shafi na Bakwai

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ πŸ‘ŒπŸ»

0⃣7⃣

Musa ne ya shigo bayan fitan mama,
To inna naji mama ta shigo tana miki INGIZA MAI KANTU RUWA,
to gaskiya ba halin ki bane ki bar UNAIZA ta bi mijinta,
Tun yaushe take miki farfaganda akan yaya QASIMU,
Idan kin lura ba haka take wa surkanta ba,
Kullum ina ji tana ce miki kin sake da UNAIZA kamar ba surkarki ba,
So take ki tsangwameta kina takura mata,
ita duk da rashin mutuncin da rashin zaman lafiya da matan yaya BILYAMINU suke yi waye bai sani ba amma kinga tana matsanta musu akan abinda suke yi??

To ki rabu batun ta don Allah,

Nidai nasan yaya QASEEMU babu abinda zai fasa kuma ina sokoto ina tangaza ,
'' Shi kenan musa nagode da ka fahimtar dani,
ni kaina sanda jikina ya bani wata manufa ne da ita,

Eh inna manufar kenan abinda 'ya'yanta suka ki yi ne take tunanin yaya shima zai bi sahu yanzu kinga dai yaya bilyaminu tun yana jan motar nan wani irin samu ne bai yiba amma kwandalar shi bai amfanar ba,
Sai yanzu da rashi ya same shi yake lallabowa abinda baba ya noma yake cinyewa,

Kiga yaya munzali ma duk samma kal,
''Haka ne kam musa,
Ke dai inna ki ringa binshi da addu'a.

Insha Allahu nagode.

Assalamu Alaikum,

Wai wani meeting ake yine musa?

Hahaha yaya shirin tafita nake,
Wu gandoki kenan,
Kai da UNAIZA bansan wanda yafi wani doki ba,
Inna inason na shiga gari,
''Yauwa dan zauna mana dama ina son na maka magana,

Musa ya tashi ya fita,
Allah dai yasa lafiya innan mu''
Lafiya kalau
,
Yaushe zaku tafi?
Insha Allahu jibi.

To Allah ya kaimu,
dama ba komai bane QASIMU illa maganar da na saba maka riko da gaskiya da amana komai tsanani duk yadda Al'amari ya tsawwala a gareka kayi iya iyawarka,
kar ka watsar da hallinka da ka tashi akai,
sannan ina maka gargadi sosai akan mua'amala da mutanen kwarai, domin mua'amala da mutanen kwarai ya kan sanya mutum ya zama na kwarai,
Kada ka zama ma'aikacin da zaka na cin amanar aikinka kamar chuwa chuwa ko danne hakkin wani,
Sannan kar kayi wasa da abinda kake taimakawa mahaifinka,
ko kuma nace gidan nan duk abinda zaka cire ka bayar shine rabon ka na gidan dunia dana lahira.

Allah yayi Albarkan nan da ake fada shi ke sanya mutun cigaba da samun nasara da daukaka a rayuwa,

Sannan wata shawara ko: kar ka yadda ka dogara da Albashi ka zage ka nemi kasuwa ka cigaba kamar yadda kake yi anan na sare sarenka,
dogaro da aikin gwamnati shi ke sanya mutum ya zama ya sa ido akan na gwabnati.

Haka ne inna,

Dama akwai mai gida na wanda nace miki dan bagudo nan?

Eh nagane shi,
To yana da babban shago ya zuba kayan na'ura mai kwakwalwa sai ya nemi na mishi aiki a wurin ina kula da wurin shine na kawo mishi shawaran ya sa na'urar daukar hoto a wajen an huta kawai idan aka zo yin photo copy din takardun akwai mai hoto ma a gefe,

To inna sai yace min wai ya bar min nasai na'urorin hoton da kudina na saka idan yaso wai sai na hada da manyan abubuwan daukan hoto irin wanda amare da angwaye suke dauka kafin biki,
To ni kuma anawa tunanin ina so idan mun tafi na tura musa ya koya,
akwai inda ake koyan?
Yanzu shi hoton ma koyanshi ake yi?
Eyyeh inna ai ni kaina abin ya bani mamaki da oga ya fada min yadda ake hotuna kafin aure,
''Hoo.
Ai inna abubuwa iri iri a birni,
To Allah ya bada ikon yin

Amin

A halin yanzu kam bani da kudin da zan saya don yana da tsada gaskiya,

To Allah ya yassare,
Amin,
To sai kana yi kana jawa musa kunne kasan su ba irinku bane,

Inna kisa ranki a inuwa insha Allahu zai biiyu ai musa bashi da rashin kunya yanzu kin hada shi da Shazali,
To ai kasan yaran ne idan basu ganin idon mu sai a hankali,

''Haka ne kam
Amma insha Allahu bai samu saken ,
Hakan ba,
Kuma ina son ka sa mishi ido sosai akan zaman su da UNAIZA kar ka sake mishi ya rainata duk da cewa dama basu da matsala amma yau da gobe ya wuce wasa,
Allah ya muku Albarka ya kara daukaaaka
Amin inna nagode Allah yaja kwana tare da imani da karin lafiya,

Sai ga UNAIZA,
inna zanje gabasawa ina son naje na musu sallama,
Eh ya kamata,
Yanzu wa zai taimaka miki da yan biyun nan ,
Na roki lawiza zata rakani,
Adawo lafiya ki gai dasu,
Zasu ji insha Allahu,

Sokoto

Maman Auwal ta isa gida cikin fargaba domin bata da matsala da mijinta,
Fitinannun iyayenshin nan sun fi tsaya mata a rai,
Inna dije kuwa dama ta cika fam domin dama ta debo yunwa ga gajiyar hanya,
Tana isowa kuma bata samu matar gidan ban,
Yanzu kai mustafha haka zaka ji gaba da zurawa Asiya ido tana yawo,
Ashe har yanzu bata nutsu ta daina ba,
'' Wallahi inna ba yadda banyi da ita akan ta daina fitinnan ba amma abin ya gagara inda kika san wata mai Aljanar tashi muje ba dama ta zauna a gidanta, Allah Allah take na fita ta fice itama,
Rufe min baki ba wani Aljanu,
Wallahi babu wani Aljani,
Kasan Allah ko? ka tuba wa Allah ka nemi yafiyan Aljanu kuna musu sharri,
ba su san hawa ba basu san sauka ba sai ku ringa kakaba musu sharri, sai mutum yayi ta iskanci a fake ace wani Aljani,
Ahir dinku randa suka gaji da kakabe kakaben da bil adama suke musu,
Dama ina shiyasa muka hanaka auren Asiyar,

abinda ta tashi taga anayi kenan a gidansu,
uwarta da kake gani babu wanda bai santa ba a SHEMA tsabar yawunta, GYALENKI A KOFA ake ce mata ta watsar da yara, ta fita yawon ta zubar yawon gulmace gulmace gidan mutane, shiyasa aka kakaba mata sata a gidan mai unguwa wata rana, ta shiga ta fita kenan aka gunduma sata~

kai dija ya isa haka mana shikam ai yaji yagani,
Yana zaune da ita,
Haba malam dube shi kaga yadda ya zama tsabar ba ya samun abincin kirki ai da gangan na turo sama'ila kaninka nan domin yana nazar tanku,
yawon ba fasawa tayi ba,
Bata da lokacin nutsuwa tayi abinci, ta yaya bazaka lalace ba,
To bari na fada maka maryama da kaki ta saboda Asiya iyayenta suka aurar da ita,
To Mijinta ya rasu,

saboda haaka umurni nake baka ba shawara ba idan ka tashi mai damu ka kai kanka ku sasanta dama ita tana kaunarka,
Sai ga shigowar maman Auwal,
ayawo an dawo?
Nace ayawo an dawo ne? ai da zama kikayi kika ba wa mai aikin naki sallahu,
Malam yace ya isa haka dije,
Ta ajiye ledar kankarar,
Ta samu kujerar gefen inna dije ta zauna,
tsabar rashin tarbiya shi kanshi baban Auwal din yana zaune a kasa,
amma tsabar rashin tarbiya tana sama dal ta gaishe su ta wani mike ta shiga kicin tana wani yatsina
inna dije ta bi bayanta da tsuka '' mtswwwwwss DA BA'A SAN ASALIN BALBELA BA DA SAI TACE DAGA MASAR TAKE''
wai ke dije baki gajiya da fada,
Malam ba fada,
gaskiya ne dole na fada ehe!
ta kawo abincin gaba daya dai ba kan gado, miyar tsabar dadewa a frigi har ta salince,
Lomar farko inna dije tace,
''Ki tashi ki kwashe abincin bazan ci dadad-diyar miya ba,
'dan nan kana da garin kunnan na buhu mai laushi,
''Oh $emovita ko?
Eh,
To shi nake son ci da miyan kubewa danya,
Ta sude hannunta ta shafe
Ta kuma sa kafar ta daya akan daya,
Baban Auwal yace to hajiya bari naje na sayo kubewar'
na barka Allah ya tsare ya sadaka da Alheri,
Ya miki dama Allah Allah yake yi ya kauce, saboda sababin innar tashi, yasan zata cigaba da maganarta ce ba tsoro ne da ita ba balle ta yi shakkar Asiya taji,

~~~~~~~~~~~~~~

Haka dai maman Auwal tayi tuwo da miyar kamar ta zunduma ihu take ji.

Babu yadda ta iya,
tasan inna tsaf auren ma da yaya akayi,
Da ba don uwarta mai shige shige bane bama baza'ayiba,

Sukai kwana biyunsu bayan taga likita ya debesu sai shema.

Maman hanifah ne gaban motar mijinta shi yana gefe yana tuki hanifa da hanif suna bayan mota,

Zasu shiga cikin gari,
Ashe maman daddy dasu maman Auwal da maman hydar sun fito daga gidan maman daddy suna kara tattauna matsalar maman Auwal din domin ta kwashe yadda sukai da inna dije ta fada musu,

Sannan ita maganar karshen nan yafi daga mata hankali wai ''
har yanzu tana sonka ai''
Ke kwantar da hankalinki inji maman daddy

Saboda tsiyar da kike mata ne take cewa ita tana sonshi,
Kai haba!!
Maman hydar tace tabbas kuwa ,
Har naji sanyi wallahi,

sai ga su maman hanifan sun zo sun wuce a mota bata ma kula dasu ba,

To idan akwai abinda yake bata musu rai bai wuce, wannan fitar motar ba,
Su dai ganta a gaban mota abin yana kunta ta musu rai,

''Wannan munafukar mata mai girman kan nan na washe ta,

Maman Auwal kenan baki kaini wasar taba,

Shi kuma mijin a haka ji yake da ita mai kama da kuncen shawara''

Ke maman daddy ni gani nake kamar da gayya suke fita da motar nan,

Kullum fa sai sun fita da yamma,
Maman hydar tace ai baku sani ba,
Ta raina mana hankali nefah shiyasa ko kallon inda muke bata yi idan suka zo wucewa
Na rasa gidan ubanda suke zuwa,
''Wallahi gantali ce kawai''

Kai maman Auwal,
Billahil lazi rahamanu,
Idan ba gantali ba ko ina miji zai je sai kin leke kin bishi.

To baku da labari ma,
Muna jinki maman daddy
''To wannan da kuke gani har shagon aski binshi take yi,
a'a haba ?
Wallahi zaku ganta da jakar clipper a hanunta,
Eyyeh samun wuri kenan
Hakan da take yi ba shi zai hana ya mata kishiya ba,
Idanma don ta sa mishi ido take yi,

Kwarai da gaske maman Auwal,
Ai SHORE- SHORE BAYA HANA MUTUWA,
gaskiya kam,

Kinsan abin mamaki akwai fah randa akace min hanip bai da lafiya,
Baban daddy yace naje na duba shi,
Ina shiga sai gani nayi tana wanke mishi kafa a cikin baho, gefe guda kuma turararruka ne masu kamshi na wanke kafar,
A hakan da nake fada muku tana gamawa ta daura kafar akan cinyarta ta dauko tawul ta goge kafar ta mulke ta da wani mayin,
Nace wuu lalle zakiyi har ki gama,

Ina ruwan miji dan gata,

Inji maman hydar
ina tausaya mata indai namiji ne,
Duk bata lokaci da zatayi tana lailaya shi, sai dai idan bai zo maka rashin mutun ciba,
Maman daddy harda wallacewa
Wallahi sai yayi,

Maman hydar tace ai ni tun farkon kawota unguwar nan na fahimci yar dunia ce,
Idonta a tsaitsaye suke.

Mi ma kika gani,
Ni da gidana yake kusa dasu ai nafi shan kallo
Tana da cikin na biyun nan fah bata aikin komai,
Kullum mijin na cikin aiki a gida
hmmmmm
Samu wuri nefah idan nine ko wallahi sai dai na mutu,
cewar maman Auwal

Ah toh ke kin iya SANABE ne?
a'a nikam ba dani ba GADA A HURUMI,
Ai kuwa basu gushe ba sai gasu nan abin gwanin ban sha'awa hanunsu dauke da ledoji daga gani super market suka je,
Wu huhuhu kar ka ga idon yan gulma kamar zasu fado.

Yadda ta burge ni bata bi ta kan kowa ba, yaran suka shiga gida, ita kuwa sanda ta jira mijinta ya gama rufe motar kafin suka shiga ciki suna murmushi,
Dukkansu ba wanda bai zo wuya ba,

KASHE GARI

Ganin lado sukai yana share share da wanki wanke,
ba'a dade ba sai ga maman hanifa da labulaye ta iso a motar mijinta.

maman daddy tana jin motsi sai gata ta shigo,
maman daddy tace
'' to ikon Allah hajiya kice a gidan? dama motsi naji da kuma maganar mace shiyasa na leko naga ko mai gidan ce ta iso?
tana tafe insha Allahu zuwa anjima,
to
Tana ta leke leke,
Lado ne yace
'' Aunty bari naje gida na dauko turmi,
To lado
Maman daddy a bari na kawo mana ta fita
Sai gata da turmi fagam fagam ta sauke,
tsabar shishshigi ba da ita ake aiki ba amna ta sa kanta.
Bari naje na daura musu abinci, maman hanifa dai kallonta take yi
Suka gama suka kulle gidan,
Mubaraka don Allah kar ki gaji dani, daura min jollof ki dan watsa Mata kashin nan,
To Aunty ayi mata per boiling ne ko kuma?
Ki watsa musu jallof kawai ai kauyawa ne,
Basu ma san wani perboil ba,
To shikenan,
zabga musu Ajino kawai kinsan suna son suji rau din nan,
Haka ne,
Yauwa kinsan miye nake son fada miki dazu na manta,
Idan T.J yazo ki saki jikinki ki ci kudin dan banza, zancen neman gaske kam babu,

Wallahi nima Aunty abinda yake damuna kenan ance fah har ciki yake wa yan mata,

Ba wai haka ne,
dazu ma yake cemin wai zai kawo min majinya ciya wai zan kula da ita,
Nasan irin wadanda yake musu ciki ne,
sai ku zauna daki daya,
to Aunty

Alhamdulillah
UNAIZA ta fada, umaima tana kan cinyar Baffanta musa tana bacci yayinda KHALID yake hannun uban,
Motar ta faka a dai dai harabar gidan nasu,
Suka sauka, musa ya faki idon QASEEM yace maman umaima gamu fah a QUATER'S,
To gandoki ai tun shigowar mu naga kana babbaza ido a mota,
Ai dole ne,
Ya dawo dauke da yan makulan gidan a hannun shi mamana kin tashi? ya bude kofar suka shiga,suka samu wuri suka zauna.
Jigum jigum,to musa tashi biyo ni kaga dakinka,
Zumbur ya miki
Yaji dadin ganin dakin kuwa ga manyan winduna,
Maman umaima taji sallama ta amsa taga wani dan matashi ya gaidata ya mika mata kwando kayan abinci babbar warmer ce sai wani kwano an rufe da shi poil paper cole slow ne,
Sai kayan sha a gefe ta karba tayi godia,
Daga ina ne,
Gidan maman hanifa ne
Kace mata na gode ina gaisheta,
To zata ji

'' tace ace miki tana miki sannu ma kafin ta shigo''
To sai ta shigo an gode,
Keda wa kike magana ne kuma?
Lah wai gidan maman hanifa ce ta aiko mana da abinci ayya Allah sarki ,
Musa! musa!
Na'am yaya,
Cikin shirginmu nan akwai plates dauko ka debi abinci kaci sai mu tafi kasuwa.

Ai baban umaima kaima ya kamata kaci abincin tukunna,
Nifa yanzu manyan kayayyaki zan sayo idan ankwana biyu maman hanifa tana tuka motar mijinta sai ku tafi da kan ku ku zabo abinda kuke so.

To

Ba damuwa
Bayan fitar baban umaima ne
Sai ga sallamar maman daddy, ta shigo da foodflaks dinta a taimaki mai gadi,

ashe Baki sun iso?
Sannunku da isowa,
ta zauna tana kare mata kallo don tayi tsammanin zata ganta GAJARABLE sai ta ganta yar gayu da din kinta doguwar riga ta atampha
ta kananun JAVA din nan suka gaisa
ta tambayi sunan yaranta,
ta fada mata

sunana zainab amma anfi kirana da maman daddy, yarana hudu ne,
Nice nake jikin gidanki, Allah yasa kin dawo a sa'a,
Dafatan zamu zauna lafiya,
Mi zai hana?
wa zai ki zaman lafiya,

ai ZAMAN LAFIYA YAFI ZAMA DAN SARKI.

Gane min hanya yar gari,

za'a tafi dake,

Tunda bakin ki a bude yake,
to mi za'ayi da jugum gayyar ciwon baki,
Yauwa yar uwa.

Maman daddy ta
kari shi rakadin ta mike tsaye zan tafi,

Insha Allah zuwa gobe zamu shigo da matan kungiyarmu,
Kungiya kuma?
eh ai muna da hadin kai a unguwar nan, komai tare muke yi kamar zuwa gidan suna, biki, jaje da sauransu,
''kai ???
ina fatan kema zaki zama daya daga cikin mata masu bada hadin kai a QUATER'S din nan??????

Ta'aliki
Zaba
Watsa

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

Comment