Shafi na Talatin da daya

🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
 
MATAN QUATERS


✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman


Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com


🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)


_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
 
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI,


3️⃣1️⃣


Shirye shirye ya kankama a bangaren Amarya LAURATU, duk da cewa babu  wani abinda zata yi,
so take tayi aure mai albarka,


" LAURATU jiran ki fa nake yi,  kin tsaya kina ta suku suku kinsan wahalar da muka sha jiya a kasuwar nan yau ma kina so mu maimata  ko?


"Ki yi hakuri Aunty gani nan hijabi  kawai zan sanya,
Yauwa Aunty zamu fara bin shagon dinkin nan ko?


Tsoron mi kike yi LAURATU?
bayan munyi dashi zai kawo mana har gida idan ya kammala,


" Aunty ai basu da tabbas ne telolin,
  
Kwantar da hankalinki, banyi tsammanin ya fara tsiyar nan ta teloli ba, shidai idan ki ka bashi kudin shi to angama, ko cewa kikai zuwa dare kike bukata zaki amso abinki,
Zai fi kyau mu fara zuwa kasuwa mu gama da masu labulayen nan.
   
BAHIJJA tana ganin  ikon Allah, wai ace mutum bashi da aiki sai kallo da tabe taben waya, kwanan ta uku a gidan yayar tata dai dai da Cokali bata ga ta kawar ba,
Damuwarta kallo da Bacci da waya,
  Abin da ya ke kara daure mata kayi yadda bata  da lokacin  kulawa  da IMRAN da tilon diyar su SALIMAH,
  Ita dai sheda ce kullum babarsu sai ta mata fada akan  sakaci da rashin kulan da take yi, amma ko a jikinta bata ma san anayi ba,


    SALIMA ce ta katse mata tunanin
" Aunty BAHIJJA zo ki wanke min kashi,


Ki je wurin mamanki ta wanke miki;
   Baki ga ina gyaran kayan miya bane?


  To zai miki yaji kinji,
 
Ammi na tace ki wanke min tana kallo ne


Mtwssss
Ranta ya kara baci lalle kuwa zata fadawa Babarsu,
Halin dai yana nan.


ARKILLA


Wai in kasan na fada baka san na mayarwa ba!
   illahirin su maman  Auwal da maman hydar sun fahimci inda zancen UNAIZA ya dosa, kasancewar sun san alakar dake tsakanin MUBARAKA da baban daddyn, amma da yake kawancen ba don Allah bane ko da wasa babu wanda ya taba sanar da ita,
Don ~IDAN DA AMANA RUWA BAZAI TABA DAFA KIFI BA~
  MAMAN DADDY kuwa ko a ~jikinta WAI AN TSABIRI KAKKAUSA~ bata ma san da ita ake ba,


   " Ku zo mu shiga ciki ~, IDAN KIRE NA YAWO ZABUWA NA YAWO ZA SU HADU~   wannan kiran da Baban umaima ya mata  bai min dadi ba,
  To  ko ya ji mune?


  MAMAN HYDAR
tace a'a inaga bai ji ba gaskiya,
    Suka yi ido ita da MAMAN AUWAL tai mata isharan da su tafi,

SHUGABA zamu ce sai zuwa gobe idan Allah ya kaimu, magariba ta gabato,


Haka ne nima nasan yanzu Baban Daddy yana dab da isowa,
 
Ke MAMAN AUWAL yaushe ULCERN gidan ki zata tafi ne??


     ai tafi karfin ULCER wannan,
Gobe zasu wuce ita da wannan matar,
  Wace mata kuma MAMAN AUWAL ??
   " Matar ubansu mana, yadda na tsani mutuwata haka na tsani matan,
  Wai zata tafi haihuwa gida hmmmmm,
     Kice gobe dabar a gidan ki take,
    " Tabbas shi zai kaisu ma,
     UMMA TA GAI DA AISHA cewar MAMAN HYDAR
Ki godewa Allah, ba don kema kina da cikin nan ba; da  ban san sanaben da zatai miki ba,


Kyalesu kam,


Ke yarbawa suka ce AMEGBO!!
Suka mika hannu suka tafah,
Yanzu maman haydar ashe kowa yasan abinda ke tsakanin Baban daddy da MUBARAKA,


Nifa naji tsoro da UNAIZA ta faccaka mata maganar amma naga ko a jikinta,
   Ke dai bari MAMAN AUWAL
Yau da ta ballo ruwa kuwa, yau da MUBARAKA ta gane ba ta da wayo,
   Yo ai ba ma ita kadai ba;
Har shi baban daddyn kin tuna lokacin inyamura  yar bautan kasan nan, sanda fa ta fasa mishi kai fah, amma ta lauye  mana wai ya buga kanshi ne,
   M AUWAL ni bar wannan batun kina ganin mutumin  nan zai iya rike mata biyu kuwa, yana da halin hakan kuwa, kana maleji da dakuna biyu ka debo aure, wani asararren uba ne ma zai bashi yar shi,
  
Hmmmmm M HYDAR ina ruwan ki? Wanda ya debo da zafi ai bakin shi, ke nashi kika gani baki ga nawa ba, a hakan  fitinanniyar uwar shi tazo ta takura mana.


 
Karfe shida da mintin sha bakwai dai dai jirgin su BILKISU ya sauka a filin sauka da tashi na malik FAISAl BIN SUAD da ke birnin RIYAD, babban birnin a kasar saudi Arebia,
Nan jami'n shige da fice  da  fasa qauri da kuma jami'an hana sha da fataucin miyagun kwayoyi  suka hau aikin su,
bayan kammala tantance kayansu ne suka isa inda aka tana da don haduwa da wandan da suka zo tar yensu,

  HASEEN da Kanwar shi HASEENA  'ya'yan  AMB. MUKHTAR YARIMA  ( ya kasan ce  kawu ne wa BILKISU ) jekadan nigeria,
Suna jiran  fitowar su,


" Kai Aunty BILKISU kinga yadda ki ka zama RUMBU kuwa?


   Kin fara ko ta  dan daki kafadar ta


" Kina hanya kema, Kawu yace min saura kirisss"


Da   yake su uku suka  taho tsaf motar ta dauke su,
Shi mai gidan sai daga baya zai biyo su, baya son yazo ya bata lokaci don ita haihuwa ba'a fiye jiranta ba, ( kamar yadda malam bahaushe ya chanfa ) su uku ne: da ita, da Baba mai mata aiki sai kanwar mahaifiyarta Aunty fati,  da yake mijinta ya rasu shekara biyu da ya wuce, kuma ba  'ya'ya ne gareta ba, ta taba haihuwar yan biyu, ba'ayi suna ba suka koma ga mahaliccin su,
To har  mijin ya rasu ko batan wata bata taba yi ba,

Bangare guda aka basu, mai dauke da dakuna uku, amman guda biyu aka gyara musu baba mai aiki  tana daya sai su a cikin daya,
HASEENA ma nan ta dawo suke kwana ( wai ita a dole lilita tana jiran haihuwa ta yanke chibi ) da yake ba wani rata ne a  tsakaninsu ba,
Sha'anin zaman su a chan din ne ya hana ta aure da wuri,
To kowa na tsoron zuwa yace yana so,
  Gashi dai basu da matsala, Allah ya hore musu son mutane da mutunta su,
    ( Ko da yake komai da lokacinsa)
 


IMRAAN ya rasa yadda zai bullowa maman salima da maganar auren shi,
Gashi abu ya karato, tunda jibi ne,
  amma a matsayin shi na namiji dole ne  ya jajir ce ya sanar da ita ko da kuwa zata shiga jeji ne  dai gwanda ya sanar da ita,


" Idan kin gama kallon ki same ni a daki "
  
Aunty Baban salima yana miki magana
" au haba Bahijja ?
Wai ki same shi a daki ,
  Oho to sai na gama kallon  [THE VOW ] din nan,
   Oh ni Aunty na rasa mi kike kalla a fina finan nan?
    Kinga don Allah dauki salima ku tafi daki kar ki damen,


Kamar saukan ruwa sama ba zato ba tsammani haka taji maganar,
 
Kan uba nan"
(  Tofah zuciyar shi ta yanke domin yasan dama ba sassauci )
    zubur ta miki ta fara zazzago bala'i munanan maganganu da bala'i da ta dinga ambata, kamar zautacciya,

Yana sauraronta kala bai ce ba,
 
Kinga tunda Bahijja tana nan
   Ta taya ki kwashe kaya zan turo mota ta kwashe zamu koma sabon gida.


Sannan gobe in Allah ya kaimu zan karbo miki dinkunan  ki na fadan kishiya,


Kar ma ka fara,
Wallahi konawa zanyi
Wa yace maka ina da bukatar su??
   Ta wuce fuuu ta banko mishi kofa sanda ya razana BAHIJJA dake daki sanda ta fito,

Aunty lafiya???
   Bata saurare taba ta wuce daki,
Allah sarki! Mutum da nashi hankalinta bai kwanta ba sanda ta bi ta har dakinta,

Aunty miya faru?


ta aji wayar,
Mama nake nema a waya ke,


Baza ki samu mama ba saboda tana kashe wayar idan zatai kwanta,


   Aunty don Allah minene?


Wai BAHIJJA ni IMRAAN zai wa kishiya,
   Kishiya kuma Aunty?
BAHIJJAN kanta taji wani iri,
   Amma tasan dole irin wannan rana tana zuwa,

ace mace bata san martabar mijinta ba, bata san kula da  aurenta da kulaa da gidanta da 'yarta daya tilo ba, sai kallo sai danne dannen waya, haba ai dole ma,
 
Bata ankara ba sai ganin Auntyn nata ta jawo akwati tana zuba kaya,


Haba Aunty gaskia hakan da  Za kiyi
Ba dai dai bane,
Ina zaki?
amma kinsan halin Maman da baffah,
ta dai lallabata da maganganu masu kwantar da hankali ,
  Kai kishi masifa ne  ( ga wanda ya dauke shi da zafi)
  Haka ta kwana a tsaye
Idan abin ya mintsine ta ta tafi dakinshi ta juye mishi wutar bala'i ta juya,
   Namiji dan baban shi ko a jikin shi,
    Asuba nayi kuwa ta kira wayar maman tasa mata kuka,
 
Waye ya rasu ASMA'U?
  Fada min don Allah fadamin ki daina kukan,
  Sai shshikan kukan take yi,
Can mahaifiyar ta kashe ta kira BAHIJJA tunda tana gidan,
   Mi ke faruwa ne kam BAHIJJA??
    Wai Ya IMRAAN ne zai kara aure jibi,


   "Kut akan haka ta tsinkar min da zuciya,
bata wayar
Kin bani kunya , kishiyar kike wa kuka?
Wa kika fi zane da baza'a miki kishiya ba,
Ni ba kishiyoyin ne dani ba?
Eyyeh tambayar ki nake?
  ai yayi kokari ma,
da ya iya zama dake malalaciya ai nasha fada miki irin wannan ranar tana zuwa  baki san cin shi ba, baki san shan shiba kukan mi zakiyi?
Ashe kinsan kina son shi kikai watsi dashi?
Ki ka kama talabijin da waya,
Ni da nasan yana da niyyar aure ma da nice da kai na zan nema mishi mata mai nutsuwa da iya lura da miji, ta kashe wayar,


BAHIJJA kinji mama ko?
 
Wai aiki ya samu BAHIJJA sai rarrashi
Don ma bata san waye Amaryar ba,


Aunty don Allah maganar da naji a wajen BELLO da gaske ne??


    Na miye BABA MUSA??


    Naji suna waya da INDO yana mata godia wai sanadiyyar Albishir din da yayiwa makotan ki har tukwaicin kudi suka bashi,
      Haba BABA MUSA nayi mamakin inda su maman daddy suka san maganar, gashi ban fadawa kowa ba sai wa Maman su hanifah, zato zunubi har zuciyata ta fara hararo min itace ta fada musu,


Haba Aunty mai zai hada ta da wannna jahilan?


Ai zuciya ce Bata da kashi,
 
Tabbas gaskiya ne, kuma ina sha Allahu ina kyautata mishi tsammani, Allah  ya bashi ikon yin Adalci,


  AMEEN!  amma Aunty kina ganin bai yi gaggawa ba mi yaya yake dashi?


    Haba BABA MUSA aure ai ba'a shirya mishi,
  Addu'a zamu mishi, Allah yasa sanadiyar Arzikin muce,


Wai shin Aunty a ina ya samo matar?
  
   MUBARAKA CE.


   A'uzu Billahi minash shaidanin rajeem


Maman Nasreen ce

Comment