shafi na talatin da biyar

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

3️⃣5️⃣

Kina nufin kice min ta koma dakinta,
Kuma maman umaima ce ta rakata,
Na shiga uku shikenan ta kwashe sirrin mu
ta fada mata hmmmmm
  Aunty kenan wai wannnan mamar umaima har ce min take wai na fada miki ramin karya kurarre ne,kuma yanzu suka fara hadin kai da maman hydar,
Ke kyale ne don Allah zan ci ubanta a nutse ina mijinta ma aure zai yi na dau Alwashi?
ita da zaman lafiya da samun kwanciyar hankali har abada sai na barbarce kishiyar na sata a hanyata na hanasu zaman lafiya,
Aunty ance yar masu akwai ce ko?
Ehh haka ne yar BAGUDO ce fah;waye bai san shi ba a garin nan,
Ohh Aunty na rasa mi yarinyar ta gani ma a wurin shi ga talauchi.
Ba talauci bane yana da wasu abubuwa a jikin shi da zai iya jan hankali mace dasu.
Ko da yake da fari ne fah ba karamin kyau ne dashi ba, Aunty kenan
  Bari na tashi saloon nake son zuwa ayi min kitson

Don Allah kar ki sa wannnan Mai ruwan kasan; asa miki bakin kawai wancan kalar yakan mai dake kamar wata kabila,
   Hmmmmm Aunty nifa ba don inplanon ya xubar min gashi ba ma da ba ruwa na da gashin doki,
    Yo dama ai ba gashin ne dake sosai ba mubaraka,

********************
Cikin hukunci ubangiji maryama ta santalo yarta mace kamaar an tsaga kara an raba ita da inno (wato kakarta ta wajen uba )
Abin yayiwa inno dadi dama gashi ana son uwarta ga kama kuma a take tace a mai da mata sunanta
Hafsatu " kuma bana son a canza mata suna,
Haba inno fadar sunan kuma haka gatsau ai rashin kunya ne,
To ni dai ban son sunan zamanin nan wai ya ma sunan  takwarata yar gidan zuwaira  nan??
  Wai fanka ko farka?
Kai inno
  FARHA fah,
To ki ji fah miye amfanin sunan don Allah ?
Lah ai mai farin ciki kenan.

Wayar maryama ce ta hau kara
Lahh 'yar halak wai kin ki ambato
  To gulmata ake kenan??
  Eh gulmarki muke yi da inno
Tai mata barka da fatan Allah ya raya zuria,
  In sha Allahu muna nan tafe,
Allah ya kawo ki lafiya yy dinkin mu angama kuwa,?
Bude whatsapp na turo miki,
Wai yaya sunan yarinyar
Sunan inno ce
Kai kai ashe uwata ce  to ko dole na kara shiga kasuwa,

Ko ?

Ki ce FARHA tayi takwara don Allah ace mata FARHANA
Wuuu ga inno yanzu take kashedi wai kar asa mata inkiya
   Bata son farka
Bani ita kawai,  gwanin sha'a wa inno ta gaisa da autarta,
    Suka ce gaba da tadin su har aka zo kan sunan  takwarar tata
  FARKAN a'a rabani itama  takin hafsatun don ubanta ne ya rada mata  shiyasa na kyale amma da ke ce da tuni nasa ba miki,
Haba inno zamani ya canza fah,
Bari na kira ya mustaphan?
   To naga mustaphan ma bai isa ya tsallake umurni na ba,
Ta kashe wayar nan sababi ya dawo kan maryama
Kamar itace ta kar zomon
Maryam dai dake tasan hali ko a jikinta.

********************

   Hanifah kawo min ruwa mai sanyi yau katin mu ne ya kare ga baban umaima suna meeting,
Kari so dakin UNAIZA

  To,

UNAIZA ta watso mata bayani tsaf har maganar da sukai da baba musa,
    Ehhh gaskiya ki kwantar da hankalinki gaskiyar baba musa ne ba'a shaidar mutum musamman a zamanin nan da mutum ya zama abin tsoro, amma kuma alamar karfi ai yana ga mai kiba,
Amma kamar kullum nakan fada miki ki dage da addu'a kina kama sunanta insha Allahu bazata zama mai tayar miki da hankali ba,
Ina yi Aunty insha Allahu zan cigaba
Zan cen kaya kuma ba gazawa kikai ba
Yanzu kudin kin ciro a bankin ne?

" 'a 'a ban ciro ba,"

   To ki bar kudin ki je kiye istihara ki neme zabin Allah akan kudin da niyyar zaki fara juya su Allah yasa musu albarka kuma ya zaba miki sana'ar da zata fi miki alheri da albarka,
Insha Allahu zanyi Allah ya biyaki maman Hanifah.

Nikam ina mutuminki ne Bello bana jin duriyarsa kwana biyu??
Hmmm ya tafi TANGAZA amma inaga zuwa jibi zai dawo,
   Oh Aunty abun dan adam yana bani mamaki wai Bello ne ke kwasan sirrin mu yana fada a wasu bare wadanda bai. San su bama sai a sAma.
  
Hmmmmm UNAIZA ga mutum kawai musamman a zamanin nan kuma kin manta dan ubane fah,
Yanzu musa ya yi ne???
Ko kin manta lokacin da musa ya ma Mubaraka duuka da tai kazafi wa baban umaima.
Ehhh
Haka ne gaskiya musa yana bani labarin wahalar da mahaifiyarsu tasha a wajen mamar su Bello abin ba dadi,
Sai zuciyata ta yanke,
haka zalika  idan na tuna dambe da masifar da ake yi a gidan yayansu nan ma Sai nai ta tunanin hakan maman hanifa,

Kowa da kaddarar shi unaiza,kar kisa wAnnan a ranki;

To in sha Allahu,

Yanzu dakin yaran ne za'ata  zauna  kenan ,???
  Ehhh Aunty ni gani nake kamar ya mata kadan fah
Da naji kamar yace wai za'a daga su maman daddy su koma gidan gaban nan da suka tashi,ita kuma sai a gyara gidan su daddyn  to ohoo musu dai,
  Ehhh gwanda hakanma kazantar da baka gani ba tsafta ce' ko unty?  yanxu kina ganin zai iya rike gida biyu??

  Abin na Allah ne
Ki dai kwantar da hankAlinki  duk da cewa kina kokari ma,

.********************
   Wai shin ba kowa a gidan ne sai sallama muke ta rafkawa,

  Auwal mamar taka bata nan ne?
  Tana ciki bacci take yi,

    Wa nake ji kamar shugabaa?
   Wai kin tashi kenan
    Eh ni ce ai tambaya nayi aka ce wannan tsohuwar  banza bata nan wai ta dauki 'yar gwal ta kaita gida haihuwa;
Hmmmm tafi karfin ta banza ma ai har ta wofi mA
Amma Albishirinku;
  Kunsan mace ma ta haifaa ake ta wannnan kadi firin.
  Kai ki bari don manxo,
   Akai shewa akai guda aka tafaa haba kin cinye gida mutuniyar mazan ki hudu fah
A kadarance tace
" ehhh"

Mtwssssss
Aikin bur inji tusaaa ai wallahi maman Auwal idan nice dah wannan tsohuwar  tune zan yi maganinta sai tayi nadaman haihuwar shi da tayi har kika aure shi
Ki zame mata karfen kafa don Allah yadda tana ji tana gani dan sai yafi karfin ikonta,

Shugabaa wai abinda nake ji gaskiya ne??

Kawancen maman hydar da UNAIzA??

Uhmmmm haka nake ji wai kinsAnai  dole su dinki,
jiya bayan rabuwar mu mijin ya dankara mata saki gidAn unaizar ta kwana,mijin ne da tsabar shishshigi ya samu baban hydar din ya sasanta su,
Kai maman daddy!!!
  Ahhh kice dole ayi sulhu ayi kawance kice da ana gida yanxu an koma cin tuwon dawa da gero,
  Hmmmmm ai UNAiZA sai na zame mata masifaa,
Muna nan a bayanki kamar jela wai ita mai miji ko
  Maman daddy yanxu kam taga miji ai
Tunda zai karo mata kishiya, kishiyar ma yar manya.
Ai nasa anyi min bincike tsaf akan ta.
Kai maman  daaddy kin bani tsoro!!!
Ni ce fah sai dai zamu wahala kafin mu shawo kanta ance ta samu tarbiyya sosai
Ko maman daddy??

  Haba maman daddy kice fah.
   Akayi shewa aka tafaaa yauwa maman Auwal don Allah hungo karbi wannan ki je gidan maman hydar a matsayin kin je mata jaje ki  soke mata a jikin kujerar ta amma ba wacce kika zauna ba
  Ta miko mata farar takarda,suka karanta  kai shugaba shedan ma irinku yace yake jin tsoro
   Hahhhhhhahh ni wasa ce?? Ki dai
Ki tabbatar kin aiwatar,
  Kar ki damu zaki ji labari insha Allahu kinsan duk wani motsinsu inaji idan ina madafi,
  Bari na tafi nasan mijinki yayi kusan dawowa,

Ummn kyaleshi Auwal ya dafa mishi macaroni da mai da yaji,
   Kai yar daki na baki da sauki,
Ah tohh yaje chan ya ka rita ya kwala da yunwa  kafin yar gwal din ta dawo...

Bari ki ga ma mu fita tare naje na aiwatar da kudirin.

********************
  
" Barka da warhaka "
maman hydar ta amsa fuska a daure tamau,domin ta kuduri aniyar rabuwa da yan kungiyar tasu gaba  daya domin samun maslaha a rayuwar auren ta,
   Maman Auwal Ta hau kame kame  don bata taba tsammanin hakan ba,
Wai tazo mata jaje ne,
Kinga inada abinyi idan baki da abin fada
  Ta barta a zaune  ta nufi  madafi ta kyale ta; da yake maman hydar bata iya boye maitar ta ba kowa sai ya gane kiyayyarta da soyayyarta,
Ita kuwa maman Auwal dama ta samu ta soke takardar, ta koma inda take tsaf kamar ba komai cikin ikon Allah kwatsam sai ganin baban hydar tayi ya shigo,

Ta kidima kwarai  da ganinshi domin batai tsammanin zai dawo a wannan lokacin ba,tasan yakan kai sallar  easha kafin ya shigo domin duk motsin da ake yi takan jiyo daga gidanta,

Ta kuwa rasa yadda zatai gashi a kujerar ya zauna ba abin ta dauke ba,
Ta tashi tana ta kame kame bari na tafi idan ta fito ace mata na tafi,
Fuskar shi a tamke yana jiran maman hydar ta fito ya tuhume ta
Dalilin zuwan ta bayan ya hanata muamala dasu,
  Chan ya tuna ashe zai dau takardar biyan kudin ruwa ne sun kawo musu bill zai je ya biya kafin su dawo,
   Maman hydar!
Maman hydar!!
Jikinta na rawa ta taho a kidime,
Bani bill din gidan ruwan nan;sai zuciyarta tai sanyi tunaninta zancen maman Auwal zai mata,ta wai ga taga bata nan:a zuciyarta tana adduar Allah yasa ma basu hadu ba,
tai daki bata ga takardar ba,  har kan firiji duk babu chan sai ta hango  takarda a soke a gefen shi,
Lah Ka ganta nan a gefen ka ma fah,

  Ya dauka yasa a  aljihun shi.......
   To lallle ko miye takardar ta kunsa??
Shin dama sakon nashi ne ko na matar shi??

✍🏽✍🏽✍🏽
Maman nurain

Comment