shafi na hamsin

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

5️⃣0️⃣

Sam Bata kula  abinda  indo take faɗa ba,
Ta kama hannunsu suka tafi ɓarayintta tai musu  wanka ta shafe su da mai ta kunna musu katoon suka nutsu kuwa,
   Suna tsaka da kallon ne beeba ta kira ta,
  Mikewa Ta yi ta shiga uwar dakinta,.
Ke dai bari beeba  ai na gasgata abinda naji,
Musamman indon nan maman umaima bata da lafiya fah amma sai ce min take wai jinyar karya ce"
  " To ki dai kara kula kar ki bari su tarwatsa ku,
   Haba habeeba sai kace wata yarinya,duk da ban tashi gidan kishiyoyi ba;amma ina ganin abinda dangin uba suke yi"
    Haka ne to
  Ina ango ??
     
   Angoo ya yi tafiya,
   Shine baki bishi ba; ai da kunje kunyi SHAHARIL ASAL din ku ( HONEY MOON ) ??
    Ehh haka matar shi tace,
     Ni kuma naga bata da lafiya bai dace na bishi na barta a halin da take ciki ba,.
       Yauwa Adda zuby  kinyi tunani !gwanda da kikayi hakan,
Tunda lamarin ciwo yau gare ka ne gobe ga wanin ka,
Kuma hakan zai kara miki martaba da  ƙima a idonsA,
  Ko beeba?
        Tabbas kinsan maza suna da wani Abu guda  ga abinda ransu yake so amma sai su ki fada suna son ganin gudun ruwan ka yaya  zaka yi,

   Zubaida tace haka ne kam,
Allah yasa mu dace,
  Yanzu ma Abinci nake son na daura na rana,
   Kai to bari nazo na tayaki,
Zubaida tace ai kuwa dAna ji dadi,
  Ina musa?? 

  ai kuwa ban ganshi ba,
    To sai nazo.

  Umaima zaki taya ni kwana yau??
   Tai murmushi tace ehh amma sai na tambayi mamana kar ta min fada,
   Ba zata miki fada ba ai nima maman ku ce,
  Eh haka maman mu tace,
Tace kema maman mu ce kamar ita,
Ehh haka ne,

Wajajen sha dayan rana beebalo tazo,
Suka daura sanwar dafaduka

Habeeba muje ki dubo Auntyn naki
    Oh har ta xama Auntyna kenan????
   Ehh alamun ku ya nuna akwai ayar tambaya a kanku,

Suka shiga sun sameta a zaune taɗan  jingina da filo sam bata jin karfin jikinta  ga kwaɗayi da yake damunta,
  Ganin zubaida ta shigo ta ɗan saki murmushi
" Sannu da aiki Amarya,
Sannu kadai,      
mamaN umaima ya jiki??
  Beebalo ta gaisheta yaya jikin?
  Da sauki sosai ma sai rashin karfin jiki,

  Adda fauxia tace wannan dole ne ai,
 
   Zubaida ta numfa sa tace amma kin samu kinci wani abu ko?. 

  Adda fauxia tace ta dan taba kunu kam,
Yanxu maganar da muke yi kenan,
  Wai faten shuwaka take so,
  Amma bata san inda xata samu shuwaka a unguwar nan ba,

   Beeba ta cafe lah rashin sani da na taho miki dashi,
Muna dashi a gidan mu ai

Unaiza ta zabura don manzon Allah,!!!

Gaba daya suka sa mata dariya
  Bari na kira musa ki mashi kwatancen gidan, sai yaje ya karɓo min,

  Beeba sukai dariya ita da zubaida,
Ta kuwa danna kiran musa,
Yana ganin kiranta ya kashe ya kira,

Lafiya kuwa???

  Lafiya kalau Baba musa so nake ka karbo min shuwaka
amma ga wacce zata maka kwatancen gidan su,
  Beeba ta karbi wayar
Tace UMAIMISHHH
       Yayi dariya don ya gane mai maganar
    
    Don Allah kaje gidanmu ka karbo sako zanyi waya yanzu su tsinka kafin kaje,
  Owk ba komai sai nazo,
    Unaiza tace " kun ma san juna kenan )
Tai murmushi,

Zubaida tace ai kanwarki ce wannan
  Beeba dai sai murmushi,

  Sai ga umaima ta shigo da gudu tana kuka tai kan mamanta,
  Lafiya umaimah?? Zubaidah ta tambaya

Mama Aunty indo ce ta kore mu muna kallon katoon a dakin Aunty,
  
Wai zamu lalata mata kujera
Nace mata itace ta kunna mana tace karya ne wai ɓaarna za muyi matA,
      Wai ai kema kina da T.V miyasa muka taho nan ,
  Adda fauxia tace"

Ba mamanki ta ja miki kunne akan kawo magana ba??
  
   Beeba tace yarinya ce ai bata kai wannan lokacin da zataa gane hakan ba,
Chan sai ga khhaledd da khaledda sun shigo,
Indo ta tuso keyar su,. 
  Ta mikawa zubaida  key "

"gashi nan  kin bar shi a buɗe"
   Ehh ina sane ni na kunna musu kallo ai nace su zauna su jira ni,

Indo tace" ehh to ki dai kiyaye su ma ai suna da kayan kallon yadda aka hado ki da naki haka mahaifinkin ya hado wa uwarsun,

   Subhanallahi indoo wai mi yake damunki ne kam,
  Yaran nan duk inda suka ga dama zasu shiga tunda itama uwarsu ce tunda matar ubansu ce,

   Indo ta ce " ehh fauxiyya ko kece daga zuwanki ko kwana biyu ba'ai ba   yara su fara sukwanan dakin ki ai zaki yi magana,
Ko don baza ta iya hanasu ba,
Tana jin nauyi
   Unaiza tace Adda fauxia ki kyaleta,
  "" Yo kar ta kyalan mana mi zaku iya yi???
   Beeba tayi caraf tace

a'a ba'a haka gaskiya  yara kam na kowa ne ai, itama kuma 'ya'yanta ne, yanzu na tambaye ki mana Aunty indoo
Shin zubaidar ce tace miki  suna takura mata zasu bata mata ko kuma ra'ayinki ne?. Idan kuwa ra'ayin kine,
Miya sa kike son shiga tsakaninsu?
Bari kiji  a nawa tunanin  karyace tsagoranta mutum ya auri mai mata ya nunawa ubansu so,
Alhali kuma yace baya son 'ya'yanshi,
Kina ganin zai yuwu kuwa???
   Sannan

Yanzu idan ace zubaida ta haihu sai ace'ya'yanta baza su shigo nan dakin ba??
Gaskiya ba haka rayuwa take ba,
   Indo tai zuru zuru da ido,
Kinyi shiru,
Inaga da ace zubaidan ne tace miki sun isheta to sai ki yi hakan,
  Zubaida ta yunkura beeba mun manta shinkafa a kan wuta, taho muje mu duba, umaima zo mu tafi,
Maman umaima yau fah tare zamu kwana da ita???
  Amma tace sai na tambayeki tukunna,

   Kar kije komai kiyi yadda kike so dasu 'ya'yanki ne,

Haba zubaida ai  ina nan zan taya ki kwanan fah miye sai kin dauki yarinya ta zo ta miki fitsarin kwance ?

Suka sa kai suka fice,

Indo ta dawo kan unaixa,
Amma yanzu abinda kikai kin kyauta ??
        amarya daga kawota kin lAnkwaɓe wai baki da lafiya,
Don ki hanata sakewa da miji ko?
To ta Allah ba taki ba,
So kike kiyita axabtar da ita,
Yarinya yar masu kudi bata saba da wahala ba,
daga zuwanta kin hanata sakaT

Fauxia tace " to ke mi ya hana ki ansa ki mata, naga ke ya dace ma da kiyin??
    Amma kina son ki hana mai yin,
  Ki dai ji tsoron Allah kar ki zama kanwa uwar gami a tsakaninsu, yarinya taxo da halinta mai kyau kar ki zama haddAsana, ki shiga tsakaninsu,
  
Yanxu ba abin alfahari bane hakan,
  Zaman lafiyar ai yafi fitintunun nan,
    
indo tace musu " Ita ma dai kuna son ku mallaketa yadda kuka mallake yaya kasimu,
   Kun mai dashi masa a tanda ku jujjuya shi yadda kuke so,
    Sallamar musa ce ya katse ta,
   Gasshi nan Aunty,
yaya jikin,??

Da sauki sosai  Don Allah musa ka mikawa Auntynku shuwakan,
Owk to shikenan,

    Indoo takaici kamar zai karta,
Ta fice a gidan tai gidan maman daddy,
  
Maman inti maman inti, wato kin samu katifa mai taushe kin gagara tashi ko?
Kai baban inti  bana son walakanci,
  Ba walakanci bane, gaskiya na fada bilkisu ta taimake ki,
  Don Allah daina fadin haka,
  Tashi magana zamuyi,
To ina jinka mi Anka samu????
Ya murmusaa mi zan samu dai

Hahhhhaaa
Ta murmusa

kinga tunda kin sai da tsohon kayanki mi zaisa bazaki fara juya kudin ba??

Kinga zama hakan ba zai yuwu ba,
Musamman ke da kike da kannai mata,
       Eh toh kaima fah ka kawo shawara,

To mi kake ganin zan fara saidawa,??

"" Ehh matsalar sana'arku ta mata bashi, ai ta kace nace,
Amma dai kiyi nazari,
Tace nifa yanzu inaga na wuce yin bussiness din atampu,
  "" Yauwa maman intee mi zai hana ki tuntubi balkisuu idan an kwana biyu  ku fara harkar turare irin na larabawan nan?.
Ina nufi OUD's dinnan,
  Ehh haka ne,
  Amma nifa kasan bana son raini,
Don idan abin ya karɓen zata iya min iyayi tace itace hanyar arziki na,
      To kinji ki,   sai mi ? Idan ta fadi hakan ba dai ke kin samu cigaba ba,
Kuma abinda kika gagara ganewa itafa Ba irin mata masu gori da hassada nan  bane,
nayi imani da Allah da hakan take bazata buɗa miki ki samu ba,
Ki tuna jarin da ta baki har ummi yar Benue ta damfare ki,
ta taba miki gori?
  Kai ba wannan ba ma abubuwa da yawa ta miki su, kuma ban taba jin kin gayamin ta goranta miki  ba don nayi imani da Allah da ace ta mike nasan ba makawa sai kin faɗa don haka ki cire wannan a ranki,
Wanda ya fika ya fika,
  Uhmmmn kaga kamar abin arxiki mun fara magana tiryan tiryan yanxu kaxo ka shigo da wani lamari kuma,
kai dai kullum cikin kambama bilkisu kake yi kamar wata cikin umar ka,
    " To maman inti gaskiya nake fada miki,
  To abar maganar bana son ji,
Sannnan zancen farkon kuma zan yi shawara,
   To Allah yasa a shawarta mi kyau,
Yauwa Baban inti  don  Allah ina son na shiga makotan mu ta baya nan an kawo amarya ban samu naje musu biki ba,

  Ba damuwa bana son ki daɗe kinsan bana son kina tsananin alaka da 'yan kwatas din nan,
 
Ai ko baka fada ba nima bana so,
Don ba sa'an nina bane,
Duk 'ya'yan malam shehu ne fah irina,
Dame za su karen?
Itama dalilin da yasa zanje din ance diyar BAGUDO ce na bayan layin mu ,zanje mu kulla alaka da ita,

" Au bama wajen uwargidan xaki ba kenan??

   Ai naga kamar kuna xumunci da ita ko ba ita bace suka shigo miki jaje da matar farouk ba?

  ai kuwa itace,

To gaskiya bana son haka,.

Yanxu ace kice na miki kishiya sai bilkisu ta koma wurin kishiyar xaki ji dadi????
.
Mi ya kawo zancen  kishiya kuma malam??
 
" ah ban kai bane??

   Don Allah ka bar zancen banson misali irin wannnan,
  
Ai kuwa ki shirya kishiya tana nan ta kusan shigowa,

    "" Ka ga baban inti bana son irin wannan maganar ko so kake B.P na ya hau???
  
   To ai dama ban miki alkawarin ki kadai bace,
don haka kuwa ai bazaki fidda tsammani ba,
  
      Baban inti don Allah tashi ka tai sha'aninka nasan kana da uzurinka,
   Shawara kuma na gode zan tuntubeka idan na gama,

   Yayi ficewarsa yasa dariyaa,
Mata mata mata hoo !!!!!!

   
Mubaraka ta kira wayan T.J yafi abinda yafi,.
Da kyar ya ɗaga
Chan ya dauka,
Tace mai " Haba habibina kwana biyu shiru,
Ko lafiya?
na kira ka sau nawa baka daukar wayan ko wani laifi na yi  maka,
  Ko kadan mubaraka,
Kawai dai na samu sabbin zubi ne,
Na hanaki yin  bleaching din nan amma kinki dainawa ni kuma kullum muka kasance dake bana jin dadin odourn da kike yi sai naji kamar warin Albasa ne  ko tafarnuwa ne ohoo,
Shiyasa kawai na canxa shekaa,
  " Oga T.J  baka min adalci ba
ya zakayi ka wufantar dani,
Bayan kasan kai kaɗai nake kulawa . ......
  T.J ya katseta karya kike yi,
Banda ni kadai kam,
Ko kinyi tsammanin. Bana bibiyar kice,

  To wallahi ko ka dawo mu cigaba ko na haɗa maka wani kitifin  a wajen matarka,
    Bismillah kar ki fasa matana tasan waye TIJJANI don haka ba zata damu ba
Ke kuwa xanxo na samu yayarki na fada mata dalilin rabuwata da ke,
Sharing kike yi da baban daddy ni kuma ina jin nauyinshi bazan iya takara dashi ba,

    Kinga kenan anyi one one,

    baka da hujjar da zaka nuna mata ta yarda,don tasani bazan ci amanarta ba,

Haka kika ce??

Ehh tabbas!!!
ni kuwa nake da hujja buɗe Datar ki na turo miki wani abu to,
Ta kuwa bude ba gardama,
  Sai ga hotunansu a manne da juna ita da baban daddy,
Kut me lesi,
Ta tuna lokacin da sukai hoton a makaranta ne, wata la'asariya baban daddyn ya kawo mata take away don taci yunwa take ji gashi suna da lectures din dare,
  Kuma ba wata lectures xasu fita ne da T.J
Tai ta rungumar baban daddyn a bainar jama'a duk da dama da yawa daliban kallon kabila suke mata saboda yanayin shigarta
  Shi kuma T.J dai dai shigowarsa kenan ya hango su,
Bai yi wata wata ba ya hau zooming camerar shi ya musu hoto,

   Don Allah don Annabi ka rufa min asiri wallahi duk randa Aunty ta sani sai ta kusan kashe ni,
    To nima don haka kada ki kara bibiyata,
    Ki barni na shakata
  
✍🏼✍🏼

       U.K.B

Comment