shafi na hamsin da uku

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

  5️⃣3️⃣

Isaa dole ne mu shiryaa mu dunguma muje mu ma Alhajin nan godia ;
  Yaushe ne  ma kace?
    Son samu nan da sati biyu ace ina chan,
Yanzu baba ina neman shAwarinka,
Shi wannan da ya min hanyar har aka cimma gaci ya kamata na sam mishi wani abun,

Gwoggon shi tace tabbass dan halak bai manta Alheri abinda ya maka a rayuwa ko wanda kuka fito ciki daya iya abinda zai maka kenan"

",Gwoggo yadda nasan halin shi ba zai karbi kudi ba sam,

   " To miye abin yi ??

  Baban yace to! ikon Allah, Haka Allah yake abinshi,
  Ashe har yanzu akwai sauran irin shi da bai damu da abin dunia ba ko nace *KUDI *.
 
Hhhmmmm baba kenan;
Baba musa ya wuce yadda kake tsammanin tun ina U.D.U.S fa idan aka bamu " hand out" " MUZAKKIRA" yana saya mana ko na  bashi kudin daga baya bai  ansa,
  Da yake dama yana sana'ar shi tuntuni,

  Gwoggo tace " ai sana'a tayi takan kare wa mutum  martaba, mutum fa idan yana da sana'a yakan fi karfin reni,
Domin bazaka taba  zuwa kana karamar murya a taimake kaba,
Ko ka ga kayan mutum ka dauka.
  amma idan da sana'arka k komai kankantarta ta isheka dogaro da kai,
da nisantar kayan mutum,

Haka ne  gwoggo,
   Duk yadda zaka yi ka nemi asusun ajiyar shi kar ka tura mishi sai kunyi sallama kana filin jirgi ko kuma ka tashi ka isa can,
  Ina zai yuwu ka turo mishi??

    " Ehh sosai ma baba "

  To haka zakayi,
  Kuma yanzumma tare dashi zamu tafi mu yiwa Alhaji godian,
     To zan sAnar dashi,

A can sheme ta jihar katsina kuwa maman Auwal ce tsugune a gaban inno kamar mumuna,
Tana karban sakamakon rashin ɗa'ar da tayi ,

" Ki tattara ki koma inda kika fito
Ni zaki rainawa hankali,
Ni hafsatu,
Habaa kinyi kaɗan ko malam ilu mahauci ba zai min haka na ƙyale shi ba ballatana ke,
   Wanda karan kaɗa miya ma ya fiki daraja da mutunci a idonaa,
  Tunda kinsani albarkacin rabon kaddarar 'ya'ya kike zaune,
To amma naga alama raini ya shiga tsakanin mu,
 
 
             " Don Al-l........

  " Rufen  Baki bana son jin maganar ki,
Ki kuma tashi ki kama gabanki sai randa na nemeki,
Bari na kira mustaphan ma,
     Ta kira ikilima ta lalubo mata lambar shi,

Hankalinshi kwance ya dauki wayar tunda suka gaisa ta hau zuba mishi tijaraa

  " Kar kaji da wai matarka ta kaddara na tura ta gidansu koyan tarbiya da ɗa'a,
    Wani abin tai kenan.????
      Ehh ta mai dani sa'arta yarda ta mai da kai SAUNA KIRA MANA SHASHASHA IN KAGA SAKARAI KU TAHO TARE nima haka take son ta min ,
Yadda ta saba ta zari mayafi ta fice gantali ba da izininka ba nima haka take so tamin don haka
Na ce ta koma gidansun.

  Gata nan tana jina.
ina  takwarata???

  " Ohh Farhanah gata chan hannun Ameera "
To ka gaida yaran da Maryamah Allah ya muku Albarka,
Allah ya yassare maka abinda

Kake nemaa,
  Ikilima idan ta fita ki kullo min daki, ki bani makullan,
 
Maman Auwal maganganu biyu suka ɓata mata rai,
Da tambyar  farhana  da tayi, wai tana hannun ameera wato yarta ma raino ce aikinta su suna chan suna holewa ,
Kai ita tana gani dama hadin baki ne,
Tabbass da niya inno ta taho da ita so take  mustapha da maryama su sake su wataya
 
Sai na biyu wai a gaban kanwar kishiyarta za'a toxarta ta har wani ta jira ta fita ta kullo daki,.  
   lalle inno bata san ko wacece ni ba sai nayi sanadiyar ruShewar farin cikin gimbiyar taki,
Kuma mustapha ne tunda kika bari na aure shi ai zance ya kare,
Ko ta nan na gama da ke,
Shiyasa duk wani tijara baya damuna,
Ta gama zancen zuccinta ta tashi ta nufi gidansu,

Da ashariya ta shiga gidan tana ta zage zage, ala tilas sai taga bayan su,
   Uwar ta ce waya taba min ke uwata!???
  Ta koro  mata bayani yadda sukai da sirkarta,

"  Ke ina ragan musu ne fah dalilin haifayya amma yau sun tabo ni tunda suka tabo uwata,
  Sholi zo ki kari sa min girkin nan ke kuma miko min mayafi na akan kofaa,"
    Sun gurfana a gaban dan tsubbunsu aka koro mishi bayani tiryaN tiryaan
  Yayi shiru can ya ce
   " Ba za mu iya samun kan kishiyarki da sauki ba,
Saboda bata wasa da ambaton Allah,
    Kinganta nan duba ya nuna mata kwarya mai dauke da ruwa sai ga maryama  ta ubayanna amma dishi dishi  tana zubawa Mustapha Abinci,

  Ki lura kin ganta sosai garau,

"  Tace a'a "

    To ba  don ta rike littafin Allah da Addu'ou'in safiya da maraice ba,
Da yanzun nan ba sai anjima ba zan gama da itaa,
To tana da hirji tsakaninta da duk wani iblishi,
   Dama dama mijin ne ma to duba kigaa

Suka kara lekawa taga yana kan cin abinci,
Kin ganshi to duk abinda kike so na mishi yanxu zai same shi bari na dauko kiga "

ya
dauko tsinken tsintsiya ya sai ta goshen shi , ya dan taba sai kuwa suka ga yana sosa wajen
   To duk abinda kike so zan mishi yanzu,
   
  'a "a banda shi gaskiya""
Uwar ta watsa mata mugun kallo
Xo miye ina uwar sace take nuna  miki tsantsar  kiyayya kuma da shi ta dogara ai kawai a kau dashi kinga uwarshi ce da asara,
Ita kuma maryama jego ne a gabanta,
Kinga kina gama takaba ki sheka aurenki,
   
a'a mama babu batun kisa ko jinya bana son a sa mishi saboda ina son shi,
Kuma idan na cutar dashi kai na na cutar,
Kuma yadda nake ba sana'a ba  karatu, kuma  bashi da yan
Uwan da zasu tallafi yaran ,
a'a ni dai ya tsaya akan maryaman
  
Kaga sha sha sha wai ke soyayya ko  ba kiyi halina ba gaskiya domin da kinyi halina baxaki yi wannan tausayin ba
Miye soyayya ??
  SoyYyar banxa ,
Ke soyayyar ma kaxa kaaxan ubanta,
   Kuma karyacee,

Ya katse su,
  "Miye abin yi kuna ta musu,
  
Kasan yadda zakayi da matar shin to,

  Uwar tai zuciya  fuuu ta mike

  Bokan yace inaga zan tura dan sako yayi ta fakonta tana fara Al'ada ba kowa yake nutsuwa ya yi addu'o'e ba,
Zan ai watar zan sake mata jini da kurajee a gabanta,
amma idan aka samu akasi zance zai kwabe.
   Ta ajiye mashi kudi ta miki
amma nifa yau nake. Ranka ya dade don na huce haushin.

To kunsan kana naka Allah yana nashi e abin mamaki ko da yake hausawa suka ce TSAFI GASKIYAR MAI SHI ya cigaba da kulum botonshi,
   Yayi ta tsatsube tsatsuben shi aakan wani kadangare wanda ya kasance kafirin Aljani ne da ya sadaukar da kanshi wajen cin zalin bil adama,
     Bokaye da masu tsubbu sukan yi amfani da aljanu su tura su jikin bil adama don su cutar dasu wasu asa musu hauka wasu jinyaa da za'a gagara gane kanta,
Da dai sauran su,
Tunda su Allah ya basu dama suna sauyawa zuwa kowace irin halitta.
   Ba abinda zai yi hirji a tsakani  ko ya  tsare da  irin wadan nan Aljanun sai addu'ouin kariya musamman na safiya da maraice da akeyi,
  
  Maryama ta kasance bata wasa da ambaton Allah ,
Musamman su

Bismil-lahil-lathee la yadurru ma'as-mihi shay-on fil-ardi wala fis-sama-i wahuwas-samee'ul-'aleem. 3
Da
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, yuhyee wayumeet, wahuwa 'ala kulli shayin qadeer * 10
Hasbiyallahu la-ilaha illa huwa Alaihi tawakaltu wa huwa rabbul arshil Azeem
*7
Bata wasa da wadan nan ukun ko bata ssamu nutsuwar yin azkar cikakke ba sai tayi su,
  Ana cikin halin nan  ne mustapha ya tafi sallar magrib ita kuma maryama ta idar  da tata sallar tana lazumin a dakinta  Ameera tai sallama ta mika mata farhanahh,
    Tazo fitowa kenan daga daki taji ta taka wani abu mai kurzunu kurzune,
   Da taga kadangare ne sai ta daka tsalle,
   Tasa ihu,

Ya watsa mata wani. Bakin abu a da ya fito
Daga  bakin shi,
  Maimakon tai addua sai ihu,
Kafin kiftawar ido kuma ya bace,
  Maryama ta fito rike da casbahaa a hanunta
   Lafiya Ameera???

   Ameera  ta nuna mataa,
  Aunty zafi yake min duba ki ga ta hau tube wando abin mamaki sai ga wasu irin jajayen kuraje masu girma,
Maryama ta hau tambayarta,
  Ameera tun yaushe kike fama dasu ?? 

Aunty ni bani da su,
Yanzu dai naji zafin,

wani abu ne kamar kadangare na gani a bakin kofar nan ya cije ne ya watsa min wani  bakin yawu
Maryama tace"
,
   YA SUBHANALLAH!!!
  nan kofar dakin ???
   Ehh sai susa take,
  Kinga tsaya na kira babanki mu tafi asibiti,
    Ashe kadangaren ya dade a makale a kofar dakin akan idan taxo fitowa daga daki sai ya watsa mata wannnan dafin daga nan sai kuraje su feso mata kuma jini ya yanko mata to Allah da yake AL MUS-SAWWIR NE KUMA MUDABBIRUL UMUR wato mai cach -canza Al'amura sai yayi TASRREEFIN ( juyawa) zuwa kan  yarta
  
Suka dunguma zuwa asibiti akai iya bincekin da akayi ba'aga musabbabi ba,
abinda ya daure musu kai ma ba kamar ya jinin da suka gani yana zuba mata,
Ba kuma na period ba,
Suka dai basu magunguna suka juya gida abin tsoro,
  
Maryama ranar gagara bacci tayi tsabar tsoro,

Mi zata ce?
An. Bar mata yara ga damuwa ta afku,

INNA LIL-LAHI WA INNA ILAIHIR-RAJI'UN
  take ta nanatawa,
        baban Auwal ya sayo pad aka makala mata a jikin pant ga kuma zafin kurajee
   Maryama a tsaye ta kwana ranar saboda tsabar kukan da Ameera takeyi,
  Ga farhanah itama kukan dare,
  Tai ta zuba ruwan dumi a baho da  gishiri a haka har ta samu tai bacci,

   .to miye na kukan maryamah???
  Ta fada cikin shi tai mai isarta tukunna,
" Baban Auwal mi zance wa uwarta idan ta dawo??
Baka tunanin hakan zai zama abin zargi?
   Kuma gaskiya ina tunanin hidimar nan kamar akwai ture a ciki,
  Ki fawaalawa Allah komai shi zai warware mana komai ya bata lafiya kuma,
In sha Allahu

Tace in sha Allah.

    Gari na wayewa delu makotan gidan inno ta shigo mata kamar yadda ta saba kunsan tunda inno tana da farcen susa dantaa yana taimaka mata bata rabo da mutane musamman da yake mai kyauta ce,,
  Ga son ciyar da mabukata,
" Inno ni kuwa dai naga surkarki jiya da mahaifiyarta  sun fito wajen malam na  bayan GULBI,
Uwar a gaba ranta a bace sirkarki  na binta a baya.
  " Delu mai hali yana barin halin shi ne???
Ai a haka zasu kare Allah zai kare mu daga sharrin su,
   Sai  ga wayar maryamah tana kuka,
    Ke duba min sakarci ya za'ayi ki kirani kuma kina kuka,
  Mustaphan ne babu shi?
  Ko hafsatun ko su Auwalu??

Da kyar ta fadawa inno abinda ya faru da Ameera,
Ta kara sa kuka inno damuwata bazan fita ba,
Kowa zargena zaiyi

  Ji batun banza don Allah kwantar da hankalinki
  
Delu kinji ko??? To ƙullunsu bai yiba bara na aike ki gidansuu ki fada musu yarta bata da lafiyaaa kaikayi ya koma kan mashekiya.
   
MarYamah tace inno ban gane ba,
  
Eh koma minene mugunta sukai niyar yi ya koma kansu,

Ina mustsphan???
Ki ce ya kira ne,
  
Kai haba inno nifa ban yarda da wannan amma kisan miye ?? So nake gari ya waye sosai zan canxa mata asibiti ko zasu gano miye matsalar,

    Yaro yaro ne,
Yaro man kaza na fada maka magana kana ja dani to ka gwada zuwa wajen masu magani mana ka gani,
  Ko kuma tunda gobe zaka zo ka taho da su har maryaman naga hankalinta ya tashi.

UDUTH suka nufa nan ma akai ta gwaje gwaje suka ce gaskiya basu ga komai ba,
Amma dai suna basu shawaran tsaftace makewayi ana lura da panties dinta sai aka basu cream wanda za'a shafa mata,
    "To dr jinin fah?
  Shekararta takwas ko? Zai iya kasancewa Al'adarta ce tazo mata da wuri, ba komai bane kar ka damu kowa da irin nashi,
   Cewar likitan

Kashe gari suka bazama sheme ba kunya ba tsoro Allah maman Auwal ta zo don ance mata Auwal yazo da mata da yarsa,
     
ta yi dace kuwa mustaphan ya fito suna tare da uban Amarya yana mishi bayanin matsalar da ta same su,

"Ba komai kwantar da hankalinka ; chan wajejen unguwar makera akwai wani malami zai warware mana komai in sha Allah.

" Ba dai malamin tsubbu bane ko ??
  
Haba mustapha tun muna kuruciya muke tare ka taba ji ko ganina da irin wadan nan mutanen??
Malami ne na sunna dan izala,
      Ga can mai dakinka inaga taji labarin zuwanku ne ; bari na shiga gida nima.

Baban Auwal miya sami Ameeran???
  Hmmmm,
Ba sannu da hanya ko a jikinta,

" To Allah dai ya barwa kansa sani, munje asibitoci ba wani abinda suke ganewa,
   
To shin baban Auwal wai shi ciwon bai da suna ne ko mi??
 
Kusan haka, don kuraje suka fito mata da kuma jini,

  Kuraje  ? jini? Na banu wayyo
Wallahi bazan yarda ba,
 
Ta koma gidansu ta labartawa mahaifiyarta  komai, suka dunguma gidan boka,
 
Basu same shi ba,
Iyalan shi sunce ya tafi kankara daurin aure amma zuwa yamma zai juyo,

ARKILLAH KWATAS

     Kasimu dai yau hankali zai kwanta ya cika kwana bakwai, zai koma dakin unaiza,
    Ba laifi Amarya akwai iya girki ga tsafta ka kunya da kawaici, amma abu daya ya mata cikas rashin kasancewarta a cikak-kiyar mace
  
Ta bangaren zubaida kuma gani take kamar ya barta ne kawai saboda ta huta don ita mai karance karance ne kama daga na turawa dana namu na hausa,
  Ko da yake harda zuwan jinin hala,
 
Ta gama girki kamar kullum ta mikawa unaiza nata sannan na kasimu,

Auntynsu kinsan mi za'ayi koma da na babansun nan
  
Hala baki lissafi yau fah kwana na bakwai ai,
  
    Eh ina sane, na kara miki ne,
  Na kara muku sati,
  Kuma in sha Allahu zuwa gobe zan fara girki ai kinga jikin da sauki kar,.....
  Kai maman umaima kina ta fam a da O.R.S fah kar ki damu zanyi amma gaskiya batun girki  babansu yace na kawo mishi nan,"
 
    Eh bai sani ba amma idan ya shigo zan mishi magana,
      Bari naje nabar heater a kunne"
  
To dauki abincin mana??
    Ina zuwa bari naje to zan dawo,
  Allah sarki wai zubaidan tana haka ne don kar a ga zarmewarta,
    
 
Kasimu yana daawowa ya tadda abinci a wurin ta
   ""  miko min plate da ruwan wanke hannu naga tuwo ne ko??

   a'a baban umaima ba fah nan kake ba ita zubaidan sanda nace ta mayar sas-santa ta yimin dabara ta sulale,

    "Wai ko kin damu dani anya???
  Ace kwana bakwai amma  baki lissafi,
Kin bani mamaki gaskiyaa,

  Ina sane kawai dai na kara muku hutu ne na kara muku sati guda.........
  
    Haba ai baki isa ba nine nake da ikon yanke wannan hukuncin ba ke ba; amma ina sam bazai yuwu ba,
 
Har kana bazai yuwu ba baban umaima na riga da nayi mata magana don haka gaskiya bazan iyaba ko so kake ta fara raina ni,
Ko ta dauken mayaudariya,
Na mata magana kuma na sauya,
  a'a ba da niba,

  Kinsan Allah ki tashi ki je ki warware mata don ba da yawuna kikai ba"
    Yau nake ganin ikon Allah unaixa,
  
Ta kuwa haɗe girar sama da ta kasa " nifa bazata dauke ne mutuniyar banza ba"
     Ki cewa su umaima suje su kwanta ki yi musu addu'a.
Ina jiranki na ma fasa cin abincin,
  Babban abincin nake son ci yaxo naga ta gardama,.

    " Haka kace??
  Ehh haka nace ko ba abinci na bane?
 
  " Oho maka,
    Ta ja wuri kuwa ta matse,
  Sukai ta jidali,
   Da dai yaga bazata hakura ba sai ya mata dabara,
  To naji zan koma amma sai nayi,
  
Kayi mi??
  Ni baban umaima miye haka? 'a 'a banso don Allah,

    To kuwa zan fasa nima kije ki kwantar da yara nace miki,
         Ta dawo tana ta kumbure kumbure, tana cire kayanta tana kunkuni " haka kawai in ba jaraba ba kayi sati kana abu daya waya sani ma ko harda rana yi kake yi"
  Ehh koma sau nawa zanyi ina ruwanki,
  Bata san ya fito ba sai da taji amsar da ya bata,
   Taji zafin maganar shi wato ma zai nuna mata yana yin,
  To sai mi kayi sau dari ma mana a rana,
 
    Wai unaiza yaushe kika zama haka ne??? Ina fada kina min jayayya?

  Baban umaima Ka sani bana son yawan abin nan idan ina da ciki, ni wallahi ko kamshin jikinka bana son ji,
    Ai kuwa bai isaba,
Bazaki hana yiwa ajiyata binciken lafiyar shiba.
    Ya tashi da kyar ya kashe wuta don tunda ta fara cire kaya yake haɗiar yawo ta cika komai nata ya kara girma ga daukar ido,
Ya  rutsa ta a jikin wardrobe,
   Tai ta mamakin tun daga tsaye yake sarrafata kamar wanda yayi wata rabon shi da mace,
     Da kyar ya kaita gado,
   Surutu ba halin shi bane amma sanda yayi tsabar abubuwan da inna ta bata domin lokacin bata san da cikin ba ma;
Uwa uba ga ni'ema ta musamman da Allah ya ke yiwa masu ciki,

   Tasha Albarka yana ta yi mata zantutuka,
  Baban umaima don Allah ka tashi kayi wanka ka tafi,
  
  Gaskiya kiyi hakuri wallahi zan kara

Idan kika ƙi kuma  na baki kuunya yanxuu na kiraata  nace kin rike ni sai na miki kema adadin kwanakin da na mata har da na rana da muke yi..........

Comment