shafi na arbain da daya

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣1️⃣

Hasbunallahu wa ni'emal wakeel!
Wa lahaula wala kuwwata illa billahil Aliyuul azeem,
Abinda Alhaji yake ta maimaitawa kenan,

   Ya kasa tsaye ya kasa zaune, ya ci gaba da ambaton INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR-RAJIUN,
Ya fita kenan da niyyar zuwa asibiti  sai yaji an  fara kiran sallar magariba,....

Da ba don kar Ya rasa sallah ba da asibiti ya nufa,amma kasancewar ba halin shi bane rashin yin sallah a jam'ei ba, ya  shiga masallacin kofar gidan shi,
Bayan sun sallame  sallan ne  ya ke cewa liman "" a sa mu a addua,"

Sun sha mamaki domin kowa yasan Alhaji sai anyi sallar isha yake shiga gida.

Bai tsaya a ko ina ba sai H.M.C,
ya sameta tana kuka akan sallaya ,
Haba hauwa'u yanzu kukan magani ne?
Yaya abin ya kasance?
A dai dai ina ne kuma?

  Da kyar ta kwashe abinda ya faru ta fada mishi ,
Yace masu GARKUWA DA MUTANE ne tabbass,
YA HAYYU YA KAYYUM  BI RAHMATIKA ASTAKISUU ASLIHLI SHA'ANI KULLUHU LA ILAHA ILLA ANTA!!
likitar ce  ta shigo ta  karisa mata Alluran,
Alhaji  ya ce  " ya akai kika kawo kanki asibiti?
Ta nuna mishi  wacce ta kawo ta wannan  ce, kuma maman ta ce likitan nan"
Ya musu godia,

Ya kama hannunta suka nufi police station don su bada report,
An gama dauka report suka dunguma sai A.A SOKOTO,
Suna sa ran Abin zai zo da sauki tunda akwai na'urar  C.C.T.V by camera da take leki a mashigar  kuma komai ya faru tana nadewa,
DETECTIVE MU'AZU  ya kwantar musu da hankali bayan sun gama ganawa da ENGINEER mai kula sashen Camerar.
Ya mika mishi kundin ajiye ajiye wato ( FLASH )
Ya tura mishi komai tas rangadadass

Dare yayi Alhaji kuyi hakuri ku tafi  gida in sha Allahu komai zai zo da sauki"
Duk da sun rufe fuskar su da MASK  amma gobe in sha Allahu zamu tafi V.I.O'S zasu binciko mana mammalakin motar,
Yanzu gida zamu tafi kenan ?
Mu barta a hannunsu,
Kawai ta fashe da  kuka
 
Hauwa yaya zamuyi ?,
Ina muka san zamu fara neman ta,
Adddu'ace mafita kawai,
zata dauki wayarta ta kira yan uwanta ashe jakar ma sukutum ta manta a asibiti,
Wayar shi tana aljihu yaji karar ta
Ya juya ya kalleta "ke ce fah kike kira na",
Na manta Wayar a asibiti,

  Assalamu Alaikum ,
Ey yanzu take fadamin,
Ya musu  kwatancen gidan,

  Basu sha wuya ba suka gano gidan,

ya tara ma'aikatan gidan da limamin yana musu bayanin abinda ya faru da Tilon 'yar shi Zubaida,
Wayar shi ce tai kara yana dubawa yaga lambar haj hauwa da alama sun iso kenan,
Ya umurci mai gadi da ya bude musu gate motoci biyu ne suka shigo,
Yaa salam sai lokacin ya farga bai ga motar ta ba,
Suka shigo harda maigidan su,
   Ah ahaaa Alhaji (Bagudo ) dama 'yar kace
Ikon Allah ai ni mai dakina ce take min bayani marar lafiya da Habeeba ta kai mata ita, kuma aka manta motar
Subhanallahi!!! Allah ya kubutar da ita,Allah yasa tana hannu na gari,
Ya ce " anyi report ne ??
" Eh mun je POlICE STATION "
bari na kira kanina S.S ne dan sandan farin kayaa,
Ya mishi baayanin dole sai sun je C.I.D OFFICE
Kai tsaye ANTI TERRORIST S2AURD suka nufa,bangaren manyan laifuffuka da kasa ta haramta
Sashin KIDNAP,
Bayan daukar bayanan ne suka koma gida inda suka iske DETECTIVE SADEEK TAHEER WURNO ya iso,
Matan suka haura sama don yin sallah
Hajia da kyar ta karisa dasu sama dakinta,
ta nuna musu make wayi suka shiga sukai sallah,
Hotunanta ne kaca kaca a kewaye a gidan,

Haj mairo tace ""  ina sauran yaran  ne,
Nan ne ta samu ta fashe da kuka,
  ta musu isharaan ita daya ce ai ,
Habeeba tace wayyo mommy,
Suka rungumeta suka rarrasheta sosai,
Da yake habeeba sociology ta karanta,
Yanzu haka a USMAN DAN FODIO UNIVERSITY TEACHING HOSPITAL take aiki sashen kwakwalwa wato ( PHSYCHIATRY WARD) tana THERAPHY musamman wa masu fama da cutar damuwa DEPRESSION har hayarta ake yi gidajen masu kudin nan taje ta debe musu kewa tana sa su nishadi da dai dabarbaru,

Aka kirasu DETECTIVE SADEEK TAHEER WURNO ya na son ganin su,
  baki ne kakkarfa .

A nutse yake mata tambayoyi ,

Dama tun muna mota take cewa kamar tai mantuwa sai daga baaya take cewa ta manta batai azkar din maraice ba,
,Yauwa muna cikin tafiya take nuna min wata mota wai kaman suna tsere damu;
Ni kuma ban lura na juya na gansu bama,; nace mäta wani tsere sai kace yan wasan daukar amarya,kedai hankalinki yake wurin,,

  Zaki iya tuna a dai dai ina ne ta  fada miki,??

  Ehh toh a MABÉRA ne kan hanyar SHUNI dai dai CHICKEN REPUBLIC din nan,
amma akwai wanda yasan da fitar ku ne?
" Kai bana tsammani,"

kuma baku da abokan hamayya ko fada ko?

Alhaji ya karba yace "kai mi ya hada mu da 'yan hamayya ni ba dan siyasa ba,
Kuma bata da wani abokin fada ?
" Ban yi tsammani ba saboda ita ko tarkacen kawayen nan ma bata dashi "

Wayarta fah?
,
Yana hannunta amma mun kira a kashe,
Owk yaya muamalar ta da samari fah; ina nufin tana tara irin tarkacen samarin nan,yan sharholiya,?

Alhaji bai ji dadin tambayarba,
" bana tsammanin mun yi mata wannan tarbiyan da zata tara tarkacen nan kai hasalima bikinta sauran sati biyu ne ma,
Alhaji maude baban habeeba yace ya salaaam!!!!
   Dtct, S.T WURNO yace yanzu ina mijin? Yasan da lamarin?

" Bai sani ba dazu dab magariba abin ya faru,
" To ai da kun  tuntube shi ko suna tare ;baku ganin zasu iya yin hakan saboda su kebe ko baza su iya hakuri lokacin ya.........
Alh maude yace haba Sadeek gyara maganar nan mana,
Kamar wasu kabilu,
Kana ganin 'ya'yan  hausa fulani  zasuyi hakan?
  Kuyi hakuri yana yin aikin kenan
Ya kamata a kira aji daga gare shi,

Haj Hauwa tace " gaskiya bazai yi wannan ba,
Haj mairo tace " yana da kyau a kira shin ko ya san wani abun ko da karin haske ne   zai mana,

   Kasimu kuwa yana chan wurin  baban daddy batun kwashe kayan su don masu aiki zasu zo,
" Bari na amsa waya"
Wa'alaikumus-salam warahmatullahi wa barkatuhu,
Ina son ka bani nutsuwarka kasimu,
To ranka ya dade,
Ya subhanallahi,innalillahi wa inna ilaihir -rajiun!!!!
  Dazu fah wajajen biyar saura na kirata tace dani zasu fita,,,
Gani nan zuwa,
Ya shiga ya fadawa su inna da unaiza,
Sukai ta jimami,
Shima abin ya taba shi,amma yana dannewa saboda baya son yana zakalkalewa a hidimar auren,

Unaiza ce take ta kwantar mashi da hankali har ya shirya,
Har zai fita tace yana da kyau Kar ka tafi kai daya; bari na kira B musa ya ja ka a babur dinshi,
Bai mata musu ba,
Ya kimtsa tsaff,
Suka tafi,
  " Alh ina son a tara min ma'aikatan gidan nan gaba daya musamman mai gadi da driver"

Domin Sune suka fi sanin shige da ficcen gidan nan
" Tabbass haka ne "inji Alhaji
;
suka shigo yai ta bincikansu daya bayan daya,
Ana kan driver ne su kasimu suka shigo da kamalarsu da mutuntawa, suka zube a kasa sukai jaje tare da adduan Allah ya bayyana ta,
S.T WURNO ya cigaba " wanne ni angon a cikinku?

B musa ya nuna KAsimu,
Yasha tambayoyi kam,
Na karshe ne ma ya bashi haushi,wai " to yanzu anyi PRE WEDDING PICS ne?
Babu shi a tsarin auren nan,
Su muke muyi koyi da sunnar ma'aiki sallallahu alaihi wa sallam,
Ya karewa kasimu kallo,to kai a hakan ka shirya auren kenn?
Kayi kayan lefe an kawo??
Ko shima bidiar ne?
Alhaji ya katse shi ranshi a bace inaga wannnan kamar bai shafe ka ba,
No Alh kayi hakuri, ina son na sani ne last week muka gama case din nan wani ango da abokan shi sukai KIDNAPPING amaryar wai Ashe bashi da kudin auren ne, kuma ansa bikin kusan sau hudu ana dagawa, shine daga karshe dabarar hakan ta fado mishi,suka nemi RANSOM MONEY mai kauri   asiri ya tuno muka warware shirin,
To kasan sukan hango gidan masu akwai ne su shiga neman auren saboda haka
B musa yayi caraf yace to mu ba haka muke ba,talauci ba zai taba sa mu aikin da na sani ba,
Ba zai samu cin amanar mutanen da suka yarda da mu ba.....
Kasimu ya umurce shi da yayi shiru a bakin aikin shi yake,
Haka dai har sha daya saura tukunna aka sallami kuwa,
Alhaji maude suka mike zasu tafi, haj hauwa tasa kuka, kuma tafiya za kuyin?
Sai jikin su yayi sanyi,
Alh maude yace to ko zan bar miki habeeba ta debe miki kewa ne??. Haj mairo tace eh hakan yayi Alhaji,
Dama tana hutun karshen shekararta ai,
Da kyar da yaudarA irin ta yan SOCIOLOGY tasa hajiya cin abinci, ammafa ranar basu runtsa  ba,
Kan kace kwabo zance ya karade lungu da sako, gidan ya fara daukan harami na birni dana kauye suna zuwa jaje
A.S.P MU' AZ
Ba'a
Barshi a baya ba shima suna ta bincike, shida  WURNO  suna ta shige da fice sune A.A SOKOTO sune gidan Alh bagudo,

kana bude gidan T.V ko na Radio cigiyar dai ake sawa,
Kwatsam washe gari ds  la'asar lis sai ga kira,
Muryar zubaida suka fara ji,
Sai aka kwace waayar
Miliyan biyar kawai zaka bayar ka fanshi ran yarka, abinda ya fara ji kenan,
Kit aka kashe wayar,,
Ba wasa ya kira muaz da wurno ya shaida musu, duk sun bayyana a falon bagudo,
Kasan miye Alh,?
kana nan 'yan iska ne ma, saboda idan gawurtattun ne, makuden kudade  zasu nema,
Ina number??
Sun boye, ai
Zasu kara kira dole,
Bari ni kuma na kira wurin su V.I.O.s dinnan sunce sun gano address din mamallakin motar.

Yanzu zanje na karbi bayanan su muyi inviting dinshi
Washe gari da safe sai ga inna da unaiza sunje jaje,
Gwanin sha'awa unaiza ta sake  ta tashi ta gyara dakin   Ammi tsaff,

*********************

S.T WURNO yana falon Alh Bagudo suna tattaunawa,

Sai ga kira ;
yana dauka kuwa sune ya sa handsfree ya saka,
Alhaji zuwa yamma muke son kudin mu don gobe zamuyi damuwar mu da kudin "suka turo indaa
za'a ajiye musu kudin,
To ba damuwa Allah ya kaimu,
S.T WURNO yace "  kaji ko?? nace maka yara ne,
yauwa yanxu ga number tasu nan,
Alhaji ya mika mishi wayar,

Alhaji bamu bukatar number tunda sun fada inda suke dabara zamu shirya musu.

*********************
Maman Auwal cikinta sanda ya tsuree don tayi tunanin dukan su za suyi ,
Kai maman daddy Amma wannan amaryar dabba ce, ko kuma nace tinkiya, idan ba shashasha ba har zata hada baki da kishiya,
Lalle agaishe ta ki ga tsabar jaka ce ma ita tana nade a daki ta bar mata 'ya tana wahala da ita,
Suna kari sawa gida ta samu su mubaraka suna kwashe kaya zuwa wancan gidan
" Kut me le si mubaraka uban wa ya baku izinin taba min kaya ba tare da izini na ba?
Ta ce " baban daddy ne"
To mi ya sa ba ki  kirani a waya ba,
Bello yace ah toh nima dai gani nayi da an hakura da zancen tashin tunda Amaryar ma an yi Kidnapping dinta,
" Kidnapping "
Maman Auwal da maman daddy suka hada baki,

a'a unaiza ta shiga ta fita dai ta mata kurciya,
  Shiyasa ta kwantar da hankalinta,
   Kai haka ne mana,
  Bello ya garzaya cikin gidansu, ya ce wa umaima,
" Ke ina uwarki?
" Tana madafi,"
  Aunty tsabar bakin ciki da hassada kikai wa Auntyn namu kurciya don kar tazo  mu sha danshin masu arziki,
To wallahi ko kinki ko kin so sai an aureta kuma kar kisha mamaki ta fidda ke ma,
Unaiza idonta ya rufe ta gayyaya mishi bakar magana duk da ranta yayi daci yana kuma mata kuna,
  Amma saukin da ta samu shine amayar da abin da ya dade yana damunta " don shiru shiru ba tsoro bane gudun magana ce"

Ta mishi wankin baban bargo
Inna ta fito" Bello yaushe kasimu ya maka magana akan iyalan shi??
Haka kaga musa yake yi??
  Ni daban musa daban
Gaskiya,
ya cigaba da kunkuni ya fita, a zuciar shi kal dama so yake ya kuntata mata kuma ya samu ta amsaa mishi,
 
**********************

Maryama tayi kyau sosai ta kintsa kantaa dukkanin bangaren, wato  na fili da na badini,
Tasha kunshi da kitso, dinkuna kashi kashi,
Inno ce tace kar ta sanar wa mustapha zasu taho, domin tasan maman Auwal da shige shige,
 
Kimanin karfe biyar na yamma Mustafah ya dawo daga wajen aiki ya samu gidan a garkame,
Mtwsssss,
Ta kulle ta tafi yawo,,
Ya dauko wayar shi da niyyar zai kirata don yau bai dauki dan makullan shi ba,
Ya fasa yana son yaga  gudun ruwanta,
Ga su Auwal suna islamiyya,
Yayi tsukaa ba adadi,
Can sai ga mota ta tsaaya,
Inno ce dauke da Farhanah,
Ah ahaaa inno kune?
Jikin shi na rawa ya karisa maryama ta fito,
Inno ta tunkari kofar,
Ido ya rufe kamar zai yi mi? don tsoro yasan yau kam kashin shi ya bushe,
Ina matar gidan?
  Ban same ta ba,
Ina makullanka??
Na manta ban dauka ba yau,
Inno tace " wannna wani irin lalacewa ce??

    aka sauke musu  kaya, yace su shiga gidan kasimu, su jirata,
Anyi sa'a yaran sun taso daga islamiyya  gashi bata dawo ba,
Auwal kaje gidan da mamanka take zuwa ka karbon key,
Yaje ya karboo ya ma wasu  maryama waysa su fito, an samu key,
Ta gama  felekenta ta fito kenan maman daddy ta rakota sukai kicibuss da maryama da inno unaiza ta rako su, tashin hankali gobarar gemu,..........

Comment