shafi na sha shida

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ πŸ‘ŒπŸ»

1⃣6⃣

Hmmmm yanzu Aunty ba don kin gani ba da shikenan ya cuce ni na rasa ko?

Baka da hakin shi shiyasa Allah ya bayyana maka ba tare da ansha wahala ba
,
Baba Musa
Ba don na ga idon ka ba a zamanin nan da wuya a samu matashi mai hakuri da hangen nesa uwa uba biyayya wa na gaba da shi irinka,

To duk wanda ya hada wadan nan abubuwa kuwa karyar wani bawa ya cutar dashi,
Sai dai kuma idan jarabawa ce daga ubangiji,

Baba musa

Na'am maman umaima'

da ace zamu na kiyaye hakkokin Allah yadda yace mu zauna da kowa zuciya daya yadda Allah ya umurta,
makota mu basu hakkinsu,abokan zama da Allah ya hada mu zauna dasu zuciya daya, da abin zai mana sauki,

Uhmmmm haka ne Aunty,

Wallahi ina mamakin mutane Aunty,

a rayuwa miye ribar ka cutar da mutum ne bare dan uwanka,
wanda duk duniyan nan ba yashi kusanci,

Baba musa ka gode wa Allah da har aka fara maka hassadar,
Kasan hassada kuwa?

Wallahi mai hassada da yasan yadda hassada take daukaka wanda ake mishi hassada to da wa kanshi zaiyi,

Saboda ya samu ya ci gaba shima ,

Tashi mu bar wurin kafin su dawo, ka gyara wajen sosai kar ma ya gane,

To,

Maza maza musa ya gyara wurin ya wanke hannun shi ya dankawa maman umaima yace gashi ajiyi a wurin ki gobe insha Allahu zan wuce dashi,

Ah to shiyasa fa nace wa yayanka ya ajiyi a dakin shi ya kasa ganewa,

Eh toh Aunty ai bazai gane ba kinsan gani yake kamar duk daya ne bai san cewa yan ubanci yake son yana nunawa ba,

Hmmm baba musa na rasa mi umaima ta mishi?

Musa yace ''
Wallahi ba abin da ta mishi Aunty''

Wai baki san idan ana son a kuntatawa uwa sai a taba danta ba,

UNAIZA tace ''
To ai yayi a banza tunda a nawa tunanin inaga umaima ai yar shi ce halak malak,

Wauta ce ke damun shi ai Aunty da kuma zugar mahaifiyar shi,

Wallahi ko a jikina domin a kanshi yake yi,

Kuma Aunty naji dadi da baki sanar wa yaya kasimu abinda yake yi,
Kinsan yaya bai iya fushi ba idan an tabo shi,

Haba baba musa sai kace wata yarinya,
Abinda baka sani bane santsin takalmin shi zai kadashi da ganshi,
Ai banga ribar hada dan uwa da dan uwa ba ,

A JURI ZUWA RAFI NA TABBATA WATARANA TULUN ZAI FASHE,

Tabbas maman umaima,

AI IDAN KERE NA YAWO ZABO NA YAWO ZA'A HADE''

Sosai ma inji musa

Allah ya rufa asiri,

Amma kasan indai yamin rashin kunya bazan kyale shiba,
wannan ma saboda yar shi ce shiyasa bana tanka mishi,

Ka ga kamar ana kwankwasa kofa sun dawo,

Bara na duba na gani,

a'a lado kaini?

eh Aunty ni ne,
Ina yini?
Lafiya,

dama maman hanifa ce ta aiko ni wai ga foam nan a cika ta sayo musu wa hanifa da umaima ne,

Allah sarki Allah kenan mai yin yadda yaso,

Baba musa karva ka gani,

Su kai ta godia suka sallami lado tare da bashi tukwici,
yaki karba akai akai ya karba yaki, sai robar zobo aka dauko mishi mai sanyi sannan yasa hannu ya karba,

Ka mata godia insha Allahu idan baban ya dawo zan bashi kuma zan shigo godia.

Maman intisar anyi arba'ein har an gwangwaje anfara shiga gidan makota kamar yadda aka saba,

Suna zaune da Bilkisu makociyarta sai ga mijin bilkin ya shigo da DISPENSER sabuwa dal a leda,

Suka gaisa bilki ta wuce daki wurin miji ta barta a zaune da dai taga zaman yayi yawa ne ta tafi gidanta,

Batare da bata lokaci ba ta kira maigidanta a waya domin Bazata iya jira ya dawo ba ma,

Baban inti,

na'am yaya akayi ne maman inti?

Kalau kawai so nake ka saya mana DISPENSER,

DISPENSER kuma?

a zuciyar shi yace yauwa abin yazo kenan,
Mi zakiyi da DISPENSER ke kuwa bayan ga fridge nan?

Kawai dai bana son rainin hankali ne,
yanzu wannan makarya ciyar balkisu ta shigo wai na kawo mata ruwa zata sha,

Na kawo pure water wai a'a bata yadda da nagartan pure watern ba dama ruwan dispenser ne tafi yadda da ingancinshi ko ruwan gora,

Kasan ni kuma na washi rainin hankali nan da nan sai raina ya baci zata nuna min DISPENSER itama da bata ajiye kowa ba mijinta yake mata balli ni da babu abinda ka rage mu daahi nida yara':

Ta gama mishi dadin baki kanshi ya huru,
To ki bari idan na dawo ko anjima ne sai muje mu sayo tare ko?

Sai ki zabi camfanin da kike so,

Yaauwa nawan haka za'ayi nagode sai ka dawo.

Baban umaima ne suka dawo,

Musa Unaiza ya na ga. Bakin ku a washe?

UNAIZA tace ''
Ba dole ba baban
umaima ''

Baba musa kawo mai takardar makarantar,

To,

Ya mika mishi cikin ladabi da rusunawa, QASEEMU har cikin zuciyar shi yana jin dadin yadda kanin nashi yake girma mashi,

Yasa hannu ya amsa,
Eyyeh musa yaushe ka sayo mata foam?

yanzu muke maganar da bello fah yake cewa a bari sai ta dan kara yanzu kam ai asarar kudi za'ayi,

Musa da UNaiza suka hada ido,

Yaya ba ni na saya ba,
Maman hanifa ce ta sayo musu ita da yarta.

Ayya matar ELFAH kamar tasan abinda yake zuciyata kenan,
Allah ya saka mata da Alheri

Anjima ki shiga kiyi mata godia sai kuma kiji yaya yanayin kudin makarantar yake ?

Insha Allah,

bari wuri yayi sanyi zan shiga na mata godia kuma naji. A ina makarantar take,

La'asariyya tayi maman umaima ta shiga gidan UBAIDA,

sukai gaisuwan mutunci domin a haife ta girme mata saboda dai ita tayi karatu ne shiyasa ba'ayi auren da wuri ba,

Kawai sai naga lado da foam din makaranta mun gode Allah ya kara zumunci

''Amin''

Babansu ma yace ayi miki godia

'' Lah haba ba komai ai 'da kam na kowa ne''

Haka ne amma duk da haka sai wanda aka sanyewa ai,

Babansu ma yace a tambayo makarantar a ina take kuma yaya ne sha'anin biyan kudin?

''Eh sai jibi za'a kaisu a musu interview ''

To Allah ya kaimu,
Bari na tashi nabar su khalid a gida kar ya dame su da kuka

Ta rako ta har kofar gida sukai sallama
Kyam akan idon maman daddy sai binsu take da kallo a zuciyarta tana cewa wadannan matan sunki rabuwa amma zan yi maganinsu yan iska kawai kodaddu kawai

Maman intisar ne agurguje ta shiga gidan bilkisu

Assalamu Alaikum,

''Wa'alaikumus salam''

Maman inti ban san lokacin da kika tafi ba dazu,

Eh ba kin manta dani ba anbi oga ciki,

Sukai dariya,

Ni DISPENSERn take wace product ne?
zamu je saye ne da baban intisar,

Samsung ce

Owk to sai mun dawo,

Ta fita Bilki tace Allah ya tsare!
ta bita da kallo iska na wahal da mai kayan kara.

Auwal kaje dakin Auntynku kace mata tazo ta same mu a falo da babanku,
To mama ba kince kar mu yadda muce mata Aunty ba zaki fasa mana bakin mu,

Ta dan kwaleshi da kenan,

Baban Auwal yana ji yayi dariya
Yace mata

'' miyasa zaki dan kwaleshi ba huduba kika mishi ba,

To ai yanzu nace yace din don Allah a wuce wurin,

To an wuce,

Maryama ce ta shigo da kyar

Nan da nan maman Auwal ta ce lafiya na ganki haka ko baki jin dadi ne?

Juwa ce take damuna kawai

Mustapha yace tun yaushe ne?

Wallahi dazu na fara ji,

baban Auwal ya kamata akaita Asibiti fah,

Lah ba sai mun je Asibiti ba ma,

zan daina ji kar ki damu ,

Gani ance kana kirana na

Eh samu wuri ki zauna magana zamuyi gaba daya,

Owk to,

Ya musu nasiha mai ratsa zuciya tare da ba wa juna hakuri,
Aka yafi juna da zummar komai ya wuce,

da kyar maryama ta koma daki da yake girkin Maman Auwal ne daki suka wuce,

Kamar gaske washe gari aka shiga har daki aka dubo maryama tare da mata sannu,

Kinki zuwa asibiti,

ba naki bane dama ni idan zafi yazo nakan fuskanci hakan,

ayya amma da kin daure ai anje asibiti zama a gidan ba dadi sam
Cewar maman Auwal

haka ne kam

Maman Auwal tace ''bari to na shaida mishi idan yaso sai na raka ki akwai clinic anan ba nisa

Ta wani fita tana rawar kai

Maryama ta kare mata kallo tas tayi dariya a zuciyarta tace hmmmmm
Ni zaki yiwa shunku

Ta murmusa kawai

Ba'a jima ba sai ga baban Auwal sun shigo tare da maman Auwal ki tashi ki shirya zan sauke ku a clinic zan wuce wurin aiki,.
Ba tayi musu ba suka tafi,

Sun samu mutane sosai A wurin layi ya kusa iso wa kansu kenan maman daddy ta kira ta ta mike ta koma gefe,

Shegiya ashe zaki iya kwantar da hankalinki haka?

Naga kun wuce da matsiya ciyar nan a mota ynzu

Bar shegiya wai jiri take ji tun jiya shine nace muje asibiti
Mutumin naki sai falli yake yi yana tsammanin har cikin zuciya ne abin,

Ko dai ciki tayi ne?

Haba ciki?

Cikin wasane aka ce miki?

Allah kuwa maman Auwal

Ke don
Allah bari batun nan koda yake kinsan wannan mutuniyar tace tayi musu farraku na har abada
Idan sun gaji da hakurin haka zasu rabu,

Kai kefa sharrinki nada yawa maman daddy,

Bari kawai ba ayi min ba amma don ubanta ko yau tazo zata san wa ta aura balle ma Allah ya sauwaka nida kishiya hala sai a qiyama idan anayi,

Yanzu ina kika barta?

Tana layi,

Ta juya sai taga bata nan har ta shiga bari na bita ayi komai a idona

Attandance ce ta hana ta shiga

''ki dakata mana sai wacce take ciki ta fito tukun,

Eh tafiyar mu daya ne rako ta nayi ai

Ta kare mata kallo itan karamar yarinya ce da sai kin bita wurin likita?

Dole maman Auwal ta koma ta zauna ba don taso ba

Yaushe kika fara jin jirin?

Nayi kusan sati ina ji amma kadan kadan jiyan ne naji yamin worse

owk kina da B.P ne?
likitan ya tambayeta,

a'a bani dashi
Amma gaskiya na taba yin low sau daya lokacin ina da ciki,

Owk to yanzu ma kodai cikin ne?

gaskiya ina jin yanayin kam kamar hakan,

Miko hannunki na auna miki B.P nagani to

Eh ya dan yi low kam amma yanzu dauki wancan kwanon silver ki shiga kiyi fitsari da kaina zan gwada,
Tayi duk abinda
yasata

gwajin farko ya nuna ciki
Ya umurceta da shan O.R.S da yawan shan markaddadiyar kankana da cucumber domin sune zasu sa jinin ya haura kuma tana kara gishiri a cikin abincinta domin saukar jini bashi da wani magani wanda ya wuce wadan nan din.

Ta mishi godia ta fita

Ta ga maman Auwal a zaune ta danyi mata murmushi''
muje nagama

Mi aka ce miki?

Hawan jini ne suka ce,

Kai haba mi zai sa ki hawan jini maryama ?

Nima dai Haka nace ma likita

Suna isa gida ko gidan bata shiga ba ta wuce wurin maman daddy

''To Albishir shegiyar hawan jini ke damunta ashe,

Maman daddy tana kwance sanda ta tashi ta zauna,

Eyyeh

Wallahi kuwa

Maman daddy tace'' kadan ta gani mu wasa ne suka tafa
nan suka rankaya sukai gidan maman hydar an je tsegun ta mata Maryama ta gamu da hawan jini saboda aikin malama ya fara aiki tsabar jaraba ta kasa jurewa.

Ta'aliki
Zaba
Watsa

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

Comment