shafi na sha biyu

๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜

MATAN QUATERS

โœ๐Ÿผโœ๐Ÿผโœ๐Ÿผโœ๐Ÿผ
Kulsum Bappah Azare
Ummu imanฺค

Follow me on wattpad
@facebook: @[email protected]
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and ู Writer's)_ ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
kulsumbappa
Alhamdulillah ina taya daukaci Alummar jihata ta Bauchi murnan kammala zabe lafiya tare da kyakyawan canji da muka samu Allah ya taya kaura riko ya bashi ikon yin abinda ya dace, CHAU CHAU KAURAN BAUCHIโš”โš”

Ina jajantawa jama'ar kano abinda ya same su na daga zabensu,
Allah yana tare da ku,

ABBA GIDA GIDA KANO SAI TA ZAMA TAKA DA YARDAR Allah,
ูŠุฏุงูƒ ุงูˆูƒุชุง ูˆููˆูƒ ู†ูุฎ

BAKI SHI KE YANKA WUYA!

1โƒฃ2โƒฃ

Bayan dawowar baban umaima ne, ta same shi a daki,
Ya ishshire akan gado dag gani ya dauko gajiya

Assalamu Alaikum

Wa'alaikis-salam

Maman biyu

Na'am baban biyu

Ina kika baro su umaima ne?

Sunyi bacci,

Da wuri haka ?

Eh,

To kin biyo abun ki ne?

Wani abu kenan
Ya nuna mata kanshi
Nasan kina muradi,

Ni?

Allah ya rufa min asiri!
Haba baban umaima
Na kai ina
Rufa min asiri,
don Allah zo ki man matsa
Wallahi nagaji gwanda da Allah ya kawo ki,
Ya ishishire mata kalar tausayi mura ran,

Kisan mace da rau ni idan ta danna yace washi ,haka har ya samu ya fara lallabata aka kai ga ci,

Allah ya miki Albarka matata shiyasa nake Alfahari dake,

Ta lumshe ido,
Dama wani karan bani nayi ban fada maka ba har na yanke hukunci,

Mi ya faru,

To dai karan bani nayi UBAIDA ce mai aikinta tayi tafiya,

tana ta gara ranbar neman wanda zata zauna mata da yaran,

shine ni kuma nace nace ta kawo min su na rike mata ,

kayi hakuri ban nemi shawarar kaba,

da kyau!
gwanda da kikayi hakan,
Hakan yayi dai dai ai,
ka taimaki mutum lokacin da ya ke bukatar taimakon,

Allah ya tayaki rikon su nasan dai baki da matsala akan yara,
To nagode!

Bari na tafi wajen yarana na barsu ba kowa,

Ya kashe mata ido da kika kwashi dadi kika manta dasu ko, sai yanzu zaki tuna dasu,

Haka ma kace ?

Eh,

Ta tsaya tana kallon shi kawai,

Gobe ma rana ce,

Washe gari da safe sai ga maman hanifa da yara harda kayan breakfast dinsu sama sama suka gaisa,

Ta wuce suka tafi,

Baban umaima ya fito hanifa da yake tafi wayo ta gaishe shi yaga kwandon abincinsu,

UNAIZA miye wannan?

abincin sune wai, ta kawo su dashi,

To kar ki yadda ki basu,
Ai bai kyautu ba 'da kam ai na kowa ne,
duk abinda kika dafa su ci,
Toh
Ya mika mata kudin cefane

Allah ya tsare ya kare ka, ta rakashi har kofar gida ya taf.i

T.J ne yaje gidan maman daddy ya dauki chinyere zai kaita makaranta tana da test

Maman daddy tabar sallahu wa mubaraka abinda zata dafa da rana don tana tunanin bazata dawo da wuri ba kasancewar duk ran monday Asibitoci suna cika kuma kwana sukai da Abdul yaronta na uku a zaune ciwon hakori ya matsa mishi,

Har ta fita sai gata ta dawo

'' mubaraka na manta ki kaiwa baban daddy ruwan wanka idan ya tashi'

To Aunty A dawo lafiya,

Allah yasa,

Ta tafi kenan bata dade ba sai ga baban daddy ya tashi, da niyar zai shiga kicin ya duba ko an ajiye mishi ruwan wanka,

Mubaraka ce tsayi tana wanke wanke,

Ita da kanta sanda ta tsargu saboda kayan da yake jikinta
Sun matseta

Wani masifaffen kallon ya watsa mata

Abinka da dan bariki,
Matsowa yayi daf da ita,
Ya kai hannu ya kamo kugunta tai caraf ta matsa,

Ke ban son rainin hankali miye kuma?
Saboda ke naki fita wurin aiki da wuri,
Mubaraka don kina kanwar matata ba shine zai hana mu kulla boyayyar alaka ba,

Na dade ina kwadayin kasancewa dake,
amma fir kin gagara bani hadin kai,

To amma baban daddy matsayin mijin yata kake fah,

Nasani mubaraka,
Ki fahimce ni babu wanda zai gane abinda muke ciki fah ki taimaka min pls,

Ya juyo da ita suna fuskantar juna,

Yarda karara ya gani a idanunta,

Ya kama hannunta kinsan miye?
na dadi ina tare da kishin ruwan kaunar ki musamman ida kika daddame jikin ki da irin wannan kananun kayan,
Tai murmushi ya tallabo fuskarta
Ta kau da kanta domin ba karamin nauyin shi take jiba,

Kunya ta kike ji?
ai ba'a kunyar masoyi,

Hannunta yaja ya kaita dakinshi ya zaunar da ita a bakin gado,
Ina zuwa,
Kofar shigowa gidan ya kulle ya dawo gareta

Ya fara shashshafata yana mata wasu abubuwa tun daga kwakwalwar kanta har yatsar kafarta viberating take ji bai ida kashe mata jiki ba sai da ya rankwafa kanshi a akan dukiyar fulaninta,
Shikenan anzo wurin bata san lokacin da tai watsi da kunya da fargabar da take ji ba ta fara mayar mishi da martani,
Duk barikin shi yayi mamakin mubaraka,
Ba su hakura ba sanda suka biyawa juna bukatan su,

Ya jawota jikinshi yana shafa kirjinta,

'' ka daina don Allah kaga ya kamata naje na daura abinci na ci gaba da ayyukan gida,
Kwantar da hankalinki bazata dawo yanzu ba,

Ya hade bakinshi da nata a haka dai sanda suka sake maimaitawa
,
Bari ma zansa Auntynki ta nemi mai aiki ta rage miki yawan aikin nan,

Taashi ki kawo min ruwan wanka nayi,

Ta maida kayanta ta nufi kicin,
binta da kallo yayi tayi har ta fita ya saukar da numfashi,

Asara kenan yawun bacci don ka auri bazawara ce kake ta wani rawar kai,

Maman Auwal ita bazawaran ba mutum bace?
An dai ji kunya wallahi,

Maryama ce ta fito sanye da wata shegiyar rigar bacci ,

Musty na yaushe zaka kaini kasuwa ne kam?
kasan inada abubuwan da nake son saya na amfani,

Da gangan da ganganci ta yi wata mika,
Gaba daya hankalin shi na kanta ya zuba mata idanu
Tsukar maman Auwal ce ta dawo da shi hayyacinshi,

Mustapha kaja wa matar ka kunne ta daina shigar banza tana fito mana cikin gida,

Aunty Asiya wani irin shigan banza kike fadi?

Ke banyi dake ba,

To ai ni banga abin rashin dacewa a shigar nan ba naga daga bacci na tashi kuma yaran sun tafi makaranta

Eh to nidai bana so a iskantar min da yara,

Ke wai da kike banbamin ina yaran suke yanzu?

Ba wannan ba ina abin karyawata ne Asiya?
Ban yiba,
A wani dalili ?

Ganin damata,

Owk to tashi kika dama kije ki girka,

Bani da wannan lokacin ,

My musty nah bari na shiga kicin din na girka mana mi kake son ci?
suna da yawa abubuwan da nake sonci,

Fada min ko miye shi zan dafa maka,

Ya kama hanunta kice abinda nake son ci sai kuma ki min kunun gyada da soyayyar doya,

Ta kalli maman Auwal tai murmushi don wannan baka da matsala ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne,
Sai dai ina neman Alfarma daya,

Micece Alfarma taka
?
So nake ka bani dama na fara gabatar da girkin saboda kasan idan da yunwa ba abinda zaka iya aikatawa ,
a'a ban yarda ba ban kuma amince ba,
Haba my musty nah
Mai ubanki ne ba my musty ba sai kuyi nagani,
Tsabar su kara tunzurata,

Ya kama hannun maryama sukai daki gam suka kulle kofah

Wayyo abin nema yasamu,

Ta fara surfa zagi ba kama hannun yaro

Namiji dan babansa,
ba ruwanshi da kunya.

Maryamace daure da zani sai wani towel akanta,

Ta wuce kicin

ta umurci mai aiki da ta fere mata doya,.

Maman Auwal ta biyo bayansu ,.kar ki yadda ki sata aiki ba mai aikin ki bace,

Bata saurare taba tai diban karan mahaukaciya da ita,

'' yauwa idan kin gama ki dauraye kisa a tukunya zanzo na daura

Ta kama hanyar ta da niyar zata koma falon kenan ta tsinkayo maganar maman Auwal.

Ke karamar yar iska dake nake magana,

Oh dama dani kike ne?
To da da uban wa zanyi inba ke ba mai nacin tsiya baki da aiki sai kwanciya da miji

Dakata Asiya!!

'' IDAN KINA CIN KASA KI KIYAYI TA SHURI''

an kwanta da mijin
Ke hanaki akayi ki kwanta dashi?

Ballagaza shasha sha wacce bata san ciwon kanta ba sai yawo, baki da aikin yi sai bin gidajen makota gulma, duk tsiyar da kike shukawa mustapha babu wanda ban sani ba,
Tun ina gidan tsohon miji na labari yake iske ne,

Ta juya zata wuce kenan Maman Auwal ta fisge mata towel din dake kanta

Wallahi zaki raina kanki

Ko ke ki raina kanki ba,

Ya ce mata '' baki isa ki hana mai aiki tayi mata aiki ba tunda ba ke kike biyanta kudin ba,
Saboda haka aikin kowa zatayi a cikin gidan nan,

Kyaleta baban Auwal zo mu tafi,

Bata ga kunyar mai aikinta ba ta cigaba da zage zage,

Ta koma dakinta can bayan minti goma ta kara fitowa ta samu larai har ta daura doyar akan wuta
Tana gyara inda tayi aikin,

Tana ta laluben abu kamar mai neman wani abu,

Larai tana fita da sharan kenan Maman Auwal ta sheka kananzir a cikin doyar,
Ta fice,
ta zari mayafi tai gidan maman daddy ta ji kofar a rufe gam
Daga nan tayi gidan maman hydar

Maryama ta gama shiri tasha daurin kwali abinka da mai kyau nan da nan ta haska,

Ta umurci larai da ta saukar mata doyan ta tace,

Aunty Amarya warin kanazir nake ji a ciki

Kananzir kuma?

@ ina aka samu kananxir din?

Wallahi Aunty ban sani ba,
Tabbas kananzir ne kar ki damu sauke ki zubar
Ta kara daukar wata doya ta fere ta kasa ta tsari bayan ta soya ne tabar wa larai nata ta tafi da nasu ciki,
Bayan sun gama ne ta rakashi

Bacci take son yi amma tana tunanin idan yara suka dawo daga makaranta babu abincin da zasu ci dole ta wuce madafi ta daura,

TANGAZA

BELLO gwanda kasa himma ka samu mahifinka kayi mishi zancen komawa makarantar,
Jiya naji musa suna waya da baban naku yana cewa. Ya fara zuwa wurin koyon sana'a,

Na dai fara fada mishi
Yace wai bai yarda ba in har da gaske ne a'i zaka same shi,

Yanzu idan akai sallar isha ya shigo sai ka same shi,

BAYAN ISHA'E

Baba ina wuni?

lafiya,

Yaya akayi naga kayi shiru ne?
dama baba so nake na koma makaranta na karisa ,
to shine nace bari na sameka na fada maka kafin Yaya Alkasim yazo,

Gyatumarka ta fada min,
Hakan yayi dai dai,
da ba don wasa bama ai da yanzu ka gama jami'ar ma,
amma bai baci ba,
Allah ya kawo shi lafiya zan sanar dashi. Idan yaso sai kuyi tafiyarku Allah ya bada sa'a
Amin Baba,

Yaya kuka yi dashi?
Ya amsa min yace Allah ya kawo YA QASIMUN

Naji suna waya da uwar ai zai shigo wani sati,

Sai ka fara shiri,

Kar ka yadda ka ragarwa UNAIZA KA zame mata KADANGAREN BAKIN SHANTU,
haba mama ki daina fada don Allah

ai kisha kuruminki,

SOKOTO

maman daddy ce ta dawo taga har karfe daya da rabi Mubaraka bata gama girki ba,
Gashi ta kwaso yunwa,
Mubaraka yaya akayi ne naga baki gama girkin ba,

Wallahi Aunty bayan na gama wanki wanke ne na kwanta kawai sai bacci ya debeni,

Sai dazu na tashi,
ayya kin dafawa babansu daddy kuwa ruwan wanka?
Eh,
Ta kawo mata ruwa tasha

Kai nagaji don Allah taimaka min na jika wankin kananun kayan ciki na baban su daddy wanke min mana ki gyara mish dakin da gadon''

To Aunty

Maman Auwal bata koma gidan taba sanda tasan yan makaranta suna hanyar dawowa,

ta washi ta bude ido taga maryama a cikin gidan,
maman haidar ta kara mata pampo

tadan samu sauki don ma bata samu maman daddy ba,

Haka rayuwa ta cigaba da gudana UNAIZA kullum cikinn mai da hankali take akan dawainiyar cikin gida da kuma kula da yaranta ko yaushe zaka gansu tsab tsab.
Maman hanifa hankalinta ya kwanta sosai domin yanzu dai dai da tsifar kan hanifa ta daina UNAIZA ce take musu ita da umaimanta

Gashi idan ka gansu kace yayan mutum daya ne saboda yanayinsu iri daya ne,farare kyawawa sirara masu yalwar dogon gashi kullum kitson su iri daya ne ga lalle a yatsunsu,

Maman daddy tun da ta kyalla ido taga maman hanifa tana barin Yaranta a wurin UNAIZA sai ta fara tunanin lalle maman hanifa ta saye UNAIZA ne
,
Takanas tayi tattaki taje gidan maman yanbiyu inji su da fada,

Maman daddy kice a tafe?

Eh

Suka gaisa ta kawo mata robar kunun ayan da take yi na sayarwan,

Maman yan biyu magana nazo muyi dake,

to lafiya?

Lafiya klau,
Dama ina son na miki tallan adashe ne da muke yi

Wani irin Adashe ne wannan?
dashen kati ne,
Kinga duk abinda kika samu sai ki zuba,

Kai maman daddy ina nake da abinda zan zuba dashen?
ai haba kice kuwa kike da hanyar dashe ga sana'a da kike yi ga kuma kudin raino da kike yi,

Raino kuma?

Eh

To rainon wa nake yi kenan

Su Hanifa da hanip mana

Owk ce muku akayi na kudi nake yi?

gaskiya haka mamansu take fadi don naje gidan maman zuhra kenan na tarad da maman intisar tana mayarwa maman zuhran,

Van boye miki ba har maman zuhra na cewa zata zo ta same ki

Mi ya kaiki wannan abin da rufin asirinki da komai,

Wai har tana ikirarin zata zo ta same ki akan yadda kullum kike loda musu abinci marar amfani bata son ta fada miki wai baza kiji dadi ba,duk da cewa kudi take baki

Wai duk inji maman hanifah?

Eh

ai ni kaina da naji zancen abincin nan nace wa maman zuhra sharri ne fah nikan nakan shigo gidan ki nakan ga abinda kuke ci,
amma ni kaina zancen abincin nan ya damen
Sanda na kara tambayar maman zuhra ta kara min dacewa
Tabbass haka tace mata har ta karamin da cewa;

Wai kulum kina cikin dura musu abincin gidanki,
Ita kuma a rayuwarta bata kaunar hakan saboda tana tsoron 'yaranta kar su kamu da wata cuta,

Ke maman daddy duk wanda yace miki na kudi nake yi to karya yake yi muku,

'' ai kuwa idan baki yarda ba yanzu zan iya zuwa na kawo miki maman zuhra ki ji daga bakinta,

@'a ba sai kin dauko taba nagode.

Ita dai UNAIZA a ranta cewa take lalle matar nan zan gwada mata tayi kuskure nayi abun don Allah amma taje tana ya dani don kudi nake yi mata bata sanni bane!

To maman daddy na gode amma zuwa yamma zaki ji ni insha Allahu,

Kamar da gaske ke da baki son shiga cikin mutane,

UNAIZA kuwa wanke kafa tayi bayan maman daddy ta fita taje gidansu hanifa suka gaisa amma fuskarta ba a sake ba
Maman hanipa nazo wurin ki ne,

To bismillah,

Ta kwashe abinda maman daddy ta fada mata shine ''nace bazan rike ki a raina ba gwanda na fada miki
Abinci kuma insha Allah bazan kara basu ba kiyi hakuri
,
Ta tashi ta mike babu ko sallama ta fita........

Ta'aliki
Zaba
Watsa

๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜

Comment