shafi na Arba'in da biyu

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣2️⃣

Alh danjuma ne zaune  a  INTERROGATION  ROOM,
Zaune yake gaban  A.S.P MUAZ
Yana amsa  tambayoyi,

" Tabbass nine mammalakin motann nan; amma kamar yadda na fada maka kuma kaima ka shaida da idonka daxun nan na iso garin nan daga inda nake aiki a niger,
Kuma tabbas motar ba da ita nake tafiya ba,
  Na kan barta a gida a hannun yara suna dawainiyar makaranta dasu da kuma kannenSu,
Mu'az yace "yaran maza ne ko mata ne??
"
Namijin daya ne  Allah ya bani,
duk sauran matane;
daga shima ban sake  samun wani namijin ba
To kasan dalilin da yasa muka gayyace ka station dinmu?

" A'a"
  Muna zarginka   da yin garkuwa da
Yar gidan Alh Bagudo, wanda kuka sace ta a A.A SHEHU SHOPPING MALL,
tsaye ya mike tsam  "subhanallahi,
Kana nufin KIDNAPPING?
" haba haba ta yaya  za'ayi ni da bana garin a zarge ni da wannan mummunan abu,sam inah!!

  Zaka mana musu kenan?

ya jawo NAURA MAI KWAKWALWA ( COMPUTER)
ya saka FLASH ya tariyo dai dai zuwan su zubaida har yadda  suka turata cikin mota,
Ya mike tsaye kalu
" INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR-RAJIUN,
tabbas itace

jikin shi ya fara kyarma, duk da ya rufi fuskar yasan Haseeb ne,
Wato ta nan ya bullo,,
Zuffa ce keta keto mishi,

A.S.P MU'AZ yace,
"" Yan zu ka gani to ya akayi hakan ta faru ? kaga da mutuncinka bana son na kaika INVESTAGATION UNIT din mu su azabtar da kai; amma idan kace zaka mana taurinnkai kalli nan,
Ya danna kararrawa wasu karti suka shigo da ganin su kasan jinin samudawa ne,
Sai huce suke yi jira suke ace musu KULE SU KUWA SU CE ASS ,
Jikin su a murmurde idan sukai numfashi sai kirjinsu ya dagu sama,
Ya musu isharan da su koma,
"To ina sauraronka,
  Ehh to kaga dai gaskiya da gani kasan ba ni bane tunda ko yanayinsu ka gani  kasan matasa ne,
Yai ta inda inda,
MU'AZ ya kira akazo aka tisa keyarsa cikin keji,
   Kai haba da mutunci na zaku min haka ?
"yace
na barka lafiya idan kaji matsa na kwana daya zaka fada mana gaskiya"
yayi ficewarsa,

Alhaji kuwa ya gama jera kudin a cikin jaka,ya kirasu sukai mishi kwatancen
" Amma Alhaji kar kayi gigin zuwa da yan sandaa don zamu tarwatsa kanta matukaa,"

Alhaji yace " ba damuwata a kamaku ba, ' ya tace kawai a gaba na""

  Sukai wata  dariya irin ta basawan nan,

  Ko kai fahh,

Ya kiraa
S.T WURNO ya mishi bayanin yadda sukai,
Bai fi mintuna ba sai gashi ya  bashi kudin; sannan yace dashi da kasimu zasu tafi,
  Hanyar Tambuwal suka kama kamar yadda sukai musu kwatancen suka hangon bishiyar tsamiyar da suka fada mudu, kasimu ya ajiye kudin a karkashin bishiyar,
Suka shiga mota suka fara tafiya da takai  ta Minti biyar sai Alhaji ya kira WURNO yace su dawo cikin garin, hanyar da zata sada ku da BY PASS na WAMAKKO,
Ba ta lokaci suka  dau hanyar basuyi nisa ba sai ga zubaida a gefen titi,
A skwane kasimu ya ajiye mota,
Ya fita cikin kuzarin shi, "zubaida basu cutar dake ba ko?
" Ba abinda sukai min kasan yara ne ma ko makami basu dashi,

(:Bata wani galaibaita ba sai dan duhu kadan da tayi)
WURNO ya kira Alhaji yace " gamu nan tare da ita,

Ya ce musu su hadu  kawai  a  asibiti don yana son a  dudduba lafiyarta

" Gaskiya inaga ba'a bukatar hakan Alhaji saboda lafiyarta kalau ba abinda suka mata,
Ni dai ina son mu kara komawa wancan hanyar ko zamu isko su,
Kar ka damu,
Ai yanzu mukai magana da ASP MUAZ sun kama mamallakin motar yana tsare a wajen su,,
Owk to bari mu kariso gida.

Duk kawaicin hajiya da Alh sanda suka fito kofar gida suka  jira isowar tilon diyarsu abar kaunar su, Habeeba ce a  gefen su,
Da gudu ta kariso wajen ammi abinda ya dameta bai wuce zabgewar da taga sun yiba,

Ammi ta rungumeta
" Basu miki komai ba ko?
Basu taba kiba ko?
Ba abinda sukai min Ammi yara ne ma; hasali ma kamar yadda naji yana waya da abokanshi kamar Birthday suke son hadawa, kuma a yau zasu yi, kamar yadda naji suna fadi, basu da kudi shine suka shira hakan?
WURNO yace"  na fada muku na gida ne sukai wannan aikin; amma mu shiga ki huta zan dawo bari  naje wurin A.S.P MUAZ,
   Habeeba ce ta kira mommynta ta sanar mata da dawowar zubaida,

" Kai barka !!! amma ina da majin yata da yawa idan na tashi zan biyo

" Ammi wacece wannan?
haka nan  naji ta shiga rai na.
" Hmmmm kedai kije kiyi wanka,
Habeeba tace" Ammi inaga kamar zata fi bukatar abinci,

Ehh to ina son abincin amma dole sai nai wanka na goge baki na tukunna"
ta kama hannun habeeba tace nagode zo ki rakani daki wallahi tsoro nake ji,
Dole kam suka shiga daki ta jirata tai wanka kafin ta fito habeeba ta zabo mata doguwar riga marar nauyi da hijab
Tai sallah,
tace sis    yaya sunanki ne,
Ta rangado mata sunanta dana  babanta, idan kin so zaki iya kirana da beeba ko beebalon babanta,

Suka sa dariya,
Sukai falo ta sa wayarta a chaji da ta mutu,
Suka sauka kasa har lokacin kasimu bai tafi ba .
Yana zaune  gaban su Alhaji ya kira unaiza ya sanar mata an samu Zubaida,

Ta taya su murna,
" Kayi musu murna kafin mu zo" ki turo min musa yazo ya dauken,
Ya isar da sakon unaiza wa su haj,

Musa ne ya shigo cikin girmamawa ya gaida su ya musu murna ya isar da sakon unaiza da inna,

Habeeba sai binshi da kallo take yi,
Ita dai burgeta yake yi,
yadda yake biyayya wa yayanshi,
Kai ita kam haka kawai taji ya mata,
Duk da ita a burkice take duk wanda yace yana son ta to gaskiya daga rannan zata dauke mishi wuta, kamar mai TAMBŌTSAI,
dadin dadawa ma tana da wasu  kwalities din da take so,
Kuma ta lura shi wannan musan yana da 80% tasan bazata samu duka ba kam,
Amma ta lura musa yana dasu,
Kai ita komai nashi ya mata,  mussamman yana da irin suffar da take so, wato irin ta mutanen YERWA BIRNIN SHEHU  ingarma ne baki mai  sufar kanurai ( duk da cewa ta can wajen inna zai iya debo ruwan kanuran saboda kakanninta fatu suke kawowa da  ga gabas har suka samu mazauni,suka kafu suka hayayyafa,)
Allah ya hore mishi idanu manya amma lumsassu wanda idan ka ganshi zaka iya cewa barci yake ji,
Ga tsAyi ba laifi,
Sannan wani abinda ya kara kwanciya mata a rai biyayyar sa,
  To bari taga yadda zasu kaya,
   Kasimu ya tashi zai tafi ,
suka mike duka zasu raka shi,
Kasimu da zubaida suka kebe ,
musa ya koma gefe, don ya barsu su gana,
   Wai tsaya kana nufin kai ne mammalakin UMAIMISH PHOTO?
Yaya akai kika san haka???
  Ta nuna mashi rigar shi,
Yayi murmushi,
  Ai kuwa faduwa tazo dai dai da zama, zanyi birthday jibi kuma dama ranan ce ANNVERSARY nasu mommyn mu,
To yanzu ke har wani bikin Bday zakiyi???
   Ehh mana,,
  Ba kyau ne??.a
To ai hoto kawai muke yi bamu wannan kade kaden dasu cake din nan, ni dai saboda tarihi nake yi kawai,
  Ta zaro wayarta a aljihun doguwar rigarta ta material ta bashi ya saka lambar  shi,
ta karba ta kira shi " to ka adana kar na kira baka da lambar
Suna fah???
    Beebalo
Sanda dariya ta kwace mishi
  Ehhh sunan kenan,
   Don Allah mi UMAIMISH yake nufi don muna yawan  musu da yan gidan mu sunce hada sunan akai,ni kuma nace larabci ne ko fulatanci,......
Kasimu ya yanke musu hiraan, suka bude musu kofa.  hankali tace da musa zan " maka magana ta whatsapp ka fada min ma'anar, amma a hankali don ko zubaida ma bata jiba ,
Ya daga kai don baya son yaya kasimu ya gane, shifa idan yana gaban kasimu kwakw-kwaran motsi bai son yi saboda girmamawa,,

Inna ce ta tare su tai musu barka da dawowa,

Unaiza ta kawo musu  ruwa da abinci suka ci gaba da tattaunawa,
Kasimu ya numfasa  yace " wai kinsan musabbabin fitan nasu ne?
sayayya suka je yiwa su umaima fah har keke suka sayowa khaleed kinsan sai yau aka fito da kayan?
  Wayyo Allah,
Allah ya saaka musu.

Acan INTERROGATION ROOM fah ana ta fama da Alh Danjuma,
kawai yana ganin ya fada musu danshi ne motar take hannun shi,
A.S.P MU'AZ yace" tunda baza ka sanar mana da gsskiya ba to zan kira wadancan,
   WURNO yace barshi kawai ya zaro naurar mai dauke da SHOCKING  zai juna mishi yace " A HANUN HASEEB TAKE
waye haseeb???
  Yaro na neh yana ina yanzu???
Wallahi ban sani ba,
Suka mika mishi wayaar shi kira shi muji yana ina yanzu???
   Kira shi,
  Ya kira yafi sau uku kafin ya dauka,
WURNO ya mishi ishara da ya sa wayar a handsfree ya danna,
DAD kana ina?
Ka dawo ne?
Haseeb kana ina ne nake jin hayaniya??
  Ka manta yau birthday dina,
Ina ka samu kudin kenan; bana hanaka kudin ba?
Haba tuni munyi wani harkaa mun samu ai kasan a matsayina na babban yaro bazai yuwu ban yiba fah,
Yayi kyau a ina kuka hada nazo nasa muku Albarka,
Yesssss
SNOW WHITE fAMUSEMENT PARK,
kyaaat aka katse aka tusa shi a gaba sai wurin shagalin
Ana tsakiya da chasu sai ga jamian tsaro sukai wuff dasu sunkai su goma,,
Aka watsa su a hilux sai STATE DEVISION,

BA bata lokaci suka amsa laifin su,
aka tambaye sauran biyu su fadi iyayensu ,
abin takaici ma ba 'ya'yan wasu bane face daya ubansa maigadi ne ma, daya kuma  shago ne dashi uban yayi iya kokarin shi ya samu na kanshi ya sha kaishi wurin sana'a amma ina!.
ala dole shi ~BABBAN~ ~YARO~
sukai kwatancen inda iyayensu suke za'a taho dasu
A na kwatancen gidan  WURNO ya buga bence na" fada dama nace akwai hannun na gidaa kana nufin kai dan maigadin gidan ALH BAGUDO NE?

Allah sarki dan kuka mai jawa uwarsa jifa,
An fito sallah la'assar  kawai sai ga motar 'yan sandaa sun tisa keyar Baba Sada maigadi

Labari ya iske Alh ,
Anzo an tafi da baba sada,
A.S.P MU'AZ da DETECTIVE WURNO suka yiwa   Alh bayani

" Kai wannan Rayuwa ina muka dosa ban yi tsammanin baban shi nada hanu ba gaskiya,da baku sa an kamashi ba""
   Alhaji kasan musabbabin neman kudin nasu ne?wai abokin sune fah zai shirya basday baban shi ya hana shi kudin,
shine Rabiun ya shirya wannan ha'incin yasan nan ne kawai za'a samu,
Wai ashe babnshi ne ya kira shi yazo ya karbawa mahaifiyarsu kudin cefane sai yaaji  kana  bada sallahun a shawo wa haj mai a mota zasu fita da yamma,
  shiyasa ya shira  wannan plan din,
Alh ya numfasa yace " don Allah ku sako iyayensu d'an yau ne ka haifeshi ne baka haifi halinshi ba mahaifinshi mutum ne mai amana da gudun zucia, bazan ce kar ku hukunta yaran ba;
Domin idan aka kyalesu a haka zasu ruk'a su zama na gaske "
Ya musu godia sosai ya musu sallama mai tsoka,
Ya tara zubaida da Ammi ya fada musu sukai ta mamaki ikon Allah ya janyowa ubansa masifa don babban case ne fah,
Alhaji na fara kewar yarinyar nan wallahi tana da shiga rai sosai,
Kinga ikon Allah ko? Zumunci ya kullu,
Kinsan mahaifinta Alh maude mun taba yin aiki dashi a works daga baya  gwabbatin data shude tai  mana transper, kuma shima bashi da damuwa,
Mutum kirki ne, zamuje gaba dayan mu anjima muyi musu godia, " amma Alh  sai da daddare  kasan yanzu masu jaje suna kan zuwa,

" Tabbass.,"

Mufeeda naseeba yau na gamu da kwaron nan?
Guess who,
Nasiba ta kalli mufeeda mufee ta kalli nasi,,
Mun baki gari,
  UMAIMISH PHOTO GRAPER
Don Allah kin tambaya mana miye ma'anar sunnan,
  To da yake nasiba ce babba,sai habeeba sai mufeeda duk tsammanin su ma zolaya ce da yake yanayin aikin ta yasa ta zama mai barkwanci indai taga wuri yayi shiru to sai ta sa an dara,.  Ita kuma naseeba, Accuntant ce,
ta gama har ta fara aiki a ministry of justice,
Mufee kuma tana final year anan UDUS.
Beebalo  ta bude whatsapp tayi searching sai ga hoton shi tangararau da
Ta fara duba status sai gashi yayi update da logon shi na  3D kun gani? ku bari zan tambaya mana shi,
Mufee tace gaskiya sis munyi kewar ki fa kwana biyu da kikai baki nan kinsan Aunty nasi gwanar chatting ce , ni kuma sai shiru tunda an hana ni ance sai na gama  jamia,

" Ehh ba hanaki aka yiba ki nutsu kiyi jarabawa ,ki samu sakamako mai kyau,
 
Beeba ta watsa mishi sallama da yake ya sauka,
amma dai tasan yana hawa zai gani
iyalan Alh maude suna zaune cikin wadata da zaman lafiya, mata uku yake dashi amma akwai fahimtar juna sai jarabawa da Allah ya musu;
Shine yaran shi kusan biyar suna zaune Allah bai kawo lokaci ba, don bayan su mufeeda ma akwai kannen su da suma sun isa aure suna jamia,
amma iyayen da yake 'yan boko ne ko a jikin su,
domin sun san tarbiyar da sukai ma wa yaransu,
To ga dai shugaba ta hango  dan matashin yaro,
ko zai yiwu domin idan baku manta ba B musa yanzu yake shekarar farko a jamia,....

Comment