shafi na hamsin da shida

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

   5️⃣6️⃣

Bayan kammala wayar unaiza da mahaifiyar zubaida suka ci gaba da tattaunawa akan yananin zamantakewa ita dai zubaida da yake bata faye azarbabin magana ba,
ita kuma unaiza a kowani lokaci so take tana dan janta a jiki saboda ta sake jikinta.
   Indo tana tsakani ta gagara samun wuri a wajen zubaida tayi iya kokarinta ta samu fuska amma abu yaci tura
Ana fara kiraye kirayen sallar magariba zubaida tai sashinta don ta gabatar da sallar Almuru
   Indo tai sallama wa unaiza
   Maman umaima dama so nake muyi  magana da fatan zaki bani hadin kanki,
  Unaiza ta  ce ina saurarenki

Yauwa dama dazu  naji kuna magana da iyayen zubaida akan  yaranki suje musu hutu to idan ke baki son su mu mana son su,
a wani dalili zasu ce suje musu hutu, salon a barbade mana su a basu shashatau,
Su kangare miki,
To gaskiya ki hana su duk salon munafurci ne,
Kinga idan suka fara jan 'ya'yanki a jiki sai ki sakankance kiga su masu son ki ne tunda suna son 'ya'yanki to a gaskiya ki kiyaye
Dabara suke son su miki
  " Kin gama?? Nace kin gama to ki saurare ni da kyau ina baki girmanki da mutunci albarkacin nasan kin girme mi ne, duk wani kullace kullace da kuke yi ke dah bello dasu maman daddy ba wanda ban sani ba shiyasa

To sai sun jen  ; idan baki sani ba duk cikin fadin garin nan na  birnin shehu wato  sokoto  bayan mijina da abokiyar  zamana zubaida da kuma Aminiyata maman hanifah  bani da wanda suka fiye min kusanci irin iyayenta don mutane ne masu mutunci dattako da yakanah, ba abinda zai sa su cutar mun da 'ya'ya a haka kawai baku da aiki sai kin son zaman lafiya, a rayuwarku baku son kuga ana zaman lafiya to ba magani za su musu ba ko shanye jinin su  idan ya so su watsar da gawar su;  ke nan har wani son su umaiman kuke yi,kar ki manta duk wata kutungwilar da kuke hadawa ke da dan uwanki Bello na sani kai kasimun ma baku so shi da zuciya daya ba inaga  yaranshi,??
  Lalle unaiza kar ki gayamin maganar banza mana fi mu son yaya kasimun kikai da zaki ce bamu kaunarshi to sannu tattabara uwar soyayya da ma bamu san asalin ki bane naga ina mahaifinki ne ya cusa mishi ke ya binciko a sihirce sihircen nashi  taurarin ya kasimu masu haske ne, ya hada auren ku don ya samu hanyar mallake shi da juya shi wata rana
 
Alhamdulillah kinga kuwa hadi yayi kyau tunda har yanzu daram ina nan cikin birnin zuciyar shi bai gaji da zama dani ya sallame ni na koma gidan mu na daga musu hankali na hana matan yayu nah da matar ubana sakewa ba
   Indo ta yunkura kenan sai ga MuSA ya shigo dakin

" haba Aunty unaiza miyasa zaki biye mutumin da kinsan matsayinsa dama

  " Musa kar ka kuskura ka fadamin magana idan ba haka ba nasa Bello ya min kasa kasa da kai,
  
Bismillah Aunty indo baki san da da yanzu akwai banbanci ba ko,
    Baba musa ba mutuncinka bane sa in sa da itaba ai ko ba komai yar uwarkace ni kuwa bare ce a cikin ku,
Nayi imani da Allah ba zan bari ki shiga tsakanina da mutanen kirki ba ba su ba ma tunda yarsu tazo gidan nan banga wani abin kaico a tare da ita ba balle iyayenta
  Kuma yara in sha Allah sun je an gama,
Ita kuwa zubaida ashe tun farkon fara maganganun indon duk a kunnuwanta tana idar da sallah ta manta da karamar wayarta a dakin unaiza,
Da yake sabon shiga jin wadan nan abubuwan ne ta koma daki sai kuka take yi an dora wa iyayenta kazafi,
Bata san kadann ta jiba indai sharrance sharancen dangin miji ne  ta gode Allah ma da unaizan basu da matsala da ita,

Sister a gaskiya zan gaya miki ki hakura da zancen zubar da cikin nan saboda wallahi mahaifarki ta illata idan muka kara sakacin nan zaki iya rasa ranki "

Mubaraka tai xuru zuru da idonta nan ne asibiti na uku da aka fada mata haka,
Ta saduda ta kokarta  ta taafi gida
Tana shiga tai cilli da jakar hanu .

To yaya anyi nasara ???

Ina duk bakinsu daya likitocin Aunty,

Ke dole fah yanzu na kira T.J yasan abinda kike ciki,

Gaisuwa rinta sha shasu ya biyo baya,
  To dai wannan karon kai hakuri kawai ka sai ragon suna,
Saboda duk asibitocin da mubaraka taje sunce bazasu zubar ba to kaga kuwa dole mu barshi don tsira da lafiyarta,

Ban fahimci inda kika dosa ba fah,
Saboda ban gane bayanin naki ba waye za'a rasa,

    " Kai T.J kar ka raina min hankali mana kace baka fahimci inda na dosa ba.
Da wa mubaraka take tarayya idan ba da kai ba,?
     Itace ta fada miki hakan to bari kiiiji na dade rabo na da bariki, Allah ya amshi addu'ar mata ta da iyaye nah kuma tun kafin nan na nisanta kaina da ita saboda ta ki ta daina shafe shafen mayukan nan Bleaching ni kuma Allah ya sani ina kyamar hakan musamman da fuskarta ta kokkone din nan,

    "  T.J Wato dai kaji zancen ciki ka fara kwana kwana to ni dai ba wanda nasan yana tarayya da ita sai kai,"

   a'a banda ni kadai kam,
Tunda mubaraka kam unguluce bata san na gida ba,
   Ita kuda ce bata barin haraam,
     
    " ka tabbata T.J zan dauketa mu zo gidanka ayi mai karewa,
  
" Aaikin bur inji tusa" ai matata tun ina tsakiyar harkallan ta sani bata taba daga min hankali ba sai Addu'a to don kinzo din ba wani abin tada hankali bane kun gane ina son ki matse ta ta fada miki gaskiya wata kila ma kanninsu daddy ne,
Tunda shima yana ban ruwa a lambun da ya haramta mishi,

Mubaraka da yake ta ranfo T.J yana son ya tuna mata asiri sai tai maza ta sa kara ta danke cikinta
    Yayar tayo kanta,
Lafiya kuwa??? Mi kike ji Allah yasa fita zaiyi da kanshi ma a huta,

   
Bata san duk bagaye bane,

    A can bangaren T.J yace lalle wannan mata kidahuma ce amma yau zan miki maganin kidahumancin nan
Ba abinda kika iya sai gulmace gulmacen matan mutane da gidan mutane, Alhali kina zaune ana kammale miki miji, idan kin san wata ai baki san wata ba ya lalubo wayar shi ya shiga ma'adanar vedio ya tura mata bakon al'amari,
  
Yanzu ni dai mubaraka kinji yadda muka kaya da T.J waye dama kuke tare da shi??
     Nifa karya yake min; kawai dai bai son a danganashi da shi ne saboda yana tsoron yin abin kunya,
   Amma waye in ba shiba

To ki kyale ni dashi ki huta zuwa gari ya waye sai mu tafi gidanshi; ke bari kiji ma wallahi idan yaki karba a cikin ruwan sanyi zai karba a dole kuma ki sani ki shirya kayanki a akwati ma  can zaki zauna har ki haihu,
 
  Yauwa kinga daga nan  matar shi  sunyi ban kwana don zaman su  dole  ya kare don baza ta yarda ta zauna da ke ba........
  Uwar dakina da dumi duminta,

       Ah Bello shigowa ba sallama miye hakan,??

  Yayi sakarai saboda ya saba ba sallama kai tsaye yake shiga kansu ba damuwa amma yau ta taka mishi birki,
  Idon shi yayi kan mubaraka,
    Abin mamaki tumbinta ya hango a cikin matsats-tsiyar doguwar riga,

   " Mubaraka je ki shafa toka ko zai sauka miki dama kema kinsan cikin ki bayason Alale miyasa kika ci,

    Bello yace " Kai uwar dakina yanzu duk wannan kumburin cikin wake ne??
     Lalle wannan waken na daban ne,
Amma jan wake ne ko?

   Ta basar kamar bata ji ba,
Miye Albishir din??

     Kinji zancen da naje Ya kasimu yana yi shi da Abokin shi mijin Aminiyarki maman hanifahh,
 
" Bello na lura raini ya fara shiga tsakanin mu makiyiyar tawa ce kake danganta ta da Aminiyata sai dai Aminiyar uwar dakinka unaiza,
    "" wa ni ita ta zama uwar dakina  ai naafi karfinta ina da irinki gangariyar uwar daki mi zanyi da ita?

Ga itama Amaryar kamar ta asirce ta kinsan  ko kadan taki yarda da maganganunmu  Aunty indo ba abinda bata yiba amma fafir taki yarda,

   Bani labari gulmar da ka kawo min

  Hmmmmm ki bari wallahi bana son fadi ma tsabar abin yana kona min rai wallahi ban san ina da hassada ba sai yau ,
Wai yaya kasimu ya samu kwangila na biliyoyin naira Aminin baban zubaida ya bashi  wai ya gina super market ashe gini har yayi nisa amma tsabar iya cin hatsi babu ko alamar  kudin,
    Kawai dai nasan yanzu zirga zirganshi ya karu  bai zama sam ashe yana chan wurrin gini har yayi nisa.
   ( To kunji fa wai dan uwa ne yake bakin cikin samun cigaban dan uwanshi Allah ya tsare mana zukata )

Cikin ikon Allah baban intisar Allah ya mishi fatahi abin nan da ake cewa dare daya Allah kanyi bature,

Ashe tun da dadewa tun suna yara babansu ya taba sayan share's yama manta bai kara bin ta kansu ba sai da suka ga shekaru aru aru sukai ta kiran uban basu same shi ba shine suka bi Address din shi suka kawo mishi arzikin shi har gida,
Abinka da namiji yaki ya nuna wa maman inti,

   Babban abinda ya fargar da ita sayan fili da yayi a gaba da Arikilla kwatas gini har yayi nisa sashen mutane uku,
  To mai hali baya fasa halinshi  ta fara kafafa da hura hanci sai STATUS sai habaici,
  A haka wata kanwar baban inti da taga status dinta ta bita ta Private take bata shawara, akan ta rage maganganun da take yadawa hakuri zatayi, duk wanda daama  za'ayi mata kishiya  jurewa take yi,
   " Kinga Aunty hakan da kike yi zai nuna kin damu ne, kuma kinga a haka har zancen zai koma wajen Amaryar ita kuma tace zata raina ki,........
     Amarya a gidan uban wa SHEMA'U????
   Ai sauka tayi a whatsapp din ta kira Shema'u
Kai Aunty kina son wasa wallahi abinda yaya har kayan uwargidancin ki ya nuna mana tare dana Amarya ki nuna baki sani  ba kuma,

  Haba ai Aunty Dazu muka dawo daga gidan Alhaji ibrahim dakin gari,
  Tsohon ministan sharia karki ga abin arziki

"Wai waye zaiyi auren ne?
Na shiga uku wai yaya bai fada miki bane Aunty subhanallahi ki ce anji mutuwar sarki a bakina kaat ta kashe wayar.
   

Shema'u ta sheke da dariya suka tafa da Hafizaa ,
Ya wani gagara gaya mata to ni na fada idan yaso sun  karisaa yau yasha tijara da fituntuni,
Aure kuma daram in sha Allah,

Hafiza tace shema'u muma talakawa ne amma 'ya'yan talaka basu iya samu ba ki ga fi'ilin da take mana don Allah kamar bamu san asali ba ta samu yaya yana rufa mata asiri amma sai sanabe iri iri yanzu shima zai yi auren yar manya yaga mutunci
Yaga kara,
Ta kira baban inti yafi abinda yafi  sai can ya dauka batai mashi sallama  sai hargagi da yake yi cikin firgici da daga murya 

Da yake dan dunia ne kuma dama a shirye yake da jin abinda yafi wannan ko a jikin shi,
  Ta gama kurari da barazane barazananta ko gezau,
  "To ki tanade su sai na dawo gida yanzu ina wajen aiki........"

Ya katse layin
   Jakarta  ta dauko ta zuba kudi ta rasa inda zata dosa sai ta tuno maman daddy  itace ibilishiya a unguwar tabbas ta san bokaye  zata rakata  wurinsu kuwa

Ta kuwa yi sa'a ta same ta a  gida,
  Bata ma lura da yanayin da maman daddyn take ciki ba ta hau koro mata bayani
Da yake abin nema ne ya samu ta tashi tace mata

" Kar ki damu duk da cewa ba dadi nake ji baa kwana biyun nan amma tashi mu tafi,

  Ba bata lokaci suka yi shatar adaidaita sahu sukai hanyar shuni basuyi nisa ba keke ya kife dasu abin mamaki kamar wanda akai jefa da maman intisar gefe ko kwarzani bata yiba sai. Tsamin jiki maman daddy kuwa ta kasa tashi ga mummunar rauni a kafa da yake ta fidda jini,

mai keken ma ya bugu sosai hannun sai lajau lajau yake yi,
Cikin gaggawa aka kawo dauki,
An kwashe su anyi UDTH dasu A & E aka kaisu likitoci sukai burus dasu,
maman inti nata sintirin su zo su duba su maman daddy suka ce

" yanzu  lokacin hutun mune ko mu din ba rai ne damu ba?
  Maman daddy ta bata number baban daddy ta mishi bayanin sun samu hatsari ne a hanya ba  tare da bata lokaci ba ya garzayo gwaje gwaje ya nuna ta samu karaya a kafa,
kuma dole tana bukatar karin jini
  To da yake mijinta yana nan da sauki aka kwashi jinin shi aka kai LAB
Daga karshe dai maman inti ta sulale tai gidanta saboda ta tsorata bata ji ciwo ba amma fah akwai firgici a ranta tace " ba sa'a,
Yanzu ni da na mutu a hanyar nan da shikenan na zama SHAKIYIYA nazo a banza zan koma a banza,
Alhamdulillah, Allah nagode maka da baka tozarta tani ba,

Allah ya so ta bai dawo gidan ya tarar bata nan ba,
   
ana jiran fituwar sakamako kenan mubaraka dasu daddy harda Bello suka iso,
   Gashi anyi dace likitan da yake on duty mutum ne mai izza da gatsali bai damuwa da wani irin hali majinyace sai shiga ba idan ya fada mishi sakamako ,

      Yana zaune a gaban maman daddy ya shigo da takardar Madam ba zai yuwu musa miki jinin shi ba yana dauke da cuta mai karya Garkuwar jiki sai ki nemo wani kuma muna neman jinin da gaggawa"

  Tashin hankali da ba'a saka mishi rana kenan kamar dirar yesu haka suka ji zancen
  A sukwane suka zabura maman daddy babu damar tashi
mubaraka bata dauki abinda zafi ba saboda ita tuni ta fara shan magani dama,

 
    Mubaraka kin cuce ni ki kadai nasan nake muamala dake bayan yayarki kin cuceni
 
Daddy kam fita yayi tunda yaji maganar likita yana kuka Bello kuwa yace sai yaji kwakwaf,
 
Kar ka kara cewa na cuce ka ka cuci kanka dai yanzu ma idan baka sani ba cikin da yake jikina ba na kowa bane naka ne,
Aunty sai dai kiyi hakuri domin ranar wanka ba'a boyan chibi
Ki ce kika sani a  hanya don na zamar miki  hanyar da zaki samu kudi da jikina Dana fahimci  gard'in abu sai na fahimci ba wanda yake zuciyata take marari da muradi  ba wanda zai iya debe min kewa fiye da mijinki saboda zatin shi da halittar shi ne nake marari shi kadai ne zai fi saurin kusar min da sha'awata shiyasa na yaudare shi kina fita yawun gulmace gulmace gidan makota nake mayewa gurbin ki a wajen shi,
Kar ki daurawa tijjani ciki ga mai shi,.......
  
    Maman daddy kam gwagwarmaya take faman yi da  numfashinta da kyar ta iya dai dai ta nutsuwarta damuwa uku lokaci guda,
Ga karaya a kafa
Ga cutar kanjamau,
Ga takaicin cin amanar kanwarta da mijinta,sai ta fashe da kukaa

،" mubaraka kin cuce ni kin nuna min cewa ke yar ubace nayi imani da Allah da cikin mu daya ne bazaki min haka ba.........

    Ni ce zan miki Allah ya isa saboda da kinsan cikin mu dayan ne tun farko bazaki mayar dani karuwar cikin gida ba,kin sai da min mutuncina,
Kinn lalata min rayuwata amma Alhamdulillah kin fara samun sakamako sauran na haife idan Allah ya baki kafar tashi ki  goya shi kuma kar  kuji da wai ina nan daram ba inda zanji zan zauna a karkashin ku na cigaba da rainon abinda na samu,
Ta fita tana hawaye,
     Baban daddy yace wayyo Allah dunia kenan Allah ka yafe min na bijerewa iyayena saboda aurenki Annabi yayi gaskiya da yace "" ka samawa 'ya'yanka uwa ta gari""

Haka zalika Annabi yace duk namiiin da ya samu mace saliha to tabbas ya samu rabin imanin shi ,sai ya nemi saauran""
Allahu Akbar kin cuce ni..............

  Ummu farhaan.

Comment