shafi na hamsin da tara

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

  5️⃣9️⃣

_SEMI FINAL_

~INA YAN ZUBAIDA'S TEAM KU SHIRYA GA DARAJAR KU TA KARU KO DA YAKE AMARE KO YAUSHE DARAJARSU A DAUKAKE TAKE~

Masha Allahu zamu ce game da aiki da kasimu ya sa a gaba komai yana tafiya cikin nasara ma'aikatan shi sai son Barka suna gama aikin su na ranan zai biya su su tafi suna farin ciki suna hamdala,
  A satin nan in sha Allahu ake sa ran za'a bude BARKINDO SHOPPING MALL wanda anyi ittifaki duk girman sokoto babu shopping mall da ya kai shi kayatuwa da girma,
  Saboda masana ilimin zane da sanin gine gine  ( *Architect* da *Building engineer s* ) sun baje hazakar su kai abin mamakin ma  harda wajen ajiye mota a kasan  irin dai ginin shagunan  larabawa nan,
   Ba tare da bata lokaci ba ya gayyaci  kasimu Abuja daga nan suka wuce kasashen ketare: musamman china, jidda da sauran kasashen da suka shahara a kasuwanci don yin  sare saren kayyayakin da za'a zuba a shopping mall din,
  Sun dawo cikin nasara wani abin ikon Allah tare da jirgin cargon su suka iso,
    Sam kasimu a wannan satin bashi da nutsuwa yana Abuja zubaida ta kira shi  ta sanar da shi Amminta bata jin dadi tana son taje ta dubata,
    Ya yarje mata,
  
Isarta gida kenan Amminta taji kamshin su habbatus sauda,

  " Wai zubaida ji nake kamar kamshin ( *DIBBUL NABAWI )*

    " EHH Ammi ni ce nake yi "

Lafiya ?
Miya hada ki dasu?

Ko Al'adarsu ce haka kawai ana  amfani dasu?
 
Hmmmmm Ammi matsala ce fah,
  Subhanallahi matsala kuma maman baba,

Ehh ta kwashe lalurarta ta fada mata,
To Ammi shine aka hada min maganin nake yi kuma wani abin mamaki baban unaiza ne yake hado min kuma Alhamdulillah na daina mafarke mafarken nan.

  Ikon Allah lalle wannan yaron dan kirki ne,
Mune ya kamata mu fahimci hakan mu miki jinyaa amma ya daure yayi hakuri Allah ya saka da Alheri Allah ya hada kawunan ku gaba daya kuma itama unaizar ya kamata ayi mata godia zan sanar wa Abbanki ma insha Allahu ;
yanzu bazaki gane kanshi ba im ba gamawa sukai da Alh sulaiman ba,
   Kai zubaida gaskiya kinyi sa'a Abbanki ba karamin farin ciki kasimu ya sa shi ba na rike Amanar da yayi,
komai ya tafi yadda ake so,

Ammi ni kai na yana bani mamaki kinsan Allah idan wani ni ya samu wannan kwangilar sai yadda karfin shi  yakare amma ba sauyin komai ko a cikin gidan shi,
idan wani ne facaka zamuyi amma ko alama babu,
   Diba fridge akwai kaza kuwa dana dafa kwanaki yana fridge sai ki dauka muku keda unaizan,

"a'a bari na dauko kinsan unaizan na da ciki, ba damar sha,
To Ba damuwa Allah ya kaimu ta haihu,
      Kafin dai ta tafi sanda  Ammin nata ta bata abubuwan gyara don a bayanin da zubaidan tai mata ta fahimci har lokacin bata san miye auren bama,
  
Tabb  ba karamin namijin kokari sukai ba a  wannan zamanin har aka samu
  Irinn haka amma suka kasa fallasa kansu,
Alhamdulillah Allah yasa mu dace,
  
Zubaida fah tunda ta dawo ba lafiya, ciwon mara da kugu kuma dai ba lokacin ganin al'adarta bane amma dai irin ciwon da take ji kenan idan ta gama period,
  Ga kuma wani bakon lamari wato ji take tana son a taba ta

(  ita mace lokacin da ta gama Al'ada  wato ovulation days dinta lokacin da kwayayen ta take fafewa suke kyankyashe  wa to a dai dai lokacin ba abinda mace take so irin bukata, shawa'a zai na damunta idan tai sa'a abokin tarayya na kusa to sai a samu rabo)
 
Tai ta mika,
Allah da ya so ta yau a dakinta yake,
    Ta tashi ta kunna kira'a ta lallaba ta shiga wajen unaiza ta kai mata tsarabar gida da kuma kayan khaleeda da ta mantaa,
Ko da yake ba mantawa tayi ba cewa tai bazata dawo ba ita har goyonta Ammin take yi

sai akai mata dabara aka ce  taje ta gaida mamanta sai ta dawo washegari,
   Nan da nan tayi sakwara miyar egusi tayi lafiyayayyar kunun aya da ta sirka shi da gyada da dabino khaleed
  A gajiye ya dawo gidan khaleedtulus saboda akwai sakon kwamishinan masan'antu da inganta kasuwanci da  tattalin arziki bai samo ganin shi ba sai dab magariba.

Kamar kullum suka sha hira a dakin unaiza yau ko harda Baba musa ma don yaje ya karbo musu dinki  da za suyi anko dashi a wajen taron
Ka bawa Bello nashi ??
  Lah na bashi tun dazu amma gobe da sassafe zan je na karbo na khaleed kan ya mai kadan,

Kai babana tela ne ya maka tsiya kar kaji komai,
ku sani fah hijab zaku sanya kai har ma da nikabb

Anya am baban umaima har da nikab
   Ehh tabbas don bazan je a kalle man ku ba,
  Zubaida tace Al- lah y-yaa kai-mu,
    Ta rufen bakin da kyar hamma ya dameta,
Amarya lalle yau kam barchi ya dame ki naga sai hamma kike yi,
 
Wallahi haka dai nan nake jin gajiya da mika ga wani irin bacci da nake ji,
  Unaiza ta kalli kasimu tace mashi mu kwana lafiya ku tattara ku tafi, Amarya na jin bacci,

Karfe nawa ne kam yanzu ?

  Musa yace tara ta gauta nima bari na tafi mu kwana lafiya,
  
Yauwa don Allah unaiza miko min wayata ,
  Ta mika mishi ta tsaya tsuru tana kallon shi ,
  Ayi Angonci lafiya
Kawai sai hawaye zarrrrrr
  Tai maza ta tura kofa kar ya fuskanci yanayin da take ciki,
Amma ina???
Unaiza ki bude don Allah bude,
amma ina? tayi cikin dakinta cikin hanzari,
  
Ta barshi kikam a tsayi mi take nufi da ayi angonci lafiya?
Ko ya kirata a waya ne ya tambayeta,

Kuma miye yayi mata take kukaa???
  
Wayar shi ya dauko ya danna lambarta

" Don Allah ki buden kofa unaiza,
   Tana shesh-shekar kuka tace kayi hakuri na kwanta nikam,

" Shine kike kuka? Ki taimakan ki bude

" a'a Amarya tana jiranka kaje ka bata hakkinta......kit ta kashe wayar,

  Tana nufin zubaida ta samu lafiya kenan,
To fada mata tayi ko yaya??
  To bari naje na jarraba,
    Kamar kullum ya sameta tayi wanka har ta surka mishi nashi ruwan wasu humrori da ouds tai amfani dasu wanda Amminta ta bata dasu ouds din kuma zuwan kasimu jidda ya kawo musu ta shafa ta kawo rigar baccinta doguwar riga mai kauri ta saka,
  Har ya fito yace mata nifa yau a can dakin nake son na kwana,
  Kai baban umaima dakinn da ba'ka taba kwana ba,
Ehh ai naga kullum a gyare yake,
   Amma kiyi Alwala muyi nafila a dakin saboda mu kore shaidanun da suke kwana a dakin,"
    Ta ko bi umurnin shi sukai sallah yayi ta watso musu Addu'a,
Sannan suka kwanta
Kai Allah inaso na duba jijjiyoyin jikin kine kinsan ba yamma tana takura muku musamman ku da kuke da hasken nan

Ba yamma kuma noor ??? ( Kunji sanabe )
Mi ye Ba yamma kuma??
   
Ya kyalkyale da Dariya yace " hooooo dadina da yan birni kenan ba abinda kuka sani wai hausa ma da ta zama yarenku baku sani ba,
'Yan *N. GEN. Mi zasu fahimta rai ohoo
 
Idan aka ce maki ba yamma ana nufin cutar shawara dake mai da fatar mutum idon shi ya zama rowan dorawa ko kore kore wasu ma chan yankin Bauchi suna ce mata koriya,
 
Owk na gane ! Itace bata son mangyada ko?
    Ai kuwa ina da ita

  To buden nagani
Zuciyarta daya ta kwaye riga,
Shi kuma kamar gaske harda haskawa da hasken waya kamar gaske  masha Allah " a zuciyar shi yace komai nata madaidaita,
    Cikin dabara da hikima ya gama afkawa da ita,
Haka dai har ya kai gaci sai salatin Annabi kake ji yana ce mata Allah ya kara miki Baiwa, Allah ya kara miki daraja😉
   Haka dai da yake  Allah ya mata juriya,
  Ina gefe naga ya shiga makewayi yana dauro Alwala sau uku abin ba sauki,
Ya galabaitar da ita sosai ya gajiyar da ita sai ya zama da kyar ta iya kai kanta makewaye domin tai wanka tai sallah,
A daddafe raka'atul fajri ma bata samu damar yi ba jiri ciwon jiki duk ita daya,
   Kafin ya dawo ta kara nadewa a cikin Bargo,
Anya ba zazzabi ne yake son ya kamata ba,
  
Ya dawo maimakon ya ganta tana karatun kur' ani kamar yadda ta saba sai ya sameta a kwance cikin bargo lafiya kike " " NURATU
   NURATU ita kuma kunyar hada ido take  dashi yadda ta zage damtse tai ta maida martani,
  
Ya janye Bargon
  Ta rufe idanuntaa
Kunyata kike ji,
Ba Abin kunya bane,
Auren kenan,
Kowa da haka ta girmaa har ta haihu haka duk iyayen mu sukai har suka same mu,
Allah ya miki Albarka nagode sosai Allah ya biya ki ina son don Allah kullum ki ringa taya ni,
Sai ta kara rufe ido,
Yunwa nake ji bani ruwan tea na sha,
  
" Owk yi hakuri ashe kefa sabon shiga ce bari naje wurin yar uwarki ta min"

  Har ya mike sai ya tuna kamar fami zai yi wa unaiza wato ma ta tabbatar anyi,

Ya shiga da kanshi ya dafa ya kawo mata,
 
Wai bata jin yunwa,

  " To ki sha ko na sake.......
   Zubur ta mike  mikon

  Lah NURATU gwanda ki shirya saboda gaskiya Allah ya hallice ni ina son  wannan abinda mukayi jiyan sai kin 'daure damtsen ki sosai,

Unaiza ta ji su shiru take ta gane lalle komai ya wanzu, namiji kenan shi da yace da sassafe zai fita don ba zai ma jira su ba yace zubaida ce zata kai su,

Baba musa ya shirya yana ta tsammanin kiran yayan shi amma shiru,
   Ashe yana gama shan shayin ya jawo ta jikin shi  yayi mata filo da kirjin shi sai bacci mai wani irin dadi ashe haka aure yake lalle dole ne mata suyi kishi,
Duk a zuciyarta take ayyanuwa, har ya kwasheta,
Kiran A.A BAGUDO ne ya shigo mishi
Da kyar barcin ya sake shi ya dauka da girmamawa da mutuntawa kamar wanda zai gane cewa yau ne ya karbi budurcin yar shi
   Ka na ina ne?
Kai muke jira,

   Ina jikin yarka
Bana son rabuwa da jikinta,

Abinda zuciyarshi  ta raya mishi kenan.

"   Gani fitowa in sha Allahu,"
  A ina zan same ku?

    Chan hotel din da Barkindo ya sauka na ma kara so tun dazu,

Gudu gudu ya shiga wanka yana fitowa ya kira unaiza ko gaisawa basu yiba yace ta bada kayan shi a kawo mai,

  Xuciya bata da kashi unaiza tace "
   " yanzu har dadin dunia yasa ka manta gaisuwa da tambayar yaya muka kwana??
   Dadin dunia kuma unaiza??
Da yake zubaida na dayan dakin yace mata

" Harda dadin duniar da ya wuce naki uwargida sarautar mata maman umaima maman yan biyu ina fata kuma yanzu Allah ya dankaro mana yan uku asamu
Kasimu,
unaiza
da zubaida,
Bai san yaushe yayi zarbabiyar nan ba

  "  To Ameen ko kuma ita zubaidan ta samu mana yan ukun ba ko kuma nace ma ta samu ba"
tai maza ta kashe wayar,

    Ya ko shiryaa zubaida ta feshe shi da turare

" Anya kamshen nan baiyi yawa ba??
 
Yau fa zaka gamu da surkayenn ka kuma mutane ne masu son kamshi,
   Haka dai aka rabu da kyar.

Ta samu unaiza a kwance suka gaisa duk da unaizan tana dan basarwa bata son zubaidan ta fahimci zuciyarta ta dan motsa ba,
   Maman umaima na gama shirin,
   Ta dan basar to bari na dauko hijab dina
"Laah na manta bari na dauko niqab nima  na manta
dashi "
da sauri unaiza ta duba yadda take tafiya cikin hikima da sassarke sawu tace " wallahi anyi.😄

Kai kishi masifa ne!!!
  kuma ba maccen da bata da kishi  sai dai kawai ayi kokarin ana  dannewa  don ana  kishin wayayyu.

 
Maman Auwal sukai sallama da inno tace "         " inno ina rokon nima ki sa min Albarka kafin mu wuce,
  "  Allah ya muku Albarka gaba da yanku,

A'a inno ina son ki ce Allah ya min Albarka ai dama su kam kin saba musu Albarkan"

   " To ke idan banda abinki kina yin abin Albarkar ne da za'a miki Albarkan?

   " In sha Allahu zanyi yanzu nima  "

Allah yasa Allah ya shiryar dake ya miki Albarka kar ki koma ARKILLANKU ki gamu da shugabar ta ku ta kara lalata miki tunani ta gurbata ki yanzu dai kin ga ishara,
  Maryama tace "  kai inno ya isa haka mana,"

" Uwariyonki bai isan ba!
na gani a kasa kawai inji kare wai ana biki a gidansu,
   Suka ba wa mustapha wuri yayi sallama da ita.
   Maryama ta bude kofar baya zata shiga,
Maman Auwal tace a'a maryama koma  gaba mana,
   " a'a kar ki damu ki zauna  anan din maman Auwal,
Suka dawo cikin ARKILLA cikin kwanciyar hankali, da nutsuwa,
Auwal ya gyara gidan tsaf  yama kowa sannu da xuwa amma banda  maryama,
Har cikin ranta uwar taji wani iri har taji kunya

" Auwal ba ka ga Auntyn ku bane?
    Na ganta ba kice kika hana mu gaishe ta ba
To na fada ka gaisheta

   ( *Mu kula don Allah mata muna da wani hali wai idan kayi fada da kishiya ko makociya sai kasa 'ya'ya a daki kayi musu huduba, kar ka gaishe ta ko kar ka kulata,
Wallahi kan mu muke cuta kuma wata ran mu zamu ji kunya ba kadan ba, don haka a kiyaye
*    )

Abin gwanin sha'awa zaman su ikon Allah kenan gaskiya Allah ne *ÀLMUSAWWWIRUL UMUR* Mai cac-canza lamura  zaman su ya sauya ba abinda ya kara bawa maman Auwal tsoro irin ganin yadda maman daddy dole ta sa ta ta musulunta,
  Ta zama ta kwarai *WUYA* kenan mai sa a canza wai har wa'azi take musu su zauna lafiyaa.
  Wani hukuncin ubangiji in ba mutanen shago da Bello ya fada musu abinda yake faruwa ba ba wanda yasan sirrin nutsuwar maman daddyn,
Allah ya rufa mata asiri Allah kenan mai yin yadda yaso kai ta tsula tsiyarka lokaci daya sai Allah ya kama ka tsaff,
  To Allah dai yasa tuban gaske tayi.

  Bilkisu ce ke ta sharban kuka wurjan jan ita sai dai a zubar  da cikin dake jikinta shekara guda kenan yan uku  suke nema don basu cika dayan ba ma


Baba ce zaune take rarrashinta

" Haba mai gado naga shekara biyu yi warhaka da ya wuce neman haihuwwar kike yi,
Allah ya baki da ya tashi bakin ma ya baki irin wanda ba a kowa ake bayarwa ba,
 
To yanzu kuma ya baki ki ta da bori sai an zubar gaskiya kiji tsoron Allah,
Wafeeya ce zaune gabanta
          " ah toh fada mata kam Baba ace Allah ya miki kyauta kyautar ma ta dan mutum
Kiyi fatan Allah ya raba lafiya  kawai ni Allah ya sa ma 'yan Hudu ne,

Ba Ameen ba.
Ashe baban triple yana jinsu ya kari so

" Baba ki kyaleta kawai,
Zumbur baba ta mike,

    To ke yanzu baki son cikin kike guduwa wa yan uku ki zo taya ni hira da daddare??
    ai kuwa kinsan duk wanda ya sai rariya zatai mishi yoyo.
     " Haka zaka ce??
Eh haka nacen
Shikenan wallahi zan rama,
Zaka ga ne ba sai ka gannin bama a dakin nakan,
   Yayi ta mata dariyaa...
Ance miki addu'ar da nayi wasa ne??
   Sai kin min dozens..

Allah ya sauwakee........... Ta murguda mai baki..........

Maman nasreen

Comment