shafi na Arba'in da biyar

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣5️⃣
Kai amma lalle kin tsula mata  tsiya,
To ke miyasa baki bashi hadin kan ba?

Amma gaskiya suna da aiki,
  indai ko miye ya faru sai sun yad'a da mijinka sai.  Ka yada a duniya ta sani,
Hmmmmm
Maman hanifah kenan ke da unaiza kuna gefe ne shiyasa suka washe ku, ke nima fa Allah ne ya tsamo ni a cikin su,
Da yake baban hydar ba'a mishi warge gaskiya;
Ke kuma maryama mijinku mai hakuri ne over shiyaasa ya gagara tankwasa maman Auwal,

  Hmmm bari kedai yana da hakuri sosai amma fah irinsu _RANDA NE KASHE MODAH_
A ruwan sanyi zai gasata,
Kuma basu iya fushi ba,
   Amma maman umaima kinyi maganin maman daddy fah,
Ke dai barta ai makaho bai san ana ganin shiba har sai an dungure shi,
Da kun barni na zungure ta ai,
   Ki kyaleta kawai santsin takalmin ta zai kada ta,
Har kasaa,

Maryama tace gaskiya nima in dan ta nice taji mana kawai, ai dama idan kasan ta fada baka san na maidawa ba,
Maman hydar tace "
Kaya sunyi kyau sosai fah gaskiya maman. Haneefah kin iya zabe,
  Tai murmushi
Unaiza tace ai yar kaduna ce shiyasa kunsan dama yan kaduna  yan gayu ne kuma yan  bariki ne,
   Maryama tace har kin tuno min da wata makociyata a katsina, fir mijina na fari ya hana ni yin muamala da ita,
Kinsan abinka da masu baki, muna tadi ne sai nake ce mishi" tana burgene yar kaduna ce yar barikice gata wayayya ce,
Ai shikenan ya ara ya yafa wai to wallahi bazan yi muamala da ita ba kar ta buden ido tunda nace idonta a bude yake,
Ina ji ina gani sai dai a boye don a  wurinta ne ma na koyi wasu abubuwan musamman girkin zamanin nan,
Tunda mu dai gaskiya bamu tashi da shi ba, sai rufin asiri,
    Wayar ta ce tai kara
   Mun dawo oga ganin tafe,
Ta yafa gyalenta oga yayi kiraa,
   Ke dai wannnan ogan idan ba _MANDA NE YA SAUKA AKAN KAZA BA_ ba zai kyaleki ba,Sukai murmushi ta karisa gaban maman hanifa ta karbi Farhanah,
Bazaki bari na tafi da ita ba????
Ah toh bari na barmiki akai wa su Humairaa,
  Unaiza tace ai kuwa keda inno da baban Auwal.

B musa bai kara bin wayar shi ba sai da ya gama da makaranta ya tafi STUDIO tukunna ya dauko wayar  ya kunna data,

Messages din Habeeba yaci karo dasu wannin yayi dariya,
Wanin ya bata amsa haka kawai take burgeshi  bata da damuwa bata da dumin kai sam,
Kar fah ka manta gobe ne bad day dina  fah,

" Ai kuwa na manta gwanda da kika tuna min,
   Ashe zamu yanka cake gobe?
    Ah ai nace maka ba cake kawai hoto ne,
Yace
Allah ya kaimu, amma don Allah na tambayeka mana
A rayuwarka baka taba ganin wacce  Ta maka bace?
Ko kana da wasu kwalities ne da kake so a mace baka samu ba,.
    
Ka ga kamar ni zan iya cewa akwai irin kalar da nake son mijin da zan aura ya kasance yana da shi,"

Shidai sauraronta yake yi kawai, shifa bai san wannnan bayanan ba ko don bai taba sawa a ranshi ma ya kai ya saurari budurwa bama balle yasan wannan ,
Shi kuma a rayuwar shi tashin da yayi yaga yayyanshi basu da aikin yi sai aure aure su bar wa iyayensu dawainiyyar  ciyar da iyalan kai dai dai da ragon suna idan sun haihu sai babansu ya nema ya yanka,
Shiyasa yake da burin sai ya girma sosai ya gama karatun shi ya fara aiki ya kuma samu gagarumin aiki, tukunna yayi aure,
Shi kuma a nashi tunanin ma yana son ace matar da zai aura ta zama tana aiki itama su  rufe gidan duk su fita wajen aiki,
Shiyasa su maman hanifah suke burgesu,
Gwanin sha'awa.
  Ko ka sauka ne?

Yaja gauron numfashi
Ya rubuta mata
Gaskiya ban taba zama na tantance  kalar macen da nike so ba,
Saboda inaga kamar da lokaci, bana son sam na hada karatu na da wani damuwa domin inajin yadda abokan mu a makaranta suke. Yawaita hiran
Sun gagara bacci, idan basu ba zasu rayu ba,
Wai sai kiga saurayi a bada assigment bai yiwa kanshi ba amma zai yiwa budurwarshi, kai akwai wani ma,
Bari na miki voice don Allah na gaji da typing
Ta rubuto mishi " kar ka damu zan kira ka,
Sai ga wayarta kuwa,
Ina jinka na lura kai fah matsoraci ne,"
Haba kinga alamar tsoro a tare dani kuwa?
ai kinga kirata ba irin ta matsorata bane,
  Ummn haka kace gashi mata muna baka tsoro,
  Ba haka bane ina jira, da lokaci gaskiya, ina tanadi ne don ban son haka kawai nai ta bata lokaci ina zance da wannan gobe nayi da wancan ba aurenta zan yiba,
  Kana da gaskiyaa, matar ka ta huta lalle zata sha soyayya da tarairaya kasan irinku da kuke komai a nutsen nan idan kuka farA soyayya  sai kun nunawa duniya kuma fa kun faso gari.
Ya kyalkyale da dariya,ina ruwan  ~NANAN GAI NANAN GAI YA SOYAYYAR ASARA~
   Tasa dariya wace irin hausa ce wannan ?
ai kuwa a bakin wani dan AZARE nake ji,
Course mate dina ne,
Ah lalle kuwa ban taba jin hausar ba,
Shi kam karin magana turum a bakin shi kamar dan mahauta,
  To mahautan haka suke???
   Tace mishi yauwa miyasa kake tsoron soyayya kana school?
  Hmmmn abokin mune yaje yiwa budurwar shi jarabawa anan aka kamashi aka cika mishi MALPRACTICE FOAM na dai gajarce miki an kore su, ita mahaifinta har ya fidda ta turai karatu, shi kuma akace mana yana  sai da rake a kofar gidansu, wasu suce har shaye shaye ya fara tunda dama mahaifinshi ba mai hali bane jajircewa ce kawai irin nashi yayi kanzan kanzan dinshi  don ya biyawa kanshi kudin makaranta,
munyi kuka ranar da abin ya faru wallahi.........
   Subhanallahi nima na tausaya mishi amma gaskiya baban yarinyar bai kyauta ba, kuma bashi da adalci, zaka iya nuna min indaa yaron yake,
Sosai ma mi zai hana,
  Muna neman irinsu a wajen aikin mu,
  Aiki kuma??. Ehh
Kina nufin kin gama jamia ma kenan?
  Mi ka gani ?
Jikin ki bai nuna hakan ba kamar wacce zaki zana JAMB bana,
   Tayi dariya ta mishi bayanin yanayin aikin su, to gaskiya muna neman irinsu domin mu kubutar dasu daga wannan ibtila'in da ya same su,
Yanzu ina hutun karshen shekara amma insha Allahu gobe idan kazo muka gama  zaka kai ni wajen shi muga ta yadda zamu fara,
Idan bai yi nisa ba da sauki kawai yan wasu dabaru zamu mishi, idan kuma yayi nisa to sai an hada da REHABILITATION  CENTER,
Yau kam zuciyar ta fal, Tsabar dadin da taki ji ta samu sun yi dogon hira,
tana ta  jan shi da zance don ita kam Allah ne ya kamata maza da yawa son nuna suna sonta amma fafur taki ta basu fuskaa,
A cewarta bata ga wanda yayi mata ba,

*****************************

Alhamdulillah satin biyun da aka kwasa wa su Unaiza da maman hydar ya cika,.ita ta zama cikakkiyar mai dinki, yayinda maman hydar ta zama kwararriyar CHEF,
Inna kuwa har ta hada kayanta akan washe gari zata tafi ai ta zauno kam,
Unaiza Bata so ba amma ba yadda ta iya, "to inna ki tsaya mana ayi bikin dake mana?
Lahh haba ke kuwa, zan tafi nasan su indo zasu taho  da mutanen gidanku naji matar babban yaya ma tace zata zo,
Don Allah ki kiyaye duk da nasan ki da dauriya amma ki kara jajircewa , kuma don Allah ki kara kai hankalinki nesa da zamanku da Bello, bashi da kunya kuma ya samu masu daure mishi gindi.
In sha Allahu
  Tai godia,
Biki saura kwana biyar duk abinda ya kamata ayi na gyaran gida an yi wuri ya dau fenti _dabara kenan KASHIN KWANCE WANDA BAI IYA BA YA BATA JIKIN SHI_
Kaamar tun farkon ginin haka akayi, daga chan gefe aka fitar wa unaiza daki ( na silin ne) aka zuba  mata keken dinkinta da kayan sana'arta, sashin Amarya ma ba laifi, yayi kyau,
Sun shirya zuwa jibi za'a kawo kayaa,
  Unaiza ta mai da  gadon ta dakin  kasimu, nashi kuma aka kai dakin Su baba musaa,
An samu cigabA, amma musa bai yi murnan samun gadon ba, saboda bazai iya hada katifa daya da Bello ba saboda  zunzurutun kazanta,

Kwance tashi ba wuya a wajen Allah, motoci biyu ne suka kawo kayan gadaje biyu na zubaida daya kuma na unaiza ba karamin kyau sukai ba don iri daya ne kala ne ys banbanta,
Tofah yan tsegumi su maman daddy a gabansu aka sauke komai aka shiga dashi,
  Tsabar gulma na cintaa gyale ta yafa a bai bai,
Tayi gidan maman Auwal don wannan tsegumin yafi karfin kirar waya,
  Tayi sa'a kuwa, ba kowa a falo kamar suna baccin rana ne ma,
  " MamaN Auwal ba dole unaiza tai ta kwantar da kai ba kinsan me nagani,
Gadaje ne yan saudiyya  ina irin na matar nan balkisu ta layin bayan nan da akace sun koma saudiya da mijinta??
" Eh aminiyar nagane ta, mutuniyar maman intisar,

Kwarai  ko  ita fah, zaki gane gadon dakinta?
to irin  shine sak sak harda unaiza kala ce kawai ta banbanta,
Kinga dukiyar da ake shigarwa abin mamaki harda akwatuna fah
Ke bari na kiraa Bello naji miye a cikin akwatin kuma,
"    Allah ya tsare min uwar dakina!!!
Ina son na miki Albishir, yayata indoo tana zuwa kuma tace a gidanki zatai masauki,
Kai ! kace ina da babbar bakuwa, Allah ya kawo su lafiya
Bello naga kuna ta aiki, dukiya kenan! naga kamar harda uwar dakinka,.....
Hmmmmm bari kawai komai iri daya ba ma ita ba harda yaranta masu gwalagwalan idon nan fah ke harda keken  ma khaleed kinga har su kafet fahhh ai na gayamiki wai tana jiran nazo na shigar mata da kayan dakinta nayi fuska na tafi wurin 'yan uwan Amarya, kinsan gwanda na fara shiga tun yanzu nasan zasu je su fada mata labari na,
Ka kyauta min, ta kira wannan mai girman kan nata ya mata aiki shege haushe yake bani sai wani girman kai kamar wani dan shugaban kasa musamman idan ya sa wannan riga da hana sallan
Kai hakuri fah dan uwanka ne,
  Ya mulmulo ashar ya maka musu ba musa ba har kasimun ma bani so bani kaunarsuu
Kar su jini sai mun hadu anjima yau akwai hira uwar dakina,.
Ta kashe wayar,
Kinji ko??
   Nikam abin nan yana bani mamaki,
Maman Auwal kice  dole tayi likimo jiya fa ina jiyo maryama tana yiwa inno tadin ita da kanta da kudinta ta hada wa mijin  kayan auren ashe tasan ribaa xata samu,
Rabu da kananan mutanen nan maman Auwal wayo ne dasu da dabara da hikima,
  Ta rakota kenan sukai kicibus da inno,
  To uwar tsugudidi yau kuma mi kika kawo mata,
Almuraa ko baki ji nane,
Kaamar tayi fitsari don tsoro,
Ta fara kame kame kenan sai ga mustapha ya shigo
Tai wuf ta fice,
  
Unaixa ba zama sai kai kawo take yi  suka shirya musu lafiyayyen girki ita da CHEF Hajara ( uwar hydar)
Ga nata gyaran dakin itama,
Gaba daya a gajiye take,
Ga jiri yana ta damunta,kusan tun tafiyar inna take fama dashi,
B musa yace ya kamata muje chemist din babangida jirin nan ba dadi,
Ta amince amma sai bayan sallar isha ake samun shi,
Kinga kafin nan Yaya ya dawo sai ki bar su umaima a wajen shi,
 
ana aunata kuwa aka ga B.Pnta ne ya sauka ya bata ORS yace ki dan samu hutu stress ne,
Bayan dawowar su ne kasimu yake tambayar ta kinyi  P.T test ne?
Raba ne don Allah,
Allah rufa min asiri,
       haka kika ce?
Tace "" Yess ""
Yace to baturiya miya faru?
Wai stress ne B.P na ya sauka wai saboda gajiya,
Amma nikam ba'a ciki kike yin wannan matsalar ba?
Kaga ba wani ciki wallahi,
Bello sai zirga zirga yake yi,
Yana gama nadeewa,
ya wuce gidan maman daddy
Gari na wayewa ta tashi da abincin baki ance mata indoo tana hanya  ita da  matar yaya ( don haka take cewa uwar gidan ya bilyaminu,)
yan gidansu sai ana gobe daurin aure zasu tahoo,
Ta yini a tsaye  jirin bai barta ba,
Tai waya B musa ya  kara sayo  OR.S wani abinda ya bata mamaki B musa ko sashin zubaida bai kalla ba bare yasan mi akayi a wajen Bello ne har waya yayi tun jiya yana fesa wa indoo abin arzikin da aka kawo ,
  Ta fita gidan maman hanifa arowa tukunya don natan ya kasa tunda dole yan jere zasu dawo,
Sai sukai kicibus da maman daddy,
" Uwar gida sarautar mata,
Yaya jiki?
Allah ya sauwaka ai na fada miki duk jajir cewan da kike yi abin bai zoo bane,
Gashi tun kafin tazo jininki ya fara dalewa,
HUMMM MM
_WAYA FADA MIKI BORNO GABAS TAKE!!!!......._

✍🏼
U.K.B

Comment