shafi na hamsin da daya

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:[email protected]
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

Asssalamu Alaikum.barkan mu da yau?
yaya ruwa da masassara da ake fama da ita,
Allah ya bamu lafiya

Gaisuwa ban girma ga :

Maman mu Salihaa Abubakar Abdullahi zaria,

Sumayya Abdulkadeer Takori

Haruna Admin beneficial writer's

Surayya Dee ( halin yau )

Gidan ikoo
.
Ummu Asgarr

Real mai dambuu

Da da duk masu bibiyata a whatsapp groups da wattpad.

5️⃣1️⃣
 
Ka taimaken duk cikin waɗanda nake harka dasu kai kaɗai ne kake gamsar dani,
Kai hakuri kar ka datse alakar nan tamu don zan shiga matsanaicin hali, ba zan iya rayuwa ba kai ba,

Ya ya kake son nayi idan ba kai a rayuwata??

"  Tare aka haifo mu dake da zaki ce baxa ki iya rayuwa ba niba sannu
" DOLPHIN" ko nace tattabaro ko "AYU"
To kinsan dama maleji nake dake,
Na samu yar gayu yar kwalisa wacce bata barin kaxanta a jikinta,
amma ke kullum sai ance miki kiyi shaving,

   Ta kara makalkale muryaa
Zan gyara To.

   " To bari na duba don Allah ki barni aiki nake yi
Kyaat ya kashe wayar

ita damuwarta da baban daddy sai dai yayi ta moranta amma sisi baya bata ga shi dan gargajiyA ne bai iya ROMANCE sosai ba .

T.J kuma da yake dan Bariki ne salo salo na jan hankali ba wanda bai iyaba,
Ga sake kudi
" tab wallahi baxan yi  kasa a gwiwa ba gani take ko zata tafi tsirara sai ta mallake shi yadda bazai iyaa rabuwa da ita ba sai,.tai kwafa tace da ni kake zancen sai na nuna maka nafi namijin  AYU  mannewa tunda shi matar tana haihuwa yake barin jikin nata,
    Laweexa( maman. Daddy ) an sau baki ana ta yiwa mutane kaxafi da sharri.

Zaune take ita da Bello a falo suna abinda suka saba na Gurmi,
" Uwar dakina yaushe zaki shiga wajen Amaryan ne ?

Nifa inason na ga kin kulla alaka da Aunyty Zubaidaa, ba don komai ba don ki konawa Unaixa rai;
Ko da yake na tuna kince sai maman Auwal ta dawo.
  Kai na fasa anjima zamu je gwanda na fara saninta tukunna idan yaso daga baya na gabatar mata da maman Auwal din,
 
Ehh in dai zaki to sai dai yanzu saboda don naji ance zuwa yamma yaya kasimu zai dawoo,
   Eh toh bari na kirawo Mubaraka taxo mu tafi,
Ina son ta shiga jikinta
  
Bello yace ai kuwa zata samu Alheri sosai don indai zai gadon ubanta kam ba sauki,
Sai dai naji indo tana cewa wai taga tana son ta na yiwa unaiza mutunci,

Kaiii!!!! Bello wani irin mutunci????
 
Kinsan wai bata da lafiya daga zuwanta har ta fara girki da wankan yara,

Durun uwata inji matsoraci!!!!
     Girki ??? Wankan yara????
    Lalle unaixa sheɗaniya ce kalan nata salon kenan??
    Bello ya zabura uwar dakina naji indo na cewa wai ciki ne da ita .......
  " Laahaaaila ha ilallahu....
Bello lalle unaiza makira ce,
     Bello ya cafe "" babba ma kuwa.
  Ke dai ki ja mata kunne idan kin shiga,
    Ki mata karatun sosai yadda zata gane,
  Kar ki mantaa ki shigar dani, ki ɗan kukkushe musaa don naga tana wani bashi mutunci da martaba ta musamman,
  
" Kar kaji komai Bello, har sai ka fada ***YO BANZA MA TURURUWA  TAI  DAKO BALLE DAKON KAYAN AUREN 'YARTA*
Sha kuruminka ɗan kanina,
  daukon mayafi a daki.
Ta isko mu chan,
Beebalo ce ta mikawa maman unaixa abincin su a babban warmer don tace har yanxu bata tantance mutanen gidan ba,
   Ta sameta tana haɗa ORS
Sannunku da aiki

" Sannun mu dai " yaya kika kara ji??

   Ai kuwa da sauki, akwai cigaba na ji na ɗan samu kuzari,
   Beeba dake gwanar zance ce tace ai OR$ yana taimKawa sosai sannnan ki samu ɗanyar gitta kullum da safe kina tashi kisa a bakin ki kina dan tsotsar ruwan zai magance miki ( morning sickeness ) din nan

" ai ko in sha Allahu zan gwada.
Nagode "
Sai ka umaima ta shigo dauke dA warmer yar madaidaiceya mai kyau da gani mai tsada ce,
a zuciarta tace masu abu da abunsu,
Mama wai ga faten shuwakan,
Ta mika mata " maxa tai madafi ki dauko min plate,
  Don Allah ki mata godia,
  kinga kunyi Abinci da babansu ne don yana hanya,?

   Kai gaski banyi tsamamin ba

  To kuwa inaga zaku daura sabon sanwaa,
   
Beeba tana shiga taga bakuwa da wani namiji daga jin maganar shi tasan na wayar nan ne,
Gam ta tamke fuskarta

   " Aunty zubaida kin ɗibawa babansu umaima Abincin ne ko wani zaki sake???. 
   Carab dan shish-shigin nan ya amsa "" ai kuwa kamata yayi ayiwa yayan mu special abinci,

Beeba ko kallo bai ishe taba
  Ki yi tunani yanxu maman umaima take tambayata nace wallahi ban sani ba,.

  Maman daddy tace" ha'a bello kaji sanabe ta lakwaɓe bata da lafiya kuma yanxu taxo tana baku umurni ita mi ya hana ta daura mishi, ai amarya bai kamata ace daga zuwanki kin karbi girki ba,
akan yiwa mutum na sati daya zuwa biyu gwargwadon mutuncin uwargida.
     Gaskiya da ace nasan zaki karba ai da na turo miki kanwwata mubaraka taxo tai muku da amarci zaki ji ko da aikin gida abinda baka saba yi a gidan ku ba kaxo kana wahala,

  Beeba kuwa dama tai fam jira take ta kai aya ta tsats-tsayar mata
""
aikin gidan mijin. Ne aikin wahala ?
yaya za'ayi mata tana ibada kuce tana wahala mi a jikon aikin?
to mu ba irin wannna tarbiyar aka mana ba da zamu tashi sakaka babu aiki ,
   Zubaida da yake tasan halin beeba,
  Bata daukan cin fuska da raini tai maza tace mata
Inaga zan nemi musa ya mana sayayyan OKAZI ina da bandar kifi amma bani da ganda da stock fish, ki duba cray fish din nan ko a nuke ne idan ba a nike bane sai na nikaa,

     Bello yayi caraf yace haba Aunty gani a kusa har sai kin nemo wani musa, ki rubuta min kawai naje na sayo miki,
  Beeba ta xari mayafinta zubin CHANTILLEY mai ruwan hodaa da 'yan mukullan motar ta tace bari na bi shagon musa idan bai aikin komai sai mu tafi,.

  Bello ya taɓe baki sukai ido biyu da maman daddy ana haka mubaraka ta karisoo, suka gaisa tana ganin sauran lemu agaban maman daddy ta dauka,
   Zubaida tace a'a bari na kawo miki naki,
Zubur bello ya miki, lah zauna kawai bari na shiga na kawo mata wai shi ala dole dan gida,
Kafin zubaida ta tashi har ya kai ga madafin saai gashi da lemu da kofi,
     Maman daddy dai tana ta mata parpaganda irin nata, tana ta cusa mata ra'ayi, kala kala,
Chan zubaidan tace bari na shiga madafi zan daura tuwo,,

aah mubaraka tashi ki bita mana ai kya tayata ko ?
bari na karisa gida.

Ta xuba mata kayan biki niki niki ta miƙa mata Bello ya karba suka fita,

Ita dai zuciyarta bata aminta da mubaraka ba saboda ita a nata ra'ayin ta tsani mutum da ya canza wa kanshi hallita wato  BLEACHING kyama yake bata to ita wannan har gashi ne ma akanta wato tai fixing attach, bata dai nuna mata ba,
Ita kuma sai rawar kai take yi da shish-shigi ta farke sabon buhu ta debi shinkafa a roba kamar ƙoƙo zubin na india don ita gaba daya robobinta daga madafi zuwa makewayi daga india aka sayo mata na kamfanin ACTION WARE dake cikin. Birnin NEW DELHI
  ta hannun kawar Auntynta fati Abba yar mutan yobe amma suna ce mata F.K.D wai fatin K.D da yake. a kaduna take zaune,
   Mubaraka ta karba mikon na wanke sai ki daura ruwan tuwon,
Tsab ta wanke mata wai tana son ta nuna mata ita ma yar gari ce Aunty miko min warmers din da za'a saka abinci na wanke sai ya bushe  kafin a gama

Naman kaxa ta ciro a deep freexer ta shiga store ta dauko bandar kifi ta gyare su,
Ta fara daura sulalen kazar,
Sukai jirim jirim a madafin ba mai cewa  kowa komai,
Chan mubaraka tace,
Aunty nikam kinsan miye???
Ina sha'awar amare komai naka sabbi ga sabon rayuwaaa, don Allah yaya dadin first night din nan da ake faɗa.........
Zuciarta ta bada dammmm DAREN FARKO sai ga beeba   sun shigo da kaya niki niki ita da B musaa,
ai a fujajan mubaraka tai sallama tace bari naje gida na bar wayata a daki zan dawo,......
Shigo musa da muguwar harara ya beeta ya rasa yadda akai har ta shigo mata madafi

Kan kace kwabo gida ya gauraye da kamshi an hada fruit salad  da kunun  aya an jera komai akan tebir

" madam zan tafi,,
Inji beeba,
Kai haba,
Don Allah ki jira mana
Mi zan jeera? a'a
" To ai kya tsaya kici tuwo mana,
Zuba min a kwano na tai dashi,
   Naga kin zuba wani a wancan ma,
Ehh na zubawa yarinyar nan ne dayan kuma na mamansu umaima ne
Wacce yarinya a ina kika samota duk fiska a kone,
  Kaunar makociyar nan ce....
To kar ki fara...
Zubaida tace  Wai dama an daura da itane ai ba dadi...
  Kina farawa  zai zama kamar kina gayyato sune.
   alhali kinsan ba mutanen kirki bane

Da har zata faɗa mata tambayar da mubaraKa tai mata,
  
a yadda ta lura da halin biba zata iya tattaki ta bita har gidansu ta tsats-tsayar mata,
sai ta tsuke bakintaa,

Sukai sallama ta faɗa wanka,

   Unaiza itama a matsayinta na marar lafiya ba yabo ba fallasa ta canzA kaya
Wurin yayi sai kamshi yake
Ya iso lafiya cikin kudirar ubangiji
 
Bello ya gani ya fito gidan maman daddy ya kariso ya karbi jakar kasimu

Ya Sallami  mai mòtar  kai tsaye dakin unaixa yayi jikin da sauki ya sameta tai freshh alamar karamin ciki yaran suka rungumi shi,
  Ta gaishe shi,
 
Ya taba wuyanta yaya kika kara ji??

Tai murmushi naji sauki amma jiya da kyar nayi bacci saboda rashin sabo,
  Kai
Baki bani ruwa ba da abinci???
  
Lah ka manta da a kofar amarya kake??
  Ina sane
Ya tashi ya  bude warmar ya ga ztuwo ne fate neh, shinkafa,

Ina kika samu waɗan nan??

Amaryar ka,

    Ina Bello ya ajiye min jakar??

  Kai banga Bello ba??

Ya tura umaima ta kira shi

  Ina jakar take?

   Yana chan ɗákin aunty ZubAidA

Ranshi ya baci chan nace ka Kai

ai naga achan kake ne shiyasa na kai.
 
Je ka kawo min,

Unaiza tace   Bello " jeka ka bari kawai.
   
Ba'a haka yanzu ma ka tashi ka je ka huta

Ya zauna ya ce magana zamuyi akan tafiar da nayi mana.

Ka nutsu ka huta munyi  maganar daga baya

Ya tashi ya karisa,

Chan kuma sashin zubaida ta gama kintsa ko ina da jikinta tana jiran karisowar mai gida motsi take ji a falo a tunaninta kasim ne ya shigo tunda taga jakarsa hakan ya nuna mata ya iso kenan,
Wa zata gani indo?
ce zaune ta yaye mata labulaye ta daura su kan kofa wai xafi take ji an dauke wuta,
Ita kuma damuwar zubaida turarukan wutan da freshners din ta ta saka duk sun fita koma nace suna kan fita,

Tsabar kauyanci kuma ta mike kafafunta akan table na tsakiyar falon,
  
abin ya bata mata rai amma ba yadda zata iyaa

Ta tunkari CONSOLE dinta ta dauki room freshner ta kara fesawa ta karisa jikin labulen da niyar ta sauke....
Turusss sukai dukkansu
  
Lallausan murmushi ta saukar mashi

Ya ko maida mata da martani
Sannu dA dawowa baban umaimaa
  Barka!!!
  
  Yana son kamshi sosai ya kamo hannunta suka shiga, kwatsam sai yaga indo,
Ya dan sake hannuntan
    Yaya ka dawo lale sannu mutanen Habujaa,
  
Ya amsa a takaice bai son ganinta a nan amma baxai iya mata magana akan hakan ba
 
Maimakon ta basu wuri a' inaaa wallll  nefa suka kawo wuta
Ta kuwa gyara zama amarYa kunna min T.v?

Ta miko mishi ruwan sanyi a tray da cups ta zuba mishi yashaa
    Na haɗa maka ruwan wanka bismillah,
Sukai cikin daki
Ta mika mishi  tawul ta fita falo don kar ta ganshi yana tubewa,

Ba bata lokaci ya fito ya bude jakar tafiyar shi a ciro jallabiyarsa mai gajeren hannu ya saka ya ga ta ajiye mishi turaree da ROXENA ya feshe jikin shi dasu hammata,
   Ya fito ta mishi jagora zuwa dinning ta debo mashi ruwan wanke hannu a wani bowl na tangaran mai faɗi,
  
Da kanta ta zuba mishi malmala daya babba,
Ta zuba miyaa

"Bismillah"

  "Nagodee, "
  
Babanki yace na gaida ki da kyau,
  
Tai murmushii
  
Ya kammala taxo ta tattare ta shiga madafi ta hau waanke plate din
 
Zubaidaa

Ya kirataa
Ta same shi a kujerar mai zaman mutum  biyu
  Miko min kunun ayar nan???
    Ta kinkimo tray mai dauke da jug din tangaran kamar shape din kwalba amma saman murfin kwallo ne na katako da ya zama shine baakacin na gilas din,
   
Tana so ta dora akan table din gaban indoo amma yai mishi nisa
Dole ta ja karamin stool ta daura akai ta zuba shi ta mika.
A zuciarta tana ayyano rashin hankali irin na indoo
( In banda hauka da kauyanci na mi baxata bashi wuri ya huta ba,

abinda hausawa suke cewa " _RASHIN HANKALI CUTAR MAI RAYI_

Zauna mana ko kin manta bamu gaisa ba sanda kika fara cika min ciki,
      
Tai murmushi " to ina yini yaya hanyaa?? Yaya ka baro babana??. 

au dama tafiyar gidanku yaje a habujan ???
 
Kum sukayi sun manta tana nan
    
Ya dauko wayar shi ya fara danne danne.
 
Aka kira salla ya tafi masallaci bai dawo ba sanda akai esha'e
Indoo tana nan
  Zubaida ce ta canza kaya zuwa doguwar riga irinta larabawan OMAN a zaune ya same su zubaida na la-llatsa wayarta  indo na kallo a inda ya bartaaa,
     dauko mayafi mu tai wurin su unaiza hiraaa
  
Baya son yabar indo ita kadai a dakin

Indo kinyi sallah kuwa????
 
Wallai yaya so nake naga karshen  shirin ,
  A haba da girmanki
  Bai kamata  ba

don dole ta miki tai masaukin su
Yace ruho dakin ki

Maman Auwal tana cikin garari.
   da isarsu ta zari kyale zatai gidansu,

Inno tace da wa Allah ya hadatA

" Yanzu saboda hankali ya miki yawa sai ki tsallake wuri duk kura  ba sharaa,
   To ajiye mayafin
Sannnan ga chan dakin ku  acan zaki saukaa,
Ki gama ki daura mana abincin rana,
  Fara kaɗe min dakin zan kwata na mike kafafuna sunyi tsami,
   
To fah ANA TSORON MU NIDA IYA INJI YAR MAYU"
 
gashi dama ita ba gwanar aiki ba kullum sai aukin sa  yara su mata don idan  yaran ba suyi ba takan iya zaman kwana biyu ba shara ba karume karumen shirgi

U.K.B

Comment