shafi na Ashirin da bakwai

,🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘


MATAN QUATERS


✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼


Kulsum Bappah Azare
Ummu iman


Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com


🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ πŸ‘ŒπŸ»


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…


2⃣7⃣


Da kyar barci barawo ya sace shi, kwana yayi yana mafarki dole washe gari sanda yayi wanka kafin ya tafi massalaci,


Maman salima bata san vgari ya waye ba ma saboda sama sama dai taji kamar baban salima yana tashinta to dama sun saba,
yakan tashe ta a bacci amma fah ita ji take yanzu ta fara bacci saboda takan kai sha biyun dare tana kalon INDIANS MOVIES,


Ya leka dakin ya karkada kanshi,
idan da sabo ya saba abin na matukar kona mishi rai, ""wai ace mace ibada ma bata dame taba"
mtwsss
Dakin shi ya shige ya fidda kayan shi da zai saka,


Ya lalubo wayar shi ya danna kiran laure tana shafa wa salima mai don tare suke fita da babanta, yake sauke ta a makaranta,
taki dauka don taji zum zum dinta kam tabbass amma saboda idon salima yasa taki dauka,


Tana saka mata kaya ne tai dabara ta shiga bandaki ta kira shi,
ba tare da dogon magana ba yace yau za'aje neman aure kina ganin zan bada harda sadaki da kudin kayan lefe ko kuma a hado a kai musu,


Laure fah gaba daya bata sauraran shi,


Ta tsunduma duniar tunani yau itace zata auri IMRAAN,

Chan taji yana cewa
" kinyi shiru"
ta rasa abinda zata ce mishi tunda bata riski maganar shi ta karshe da ya mata ba,


" Eh toh duk yadda kayi dai dai ne, kayi hakuri zanje madafi na dubo dankali akan wuta,


" Kiyi a hankali kar ki kona min jiki,


QASEEMU ne ya dawo daga wurin aiki ya tarar da abin arxikin da ZUBAIDA ta kawo ma yaran shi, yaji dadi har cikin ranshi gashi bashi da number wayarta da ya kira ya mata godia,

UNAIZA ce ta katse mishi tunanin


"Baban umaima kasan yarinyar ta bani mamaki,


Mamakin mi ta baki ??


gaske dai ake cewa yayan masu kudi basu da girman kai,


Mi kika gani gimbiyata ??

Hmmmm kaga aiki - kai har wanka ta yiwa umaima ta shiryata,


Nayi mamakin saukin kanta fah kasan har ( lalle) sanda tasa na diba mata wai ance mata lallen TANGAZA yana da kamu,
Gaskiya idan mahaifinta ya dawo zan je na gaishe su,


Eh nayi tunanin hakan nima,
Bari muga


Har ya fara tafiya sai UNAIZA ta katse. Shi,
Baka san dramar da mukayi ba;


Wai har cewa tayi zata tafi da KHALEEDA,
baban umaima na rasa miyasa XUBAIDAN nan tafi son KHALEEDA,


Ko tasu ce tazo daya inaga,


Ni kin cika ni da magana akan yarinya barni naje na huta,


Yo haka ma zaka ce? Bakuwar kace fah?


Bakuwar ki dai, ai idan tawa ce wurin aikin zata samen,
Ko ?


To shikenan
Amma fah har cikin zuciyar shi yana jin dadin zancen ZUBAIDA
Shi dai da ace so samu ne da zai aureta, to ina!
bashi da halin hakan
wane shi,


Mi nake dashi?


ban ajiye komai ba,


Dai dai da gidan zama ban mallaka ba haya nake yi,
Hmmmmnn.


Abban ZUBY yace uwata dambu nake son ci yau,


kuma na zogale,
Bari na sanar da ummi to,
Sai a nema ayi maka,


Ta samu ummin nasu a madafi take fada mata sakon Abban,


Suna tunanin yadda zasu samu zogale,


Sai can ZUBAIDA tace lah akwai a gidan su KHALEEDA,
Gashi banda numberta da na kira ta bayar an kawo mana, ko ma ta mishi ummi,


Ummi ta juya tace"


saboda zamanki take yi ko?

Ummi tana da kirki ga tsafta ga iya abinci ga kyau kinga umaiman nan kamar su daya,
amma ni kinsan nafi son KHALEEDA,

" Ba dole ki so ta ba tunda kina son Ubanta naga yadda zakiyi a matsayinki na yar malam Bahaushi mai kunya. Kina nuna son namiji,
Hakan ma bai san kina yi ba,
Naga yadda zakuyi"

Ummi in sha Allah, Allah zai duba min,
jikina yana bani yana da muhimmanci a gare ni,
Ummi tace " MAAJI MAGANI,MATAR MAJI TA KI KIRAN MAAJI""


jikinta yayi balain sanyi a dai matsyinta na yar hausa\fulani bazata iya tunkarar wani da namiji tace tana son shi ba,
duk da cewa ba haramun bane,hausawa ne suka
mai da shi abin kunya,
amma yadda idonta ya rufe tana ganin mi zai hana?


In sha Allah ma shine mijin saboda yadda jikinta yake bata,


Maganar ummi ce ta dawo da ita daga duniar tunani,


To ina zuwa,


Ummin da kanta takan tausaya ma yarta,


Akan son masu wanin da take yi,


Duk da cewa itama ummin
bata da burin da ya wuce ace zubaida tayi aure,
Tayi fadan har ta gaji,
Amma Allah bai nufa ba 'yayan masu hannun da shuni da abokan Abbansu da yawa sun nuna ra'ainsu akanta amma ina?


Allah
Yaso Abbanta mutum ne mai fahimta , idan ummi ta fiye mita yakan ce lokaci ne,


Ya kara kiran XUBAIDA uwata kizo ki samen a daki na
Allah Allah nake ki fada min sirkin nawa dai,


To da yake ba boye boye tsakaninta da mahaifinta ta fada mishi wannnan yaron shi na office take so amma bai san ina yiba ma Abba,


Alhamdulillah naji dadi uwata,
ni kaina zan so hakan,
kullum naga nutsuwar yaron da irin dawainiyar da yake min da mutuntani da yake yi nakan yi sha'awar ace jini na ne,
uwa uba yaro ne mai amana yanzu fah duk wasu harkokina shi yake min kama daga BBC&PP ke komai ma shi yake min har ina fada nakan ce " Allah bai ban 'da namiji ba amma cikin ikon Allah na samu wanda yake debin kawar magaji, Allah ya miki Albarka
Kibar komai a hanuna.


Sumi sumi ta mike tayi dakinta,


Maman inti kuwa kullum cikin tura status,
Na kayan sayarwa,


Wata kawarta mai suna ummi yawuri da sukai makaranta tare yaudareta,
Ta hanyar online Business, da yake sun bude group na OLD SCHOOL tana tura musu kayayyaki, kwatsam sai kawar tace tana so,
Maman inti jiki na rawa. Aka koma ta P.C aka hau kasuwanci


Ummi yawuri tayi zabe iya zabe, tace mata in sha Allah gobe zaki samu sakon zan saka a motar BENUE akawo miki,
Sun yi Alkawarin gobe zata je Banki ta turo mata kudi domin tunda kawar ta gane maman inti bata da wani wayewa sosai akan harkar banki karyar kawai take so taci zanyi maganinki,


Jikinta na rawa ta tura mata kaya,


Tayi waya ta sanar mata zuwa yamma zata karbi sakon da yake yar bariki ce kawar tace ba komai Amimiyas nagode nima so nake idan karfe goma tayi na tafi banki nasa miki kudin,


Akai sallama,
Maman inti aka barta cikin jira,
idan taji MTN sun turo sako har gaggawa take ta bude taga Alert,
sai taga mtn ne haka har washe gari, Allah Allah take gari ya waye ta kira ta sanar da ita tace kudi bai shigo ba,


Mijin dai har ya gane akwai wani abu,
Ta kwashe ta faada mishi ya danyi jim sai yake tambayarta ina kin santa dai sosai?
Tare mukai makaranta yar yawure ce amma yanzu suna BENUE da mijinta,

Baban inti yace duniar ce ba yarda amma zai kasance network ne ya hana kudin shigowa,
Ai ko gari na wayewa sai ga kiran mutan BENUE Aminiyas baki ce min kudin ya shigo ba don na adana tellar ina jiran naji kin yi min waya kice ya shigou,


Ayya bai shigo ba maigidana yace min yana ga kamar network ne bai da kyau,


"" Eh zai kasance hakan tunda tun karfe goma na saka kudin ,


Kar ki damu kawata cewar maman inti,


Har zasu kashe wayar sai kawar ta ke ce mata don Allah kina ganin Alert ki kirani,


Kar ki damu wai ita ala dole tana sharewa bata san a tsorace take ba,


Yinin ranar zubur har dare ba Alert
Ta yi magana da baban inti, zata kirata ,
Yace kalli agogo karfe goma ki bari sai da safe mana,
Da kyar ta iya hakurin hakan amma da zaran ta tuna sai taji yankewar zuciya kar dai abinda take ji itama yau ace ya sameta,


Tab tace. ~CHAKWAKIYA KENNA~


Ai takwas batai bama ta kirata

Oh Aminiyas kina raina yanzu nake son na kira ki naji ko kin gani?


Ai kuwa kawata bai shigo na,


Owk kinsan karshen wata ne ana ta salary ma'akatan suna busy baza ki ga Alert ba,


To nagane AminiyaS har na tsorata,


Kai kai kai haba nikam ba haka nake ba,
Ta gama mata dadin baki
Sukai sallama.


MARYAMA ce take ta kaiwa da kawowa A madafi
Ta dauki wayarta ta kira MUSTY ta nemi izinin zuwa gidan maman umaima zata tsinko zogale tayi wa inna dambu,


Ya bata izini suka sha soyayyarsu sukai sallama,
gudun laifin sanda taje wurin inna ta fada mata zata je neman zogale a makota,


Inna ko ta daga murya don Asiya taji,


" Allah ya tsare amma dai ki san gidan da zaki shiga,
don ba na son ki yi sabo da MATAN QUARTER'S din nan mAGulmata wanda basu da aiki sai shige shige da tambada"


In sha Allah za'a kiyaye
Inna,


MARYAMA ta miki ta fito kai tsaye gidan UNAIZA ta dosa tasan itace kadai da maman haneefa masu mutunci a layinsu,

Shiganta yayi dai dai da saukan maman Daddy akan keke napep,

Ta cika da mamaki l, mi ya kawo Maryama gidan UNAIZA?
hada kansu. Sukai ko mi?
Kut akwai DUGURIMA


Bata da kati a waya take ta faSa shiga gidanta ta wuce shagon dake kusA dasu don tasai kati, suyi GURMI.


Ta so zuwa wurin ASIYAR da kanta sai Ta tuna jarababbar uwar mijinta tana nan,
Kwanaki sun shiga gaishe ta, ta gaggasa musu bakar magana
Shiyasa bata fara gangancin zuwa ba,


Alhaji ne ya gama zazzaga ko ina
yaga cigaban da aka samu a companin bai tsaya nan ba suka wuce wurin buge buge da daukar hoto,


sai abin ya kara burgeshi,
QASEEMU ya yi matukar kokari,
Wajen kula da nauyin da yake kanshi abin yama Alhaji dadi suka wuce offishin G.M aka buga lissafi ya samu ribar da bai taba samu ba.
Alhaji yayi ta godia


QASIMU


Ya dago kanshi,
Domin indai suna tare da Alhaji yakan sun kwi da kanshi ne bai iya dago kanshi yana ganin tamfar rashin kunya ne hakan,


Naji dadin amanar da ka rike min ta dukiyata,Allah ya maka Albarka domin a can baya yadda aka ce maka nayi tafiya na dawo,
To zan zo na taradda da bacin rai ne da damuwa,
su na yadda suke so da dukiyata,


Saboda haka akwai amana daya da zan baka,
wanda na dade ina laluben wanda ya dace da ya rike wannan amanar,


Na tabbata zaka rike tunda ka rike amanar kudi ma.


Ya ja dogon numfashi,


Tashi mu tafi gidana,
Ba musu ya mike Alhaji da kanshi yake jan su a mota,


suka dangana da gidan QASEEMU ya zube a kasan dardumar falon Alhaji,
asalin falon shi da yake ganawa da iyalan shi, ya musu masauki,


Ya dannna wayar Ummi yace ki turo min uwata,


Oh dama ka dawo ne,
Eh na shigo yanzu,
Hankalinta kwance ta shiga falo sanye da gyale a yarda ta shiga sam bata an kara da bako a gefe ba, Abba ashe ka dawo?


Kari so mana MAMANA ta kaina;


Zauna can kusa da wancan bakon da kika gani,
Tai saurin waigawa taga mutum kanshi a duke
a siffance sai taga kamar baban twins dinta,


Ta samu gefe ta zauna idonta ya goma kan Abba,


QASEEMU ga amanar da ta rage min na tabbata xaka fi kowa kula min da ita,
Na dade ina tunanin irin mijin da ZUBAIDA zata aura saboda Allah ya dora mata hakuri juriya ganin hakan nake tunanin duk wanda zata aura idan ba mai zurfin hankali da tunani ba zai cutar da ita, saboda na lura samarin yanzu sam basu auren mace don Allah, mafi akasari suna duba nasabarta ce da yanayin karatunta,
suna cewa baza su aure macen da zata zame musu damuwa ba,
Allah ya baka ikon daukar wannnan nauyin ,
Nasan kana da mata a gida kayi kokarin yin adalci shine kawai hanyarka na tsira,
Bari na baku wuri,

A hankali ta mai da kanta
Wurin da QASEEMU yake zaune,
Ji take kamar tayi SUJUDUSH SHUKRI, amma dai ta matse sai ta shiga daki,
Abinda ya mata dadi ma Abbanta bai nunawa QASEEMU itace ta bukaci hakan ba,
Suka hada ido murmushi yayi,
Game da hamdala wa ubangiji,


UMMAN IMAN


TA'ALIKI
ZABA
YA'DA


🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

Comment