Shafi na talatin da biyu

🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈBAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATIONπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ
( BAHWA πŸ“)

_(Matattarar zaΖ™aΖ™urai, haziΖ™ai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)πŸ‘ŒπŸ»

3️⃣2️⃣

Bai fahimci mi take ce mishi ba,
Hanyar waje ya kama ko zai dawo hayyAcin shi

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!!!

Fitar shi ke da wuya yayi tozali da MUBARAKA zuciyar shi ta bashi yaje ya shaketa kowa ma ya huta
Kawai wata zuciyar ta hana shi
Ya kare mata kallo fuskarta tamkar wanda tai wanka cikin KURKUR ( CURCUMIN ko TUMERIC) tsabar shafe shafen da tayi kasan idonta har wani tabbare tabbaren ja da baki yayi,
Xuciyar shi ta kara kuntata
Ya juya ya shiga gida shidai abincin da bai ci ba kenan,
Ya shirya ya fice wajen aikin shi
Yana ta tabka da warwara.

ZUBAIDA tace " Abba nagode sosai Allah ya kara bude,
Ya kara maka lafiya,"

Ameen hajiyata yanzu ke kayan gadon ruwan SHANSHAN BELI kika zaba wa kanki ko wa Auntyn naki???

Ammynta ce ta bada amsa da yake ita ZUBY ragowar mutanen da ce, Allah Ya yas-sare mata tana da ta ido,

ita ruwan SARARIN SAMANIYA ta zaba a madafinta da labulayyanta,
Yar uwarce ta zaba mata wannan kalar,

yauwa an karbo dinkunan kuwa hajiya?

Inason akai wa Auntyn nata da wuri saboda ta fara hidima da wuri nasan KASIMU yadda auren yazo mishi ba shiri nasan bai shirya komai ba,

Yauwa hajiyata dazu baki ga sakon kudi a wayar ki ba ce!??

"Lah Abba ai ko nagani"

To kije ki yiwa yaran na kun sayayya.
Tai godiA ta basu waje don nauyin maganar auren take mata.

AlhAji BAGUDO ya numfasa

Allah ya nufa kar yar nan hakan ya sa ta yiwa yarinyar nan dagawa wata ran,

Kai haba kasan halin yarka ai
Ba dai wannan ba.

To kinsan wani lokacin hali kan iya sauyawa,

Haba Alhaji kaine mutum na farko da ya kamata ka bawa zubaida wannan shaidar fa

Hake ne Ammy
Alhamdulilla,
larabbawa suna cewa " SHUKRAN LA FAHRAN"

Allah yasa hajiya.


Yanxu Bahijja tafiyar zakiyi?

Eh to maman salima ai mama ce tace min na koma, ta zuge zip din akwatin ta mikar dashi,
To Aunty Allah ya kyauta,

Tabbb lalle ai kuwa IMRAN sai ka gane da ruwa ake shayi,

Ta saka wancan ta kunce haka dai ta wuni cikin kunata,

Tashin hankali maimakon taji sassauci a zuciyarta amma ina!!!
Kamar wanda ake mata zuga zugi, ta fantsama falon imran ta fasa talabijin, ta zirdo shi kasa kai take wurin yayi kaca kaca,

Yayinda imran yake jiyo sautin fashewar abu yayi,
a tunaninshi tiles ne ya subuta ya fado,

Turus!

Yayi yana karewa wa wurin kallo tare da juyawa yana karantar yanayin da MA'UN take ciki,
cikin biyu za'ayi daya:
Imma dai kwakwalwarta ta samu damuwa - ko kuma motsuwar kwakwalwa da aka ce masana lafiyar kwakwalwar dan adam suka ce"ko wani dan adam a yini yakan sami tabin kwakwalwa na tsawon minti guda"
Amma akasin haka ya gani,
Tsantsar rashin mutunci ne da tashin hankali ya gani a kwayar idonta,,
Tana huci kai kace kumurci ce,
Zuciyarta tsabar kunci da kyar take fusgar numfashi.

Da yake dan duniya ne,
Ko a jikin shi, ya dagaa mata gira yace "
kai Barka sannu da kokari, Allah ya kawo ranar da zaki samu lokacin kanki,
Haba dama talabijin dinnan ya hana ki sakat kullum kina cikin bashi kulawa"

( RA UBA wai malam yaki ASHAR )

Ya sulale ya wuce daki duk da kuncin da yake zuciyar shi,

amma yana son ya zama tsayayyen namiji domin yasan kishin banza ne ya kai ta ga aikata hakan, don haka bazai biye mata ba.
Dadin dadawar ma yasan abinda take nema kenan suyi tashin hankali,

Ya sauya kaya ya fito cikin kananan kaya masu daukar hankali ga kamshin turare
Kina da sako ni zan karisa wurin kanwar ta ki munyi waya zanje na karbo mata dinkunan biki kinsan gobe ne walimar.
Bai jira amsar taba yasa kai ya wuce....
MATA ! MATA !! MATA!!! Hooo ya daki sitiyarin motar.

Nikam HASEENA na daure na cije amma gaskiya na gaza,
yaya ake gani asalin nakuda don Allah???

Hmmmm Aunty B, kina ganin zaki boye min ne?

Ai tun da muka tashi naga yadda kike zuffa da yawaita shiga makewayi nasan ba lafiya ba,
amma dai tunda baki furta bane na kyale ki.

Yauwa kinga yanzu haka ina ji,,

Tun cikin dare fah haka yake min,
Ta rike kugu.
Hahhhhhhha, kice abin yazo, muje na duba ki, da rabon akanki zan fara aiki a sabon asibiti na.

" Kar ma ki fara Alkawari ne, in sha Allahu a agarin makkatul mukarrama zan haihu,

Allah ya nufa ki fado hanuna,,,

Barni don Allah na kira hubby na kinsan ina tsammanin ya sauka,,

HASEENA ce tace
kin ganki kuwa?

Gaskiya abu ya kusa wannan budewar hanci,
Ke raba ni don Allah,

some somen hauka zubda yawu,

Kya sani dai.

Wayar BILKISU ta shiga karade musu wurin
Habeebi har ka iso kenan naga lambar

eh

Habibty na muryar ki ta sauya naji da sauri sauri kike magana lafiya kuwa?

Ta cije lebe ba komai kawai gajiya ne na dan zazzaga ne ina motsa jiki......
difff wayar ta katse
Wani mummunan ciwo taji a kugun ta

Gaskviya Aunty B kina da raki
Baki ya mutu.

daga nan Haseena tasan abin ba na wasa bane maza maza ta kamata sukai sashin asibitin sai dakin haihuwa ta dubata ta zare safar hannun
Bata ce mata uffan ba,
amma abin ya bata mamaki
Ba service sam,
Aunty B zo kwanta nan zamuyi scanning
Da taimakon Haseenar ta iya hawa gadon akai scanning,
Masha Allah kingansu nan dayan ne kwanciyar shi bai yi dai dai ba amma akwai

Amma me???

La kar ki damu ba komai bane ana iya juyawa

,sai dai matar da na sani asibinta na Makka ne SHARI'E HISHAM BIN SULAIM,

nan ta kirata a waya ta juye larabci ta mata bayanin abinda ake ciki da yara uku ne amma dayan yana kaikaice ba dama ta iya haihuwa dole aiki za'ayi amma suna zuwa kafin dare ayi musu tanadi.

( Haseena bata son tacewa B din 'ya'ya uku ne a cikin ta iya yuwuwa ta tsorata har BPnta ya hau a samu matsala, amma lafiya kalau zata iya haihuwa idan aka juyo babyn
Sannan na biyu kuma tana son cika mata burin ta tunda so take ta haihu a cikin garin makka gata ga harami.)

Ta saci kallon Aunty B taga alamar kamar ta shiga rudani,

Kira hubbynki ya tare mu nan da awa daya

Duk kin wani rikice ance guda biyu ne,
Kina zuwa za'a juyo ki haifo su da kanki in sha Allahu.

UNAIZA dai da ta fahimci B MUSA ya gama shigewa tace ka ga. Mai da wukar,
Wannan kam yar mutunci ce.
Haba M.UMAIMA har kinsar hankalina ya tashi, yarinyar da idon ta ya gama budewa, inaga ko aure tayi ban yi tsammanin zata iya zaman aure ba.

Eh toh abun na Allah ne B MUSA,
Don Allah fada min wanda zai aura mana,
Sha kurumin ka tuwon ku manku ne ai ku kam,
Kina nufin a dangi aka bashi matar???
Eh amma dangin kara ba; HAJIYA ZUBAIDA A BAGUDO.

Gaskiya yau kam kina ji da Raha wallahi; ina shi ina wannan ai ~WUTSIYAR RAKUMI TAYI NESA DA KASA~
UNAIZA tace
"Eh amma mun sakala matakala zamu kamo wutsiyar,"

( Shiru ya ratsa dakin )
Hmmmm sai nake ganin kamar bazai iya daukan al'alar taba,

In sha Allahu zai iya, ai yayan ka ba daga nan ba.
To haka ne,Allah ya bashi iko yasa ta gari ce,
Yauwa yanzu naji dai dai babu abinda yafi karfin Allah,

Kuma Aunty mi kika shirya na gyaran daki,

kayya B MUSA ba abinda zanyi,
Mi nake dashi
Karar wayar ta ce ta shigo.
Taga sunan Babanta
Cikin kaskantar da kai da risinawa ta gaishe shi ,tamkar yana ganinta,

Bayan gaisuwar ya cigaba da mata nasiha,masu ratsa zukata da sanyayyawa, daga karshe ya sanar da ita yayanta da yake aiki a fatakwal ya ce ta nemi Asusun ajiya ta tura mishi, zai bata kudi ta sauya kayan gadon ta da kujerunta,
Sannna nima anan na sai da shanu na gudu Biyu zan bayar da kudin a kawo miki,nasan kina bukatar abubuwa musamman zannuwa keda yaranki,kada ki yarda ki takura mishi sai ya miki kayan uwargidanci,
" In sha Allahu"
Yauwa Allah ya miki Albarka indai kikai halin mahaifiyarki kam baki da sauran damuwa Allah ya jikanta da rahama,ke kuma Allah ya miki Albarka ya baki hakuri.

( B musa duk yaji abinda suka tattauna da mahaifinta, kafin ta kammala har ya rubuta mata numbar asusun ajiyar shi,)

Ga numbar nan bani wayar ki na tura mishi,
A haba daga yanzu ka bari sai na kira na mishi godiya mana

a'a ba'a bori da sanyin jiki ai, da wani suna kika adana nambar tashi??

yaya Balarabe.

Lah kaga bani da kati dan sayo min ma na samu na kira dama saura na flashin ne kuma da ka tura sun janye kudin su,
Bar kudinki inada canji bari na sayo miki,
Amma zan wuce masallaci,
Yauwa lokacin sallah yayi ko ?
Eh AUNTY.

Yana cikin loda mata kati kawai yaga CR ALERT.......
300,000,00
AuNTY duba ki ga har ya shigo,duba don Allah,
Ya nuna mata taga kamar dubu talatin,
Ayya yayi kokari har talatin,
Haba Aunty wani irin talatin??
Duba da kyau fah, zeron biyu ne fah??
Ai bata san lokacin da ta mike ba, ALLAHU AKBAR!!!

Nan ta rikice sai murna sai farin ciki,
Don Allah loda min katin
Na kira shi.
Don Allah kira mun B UMAIMA na sanar dashi,

Wa??

a'a AUNTY,
Ki ja bakinki kiyi shiru iya kace ki samu M HANIFA ta kai ki nan AL GAZARU ki sai kayan gadon zamani, wanda akeyi anan cikin gida nigeria,
Ko?
Eh.
Sun fi karko
B MUSA yace
Sosai ma


✍🏽
MAMAN FARHAN

Comment