabon kwana da sauransu,......zubaida ta katse shi ...... Ba wai katsalan dan zan maka ba, baka ganin tana bukatar hutuu a halin da take ciki?
   Eh tabbass haka ne, amma akwai zancen tafiya da zanyi a gobe insha Allahu zuwa Abuja domin na gana da Alh Barkindo,
  Domin ko dazu ya jaddada min jibi zai bar kasar,
Gashi kuma baki jin dadi,

   Haba baban umaima kar ka damu jiki kam da sauki ai, tunda kasan yanayin ciwon ba wanda za'ace sauki zai samu yanzu yanzu bane,

Ina ganin sai zubaida ta shirya ta bika ku kara mishi godia a madadin mu.

Owk to ba komai tunda ga su Adda fauxiyya da indo ai zasu taimaka sosai
Kafin kasimu ya cigaba da magana zubaida ta amshe


A haba baki da lafiyan za'a tafi a  barki,,kayi tafiyarka Allah ya kiyáye Allah ya tsare,

  Unaixa tace a'a karki damu ai gasu indo dasu Adda fauxian za suyi komai in sha Allahu,

a'a ba gardama zan muku ba, amma ba hakkin su bane a yanzu miye; amfanin mata biyun??

Har cikin zuciyarta zubaida taji dadi domin hakan ya nuna mata cewa zubaida mutum ce tasan ya kamata  (ba 'a yabon dan kuturu )ko ba komai unaiza taji dadi har  cikin rantaa,.
  Baban umaima dare yayi gashi baka kintsa kayan tafiyar ba,
Zubaida don Allah ki taimaken ga chan sashin kayan shi ki ɗiba mishi ,

  Ai kuwa ta mike ta tambaye shi kwana nawa ne tafiyar??
Yace baxai wuce kwana daya ba tunda shima jibi zai bar kasar,

Bari dai musa kala uku in caase
Ta rufe
Unaixa tace kin manta da kananan kaya janyo durowar chan suna ciki,

rerass a wanke a goge abin sha'awa a zuciyarta tace lalle matar nan tana da tsananin tsafta, kal kal gasu harda guga,.ta dauka ta ajiye akan gadon ta mike zata sashinta.
Kinga zubaida karisa ladan ki dauka  mana ki tafi dasu ki sanya mishi ga can brieff case dinshi ina ga kamar zai dauka ai ko??

To bari na gwada,
Indo kuwa tana jiyo su a falo bakin ciki kamar ta mutu,

Zubaida ta fito indon tabi bayanta don ita kam zubaida ma ta manta indo tana falon.
Suna shiga sassanta indo ta fara magana, gaskiya ina ganin ki kamar zaki yi wayo amma wannnan makirar ta yaudareku
Kinsan Allah lafiyarta kalau ba wani rashin lafiya so take kawai ta hanaki rawar gaban hantsi keda mijinki, wallahi salon makirci ne da yaudara,
Ga mijinki zai yi tafiya ki bishi amma kin ki saboda kina ganin kamar da gaske ne, ki kuji makircin kishia ba'a yarda da kishia,

Aunty indo ba'a taba karya da ciwo ba,
laulayi take yi kinga ai bai dace mu waatse mu barta ba,.... . 
Kut melesi laulayi???. Wato saboda ya kara aure shine take son ta buɗe ciki tai ta haihuwa wato kar ki zo ki fita 'ya'ya , tabɗi jam,!!!!!

Chan kuma dirama ake ta tafkawa da kasimu da unaiza,

  Ashe ban fada miki na baki ajiyata ba?????
Ta kuwa zunɓura baki ai gaskiya ni kam cire shi za'ayi don ban gama shan wahalar su yan biyu ba ma,

SubhAnallahi ,wa iyazu billahi mi yayi zafi haka unaiza?
        Allah ya baki kice baki so,
Kin fishi sanin lokacin da ya dace ne?
Ko ko ki ce mai tsarawa kanki rayuwar da kike so?
.. ina ganin kamar ubangijin da ya baki a wannan lokacin ya fiki sanin dai dai, don  Allah kar ki ɓatan rai, ko  goma zaki haifo inaso, ya saukar da sicket dinta kasa ya shafi marar  ta ya sunbata ikon Allah hallitar Allah gashi kamar ba komai a ciki, ya shafe  da  addu'a ya tofahh, Allah ya tsare min kai ko ke!!

Da ba don yana tsoron hakki ba da sai ya taba ta yadda ya ga mararta tsaf ba cunkoson gashi ga kamshi Almisk yana tashi don shi mutum. Ne mai son tsafta da kamshi,
  Ta lura da yanayin da ya shiga,.....
 
" Dubi agogo sha biyu  saura,,,na shiga  lokacin zubaida" cikin kewarta ya isa dakin zubaida dab da futowaar indo kenan
a'a indo idon ki biyu ??
Ehh yaya yanzu zanje na kwanta mu kwana lafiya, ya shige ya barta tana waiwaye  tana tsoron ko yaji hirarta...
    Ya lelleka bai ganta ba daga baya ne yaji kanshi shower gel na tashi ya tabbata wanka take yi, ya zauna a bakin gado ya jira fitowarta,
Daure take da bathrobe kalar peach ya amsheta kitson nan ya kwanta a kafadunta yare yare sunan wani ciwo,

  To gashi dama unaixa ta tsuma shi,
Da kyar ya daure
   "  miko min towel a cikin kayanki mana zanyi wanka,
 

bari zanyiwa unaiza magana ta raba kayana gashi biyu ta baki rabi ki sa min anan..ta miko mishi towel
" inaga ba sai ka mata magana ba.zata bayar kasan abinda yake sa uwargidaye rigima kenan ka barta kawai nayi imani da Allah tasan ya kamata zata raba da kanta.

  Ya shiga kewayen turarruka ne da sabulai na yan gayu ya bata lokaci yana kalle kallensu, ikon Allah,
Doguwar riga ta saka mai hula,
bata da rawan kan saka sexiest night gown din nan da amare suke sawa..
Sai ta burgeshi da bata nuna mishi tsantsar wayewar ta ba irin na matan birni da sukai karatu kuma suke da wayewa,

Tana zaune kan stool na dressing mirror kamshi iri da kala yana tashi,
Nan da nan ta fara jin ciwon kai da juwa na dibanta ,ta dangana hakan da gajiya da kuma bacci,
Zo ki kwanta mana naga kin fara rufe idoo,
Tai murmushi,
Yaya zata fara kwanciya da namiji,
   Gado daya,
Tana taso wa ta fara ganin duhu, sai luuuuuu...yayi ta maza ya tallafeta,

Ya kwantar da ita a hankali  wata zuciyar na son ya kyaleta amma yadda yake jin sha'awa na damunshi  kawai ba zai iya kyale taba  gashi tafiya zaiyi,
kawai ya fara saita tunanin shi akan hot network,
Wani irin masifafen barci ne yayi  awun gaba ya dauketaa,
yana ta shafa ta a hankali
da yake matashi ne majiyi karfi yaga bazai iya tsayawa a shafar ba yayi niyyar kutsawa amma mi,, babu alama, ya kara shafawa babu alamar komai subhanallaahi,
Da kyar ya miki ya nemo Wayar shi ya dan danna botton haske ya bayyana, ya haska subhanallahi ba alamar rami wurin a shafe.........
Ya haske fuskarta yaga bacci take  mai balai'in karfi...............
😡😡😡😡😡😡😡

U.k.B

Comment