shafi na Ashirin da shida

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ πŸ‘ŒπŸ»

Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…

2⃣6⃣

YAA SALAAAAM!
faduwa yayi,
SUJUDUSH-SHUKRI ya yi wa Allah madaukakin sarki,
Ya kara mikawa likitan hannu,
Bilkeesu kuwa godia take ta yi a zuciyarta,

lalle hukuncin ubangiji ya wuce yadda ake tsammanin,
Allah mai yin yadda yaso a lokacin da yaso,
Ta runtsa idanuwanta da ta tuno irin kalubalen da take fuskanta a wajen dangin mijinta da makotanta,
Ta tuna yadda yayar HABEEB kullum bata da zancen da ya wuce yayi aure don ya samu MAGAJI,
Amma ya yi KIRMISISI yace lokaci ne,

Gashi cikin hukuncin ubangiji Allah ya kawo lokacin,
Sunyi kusan kwana biyar ana jinya, ko kwakwkwaran motsi tayi sai ya nemi dalili,

Ya tambayeta mi take sha'awar ci,
Mirmushi bilki tayi tace '' bana bukatar komai,
Yayi ta mata magiya,
tace'' bari tai maganinshi da takurin da yake mata,

GORUBA nake son ci,

Mi sauki ne, bani minti arba'in

Hahhhhaa kasan nan ba nijeria bane?

Ina ruwanki ????
Ya fice abinshi tai dariya

Shi ko bai zarce ko ina ba sai SHAHARA MANSOOR yasan anan ne kawai zai samu kayan cii ma irinta hausawa,

Yayi sa'a kuwa ya samu a hannun wata TAKARU,
abin haushen
Ma abinda a nijeria bai fi NAIRA biyar ba
Amma anan har RIYAL Ashirin ya jido mata kusan guda Goma
Ya samu tsire da yasha kuli kuli ya saya mata
A hanyar shi ta dawo wa ne ya ya ga wani Allon talla wurin sayarda kayan yara,( SUPER MARKET) da ya shiga yayi ta jidan kayan jarirai na maza dana mata har abin dariya,

BILKI na can tana tunanin mai ya hanashi dawowa , shi da yace bazai wuce minti Arbain ba,

ta tashi ta hau leqe leqe ta taga,
fararen fata ne kawai take gani suna kaiwa da kawowa, sai kuma hadiman masallacin mai ALFARMAA suna ta share share da goge goge abin mamaki yake bata basu gajiya,
masu wankewa suna yi,motar mopping na bi ga kuma kamshi,
Allah kenan!!!
Ta shagalta matuka ta zurfafa cikin tunanin buwayar Allah, bata ji shigowarsa ba ma sai qamshin goruba taji a hancinta, tana juyuwa abin mamaki sai ta ganshi da goruba da tsire,
kamshin tsiren da ya bugeta bata san lokacin da ta ruga tayi makewayi ba sai amai nan da nan ta fita hayyacinta,
hankalin shi ya tashi,
ya kira likita yake sanar dashi,
Ya mishi dariya kar ka damu al'adace ta masu ciki,
inaga ranta ne bai so.

Ya diba ya kai madafi ya ajiye abin haushin ma harda goruba da ya sayo tace bata so,

Haka dai ba don yaso ba ya zubar da goruban a dust bin,

Can taga manyan ledoji akan gadon su, hankalinta ya koma kan su, taje ta bude
TAB INA RUWAN GANDOOKI,
kai tayi ta azizita kyan kayan,
Ranshi sai ya mishi sanyi domin ya dan shaka gaskiya ,

Saboda da kanta tace tana son cin goruba,
Sanda yasha wahala ya sayo kuma tace bata so, ( ba'a sabin ba )

Nan ya zo ya dauki dayar ledar ya zazzage akan gado,

kai masoyina baasu yi yawa ba?

Mi ma aka yi?

Ki kara warwarewa zamu haura akwai inda naga kayan babies , sai kuma cikin BIN DAWOOD suma akwai kayayaa kin LUDA( jarirai ).

ZUBAIDA ta shirya tsaf umminta ta bata kudi ta saya wa TWINS kayan wassani,

Da sharadin driver zai bi office ya tambayi kwatancen gidan,

QASEEMU ne zaune a office ya dukufa yana aiki akan computer shi,
sai ganin drivern gidan oga ya yayi ,

ma za ya mike ya tarbe shi, nuna mishi yadda zai zauna yayi,

Suka gaisa yace mishi ''
da uwar dakina nake muna neman kwatancen gidan ka ne,

Ah ai mai sauki ne ya basu Adreshin gidan ARKILLA QUATER'S muje mu gaisa to, suka fita ya jawo kofa nan ya kira UNAIZA yake fada mata tana da baki,

Nan ta fara kame kamenabinda za'a tarbesu,
Amma baban Umaima baka fada min da wuri ba, ban tana da musu komai ba,

Nima yanzu drivern yazo amma abinda za'ayi musa yana gida ne?
Eh inaga bai fita ba,
To idan akwai kudi a hanun shi yaje ya sayo kayan fruit ki yayyanka musu sai pure water ko?
ai ya isa?

Yauwa to shikenan,

Yaje ya sameta a zaune cikin mota samfurin jeep,ta kamfanin FORD
Allah sarki abinda zuciya take so
Ta fito cikin kamala suka gaisa
Ashe yau anyi niyya kenan?
Ta sukwi da kai,
Eh ai na matsu naje naga TWINS dinnan ,

Cikin zuciyarta wani dadi da Annashuwa take ji,
Ka ji gobe Baba yana hanya ko?

Eh yanzu mukai waya dashi yake shaida min
Allah ya kawo shi lafiya,
Yace Amin

UNAIZA uwar giringidishi,
tana ta kaiwa da kawo wan zuwan bakuwa,
Allah ya so tana da naman ta A fridge,
nan da nan suka hadu ita da baba musa su ka daura Abincin,

Gidan bai musu wahalar ganewa ba
Suka iso,

driver ne ya kwankwasa kofar,

Musa yazo ya bude kofar ya musu iso driver ya ajiye leda ya fita ya barta ,

UNAIZA ta fito daga madafi,

Maraba lale sannunki da zuwa,
Zubaida ta miketa karbi kofin jug da yake hannun UNAIZA,
Ta ajiye sannu da aiki,
Sannu kadai suka gaisa,
nan musa ya shigo dauke da farantin kayan marmari ya ajiye mata ya zauna suka gaisa
Nan suka gabatar da kansu,
ZUBAIDA tace banga TWINS BA,
ai kuwa makociyata ta ta ai ko an dauke su,

Ah toh Aunty don su nazo gidan nan gaskiya.
a fada min gidan naje na dauko su,

Kwantar da hankalinki Baba MUSA tashi kaje kacewa maman haneefa anyi bakuwa zata gan su,

Tace'' ZUBAIDA bara naje madafi na bar abinci kar ya kama,

Zubur ZUBAIDA ta mike tace mu tafi Aunty na taya ki,

UNAIZA tace zauna baza'ayi haka ba zauna abinki,

ah wallahi Aunty mu je ba komai.
Ta bata kujera yar tsugune ta zaman mata zauna anan,

UNAIZA ta fara yanke yanken su cabbege ZUBAIDA ta karba,

sharf sharf ta karisa yankawa, UNAIZA abin ya bata mammaki taga yadda take ashe ta iya aiki,
Bata ajiye cabbege din ba sanda ta wanke shi a sink da gishiri ta tambaye kwando ta zuba ta tsane,
Hakan Yayi dai dai da shigowar Baba MUSA da LADO,
caraf ta karbi KHALEEDA domin ba ta inda tabar wa Babanta,kamar su sak,

Muje falo zUBAIDA ,

UNAIZA dai abin sai mamaki yake bata irin wannan dokin,
Ta je ta babbaje musu kayan wasa gashi yaran abin sha'awa sun sha kwaliyya musamman KHALEEDA tasha HAIR BANDS da BEADS gwanin sha'awa,kalar kayanta ne,dai dai da safar kafarta orenge ne( ruwan goro ) ga lalle kuma ,
Uwa uba kamannin. Da suke da Babanta,

An kawo abinci amma ko takanshi bata bi ba saboda ta shagaltu da yan biyu nan sosai,
.
Har UMAIMA ta dawo ta tarbeta itama da dauko mata CHOCULATE ta cire mata UNIFOAM maza kai ki ajiye a drawer,
Sai ga umaima da TOWEL ,
Umaima zauna kafin KHALEED ya gama shan nono, sai na tashi na wanke ki,
Inji UNAIZA
Ah muje na wanke ki,
ina ne makewayin,?
Umaima ta nuna mata ta wanke ta tsaf basu fito ba, sai da ta shirya ta tsab,
Da kyar UNAIZA ta shawo kan ZUBAIDA suka ci abinci,
Chan dai umminta ta kira ta taga shiru, bata dawo ba,

take tuna mata zuwansu kasuwa sayayya gobe,
Ko kin manta gobe babanki zai dawo?

Ta saka HIJAB dinta Aunty zan tafi,

Zamu tafi kasuwa da hajiya,
amma don Allah Aunty aban KHALEEDA mu tafi,

Kuma hakikanin abinda ke zuciyarta take fadi,
Da dai UNAIZA ta gane hakan ta lallaba tace mata kar ki damu tana shan nono yanzu,
amma insha Allah idan aka yaye ta akai miki ita,
Ai ni zan yaye ta ma Aunty,

Insha Allahu,
Da kyar dai ta dauke su ta sumbace su, ta ajiye,
Tace '' BABY KHALEEDA sai kin kara gani na ko har mota suka rakata,
Driver yayi barci har ya gaji,

Inna ce ta kasa ta tsare a falo,
yunwa ya dameta amma har yanzu bata ga wulgawar Asiya ta fito a daki ba balle ta shiga madafi tayi musu kalace,

Maryama har wajen tara da rabi da taga shiru ba'a miki mata abin karyawa ba ta fita domin taje madafi ta samu abinda zata ci abinka da mai juna ba'a wasa da ci,

Tayi kicibus da inna a falo,
ta lura gaba daya inna ranta a lalace yake,
Ta samu gefen inna ta zauna daga kasa,

Inna lafiya kuwa?
ba dai jikin bane?

Maryama jikin ma zai iya damuna ai kinga ban samu abinci naci ba bari nasha maganin,

Ah inna kema baki karya kumallon bane?

nima yanzu madafi zanji na ga ko zan samu abinda zan dafa,

Bani minti goma inna,

Ai yau ba kice da girkin ba kije ki kira min Asiyan naji abinda ya hanata fitowa ta daura mana Abincin
karya wan Allah yasa mustafha ma ya karya kafin ya fitan?

Daki dai wayam,

Inna inaga fah maman Auwal bata nan don naga ba kowa ,

Inna bari naje na nema mana Abinda zamu ci,

A zuciyarta tana cewa yau ina maman Auwal taje haka da sassafe kuma tasan inna tana nan bata ajiye mata abin karyawa ba,

Nan da nan ta sarrafa musu abinda zasu ci ta kuma dama wa inna kunun Alkama,
Kwatsam sai ga maman auwal kamar wanda aka hanka do ta,

Batayi tsammanin zata samu inna a falo ba,
domin tasan inna idan tayi sallar Asuba takan tsaya tayi lazimi, har sai hantsi yayi,
tukunna idan tayi sallar walha sai ta koma ta runtsa,

Ta hau kame kame inna kin tashi ne?

Ban tashi ba,
nace ban tashi ba,
ina jira ki dawo daga yawon gantalin sai na tashi ko ki tashen,

Tsabar rashin mutunci kinsan ina gidan nan kika barni da yunwa kika tafi yawon gantalinki na gulma da yi da mutane,
To yau zanyi maganinki a gidan nan idan kin gama da mustafha bazai iya hanaki abinda ranki yake so ba,
to nikam WARGE CE DAI DAI KUGUN UBA KOWA NE!
Wai ita kuwa Asiya ta rasa karyar da zatayi ta kare kanta a wajen inna,
A zuciyarta tace komai ya FANJAMA FANJAM!
dama tun farko haushin inna Take ji, dadin dadawa ma da ta sa mustaphan yin auren nan,

Gashi tazo tana sa mata ido, ga takurawa,
tasan ko mustaphan da yake aurenta,
yayi kadan ya hanata muamala da Aminanta balle wata UWARSHI,
Ta mike zatai hanyar madafi kenan,

Inna ta dakatar da ita,
Ina zaki?
daga yau nasa doka kar na kara ganin kafar ki a madafi,
Bata taba tsammanin hakan ba tai sauri ta wai go ta dubi, innar,

Inna kuwa da ba shakka take yiba,
Tace eh sai randa na zartas da hukunci tukunna,
Zuciyarta ce ta yanke ta bada sautin DAMMMM saboda tasan rashin mutuncin inna tsab dama ba sonta take yi ba yanzu kuwa komai ma zai iya kasancewa,

Tab! ni kuwa yadda na saba da dadi bazan iya rabuwa da musty ba,
Nasan yan uwana ma akwai masu min bakin ciki,
ina auran dan boko tunda kulluhumun yan gidan mu direbobi suke aura ko yan zaman tasha,

Nima Dai Allah yayi rabon Yaran nan ne yasa har na aure shi duk da ba ta hanyar Allah bane,

amma ai musty ba sa'an aure na bane,

Ta zo ta zauna a gefen kujerar da inna take kai,

Nifa kiyi hakuri ba wai na hana ki abinci da gangan bane,

Kawai dai nayi tsammanin. Baki tashi ba ne,

Inna kuwa da yake takaita makura kala bata ce mata ba,

Mikewa ma tayi maryama ina son da rana ki mana dambun acca na zogale,
idan babu kudin cefane a hannunki kizo ki karba,

Tsaka mai wuya,
Maryama ta fada,
Allah bai yi ta mace mai tashin hankali ba, bar ta da kwainane da 'yar kissa irin tamu ta mata,hakan ma sai an tabo ta,

Maryama tabi inna har daki tace
"" ni kuwa inna inaga da hakuri kikai da maman auwal ki mata addu'a kawai tunda inaga kin sha nuna mata bacin ranki akan fitan nan bata daina ba,

Maryama zakiyi abinda na saaka ki ne ko kema bijire min zakiyi naji?

Yi hakuri inna,

Tsam ta mike ta nufi madafin domin ta fara shirye shiryen daura abinda inna ta umurta, domin yadda inna ta hau tsinin nan mai sauko ta sai yA shirya

Yanzu MUBARAKA bazaki tashi ki lallaba ki koma makarantar ba?
Kin ce min fah kina da gwaji gobe,
nasan dole jikin ki yayi tsami amma daurewa zakiyi

Aunty bar batun test din nan jikin nan baya min dadi ciwo yake,

wallahi da nasan haka zasu min ai da ban fara ba,
bana son abinda zai taba min jiki,

Kar ki damu basu doke ki a banza ba Bashi suka dauka,

Ai daram sai kin auri QASEEMU kuma muci ubanta mu koreta mu kuma mallake shi,

Mu raba shi da MUSAN. Nashi muga yadda zai yi?

Hmmmmm Aunty bana kaunar auren mai mata fah, nifa gaskiya saurayi nake son aura kamar MUSAN nan don jibgata yake yi amma wallahi Aunty baki ga kyawun surah da yake da ita ba,

Amma kinji kunya mi zakiyi dashi ai tsakaninki da MUSA sai daukar fansa

Yanzu dai tashi ki fara shiri,

Aunty na fada miki kudina ya kare fa,
gashi da yawa daga cikin kayan abincina sun kare kuma na miki waya baki ce min komai ba,

Wallahi MUBARAKA abin ne yanzu sai a hankali,
Kudi ba su zama,

Amma ai Aunty dama abinda kika ban kinsan bazai ishen ba,
kuma kice kika ce kin raba abin da baban daddy ya ban biyu kin ajiye rabi saboda kar na kashe gaba daya,

To kiyi hakuri yanzu kam bani da kudi,
amma a satin nan zan aika miki,
Zan nemi T.J ya kai miki,

Tashi nasa an tsinko miki ganyen tsamiya jikin ki zai warware sosai,

Suna cikin haka aka mata waya ,

Ana tambayarta yaya bata dawo ba?

Ina nan tafe,
kar ki damu ba test din mutuminki bane ko a jikina nasan kin samo mana Q's dinma,

Ah ai nasan ki,
Maman daddy dai ta lallabata tai wanka saboda bata son baban daddy ya dawo ya sameta a narke ne,

Dole zai tambayeta miya sameta?

Duk da cewa ba tsoron shi take ji ba amma ai ya sha mata jan kunne akan shiga damuwar wasu da take yi,
Ta shirya tsab cikin riga da siket na turawa. Rigar kam akwai da babu ce,

Ta doka sallar magariba ,

Tana idarwa ne Auntyn ta bata dari da hamsin kudin babur duk da tana sane tasan baza'a kaita a hakan ba ma musamman da dare yayi yanzu,

Ranta a bace tana tunanin ta kira T.J ya kaita kawai tunda baza su ishe taba,

Tayi kusan zuwa gate din QUATER'S din su kenan sai ta ga an haske mata idanu,
har zata fara bala'e sai ta hango ashe baban daddy ne ,

Ya tsaya yace ta shiga ya kaita,
Su kai tsam ba mai cewa komai,
sanda suka zo dai dai banki da yake ajiya ne ya gangara gefen titi ya faka,

Yace" jira ni anan nasan kina bukatar kudi. Yadda na ganki empty din nan nasan Auntynki bata sallame kiba,

Kamar kasani
Yanzu haka dari da hamsin tabani kuma kasan bazai ishen ba,

Jira ni to,

Ya miko mata dubu goma sha biyar,

ya tsaya yasai mata kasashshiyar kaza da lemo,
Maimakon su nufi hanyar da zai sada su da makarantar sai ya dau hanya kamar zai bar gari sanda sukai nisan sannan ya faka motar
Ya zagayo ya ya bude kofar bayan,

ya umurceta da sauka ya tura sit din gaba domin su samu space a kujerun baya nan zance ya sauya,

( Allah ya wadaran mai budurwar zuciya!)

Ba kunya ba tsoron Allah haka sukai ta tsunduma cikin masha'arsu, sai sun hakura sai shedan ya kara ingiiza su,

Har tambayarta yake kodai zasu kama hotel ne idan yaso nacewa yayarki "tafiyar gaggawa ta kamani,

Ta marairaice mashi. Kayi hakuri gwaji nake dashi gobe da safe,
Karfe takwas ka bari sai jibi sai kazo,

Bani da komai a wannan ranar,

Da kyar suka rabu. Da ya sauketan ma sanda ya shashshafata son ranshi sai wajen tara. Da rabi ya barta.

Baban salima kuwa bai dawo gida da sai wajen karfe tara da rabi ,
Domin ya biya gidan kawun shine, yaje neman shawara dangane da auren da yake son ya kara amma bai ce musu mai aikin shi bace,

Oganniya kuwa ko a jikinta tana kallon zee world cikin shirin MEHEK ko idonta a dole take kifta shi,

bata son wani abinda zai takura mata ana haka kuwa ya dawo ya kwankawasa yafi sau biyar bata tashi ta bide mai ba,
sai laure ta kwalawa kira tazo ta bude mishi.
Sukai murmushi wa juna,
Ta karbi jakarshi ta mikawa maman salima,

Tace don Allah mika dakina,

Ta kuwa cika umurni ta shige daki da yake ta iya takunta bata zama musu a falo,

dare nayi idan ta gama abinda zatayi zata shiga daki,

Gimbiya na dawo,

yunwa nake ji wallahi",

Har ta fara tambayarshi ina ya tsaya,
sai aka dawo daga tallen aka cigaba da shirin,

Ya lura gaba daya hankalinta na kan T.V yace

"" banga abinci na akan tebur ba?

Baban salima bana son kallon nan ya wuce ni kira laure ta kawo maka abincin,

To ruwan wanka fah?

Kai baban salima don Allah barni kira laure ta hada maka,

Kai don Allah ki tashi ko na kashe T.Vn,

ya za'ayi ta bani abinci kuma kice ta hada min ruwan wanka?
anya mutunci kike ja min kuwa?

Laure laure !!

Har ta kwanta dole da taji muryar Uwargijiyarta ta amsa,

Ta fito ta rusuna mata ,

Taimaka min don Allah ki hadawa baban salima ruwan wanka,

Bata idaba ba ta sa ihu"" wayyo MEHEK memory dinta ya dawo"

Shidai bin ta yake da kallo,

Ba bata lokaci kuwa laure ta hada mishi ruwan dumi kasan cewar garin akwai zafi bata yawaita ruwan zafin ba,

Har zata fita sai gashi ya shigo ya mika mata waya,
Kina boyewa sai dare yayi ki kunna ko kuma bayan Azahar nasan lokacin tana baccinta,
kar ki bari ta gani,
Yanzu ma nasa miki number ta da kudi,

zan kiraki wajen goma da rabi nasan lokacin tana kallon KINGS OF HEART zamuyi muhimmiyar magana,

Ina yarki?

Tayi bacci tun dazu,

Ya mata godia ya fita,

SHANGAI KUWA TA SHANYA IDO TANA KALLON SU SHORIA
haaa'a

Cikin nishadi yayi wanka,
yasa three quater ya fito falo sama sama yaci abincin saboda baya son abu mai nauyi da daddare,

Yace mata "dauko min Apple a fridge mana ?
,
Haba haba baban salima sai kasa na tashi kuma idan na dawo ba labari zaka bani ba,

Ni don Allah kaje ka dauka nasan laure tayi barci balle ta dauko maka,

Ya mike ina da hannu ai,
sha kallonki lafiya,

Sai na shigo tace
"mishi,""
Yace yau kam nayi fushi dakina zan kulle,
.
Tai dariya kai ka sani na huta,

Ya jiyo,

"" da mi kika huta? raguwa abinda idan kika fara baccin nan kamar wata kasa,

Yana shiga ya danna key a dakinshi,

Ya kira yaji bata dauka ba sai yayi tunanin ko tayi bacci ne,
Can ya kara gwadawa sai yaji an dauka,

Ranki ya dade nayi tsammanin kinyi barci ne?

a'a wayar ce kamar a silent take sai dana juya ne naga tana wuta shine na dauka,

Owk to yaya yinin 'yarki?

Bani labarin yaya kuka yini?

Gashi kunyar shi take ji amma tana magana tana mishi rigima da marairaita, sai ya nutsu sosai yake gane abinda take fadi,

Nan yake sanar da ita abinda yake shirya musu,
Kamar tayi ihu saboda murna,

Amma ta ci je ta daure,

Anya baban salima wannan abu ba mai yuwuwa bane?

Nifa hadimar matar kace,

Sai mi?

Yanzu baki tausayina ashe?

Amma yanzu miye banbancinki da matar tawa?
tunda komai kice kike min dama,

a'a ranka ya dade,
RUWA BA SA'AN KWANDO BA NE!

Kuma WUTSIYAR RAKUMI TAYI NESA DA KASA!

Haka kika ce?

Eh ranka ya dade
ai GASKIYA Daya ce!

To shikenan zan tuna miki kuwa duk randa kika ji ne akan ki,

kashe wayar tayi
Kunya ne ya kamata namiji kenan,

zanji nauyinka

hmmmmmm!!!

Yayi ta kiran wayar

Kunya ta hanata dauka,

shi kuwa sha'awa ce ta ta taso mishi kamar zaiyi hauka.

Maman TOXEE ce

Comment