shafi na Ashirin da biyu

๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
ย 
MATAN QUATERS

โœ๐Ÿผโœ๐Ÿผโœ๐Ÿผโœ๐Ÿผ
ย  ย ย  Kulsum Bappah Azare
ย  ย  ย ย  Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป

ALHAMDULILLAHIL-LAZI BI NI'IMATIHI TATIMMUS-SALIHAT,

Allah ya nufa yau 2/10/2019 na gama jarabawar zangonย  farko,
Ina barar Addu'ar ku Allah yasa mun dace,

Sannan ina kara godiaย ย  ga masoyana wadandaย  suke ta bibiyar MATAN QUATER'S

Allah ya kara kauna

Jinjinar girmaย  ga REAL MAI DAMBU
Allah ya raba lafiya,

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…

ย  2โƒฃ2โƒฃ

Tana ajiye wayar,
Kishingida tayiย  akan sallaayarta, taki komawaย  gado ta kwanta,ย  saboda tasan baza'a dadi ba za'a faara kiraye kirayen sallar asuba,tana gudun makara.

Maryama abinda nake so dake shine kiย  dage da Addua'a akan wacce kike yi,

Saboda hankali na ya gagara nutsuwa da abokiyar zaman kin nan,
Wannan hadin kan da suke yi daย  matan unguwar nan marassa da'a da tarbiyya nan sam ban yarda dashi ba,

ย  '' to inna in sha Allah zan dage,

Allah ya shirye mu gaba daya,

'' Amin maryama
Allah ya raba ku lafiya,

Maryama bata iya amsawa a fili ba, can cikin zuciyarta ta amsa,
Saboda kunya da kuma tarbiyya da iyayenta suka ba,

Nan inna ta umurce ta da ta tashi taje ta bawa mustafha abin zaiย  karyaย  kumallo,

Ta dan tsaya tana wasa da yatsun hannayenta,

Inna tace mata'' ke tashi ban son shiririta nasan yanzu haka yana jiranki ne,
na gode da gaisuwa,

Ta mike,

Tana fita ta gamu da maman Auwal a tsakar gida,

Auntyna ina kwana?

ย  ย ย  Idan akwai abinda Maman Auwal ta wasa a rayuwarta bai wuceย  wannanย  gaisuwar reniย  daย  maryama take mata ba,

Ita tana ganin da gayya ma take mata harda cewa Auntynahย  mtwssssss,

Maman Auwal taso ta zuba mata rashin mutunciย  amma kasantuwar inna a gidan yasa ta hadiye.

UNAIZAย  ce ta fito rike da jakar baban umaima, shi kuma yana biye da ita a baya ,
Kana ganin su kasan ma'aurata ne da suke mutunta juna, basu da wata matsala da ta dame su,

Ta karanto mishi Addu'o'i ya hau babur din shi ya tafi,

Juyawarta ke da wuya ta amayo sautin maman daddy tana cewa''
Hajia maman umaima ta QASEEMU,
TATTABARA UWAR SOYAYYA,
To dai ki sani
Shure shure baya hana mutuwa sai dai idan lokaci bai zo ba,

ย  '' Allah ko maman daddy?

ย  Eh wannan rakiya da wani biyayya da kike nuna ma baban su umaima bashi zai hana ya kawo miki wata ba,

''Ayya maman daddy wazai ki kaari Allah ya bashi ikon kawowa ta kwarai,
ba tare da ta karaย  komai ba ta wuce cikin gida abinta,

ย  ย ย  Haka kika ce UNAIZA?

maman daddy ranta baiyi dadi ba tayi tsammanin idan ta bijiro mata ta nan zata tsaya ta saurare ta,
Ta samu damarย  bata mata rai da maganganun BELLO, amma sai ta ga akasin haka,
tayi kwafa,
SHEGIYA ZAMU HADU,

Shirye shiryen tafiyar su BILKI ya kankama domin zuwa dare jirginsuย  zai tashi,
Ta shiga gidan maman inti domin sauke hakkin musulunci,
Sallama,

Bayan sun gaisa ne BILKi take ce mata ashe an kawo kujeru?

Eh ai na shiga na sanar dake na samu baaki nan ranar,

''Owk haka kwarai ance min kin shiga,

Wai zaku umra ko?
Tare da ganin likita wai?

Wa yace miki umrah zani?

''Haka naji ance,

Ayya to kin bata ji,
ย 
maman inti ba kakkautawa ta zabura to ina zaku?

BILKI ta ramfo ta tai murmushi irin na masu ilimi tace''
ย  Kawai na gaji da nijeriar ce nake son fita nadan zazzaga na huta
Zamu fara yada zango a JORDANย  idan muka je wuraren tarihinsu sai mu wuce QATAR,
Idan mun gama ina son zuwa CHINA da AMSTERDAM,
daga nan kuma zamu juyo saudiyya muyi umrah,

Nan da nan fuskarta ta chanza,

Kai HASSADA BABBAR CUTA CE,
ย ย 
Maman inti kokari take taga ta boye maitarta amma ina!
Sanda balki ta dagota,

Chan sai maman inti tace ,

''Amma da dai saudiyar kuka fara zuwa kukai addua'a sannanย  kuย  ga likitan da zaifi saboda rashin haihuwa illaย  ce babbaย  ย  ba zaki ganeย  illar taba sai ranar da ya kara aure,
Ya auro mai haihuwa wallahi duk wannan rawar kai da yake yi mikiย  zai juya miki baya ya kama matar shi da yayanshi,

Oh haba!ย  Maman inti?

''Kwarai da gaske
Alkur'anin Allah,

To amma shi so ba anan yake ba,
ย 
Maman inti ta zabura ''waya fada miki,

Ke idan juya ce ke fah namiji a dole yake zaune dake,

Bari na fada miki baban inti da kanshi yake ce min,
'' wallahi da na kasance juya da tuni ya rabu dani gwanda ya zama talakan likis da ya zama bashi da magaji,
ย ย 
Ah maman inti akwai ayah a maganar ki
Wai shin soyayya kukayi ne ko auren hadin iyaye?

Saboda matukar kunyi soyayya bazai fada miki haka ba ko yaya ya same ki zai ci gaba da kaunar ki har karshen rayuwar ki,

Wayar BILKISU ce ta musu kutse,

ย ย  Sorry my soul mate, gani nan tahowa,
ย  Ta mike''
to kinga ya gaji da jira na biye miki munata surutu,

To zamu tafi,
A shafa man kan intisaar idan ta tashi,

Nan tai ta maza ta raka ta amma iya kacinta kofa,

Rashin sani yafi dare duhu da tasan maganar da balki zata chaba mata kenan da bataa fara ba,

ace
Wai kamar ita yadda baban inti yake son ta amma ace wai ba suyi soyayya ba,

Kai bashi ta dauka,sai ta gwada mata soyayya sukai har suka samu ribar soyayya.

A yadda ZUBAIDA take jin kanta kamar ta shirya ta nemi gidan bawan Allahn nan don ta fuskanci wani zazzafan kaunar shine ya shige ta,

Ji tayi ta matsu da taje taga iyalan shi,
wace mata CE tayi GAM DA KATAR da gwarzo ma'abocin nutsuwa daย ย  zati na halitta,ย  gashi Allah ya dora mata son TWINS din shi tun kafin ta gansu,
( hmmmnn bata san Al'amarin na Allah bane,
In dai zaka kaunace mutum tsakani da Allah kuma soyayyar ta gaskiya ce da asali wacce ba'a gina ta akan wani abu ba,dole taso yayan shi da iyalan shi,)

Mama ina son naje naga yan biyun nan wallahi haka kawai nake jin son su a zuciyata,

ย  ย  Hajiya ta kare mata kallo tace '' ai haka ne SO GAMON JINI NE,
amma ki bari sai kin je kin musu sayayya tukunna,

To ai hajiya ban san shekarar su nawa bane?
.
Eh

Bari na tuno lokacin da Alhaji yake cemin matar staff dinshi ta haifi yan biyu,
Inaga kamar zasu kai wata goma zuwa sha daya,

Haba ashe yara ne ma hajiya kai sun fi sha'a wa wallahi,
Ai da maman su zata yarda ta bani su na taho dasu gidan nan, hajiya inaย  goyon su ina musu wasa, na karbi kudi a wurin Abba na sai musu kayan wasa,

Au haba, saboda uwarsu bata da hankali ko?

Ai zan tambaye ta hajia,ย  ke bani son shiri rita,

Miko man wayan nan naย  kira babaan ki,
ย  Nan ta tuna hirarsu da baban nata, tasan halin shi bazai sanar wa hajiya sirrinsu ba, domin tassan Hajiya zata iya cewa ''daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki,

ย  Madafi ta nufa domin daura abinci, hajiya bata yarda ta barta barinta sakaka ba,
Dole ita take abinci
Tunda ta gama service ,
hajiya tasa aka sallami mai abinci,
Ba mitar da Alhaji bai yiba amma hajiya ta dage tace ya barta ba'a san inda za tai aure ba,

Kuma Alhamdulillah don ZUBAIDA ba girkin da bata iya ba kama daga na zamani har zuwa na gargajiya.

Abin mamaki QASEEM ya rasa mi yake mishi dadi a rayuwar shi,
Shidai yasan lafiyarย  shi kalau,
Amma akwai abinda yake damun zuciyar shi,
Saiย  ya tuno idanuwan ZUBAIDA,
nan da dan kuma sai ya kau da ita a zuciyar shi,domin yasan wane shi,
Mi yake dashi,
da zuciyar shi takeย ย  bijiro mishi da wannan Al'amari,
A rayuwarย  shi baice zai zauna da mace daya ba,
saboda illarย  da ke cikin zama da mace daya,
Amma yasan ba yanzu ba,
Sai ya kama kasa,
Yafi karfin gidan da zai zauna,
Ya samawa yayan shi makaranta,da zasu samu ilimi,
Ya kyautatawa UNAIZAR shi,
Nan ya hau tuno irin kyawawan halaye irin na UNAIZA Anya zan iya mata KISHIYA??????
ย  ย 
Ayi hakuri da wannan

yar mutan AZARE
KULSUUM BAPPAH,๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜

Comment