shafi na talatin da takwas

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈBAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATIONπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ
( BAHWA πŸ“)

_(Matattarar zaΖ™aΖ™urai, haziΖ™ai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)πŸ‘ŒπŸ»

3️⃣8️⃣

INNO A ARKILLA

Bata sha wahala sosai ba da yake da bello suka taho,
Haba murna a wajen su ba'a magana babban farin cikin inno yadda taga unaiza ta murje ta goge bata sa tashin hankalin karin auren kasimu a ranta ba ga jikokinta fess tunda ta sauka umaima ta makale mata,
Abinda ya bata mamaki bai wuce maganar da umaiman tayi mata ba,
Miya sa kika dawo da Baffah Bello kullum sai yana zare mana idanu yana rankwashe na wai ina da gwala gwalan idon irin na mamana,
Kaka miye mayu?
Mayu sune masu manyan idanu?
Ke haba duk kin cikata da surutu don Allah ki barta ta huta mana,
Kin fiye magana wallahi maza zo ki dauki zige-gen maman su hanifa ki kai mata kice mata kaka ta iso lafiya,
Daudawa ce mai kyau irin ta BUNGUDU mai zaki da kamshi, sai su kubewa kuka kifi banda harda man shanu,
Kai unaiza kayan bai mata yawa ba??
Ki bawa Bello mana ai ya mata yawa,
Uhmmmm ban ki bama idAn musa ya dawo Bello kam bai zuwa gidan
To bata marar nauyin ta kai mata,
Hala ita ce maman daddy??
'a'a wannan fa matar faruku ne dan Dauran nan wacce nake baki labarin tana min sare sare kayan sayarwa,
Ohooo kice min wanda sukai makaranta tare,
" Kwarai itace"
To shi kuma wannan wa ya samu wai maman daddy tun tasowar mu naji yake mata waya,
Uhmmm irin mutanen shine.
Kar ki damu kita hakuri dasu,dama ba'a bata girma haka siddan ba sai an samu kalubale ta kowacce irin siga ki xama mai hakuri yanzu ne zaki kara sanin masoyinki da makiyinki, kar ki kuskura ki zubda girman ki da martabanki, ki tafi akan halayenki da kika taso dAshi ki kara jajircewa shi kanshi kasimun sai kinyi hakuri don ba waliyyin Allah bane ba kuma ba mahasumi bane,

Ba ruwan ki da daukar zugar kawaye ba ruwanki da hidimar kawaye ba ruwan ki da makota duk da cewa ba sabo kikai dasu ba amma ki kara dagewa yanzu ne zaki gamu da mai sonki da marar sonki,
Kar ki ga zai auro 'yar manya sai kin so ki zubda kanki ki bada kanki,
Ki rike girmanki kar ki kuskura kiiyi abinda zata raina ki, kice babba kice kika san waye kasimu, Kinsan abinda yake so kinsan wanda baya so, kuma abinda kike so yayi shi zai yi matukar kika rike kanki,
Ta zaro takarda ga shi wannan addu'o'i ne nasa a rubuta miki kina karantawa, in sha Allah indai kina yi ba zai ga ya ke ba kullum ganin ki zai yi kamar wata daren sha biyar hungo amshi karanta.
Tai murmushi tasa hannu ta karba ta duba taka dai addua ce da gaske ta sanya kauna da nutsuwa tsaKanin ma'aurata,
A ina kika samu wannan inno?
Saifullahi dan kawata da yayi a karatu a jami'ar musulunci ta madina shi naasa rubuta miki,
Tai ta godiya iya kauna kenan da inno zata nuna mata Allah sarki ko mahaifiyarta nada rai iya abinda zatai mata kenan,
Bata yanke daa al'amarin inno ba sai da ta ga kaya hilimi guda a gabanta,
Dauki wannan ki dunka wa umaima da khaleeda wannnan leshin da atampar ma naki ne,
Yauwa ki duba rigar nan ko ta miki tsarabar saifullahi ne ya kawo mana ni da mamar shi amma na gwada naga ya min yawa kuma na zamani ne wannan duwatsun sai ku yara,
Haba unaiza sai murna wallahi wancan satin naga irinsu a Algazaru amma kinsan mai tsada ce fah sosai,
Eh to yar nan abu daga garin ma'aiki kam ai dole yayi tsada,
Dauko wancan galan din tsumi ne dan chadi kurba ki ji dandanon shi,
to da yake unaizar ta saba kuma ta dauke ta tamkar uwarta ko a jikinta kai ai kuwa ya sha hadi,
Ki adana shi a firiji,
Wannnan kuma chukwi ne,
Ga shi malam yace a baki dubu goman nan kiiyi dinki,
Kai Allah sarki Allah ya biya ya jikan mahaifaa,
Nagode sosai,
Ta kintsa na kintsawa zannuwa da kudin ta ajiye sai kasimu ya dawo ta nuna mishi,
Chan ma shagon hoto na Baba musa wata amarya da ango sun zo hoton aure yaga wata shadda da aka hada da lace ya mishi kyau bai yi kasa a gwiwa ba ya tambayeta inda akai mata dinki,
Ta mika mishi katin shagon a ma'ajiyarta amma tace mishi haka ta saaya a dinke sai dai idan yaje shagon zai gansu iri da kala,wanda yake so,
Yana rufe shago kuwa bai zarce ko ina ba sai kasuwar shehu shagari yabi kwatancen tsab ya gane wurin,
Wai har ya rasa kalan da zai tsaba mata chan ya hango wata ruwan sararin samania da aka mata ratsi da leshi ruwan toka,
Abinda ya kara burgeshi harda na tsaran umaima a gefe,
Ya ja kaya gaskiya don da yayi niyar saya mata zannuwa kamar kala uku haka masu kyau amma yasan wannan ko ina ne zata shiga dasu da yuyuyu gwanda daya kwakwkwara,
Nan shima ya zabi shadda iri daya da khaleed yace an dinka musu zuwa wani sati,
ya ciro ATM ya mika musu suka zari kudinsu da zummar nasu sai yazo karban dinki zai basu kuma sun amince,

Da yake yasan satin bukukkuna ne in sha Allahu zan samu na sayan shaddar

*********************

Alhamdulillahil lazih bi niematihi tatimmus salihat,
Kai wafeeya gani nake kamar baza mu dawo gida ba,zaman asibiti ba dadi wallahi.
Ah to naso ace ki kara sati ma wallahi,
To muguwa miko min Mahmoud dina naga hannun shi kamar ba'ayi aiki ba,
Ah to ai nan akwai kayan aiki, " ikon Allah" inji baba
To na hada miki ruwan wankan
Baba ina cewa bai yi zafi ba don sunce baaYA baya ne,
Lah baba dama ruwa kika surka mata ; ayya kam kar ki damu wancan dakin glass din da kike gani fah na'ura ce ta nau'ikan ruwa da kike so kiyi wanda dashi,zo muje ki gani baba na koya miki ko na tafi aiki,
Ikon Allah. Yar nan wallahi gashi nan wannna ai tafasash shine, to bari na rage yauwa dama dama amma shima yana turiri
Ohhh zamani bature agaida shi
Hmmmm garin dAdi na nesa ungulu ta hango masaiii wannan inama ace a sanyi ne lokacin hunturu.
Tai wankanta ta kintsa tsaf suka fara vedio call da mutanen nijeria gwanin dadi kannenta sai tambya suke yaushe zasu dawo,
Ayi suna?
Mamanta ta karba ku rabani da shiririta ta dai samu saukin jikinta dana yaran amma zamu shigo jibi mu kanki,
babanku ne ya hana mu zo kuna asibitin domin hankali zai tashi ne,
Kinsan ashe yasan halin da kike ciki yaki fada min ne kawai,
ai ammi maza akwai dauriya,
To Allah ya baki lafiya,
Wafeeya tace kinsan asibiti ma tace ta dau nauyin haflar da za'ayi na sunan,
Miye hafla kuma?
Owk haflatul maulud: bikin suna sun turo ganin gidan ma ko zai dauki kawa da adon da ake son ayi,
Ke yarinya kinyi kudi fahh,
Oh mamakin tsarin kasar nan nake yi wallahi,
Sallamar baban triple taji,
Fuskar nan kunshe da walwala,
Baba sidisidi ta fice daya sashin,
wafeeya tana mishi tsiya ina abokin rakiyar taka??
Ya wuce zai yi wanka wai,
Kasan bai son wahala
Ke don Allah barshi ya huta baki ga yanayin fuskar shi bane a gajiye yake ,
kece kika san hakan,
Ya dauki lemun mangwaro ya shanye ya aji kwalbar,

Albishir !!!

Ya zubo mata takardu a gabanta ta dauka taga upper ce ya samu ta d'ako ta kalle shi shikenan sun rike ka, masha Allahu la kuwwata illah billah
AlhamdulillH,

Wafeeya dake da sauran 'yarinta a jikinta ta ringa tsalle tana murna wai yar uwa ta dawo kusa duk da cewa akwai rata a tsakaninsu da muhallin da aka basu,
Tune ta garzaaya tsakar gida ta sanar musu abin alherin da mijin bilkisu ya samu.
*********************

A gajiye ta dawo gida ta shiga madafi ta debo shinkafa ta fara tsincewa,laure ta shigo tace " mi zan kama miki ??
Lah ba komai ki barshi kawai ba wani abu mai wahala zanyi ba,

Sai jikinta yayi sanyi amma ta kudiri aniyar sai ta taYa tan don ta dau alwashi yadda iyayenta suka mata halarci suka sa mijin yarsu ya aureta,ba zata basu kunya ba,
Tasan Allah ne ya dubi lamurranta ya tausaya mata ya mata sakayya da samun miji irin imraan baYan azabtuwa da horon yunwa da tAyi a gidan tsohon mijinta,
Don haka ne ta sa wa ranta zaman aure zatayi,
" Lah to miko min kaayan miyan na gyara,"
Ta dauko anyi sa'a akwai wuta kuwa ta barza musu,
amma fah taji mamakin yadda kamshin sulalen nama yake tashi ko mi dami tasa ne ohooo?
Ta tashi da niyyar wanke shinkafar,
Nan ma tai maza ta karba " kawo na wanke,
Ba musu ta mika mata.
Ita ko maman salima tana hankalce da duk abinda take yi taga ta sa gishiri a wankin shinkafar,
Ta dauko mangyada ta soye shi da albasa tafarnuwa,
da warin tafarnuwan ta fita ta watsa cardamon guda uku da kwaya kwayar kanunfari,
M salima kar kice zan miki shish6shigi ya naga kin watsa kwaya kwaya ba'a daka shi ba?

Eyh kinsan a jollof so ake a ji kamshi shi, na kwaayar ba kamar idan zakiyi miya ki daka ba, shima Aroma daban yake bayarwa ,
ita kuwa tana ta bayani kamar wata gwana h a series din indiyawan nan ta gani,
Haba kan kace kwabo gida ya gauraye da kamshi,tana gama damuwarta ta shiga wanka domin ta
Tayi dukun dukun da jikinta, madafin ma komai da gindin shi,
Data juye abincin ko a jikinta ta wuce dakin,
Laure ce ta kintse wurin tsaf nan da nan,
Ta wuce ta iske salima har lokacin bata tashi ba,
Bayan tai wankan ne ta tuno xata hada zobo fah
Ta koma maadafin abin al'ajabi har an gyara tab ta tuno ashe fah ita ya dace tayi, tab ai kuwa dole a samu mai aiki don ba zata iya hada girki da aikace aikacen gida ba ta dai kokarta ta hada zobon ta mishi ado dasu cucumber yasha bawon abarba,
To dai yanzu jira take maigida ya dawo taji. Ta'alikin shi,
Ba laifi laure kam harda kari, sai santi take yi,duk don ta karfafa mata gwiwa taji dadi a ranta duk da cewa kayan kamshin da tai amfani dashi sun dan yi yaaawa shinkAfar ta zama ruwan dorawa sAboda curry da yayi yawa,
Ga shi ta sayo ga yen parseley tai ado dashi yadda take gani a series din indiawan nan,
Sai da laure ta kwashe komai ta fita ya ce mata""
Ya sunan wannan abinci da kikai mana ne mai kalar dorawa dorawa?
Tace indian rice ne haba kice kallon ki bai tashi a banza ba?
Yayi kyau sosai a ido a baki ma ba laifi, amma ki dan rage kayan kamshi,
Kara zuba min zobon shi kuma yayi dadi amma ki rage suga,
Ya dai zolayeta ita ko ko a jikinta,
Ta

*******$*************
B musa ne yaga kiran M umaima, da yake yana kan abin hawa ne bai dauka ba don a tunanin shi gidan zai wuce,
Ko minti biyar bai yiba ya kare sa yana shiga falon yayi kicibuss da inn,
Lah yaushe a garin inno?
Ta sau mishi murmushi
" Dazu muka zo da Bello"
Kai har hutun ya ishe shi,
Yazo gefen inno ya tsuguna ya kama hannunta bakin su yake rufuwa domin inno a rayuwarta ba ta yarda da wannan kawaicin mutanen da din ba shiyasa mama da yaranta suke mata habaici da mita, da yake ta tashi da sanin addini shiyasa bata damu ba domin tace a addini bata ga inda aka ce ayi watsi daa 'ya'ya ba, bare ita da duka 'yayan biyu ne,
Da gudu khaleed da khaleedah suka zo mishi oyoyo ya shafa aljihu ya manta bai sayo musu komai ba, suka narke mishi,
Inno tace ya haka? Yaya kai kuwa gida da yara zaka shigo sa lin alin,
Unaiza ta amshi maganar
" Wallahi inno bai taba shigowa zikau ba,
"gashi na gani"
Ta ciro kudi a ma'ajiyar rigarta hungo sayo mishi bisko,
" Bar kudin ki,
Zan sayo mishi"
Inno don Allah ki barshi ya huta ko ruwa bai sha ba fah,
Ba dan shi bane ?
Umaima kawo mishi ruwa,
Ya mika mata leda gashi nan gwada ki ga ko zai miki,

To mi na samu???
Ta bude ledar taga abin arxiki ai tsalle tai a gaban inno ta rungumo inno sai hawaye,
To miye na hawayen unaiza?
Inno ta tambayeta,
Ta goge ta ce" wallahi kaunar da kuke nuna min ne kawai,

B musa shiga dakin yayanku kaga abinda inno ta kawo min itama'
Ta duba riga ga nata ga na umaima, ta mikawa inno, inno ta washe baki; tai ta kwarara mishi Albarka, da adduo'in samun abokiyar zama na gari.
Ana haka sai ga sallamar maman hanifa da hanifanta da humairanta sun shigo gaida inno hannun rike da kwando tuwo da miya ne sai farfeson kan rago, suka mikawa unaiza,
Nan ta rusuna ta gaida ta,
maman hanifa tai godian tsaraban da aka kai mata,
Wai dama kun dadi da sauka ne?
Cewar B musa
Ai tun bai fi sha daayan rana ba,

To ba yanzu nake kiranka ba ; dama so nake na fada maka ashe lokacin kana hanya,
ai kuwa na dade da barin shago ina wurin sayan kayan nan,
Ta mika wa maman hanifa kayan B musa da ya kawo mata yanzu,
Su kai ta godia
Suna zaune sai
Ga Bello ya shigo ba ko sallama
ya zo kan B musa ya tsaya " da Allah bani yan makullan daki ka wani tafi kaje ka zauna sai kace baka san zan dawo ba,kuma ina abinci na,?? Ya juya ma unaiza,
Umaima dauko mishi,
Ki zubar dan ubanki nagani sai shegen rawar kai kamar wata yar tsuntsuwa,daina kallo na da idon ki kamar na uwa......
Tasss yaji saukar mari a fuskar shi ya juya yana tsammAnin Musa ne ya mishi walakanci a gaban uwar shi sai yaga ashe kasimu ne,
Inno kuwa sai cewa take a gabana Bello;
ashe abinda umaima take fada min gaskiya ne?
Kin gani unaiza har kina wani tsats-tsareta kar t a fada to gashi nan wannan bala'in da mi yayi kama?
Musa yace " wallahi haka yake mata cin kashi a gidan nan ita da yaranta, idan nace zan mishi magana ta hanani.
To ke miyasa baki taba fada min ba?
a wani dalili?
ban ajiye ku don ku takurawa iyalina bai,
Wani irin rashin kunya ne haka?kai bazaka taba barin halinka ba,

Nan maman hanifaa ta mike shi tsabar ranshi a bace ne ma bai lura da su ba,
Ya gaishe ta a tsaitsaye.

Tai sallama da inno akan zata dawo washe gari idan yara sun tafi mAkaranta,
Shi ko maras kunyar gidan maman daddy ya juyaa abinshi,
Inno ta rar-rashi kasimu " kai hakuri ba don shi zakai ba don mahaifinku zakayi"
Allah yasa su gane,......

Taku a har kullum

U.K.B
AZARE

Comment