shafi na Arbain

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣0️⃣

Washe gari baban hydar bai yi kasa a gwiwa ba ya gane kwatancen wurin mai taken AMIBISH TAILORING & CUISINE
cikin mutuntawa da martaba aka karbe shi mamallakiyar wurin haj Amina kyaky-kyawar bafulatana doguwa mai yalwar fara'a ta karbe shi,tai mishi bayanin abubuwan da suke koyarwa,.
Ta bashi menu dinsu ya karanta ya zaba mata fannin girki,
Duk da cewa da tsada amma haka ya biya, akan washe gari zai fara kai ta
Yallabai " na manta zaka hado da kananan hotuna guda biyu"
  Yace ".In sha Allah !
Nagode kwarai"

*********************
  
Lauratu ce a falo ita da 'yarta tana koya  mata sayyidul istigfari sai ta jiyo sallama baki ta rarumi hijabinta suka gaisa  ta miki don ta  kawo musu ruwa ,
Sai taji suna cewa ," oh kiga har rungumar 'yarta tayi abin tausayi ta rike ta zuciya daya; amma ita neman haukata ta take yi,
Ita ko ta rabe don taji mi suke cewa,
Sai taji dayar tana cewa " mamAn Auwal Allah yasa ta bamu hadin kai, mu yi amfani da ita taci uban ta, kinsan bana manta rashin mutuncin da tai mana,
har yanzu fa fuskar Mubaraka akwai tabon igiyar wuta"
   Kar ki damu maman daddy bari ta shigo dai,
    Wuf tai ta shigo musu da ruwa
Da zobo
Ta zauna sai dai ban gane kuba??
"Ehh gaskiya bazaki gane mu ba makotan kune ta chan baaya mun kasance munyi zama da abiyar zamanki a baya da yake mijinku mai son mutane ne ya nuna yana son kanwata ta shiga ta ci mana mutunci don tun kafin nan ma na hana kanwata suyi soyayya duba da yadda muke dA ita,
Tazo tai mata duka da har yanzu ta bar mata tabo a fuska,
Ba'a dade ba ta bishi wurin aiki ta tsinka shi a cikin mutane,
To yanzu ma abinda ya kawo mu wurinki
Jiya ne suka hadu da makociyar nan tawa  wannan  ( ta nuna maman Auwal). abin mamaki sai wannan taji uwargidanki na neman yadda zata samu hatsabibin boka da zai haukata ki,
Shine ita kuma ta kasa hakuri ta zo ta samen,
To gaskiya bamu sanki ba; amma kirkin mijinki yasa muka zo mu kubutar daki,
  Laure kuwa tai kasake tana sauraronsu,

Yadda dai take maganar kamar gaske,
amma in dai bata manta jiy a maman salima ko gate bata leka ba, saboda M.P take fama dashi,kuma ita dai tun da tasan halin uwargijiyarta bata yadda da tsubbu ba balle boka kai idan har  zata mata adalci ko maganin mata da mata suke sha bata sha, barta dai da son jiki da son hutu,
Kuma shi din ma a sama ta dauka,

Tana hankalce dasu sukai signal sunga ta tafi duniyar tunani chan tayi nazari bari na kawo muku ragowar  kayan
Biki,

Tace musu "" biri yayi kama da mutum"
Ai kuwa naji tana waya kus kus bayan ta dawo dani take zancen; domin indai zancen  biye biye ne gidan tazo don ni ubana kullum yana kan buzuu,.
   Ku jira ne dai....
  "" Ke maman daddy ta yarda"
  Hahhhhaaa nice fah,
    ke bata ma   da wayo
Fah kiga harda fada mana waye ubanta,
Ke dai bar shashasha,
Ita kuwa dakin M salimah ta tafi ta same ta da Pad a hannunta zata shiga bandaki, jikinta ya bace da yake haka yake mata wannan haukan,
Ta jiyo salima na cewa Aunty momy tayi fitsarin jini,"
Ke ba fitsari ta yiba,
Zobo ne  ya zube mata,
Nan ta bata labarin bakin da sukai,
Amma ina son kizo muje  don ni ban san su bama,
Amma kinji kinji.......
  " Hmmmnn kai musu abin bikin ina zuwa,"
Ta kewaya bandaki don ta gyara jikinta,
 
Sukai ta zuba mata karyaa tana  ta nada a waaya,
  Ita ko sai biye mu su take chan sai ga M salima
Uban mi ya kawo ku gidan nan??.

  Suka miki a tsaye don a tunaninsu bata nan,
Domin sunga giftawar wata mace mai irin yanayinta,
sunyi tsammanin ita ce,
Aunty karaso
Zauna a anan ta dauko waya ta kunna recording,duk magan ganinsu suka bijiro
wayyo basu taba jin kunya irin ta yau ba,
   Suka hadu suka ci musu mutunci musamman laure tai musu wankin babban bargo
A sukwane suka fita jikin su na rawa

M salima ta juyo ta kama hannun laure,

"" Nagode sosai gwanda da kika musu haka da ace sun samu kofa to da shikenan fah sun samu yadda suke  so wallahi mijin na ki ma sai sun raba ku,
Nan ta bata labarin abinda a baaya,
Nima da kike gani da tare miki dasu, ashe son inna ne, soyayyar mutanen zamani ' musa a baki fir'una a zuci,
Ta kwashe tas har zuwanta banki har marin mrs Eric,
Nan dai sukai ta zantawa gwanin sha'awa sai ga imraan ya shigo,
" To yau kune a hade?
Yaaya marar taki??
Ta amsa da sauki,
Allah ya kawo sauki
Sannu da dawowa daddyn salima

" Sannu ka dai lauratu "
Ya tsinci kanshi cikin nishadi yace musu " naji dadin ganin ku haka,

  M salima ce ta kwashe yadda sukai dasu maman daddy da laure ta fada mishi,
" Kin min dai dai kunyi maganin yan Banza; aashe basu saduda ba har yanzu?
  To kunga yadda kuka yin nan ko 'yan uwa nane suka ce zasu muku haka kar ku kyale kuyi musu hakan.

*********************

Wa'alaikumus salam,
Sannu ku sannunku da zuwa, ku kara so,
Maman intisar taga baki 'yan gayu duk ta rikice  ta daddaga teddy bears dinsu inti,
Tai wuf ta kawo musu abin sha,
Suka gaisa amma ban gane kuba ??
   " Ehh  daga wurin su bilkisu ce makociyar ki tannan,
  "ohoo, nagane ashe mutanen Habuja ne, yaya jikin nata? sannunku

Sannunki dai,
  Jiki da sauki,Dama gwabnatin kasar ce suka rike mijinta sun bashi aiki albarkan 'yan uku, shine muka zo kwashe kayan ,
To tace mana kujerun ta da kayan gadon ta a bar maki harda kayan kitchen komai da komai....
Eyehhh ni din?
Allahu Akbar dadin zaman kirkin kenan harda hawayenta na karya, suka shiga nan da nan ta kira mijinta ya turo mata mai wanki su da Abokanshi munyi samuwa
Kai masha Allah ko ni kulsumu sanda na taya ta murna gaskiya _HARKAR DUMA TAYII_
inji  '''AUNTY''' '''IYA''' '''GANAH'''
yar mutanen jeka da fari ta jihar Gombe
Kai taga karan mutanen zamfara sosai har suturunta dasu mayAfai
Suka kwAshe abinda suka ga bazai zame musu kaya ba,
Kujeru an shiga mata dasu falonta an cire tsoffin gado kam sai an nemo masu shince shi,,
abin ka da mai gaugawa har ta sa an nemo mata masu aikin.
   Ta karbi number bilkisun zata mata godia.
   Baban inti yana dawowa yaga sauyi a falo,
Ya shiga madafi yaga kayayyaki lodi lodi ya shiga can dakin maman Inti  yaga ta cire tsohon kayanta,
  Ya iske ta a dAkin shi tana kafa mishi mata ,
Yace budir ......
Tace tusar tsaye,
  Sau. Nawa naake Ce maka Dare daya ALLAH  kanyi bAture,
Kaga ikon shi ko?
To dai bani bayani daga ina??
Bilkisu ce
Wace bilkin ?
Makociya mutanen saudiya mana,
ta fada mishi yadda sukai da ' yan uwan bilkisun,
  Amma kasan miye?
Ya girgiza kai ?
Kankamba zai karu,
Oh ni salihu duk wannan abinda tai mikin baki gode ba, to bari kiji nagaba yayi gaba na baya sai labari kinga abinda nake fada miki kullum ita hassada kara daukaka mutum take yi,
Kullum kina cikin mata hassada gashi abinda  nake fada miki kullum kuma ko kunya baki ji ba kika amsa kina murna.  
 
Wai waye yace maka hAssAda nake mata??
   Kin fini sani tai nesa ta barki da damuwa da talaucin nigeria da zAmAn dar dar na masu garkuwa da mutane,
  Baban inti kenan ni Allah yasa don Allah ma tayi kyautar???
  Kin fi kowa sannin hakan kuwa,
Yanzu kin  kira tane ko ko???
   Bani da kati,
Amshi waya ta ki kiraa
Bilkin ce ta kashe ta kira  su,
Tai ta mata dadin baki " ina yarana? Da wa sukai kama don Allah naga abin arziki fah Allah ya saka da alheri ya baki lafia su kuma ya musu albarka,
Shi dai baban inti yaga kudurar ubangiji

Kut ashe duk cika baki ne , itama tana cikin jerin mutanen da zasu kushe mutum amma idan suka ganshi su hau rawar jikii,
Ta miko mishi suka gaisa cikin kamala ya mata barka ya mata godia sosai
maigidan idan ya shigo ki isar mishi da gaisuwa kuma ina taya ku murnaa,
Allah ya raya,
Ya mi ka mata wayar ta cigaba  da cewa
" kamar nayi tsuntsuwa nazo nake ji 'yar uwa
Bilkisu ta dara sanin halin mutuniyar yau ita ce ke ce mata yar uwa,
Ba komai zan turo miki hotonan su yanzu idan na hau whatsapp,
Baban inti da yake bai barin ta kwana yace mata " *DOLE ACE WA MIJIN IYA BABA"*
To sai mi???
   ah to ke dai ki canza kinga ranar da ta miki yau; don haka ki kiyaye Allah kema sai ya baki.

*********************
Ammi yau bana jin tukin nan  ta mika mata
'yan  makullin motar,
Wayarta ta fara kara alamar
kiranta ake ta dauka suka fara hiraa tare da tambayar iyalan?
Ta fita abinta ta bude kofar gaba na mai zaman banza ta zauna Sukai sallama don bata yarda tai ta zance a gaban Ammi ba " " Ammi ji nake kamar nayi mantuwa ,. 
    Mantuwa kuma? Ba ga waayar ki a hannunki ba,
" Ehh haka dai nake jin kamar akwai wani abinda ban yiba da zan fito,
mu fara biyawa ta asibiti dubiyar ko?
  Eh amma wani asibiti suke ne?
Ki kira Abbanki ki tambaya mana
  Ta rusunar da murya kasa "Abba dama ammi ce tace na tambaye ka sunan asibitin da aka kwantar da Haj Asiyan gidan Baba ibrahim,
Owk
"Tana  SHEFARD SPECIALIST CLINIC NE kan titin shuni can waja jen Mabera,

To Abba,
Suka juya suka canza akalar motan basu fi mintin biyar ba suka ajiye mata kayan marmarin da katan din maltina da ruwa sukai sallama nan suka dau hanyar A.A SOKOTO SHOPPING MALL
  " Ammi baki lura wannnan motar tsere take tayi damu ba,
  Wacce motar kuma? Ke hankalinki yakai;  ina dai kin dauko ATM din kin?
Ehh gashi nan a jakata, oho da kika ce kinyi mantuwa sai nai tsammanin shi kika manta,
"  Ayya kinsan addua' ce ban yiba,
Nan suka adana motar su a kasan benin da aka tanada don  ajiye motoci suka shiga,
sunyi sayyaya sosai ma yaran khaleed kan har keken hawa na yara aka sai mishi,
Aka rako su da kayan har mota,
" Lah Ammi ashe ban karbo ATM ba "

Kai zubaida kina ganin magariba tayi....
" Kiyi hakuri bari na karbo.....
Kicibuss sukayi da ma'aikacin wurin zai miko musu ta karba tai godia juyawarta kenan, taga masu tsere dasu a motan nan suka shaka mata abu a hanci suka  turata cikin motaaa
  Kafin Haj Hauwa tai kwalala tuni sun tada kura sun   kwasa a gujee,
Tashin hankali da ba'a sa mashi rana tuni ASMArta ta tashi hankalinta ya fara gushewa Allah yasu wata budurwa da ta ajiye motarta a gefensu  tai maza ta kawo mata dauki ta bincika jakarta ba INHALER subhanallahi, da ita da ma'aikatan wurin suka gyara ta, ita yarinyar ta bada makullan motan ma wani ma'aikacin wurin da ya biyo ta da motar ta
Bata tsaya ko ina ba sai HAMDALA MEDICAL CLINIC da ke  kan hanyar EMIR YAHAYA,
Kafin ta isa ta kira wayar mahaifiyarta domin anan take aiki kuma tasan evening take yi,
Cikin gaggawa aka mata abinda ya dace ta farfado,
Sai cewa take " sun tafi da ita,
Sun tafi da zubaida?
Su waye ???
Wasu ne a mota,
Nan ta dauko waya ta kira number zubaidan inaaa har sun kashe,
Ta kira Baban
,"Alhaji kana ina??
Yadda yaji tana maganar a  shash-sha ke yasan ta samu ATTACK ne
  " Miya faru Hauwa?
Sun tafi da ita,
Wallahi sun tafi da ita,
Zuciyar shi ta yanke!!!
Da wa?
Su waye?
Kina ina?
an dauke zubaida a wata mota
LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH!!!!
  likitar ta karbi wayar ta mishi bayanin inda matar tashi take Hamdala.....

Comment