shafi na takwas

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
 
MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, Outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

0⃣8⃣

ليس الخبر كالمعاينة
GANI YA KORI  JI

A gaskiya wannan hadin kan naku yayi ai haka yana da kyau,
Ba matsala sha kuruminki,
Kuma na gode,

amma inane gidan maman hanipa ne kam ta aiko min da abinci, kin ganshi can a kwando,

Hmmmmmm
lalle wannan matar ne har ta aiko miki abinci?
lalle kin cire tutah!
   Ko?
eh mana matar da bata kula kowa a unguwar nan,
Haba?

ai bata harka da kowa a QUATER'S dinnan,
'' to miyasa?
Na shige su;

a'a gani take mu duk jahilai ne,
tunda bamuyi jami'a munyi bautar kasa ba, tsaganinmu da ita mukam sai kallo, hakan ma na banza shiyasa mu kuma muka ware kanmu a matsayin mu na wanda take kyama muke  hidimar mu da ita,
  UNAIZA dai sauraronta take yi,ta nazarin kalaman maman daddy da kuma abinda baban umaina yace mata
'' mata ce mai mutunci mai sanin ya kamata''
amma kuma taji akasin hakan a wurin yar unguwar,
Hmmmm kina nazari ko?
a'a
ai idan kika ganta ma zakiyi tsammanin  mutuniyar kirki ce,
Idan taga ke ba kalar ta bace  ta watsar da ke,
Ikon Allah,
Maman daddy taci gaba Allah ya hore mata girman kai,
Kuma gani take yi kamar duk duniya babu wanda tayi sa'ar miji sai ita,
Ke!!
Allah kuwa ke bari dai kiga na shiga gida,
Idan wani abin ma sai matan QUATER'S sun shigo
      to ba damuwa ina sauraronku

Baban umaima suka  dawo katifar babban gado  ya sayo da fridge da yake falon akwai tyles bashi da damuwar leda ko kafet musa ya gaji tili$

''to rago yaya akayi na ganka haka?
Aunty na gaji wallahi,
Ayya sannu   da gajiya  tunda muka iso ba hutu,
Gashi yanzu za'a kira sallar magariba,
Wallahi bari naje nasa katifar a daki sai na shimpida zanin gadon kafin a kira sallar ko zan samu ma nayi wankan?

To
  Ta shigar da kayayyakin amfani madafi su kayan abinci risho kalanzir omo harda soson wanke tukunya  ta killace su tsaf,
   Ta wanke kwanukan maman hanifa,. Da zummar idan akayi magariba zata bawa musa ya kai,
  Ana kabbara sallah QASEEMU ya kira MUSA suka tafi masallaci,

Da kyar UNAIZA ta samu tayi sallar magariba saboda KHALID da KHALIDA sai kuka suke mata, bayan da ta idar ne tace laifi na ne ban baku bakin zanyi tafiya ba

To nan gidanku ne ba bakunta muka zo ba,

Umaima mai shekara biyar tace mama keda wa kike magana?

da kannenki,

ana sallar isha suka dawo daga masallaci  sun samu yan biyu suna ta kuka
wai UNAIZA miya same su ne?.
wallahi baban umaima ban sani ba ko gajiya ne,
can musa yace

'' kin kuwa fada musu zaku yi tafiya?

Ina kuwa sai yanzu abin ya fado min, nake fada musu,

QASEEM yace musu''  wai musa har kai rike chamfin ne dakai,?.

yo yaya ba chamfi gaskiya ce,
ai ko unguwa ce ka fita baka fada musu ba sun ringa kuka kenan,
Amma matukar ka basu baki kafin fitar
lafiya kalau za'a fita a dawo,

Mtswwww to nidai ban yarda ba musa zaman gida ne kaima ya sa kayi riko da wannan chamfe chamfen,

   yauwa musa don Allah ga kwanukan makociyar mu nan zo ka kai mata,

to
QASEEMU yace umaima dai taci abin cin nan ko?

Eh taci inaga ai ba sai mun girka wani abincin ba ko ??
Bari musa ya fito muji,

Suka ji an doka sallama

baban umaima ya amsa yace shigo mana lado,
Suka gaisa ya mika mishi kwanukan abinci,

Ya karba yana godia,
Maman umaima ta fito daga daki hanunta dauke da maganin sauro,

''. a'a bawan Allah yanzu nake shirin bada kwanukam dazu ma akai  muku,yaya sunan ka?

Suna na zakari amma lado ake cemin,

ayya
tace ''kiyi hakuri baki tayi amma zata shigo ko zuwa gobe idan ta dawo daga aiki,

ba komai mungode, bari na dauko maka kwanukan dazu,
 
Ta dauko kwanukan da su daddawa yajin borkono  su kayan kamshi na girki, sai kuma su Aduwa da magarya, tace gashi wannan ka kai mata,

to ta gode, a'a mune da godia, ayi mata godia,
    Ya tafi,
Musa ya shigo,
yauwa ga can maganin sauro dauka ka fesa a daki,
sai kazo kaci abinci gashi an kara kawo mana,
Kai Aunty !
Allah!
Sannunta da kokari
  Kaga Baban umaima tuwo ne da miyar mirai oho?
''Na gani''
Gashi nan
Ke don Allah agushi ne,
kai
Haba
Haka yake kamar miyar waken suya,,
eh zahiri amma suna da banbanci a baki,
Ikon Allah na koshi amma sai naci wallahi,

Kinga tambayi mamana ko zata ci tuwon,
umaima zaki ci tuwo?
a'a mama na koshi?
yauwa uwata to zo ki kwanta,

WASHE GARI

Maman daddy ce zaune tana jiran shigowar mutanen nata sai ga T.J nan misalin karfe goma, da wata yar kabilu,
''Uwar dakina kina gida kenan?
Ina nan dan dunia,

Jiya na ganka shiru wallahi kuwa kinsan miye?
Ban samu na fita bane na kai barira asibiti ne
  Kinga vata wuri yanzu,
Yanzu aka gama mata wankin cikin wallahi, duk a galabaice take,
Ayya sannu yan mata,
MUBARAKA zo ga bakuwarki,
Kai ta daki, kisa mata ruwan zafi a babban tukunya,
to
Shi kuma tunda mubaraka ta shigo yake kallonta gajeriya ce amma ba can ba bata da wani kyau,bakace  mai faffadan hanci.

amma yanzu ta zama farar dole, maman daddy kullum cikin dura mata maganin nono take yi wai tafi son su ciko sosai yadda zasu na tsole idanun mazajen anguwan ,

  ( maman daddy mace ce mai son kudi tana matukar son kudi,  shiyassa  bata da damuwa ita dai idan za'a bata ko nawa ne to zata kwantar da kanta ta samu shiyasa oga T.J idan ya gama lalatarshi da matan banzanshi idan tsautsayi ya afka musu sukayi ciki yake dauko su ya kawo mata su, ta musu jinya ,
Ita kuma ya cika ta da abin kwadayi iri iri da makulashe, sai kuma abinda zata girka musu,
Musanma da yake ta kware da makirci,
Haka zata sashi ya kawo kaji a cewarta irin wannan jinyar anfi son mace taci kaji dasu madara ko kwai,
To kunga itama   kakarta ta yanke saka,
Tunda shima mijin nata malalaci ne baya tabuka musu komai,
Shima kudin shi a wurin yan banza yake kariwa'
Allah ya shirye su)

Kai kuma a ina kasamu irin wannan haka?

Hahhhaaa mi kika gani?
Naga kamar yarinya ce,
Wallahi irin yara kananan nanne da suka gama makarantar secondary da wuri,
Suka samu suka shigo jamia,

to kinsan kabilun nan iyayensu basu iya daukar dawainiyarsu,
Shiyasa su kuma idan sun shiga makarantun jamia'r suna da bukatu 
nan da nan sai idon sun ya bude musamman idan suka samu irinmu,
  Kai T.J baka da dama,
To miyasa baka amfani da CONDOM NE KAM??

A haba don Allah yana rake harka

Ko?
Eh mana.

Maman daddy tace mi zai hana kana dirka musu kwayoyin tsarin haihuwa ko Allura kam,

   tabbas kin kawo shawara hakan zanna musu amma zibar da cikin ai akwai hatsari,
Kinga kuma idan metrons dinsu suka fahimci ciki ne dasu koransu ake yi,

   to kinga yanzu idan ta warke zamu je a mata Allura kawai,

   Mubaraka oganniya ce sosai
Ta kware a manyace,
Domin maman daddy ta dorata sosai akan harka
T.J yace ''wallahi uwar daki kin hana mubaraka sakewa dani,

ni ban isa na hanata ba,
  To ai nasan kanwata ce babu abinda zan mata

ah kar ka damu nasan babu abinda zaka mata

    Mubaraka zo ki karbo kayan a mota,

  To

Ya fita maman daddy ta kirata ki kintsa ta dadda go mata rigar nono yayi chako chako kinga bana son kina daure mishi fuskar nan ki sake banda dai dogon harka,
Ki dai karbo mana kudi kawai,
Ta fesa turare ta fita,
 
T.J jarababbe ne lamba ta daya,
     Duk da matar shi tana iya kar iyawarta amma baya gani,
   Bai damu da tsaftar mace da kazantar ta ba,
Indai ta mishi to zai afka mata,
      Ba yadda barira bata yiba akan yayi aure ko nawa ne, yafi mata akan zunden da matan unguwa suke mata,

   Yace mata bai da halin kara aure

    A dalilin haka ya hanata muamala da kowa a unguwar tsavar dan iska ne rufe ta yake yi ta baya saboda kar ma wani ya shiga gidan ya kawo mata gulma,

    '' kanwata zo mana ni miyasa kike jin tsoro na ne kam?

ta wani rausayar da kai
''akan mi zanji tsoranka kai ba mutum bane???
    Yauwa ga can Almajiri yazo ya debi kaya a boot to yanzu bari naga ya zaro 10k wannan na uwar daki ne
ga dubu biyar na chinyere, ta karba duk a hannunta da yake dan duniya ne
Ya dauko 10k gashi wannan kuma na kanwata ko da abinda zata saya,
Ya soka mata a tsakanin  nonuwanta,
     nan taji wani yarrrrrrrrr a jikinta,

Ya lura da re:action dinta yasa hanu ya dauka tare da shafarsu ashe fa ba'a son ana sa  kudi a wurin ko?
  Ta gyada kai saboda darajar su ba,

Kinga bari na canza miki ma'ajiya ya dauki kudin ya zame wuyar rigar ya ajiye kudin tsakanin rigar nonon da rigar jikinta, ta rufe ido ji yake kamar ya sa bakinshi,

Nan  mubaraka ta lumshe ido tayi wata shegiyar mika

amma so yake ya bita a hankali duk da yasan itama A ce amma bai son lokaci daya  ya fara nemanta,

''Kar ki yadda kice wa maman daddy na baki kudin kinji?
  Eh naji,
  ''bari na shiga cikin kar tace wani abin ne?

  ba ma abinda zata ce,
Ta yarda da dani ai.

  T.J yace ina neman Alfarma don Allah
Ina jinka,wacce Alfarma ce??

  Don Allah ki na sake wa dani mana,
Wani irin sake kuma yaya T.J?

Ina son ki  ringa dan sakewa kina min hira irin na yan matan nan,

to yan matan har hira suke yi na daban?

  Eh mana?

To zan koya kenan
wai d gaske kike?

  Wallahi ban iya ba,
to zan koya miki

  Bari na shiga

'' zan dawo anjima duba chinyere cewar T.J

tana shiga maman daddy tace xo ki daura mana farfeson kajin,

  to Aunty ta miko mata kudin da T.J ya bayar na chinyere da na maman daddyn,
Ta mika mata dari biyar kisa kati,
Nagode
  
'' a zuciyarta tace na gama miki wahala ki ban dari biyar  zanyi maganinki,

  Sai ga maman Auwal da maman hydar, nan da nan ta shiga ta samu mubaraka maza ki rufe dakin nan kar yan sa idon nan su shigo,

  Ai na fara mata famfon fah,
Kai!!!
Sai kinyi ko ba poster
  Hmmmn
Har wani abinci  ta kawo mata ni kuwa na fara mata hannunka mai sanda,
Yauwa gwanda da kika  mata ai,
  yaya akwai kayan dunia kuwa,

Tab ba komai,
Don Allah?
Alkur'anin Allah,
Mu shiga zaku gani ai,

Kuma daga gani za'ayi tafiya da ita don idonta a bude yake,
Kai?
Tashi mu je
Suka fita kanta tsaye tayi musu jagora salam
Kanwata kina ina,
Na'am yayata
Gani,
Suka kalli juna
'' nazo maki da kawayenki fah

Ko yayata?

Sannunku da zuwa ,
Ga falon ba kujeru ku karaso,
    Ta baje musu tabarma,
   Basu samu  nutsuwar gaisuwa ba,
to ga mata masu hadin kai,

Matan ARKILLA QUATERS

mata masu hadin kai,
mata masu mutunta makota,
Mata masu son junansu,
In ji maman daddy

   Kai to sannunku da zuwa ina muku barka,

ta debo pure water ta basu aka gaisa sai ga musa ya fito,

Musa don Allah ga kwanukan maman hanifah ka mika musu,
inaga lado yana nan ai,
To'
Aunty.

Maman Auwal tace na shiga uku!
Wace maman hanifah?

Maman hydar tace' uwar yan girma kai mana kinsan yanzu taga bakuwa ai zatayi kokarin ta jata a jikinta,
Idan taga itama irinmu ce ba yar boko bace sai ta watsar da ita,

Maman Auwal  tace ''  shigiya ku kuke ji  wallahi,
Ai ni tunda na fahimci bata da mutunci ma na bar gaisauwar,

Maman hydar tace umm  to gulma dai va kyau ,

Amma ina randa nace miki naje gidan barkan maman intisar din nan?
mun hadu ai ,
eh nagane

Mijinta  ya kirata a waya  yace mata yaya akayi ta fita bata bar abincin  abokin shiba sai tace wai bata jin dadi ne,

  tana ajiye wayar tace ita ai ba baiwar su bace,

yaje ya jajibo wani bakauye kullum sai ta sa mishi abinci,
   Lah zatai abinda yafi haka
Kina ganinta kamar mumuna

Maman daddy tace ''ina ruwan lumbu lumbu wutar kaikayi''

Maman Auwal tace kina nufin ki ce maigidan nan dinne ba kauye?

lalle bata da mutunci,

Ke maman Auwal miye abin mamaki?

ni da   baki da hanci  muke da ita ko ranar da tazo tasa labulayen nan ina ji suna tadi da  munafikin Almajirinta lado

'' wai Aunty labulayen nan sunyi kyau kamar ba wa yan kauye kika sayo ba,
   Sai tace mishi ai lado wannan na yan kauye ne ma kuwa saboda  naji ance  duk yan  tangaza  gidadawa ne basu waye ba,
'' amma nikam Aunty yamin kyau
  Ina ji tace kaima ai bakauyen ne,

Ina dawowarka gidana ne ka waye?

Nidai kala bance mata ba,
Saboda nasan dani take yi,
Ko ita da take takamar yar kaduna ce nasan dole dai asalinsu bazai wuce  kauye ba,
 
UNAIZA tace ikon Allah ita kauyawa ne bata so,
ai kuwa maman daddy  duk asalin dan birni daga kauye yake,

  ''To GANE MIN HANYA MAKAHO YASO TSEGUMI''

maman Auwal tace idan kin ganta wallahi  kin fita diri maman yan biyu,
kin fita dadin gani,

Za dai ta nuna miki kodewar jiki, kuma hakan ma shawarace,

UNAIZA tai kokarin danne zuciyarta, saboda bata son ta nuna  musu  ranta ya baci bata san wasu kala bane GASKIYA CE KO KARYA CE???

tana cikin rudani:
  kuma kullun abinda surkarta inna take fada mata;
kafin  ta gasgata  magana ta dauketa   ta tantance gaskiyar lamari kafin ta dauka tayi aiki da ita,
saboda akwai mutane masu hassada.

Akwai wanda basu kaunar suga anayi dakai su raba ka da masoyanka su kuma su shishshige musu,

MATAN QUATER'S Kuwa ganin UNAIZA tayi shiru suka wani hada ido ala mun famfon da sukai ya shige ta.

  UNAIZA kafin ta dawo daga karatun jakin  har sun mike wai suna sauri mijin Maman Auwal zai dawo yana hanya domin kwanan shi uku kenan da tafiya

UNAIZA tace '' ban ji sunayen  yan kungiyar tamu ba,
  Ni sunana  Aseeya maman Auwal:
Maman zuhra tace sunana Aisha: maman zuhra suka gama gabatar da kai maman Auwal tace zamu dawo ina sauri ne  maigidana zai dawo,

''Ba komai Allah ya dawo dashi lafiya,
Ina jiranku''

Suna fita musa ya shigo,

Aunty wasu yan rakadi kika samu?
naji suna ta zagin wata,
Wallahi Aunty kinga duk naji abinda suka ce
Ba mutanen kwarai bane,
Duk mutumin da zai zo ya kawo maka maganar wani,
kai ina !! Ban yarda dashi ba  ki ga tunda muka zo take mana hidima, gaskiya ki nutsu takunna kafin ki yarda dasu,
Haka ne amma kaji wai babansu umaima ne ba kauye?
Suka ce ba,
Tayi shiru.

 

Maman Auwal tace
Wallahi zuciyata sai yankewa take yi,
 
Kai! kekam matsoraciya ce, ba komai wallahi,

anya kuwa bari dai kiga na karisa,

Shigarta gida  kenan taji tsayuwar motar Baban Auwal
a ranta ta gode  wa Allah tana cewa gwanda dana dawo da wuri.

Ya rangada mata sallama dama ba gwanar tarban maigida ba ce, duk da cewa zaiyi horn alamar ya dawo amma bazata iya taryo shiba,

     Sai ta lura akwati ne a hanunshi  yake ja, ta leka  domin ta ga Akwatin waye tasan wannan hatsabibiyar uwar tashi   zata iya turo mata yayan danginshi,

tunda  ta saba su zo hutu suna nade duk abinda tayi idan suka koma su watsata a dangi,
     AMARYA shigo,
Tuntube tayi zata fadi kasa ya riko ta
KUT MELESI!!!!!!!!!!
MARYAMAAA!!!!!!!!

  da gudu ta bankade maryama ta nufi gidan maman daddy tun a hanya take cewa
Na fada muku Aure zasu mishi,
Na fada muku auri inna ta mishi.....

Ta'aliki
Zaba
Watsa
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

Comment