shafi na hamsin da hudu

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

5️⃣4️⃣

Haba baban umaima yaushe ka zama haka ne kam ???? 
    A zuciarta tace ko da yake yanzu ya auri yar jamia zata bude mishi idanu,
      Nifa gaskiya kana son ka galabaitar da ni ne,
  Kaje chan mana yadda itama marmari abin take yi,
Sai  ka kari shi jarabarka a can,
     haka dai a daddafe ta bashi hadin kai,
Ya tattara ya koma,
  To abinda ya bawa unaixa mamaki shine dama haka ne abin, mata su damu da idan miji yayi aure yana watsi dasu a koma kan Amarya ana ta rawar kafa, to indai haka ne itakam gaskiya kasimu ya sha bam bam da sauran maza,
   Yanzu kam ma sai take gani kamar yafi mararinta akan da gashi bakin shi ya bude ba kamar da ba, ko shi kuma kalar nashi fallin kenan ta samu dai tai bacci,
     Shi kuwa tun daga ranar bai kara bin ta kan zubaida ba,
     Iya kace dai su sha hirar su ta fahimtar juna,
   

Unaixa ce ta marabci maman inti suka gaisa cikin mutuntawa tana tambayarta  labarin mutanen saudiya ,
     Ai kuwa sun yi mana nisa yanzu,
     Ina ne wajen Abiyar zaman taki,
Kinsan yar unguwar mu ce gidan babana,
Ayya to taso muje na raka ki,
  Bata taba shiga ba, sai yau albarkacin rakiyaa
  Suka  gaisa a mutunce "wannan makociyar mu ne ta chan layin baya,
Kuma akai dace unguwarku daya wai makotan gidan kune",
   Ayyah zubaida ta shiga ta debo musu kayan biki da lemu ta kawo
Daga alamu unaixa ta lura maman inti bata da niyyar tafiya,
  Tace to maman intisar bari na koma sai kin fito ,
  Owk to ba damuwa maman umaima,

  " Yauwa sunana sa'adatu mai akwai amma an fi kira na da maman inti kamar yadda kika ji yar uwarki tana fada min nazo ne mu san juna mu sada zumunci duk da cewa ke ba lalle ne ki san gidan mu a unguwar ba,
  Kanwar babana ta taba muku aikin abinci baba shatu,
   " Lah nasan baba shatu ance ta rasu ko??
  
" Eh inaga kusan shekara biyar kenan ma,

Allah ya mata rahama,
  Ameen Amarya,
  " Idan kina bukatar abu ko kina son a miki wani kamar dagan tasshi ( borkono ) sai ki aikamin zan bawa masu yi don yanzu nasan ke sabuwa ce baki da kowa a unguwar,
Duk da cewa ma abokiyar zaman ki bata da matsala bata da damuwa don duk unguwar nan ita kadai ce akaiwa kishia salin Alim ba hayaniya ba hargowa,
  Amma dai yana da kyau kema ki samu naki a kusa tunda itama tana da mutanenta da suke mutunci,
  Bari na fada miki kinga unguwar nan akwai matsalar gulmace gulmace xa suyi ta zuwa miki amma ki yi hattara kinga ko ni da kike gani irin uwargidan ki ce, bata shige shigen gidan mutane,
  To unguwarce yawanci 'ya'yan matsiyata ne ba su da komai,
To nami zaka biye su kai ta muamaala dasu ba amfanuwa zakai da tarayyar ba,
   Tarayya talaka da talaka ai ba riba,
Kinsan hausawa suka ce " KO WACE KWARYA DA ABOKIN ƁURMIN TA"
  To ki kiyaye,
Zubaida tace in sha Allahu,
   Ta rakata kofar unaixa sukai sallama ta tafi,
    Zubaida tai tsummm tana tunanin maganganunta,
    ( Ba ribar alaka tsakanin talaka da talaka,
Mi za'ayi da mu'amala da talaka )
  Kai akwai alamar su'ali a kanta,
Amma dai yadda ta fahimci ba munafuka bace shine rashin aibata unaixa da tayi,
Babancinsu da maman daddy,
Ita wannan mamam inti daga gani yar karya ce, tana son rayuwar yan karya ace dole itama wata ce kuma yar gayu ce,
   amma dai zan bita a hankali

Al'amarin kwangilar kasimu  kuwa yana nan yana bin komai a hankali  tare da shawarwarin  Elfah,

Ya bashi shawara sosai
" Kar ka kuskura ka taba kudin yanzu domin gaba daya ido yana kankaa ko 'yan  wajen aikin kuma,
Musamman yadda kace min suna ta cece kuce a wajen aikin ku, auren jari kayi saboda dukiyar ubanta ko kuma 'ya daya Tilo a wajen ubanta to duk gatan dunia za'a mata da wanda ya aureta saboda haka yanzu ka maida hankali kan aikin kawai an samu filin ne yanzu??
     Eh mun tafi chan hanyar Tangaza mun duba fili,  sai kuma chan wajajen Kangiwa polo club shima mun samu fili to dai ina jiran engineers da Town planners   din  su zaba mana inda yafi sai mu dauki daya a fara,
    Yauwa hakan yayi dai dai
Yaushe ne yace maka za su zo din??
     inaga kamar zuwa gobe za su iso sai a fara,
   
Wallahi mutumin yana da kirki sosai ga saukin kai,
 
Ai kuwa kasimu,
Kaga nima da ya kira ni batun kayanshin nan  ko a jikin shi,
  
Kasan waye shi kuwa Elfahhh???
 
  ( Waye SULAIMAN BARƘINƊO )
  
Haifafen garin Adamawa ne cikin jihar yola,
Kowa yasan cikin garin jemeta wuri ne da fulani ne ni tsagwaron su suke zama a wajen
  Alhaji sulaiman ɗa ne na goma cikin jerin 'ya'ya yen Alhaji Isi'aka barkindo,
Yana cikin jerin masu kudin jemeta domin shanayen su suka siyar suka fara kasuwanci,
Har ya zama sun fara barin jihaa ya kasance sun tsunduma a harkar safarar mai suka bude gidajen mai tun  suns yi iya  makotan su irinsu Taraba gombe maiduguri,
To daga baya da abin ya bunkasa duk fadin nigeria babu inda basu da branch kai har makotai irinsu  chad  niger cameroon suna da rassa,
   To duk cikin 'ya'yan Alhaji sulaiman ne ya kasance zakara wanda  tsabar gaskiyar shi da rikon amanar shi yayi fice a cikin su, domin sauran ko karatun kirki sun ki maida hankali suyi, suna tutiyar mahaifinsu mai kudi ne kuma ya tara musu, suna ganin su tashi su nemi ilimi bata lokaci ne,
Alhaji is'iaka yayi kokarin yaga wadanda suka ki karatun ya daura su akan kasuwanci, amma ina sai cin amana ya biyo baya, karshe dai ya gaji ya zuba musu ido,
Shi kuma sulaiman da yake yana da himma ya sa shi makaranta, bayan gama bautar kasar sa ce ya kira yan uwan gaba daya,
Ya danƙawa  sulaimanu gidan manshi dake jihar kaduna kyauta tare da takardun mallaka da yasa aka maida sunan sulaiman din,
    Shi kuma yayi hakan ne don sauran su hankalta suyi zuciya,
Amma inaa sunyi niisaa basu jin kira,
  Shikuwa ya tattara ya koma kaduna a lokacin kasancewar dama A.B.U zaria yayi under graduate din shi, don nan ne ma  yace min suka hadu da bagudo dakinsu daya,
To zama akayi na mutuntawa kasan fulani da wayo suna da kudi amma basu nunawa kuma shi mahaifinsun mutum ne da bai almubazaranci da dukiyaa akwai tattali akwai kintata,
  Sai ya kasance  rayuwarsu saffa saffa suke yinta,
   Idan abin hannun shi ya kare kafin a turo mishi sai sirkina ya dauke mishi komai,
  Da yake shima iyayensu masu hannu da shuni ne kuma sun sau mishi kudi bayan haka sun koya mishi kasuwanci da dagaro da kai,
Bi ma'ana sun nuna mishi hanyar sare sare, musamman bayan sunyi hutu maimakon ya tafi kebbi  sai ya juya  joss ya yi sare saren su doya dankali plantain da sauransu kasancewar na wahala a can wajajen Tunda su wajen su sahara ne,
   A haka har wata rana yace wa  sulaiman " kai ma fah ya kamata ka fara kasuwancin nan, bai kamata a matsayinka kana jamia sai ka jira iyaye ba,
  Duk da dai kuna da rufin asiri daga yanayinka, amma dai ba'a dogara da kudin uba ko wani,
  
" To Abokina in sha Allahu zan musu magana a dan turo min wani abu idan yaso na fara gwadawa,
  a'a sulaiman kar ka damu yanxu idan mun gama jarabawa mi zai hana ka tsaya a kano ka sayi abinda kasan basu da shi a garin ku,?
   " Ehhh toh nagode da shawara in sha Allahu zanyi hakan,
  Allah ya bamu sa'a,"
Ba bata lokaci kuwa aka gama jarabawa  sukai niyar tafiya gashi ba'a turowa sulaiman kudin da ya  bukata ba,
   uban yana ganin duk shirme ne,
  Ga arxiki a gidansu sai ya koma wani fannin,
     Da yake bagudon kamar yadda Barkindon yace min mutum ne free
  Ya dauki kudi ya bashi yayi sare saren,
Shi kuwa barkindo ba girman kai ya karba  zuciar shi fal da farin  ciki, duk da yana boyewa bagudo sahihin asalinshi kasancewar gari ya banbanta ga kuma Tazara tsakanin Adamawa da Kebbi,

Allah yasa mishi Albarka abu ya bunkasa daga chan yola idan zai dawo kuma ya sari jarkokin manshanu  haka dai rayuwa ta mike,
Bagudo bai san waye barkindo ba sai lokacin da yazo mishi da bashi kyautar gidan mai da babanshi yayi, kuma yana gayyatar shi su zo su fara aiki a wajen kafin Su samu yadda suke so,
To kunji asalin alakar su,
A haka suka koma sukai post graduate daga baya mahaifin bagudo ya sama mishi aiki a sokoto ya dawo shine sukai kokarin bude wani gidan man a sokoto,
  Kunji bunkasar arxikin su kenan
   ( To zaman arxiki kenan,
da kowa Allah ya haɗaka kar ka nuna mishi izgili ko ko shi bashi da shi ba ka san waye shi ba,
Inma shi ba komai bane baka san  mi zai zama nan gaba ba, _ ( MUTUNTAWA DA KARRAMAWA NA DA MUHIMMANCI A RAYUWAR DAN ADAM_ )
   Kaji takaitaccen bayanin da yamin,
Ya ɗora da cewa ba abinda yake sa shi farin ciki irin yaga mutumin da yake rike amana,
 
Elfah ya numfasa yace Amana tai karanci kuwa a zamanin nan,
Allah ya bamu ikon riko da ita,

KATSINA
           SHEME
Mal Bukar modibbo ya kare wa Ameera kallo,
   Yace ina uwarta ?
   Inno ta nunata
   " Kina ji inason ki je ki warware kullin da kikai da kanki don gaskiya ba aikin kowa bane wannnan sai na boka na bakin Gulbi,
  Ta tubure ta hau surutai ba abinda tai aikata kawai kage ne, ta nuna Maryama ga dai wacce za'a tuhumaa ,
   " Haka kika ce???

   Ya debu ruwan Addua ya bawa Ameera ta sha tare
Da wani. Gora yace musu ɗibbin nabawi ne, da tofin ayatush shifa'e in sha Allahu za'a samu sauki shi wancan ruwan kuma in Allah ya  yarda shine zai karya dafin da Shedanin ya watsa mata,
Sauki kuma sai a hankali in sha Allahu,
   Mustspha ya ciro kudi dubu biyar ya mika mishi,
Mal modibbo yace"  sunyi yawa bada kudin wannnan dubu biyu ne Allah yasa a dace,
  Yace ke kuma ina tausaya miki matukar baki je kun warware ba, kiyi kuka da kanki,
  
   Maman Auwal Allah Allah take ta isa gida su koma wajen  na bakin gulbi ko ya dawo,

      Inno ta lura sam ba nutsuwa a tare da maman Auwal,
     " kinga dawo,

Ina za ki?
  zauna kinci albarkacin
    Jinyar Ameera ba wai don maryama baza tayi ba
Saboda jegon da take yi ne,
    To bari na dauko kayana,
a'a kiyi waya su kawo miki "
    Bata so hakan ba,
  " Kuma ki bar ameeran a dakina,"

   Ta rasa yadda zatayi ,
    Haka dai ta hakuraa,
  Chan da yammane  
Maryama da inno suka leka gidan biki,
Ita kuma maman Auwal suna zaune da Mustaphan mahaifiyarta ta kirata  akan ta dawo mana suje,
ta aika ance musu ya dawo,
    To dai da yake shima yana amsa waya ce bai fahimci mi take cewa ba,
   Gashi ba dama ta saci jiki ta fita,
  
  " Ki je kawai kya min bayani,"

   
Ba  bat lokaci mahaifiyR maman Auwal  ta garzaya wurin    na bakin Gulbi,
  
Tana shiga taji ya fara mata wakar da dr muhammadu mamman shatab katsina yayi cikin:

    # ku gargaɗi Mai gina ramin mugunta #
   Har yazo inda yake cewa
   
*To ka gina dai dai kwabrinka
*Watakila kai ka fada  ku gargaɗi mai gina ramin mugunta##

ai na fada muku ba'a gaggawa akan masu ambaton Allah kun yarda da abinda na fada muku ko??
  
Ba fa bamu yarda bane,
  Kawai dai yanxu mun dawo ka warware mana salin alin jikanyata ta samu lafiya,
   
Yayi wasu ɓoyayyun maganganun shi
  
" Allah ya huci zuciarka, na bar zancen,
 
Tofa akwai matsala gaskiya
Yace baZai yuwu ba matukar kuna son yarinyar ta samu sauki to sai dai ya koma kan uwarta,
 
" Kan uban nan karyar ka tasha karya mushiriki la'ananne jinin lamarudu,
   Ka isa kayi aiki kace bazaka warware ba wallahi karyarka tasha karya na gaya maka azzalumai ashe ma karya ne aikin naka tunda dai bazaka iya warwarewa ba,"
 
A fusace ya mike ya yo kanta kamar macijin kububuwa,
  
" Zaki san karya nake yi,
Zaki san aikina karyana ne
  Aikina baya yuwuwa ya fada kan jikNyarki??
  To xaki shaida cewa ni nafi lamRudu rashin imani inaga sai dai muxo kafada da Fir'aunan zamanin Annabi musaa,
      Kuma daga ke har yarkin sai kunyi nadama.
        Ta wuce fuuuuuu ta fice,

  Ikon Allah baya  karewa
  Shigarta dakinta  ke da wuyaa tai arbaa da kadangare kafin ta ankara ta suntumi abu ta kwada mishi ya mata feshin dafin shi a idanu nan da nan ta taga duhu da kuma wani  abu  da yake sauka mata daga gabanta,
       A dai dai lokacin da ita kuma maman Auwal wasu irin kuraje da suka fi na Ameera girma  suka bayyana mata lokaci guda tare da jinin itama,
      Dama mustapha na zaune gaban Ameera ya gama bata maganin kenan juyowan da zaiyi sai yaga abin mamaki,
    Cokalin hannun shine ya faɗi kasa,

   Mi nake gani???

   Zubur ta mike sai ga jini yana bin kafarta,
Yana juyawa kuma yaga Ameera garau da ita ba ma alamar tabo.
  
Waya ya dauko  ya kira maryama su taho ita da  inno,
Shigowarsu dai dai da zuwan kanin maman Auwal,
  A kiɗime ,
    "  Kai lafiya ba sallama ka shigo gidan mutane??
  ,( Inno uwar masifa bata bar na gida ba balle bako,
     Mustapha lafiya ko jikin Ameeran nee..........
  
Laaa ha ilaha illal lahu muhammda dan Audullahi mai sunan maza rasulillahi,
  
Ɗan  aiki ya dora da cewa"  dama  mamace bata da lafiya idonta ya rufe bata gani ga jini yana zuba mata,
Tace wai kadangare ne ta gani ya tofa mata yawuuuu..............

Comment