Hakkin iyayena ne page 22

Hakk'in Iyayena NešŸ˜¢



Na
Zainab Yakasai
(Shukrah Cute).





Wattpad:Zainab Yakasai.


Page 22.


Washe gari sai after 10:00am suka farka tun bayan da sukayi sallar asuba Surayyah da duk jikinta yayi weak tayi lamo akan blanket inda nan suka kwana a k'asa,Assadeeq yana shafa soft Lip's d'inta yace "Good morning Damsel" tayi murmushi kawai,ya ta6a forehead d'inta yace "Har yanzu kan naki yana ciwo? Naji dai zazza6in ya sauka" a shagwa6e tayi nodding tana k'ara narkewa,d'an tashi zaune yayi ya d'agota ya rungumeta yace "kenan yau bazamu fita ba" ta d'ago kanta da sauri daga jikinsa tace "A'a please mu fita I like tourism" yaja hancinta yace "Sai abinda Gimbiya tace ai" daga haka ya saketa ya mik'e ya wuce toilet,ruwan wanka ya had'a ya fito yana kallonta daga bakin entrance d'in toilet yace "oya azo ayi wanka" ta mak'e kafad'a,yayi murmushiĀ  yana takowa inda take yace "inzo in d'aukeki to?" Tayi nodding,ya k'araso ya d'auketa yana nufar toilet d'in yakai bakinsa jikin kunnenta yace "Zaki iya yin wankan ko na taimaka miki?" Ta gyad'a masa Kai,a tsakiyar jacuzzi tub ya ajiyeta bayan ya cire mata sleeping gown,shi ya mata wankan kafin shima yayi suka fito rik'e da hannun juna,da taimakon juna suka shirya kafin suka fita a gidan gaba d'aya.


A CARRABBA'S ITALIAN GRIL
LS suka
yi breakfast kafin suka wuceĀ  cinema suka kalli movie,sai kusan 1:00pm suka fita suka tsaya a ice cream cĆ£fe suka siya suka sha a gurin sannan suka shiga near by mosque suka gabatar da Zuhr prayer d'insu.
Suna fita kuma aka kira Assadeeq daga *PORT RICHEY HEALTH CENTER* Inda anan yake aiki kan wata ta samu attack na athma ya tawo,cikin sauri suka samu cab suka wuce hospital d'in,dake baida nisa sosai befi tafiyar 30mint's bane ya kaisu.
Ā  room d'in da patient d'in take suka shiga directly Sury ta k'arasa da sauri tana kallon yadda numfashinta ke sama cike da tausayawa,ganin Assadeeq ya nufi wata drawer ta bishi ta rik'eshi tana hawaye tace "Ya Sadeeq Dan Allah you try asĀ  much as you can to save her life kaji" murmushi yayi yasa finger d'insa yana wiping mata tears kafin ya fito daĀ  abubuwan da ze buk'ata ya rik'o hannunta suka k'arasa jikin gadon da patient d'in take,ya janyo Oxygen kit yana saita shi kafin ya kafa mata tub d'in a fuskarta,dan da nan numfashinta ya daidaita Sury dake ta tsaye har lokacin ta sauke numfashi,Assadeeq ya juyo yaja cheek d'inta yace "Shikenan?" Tayi murmushi had'e da rungumeshi tace "Thank you for been a medical Doctor" ya d'agota yana kallon idanunta yace "You're welcome,are we now good to go?" Tayi nodding,ya rik'e hannunta har zuwa wani office kafin ya sake ta yace ta jirasa ya shiga yayi handing patient d'in over to wani Doctor d'in.


Yana rik'e da hannunta suke fitowa daga hospital d'in,ba tare da Sury ta kallesa ba yaji tace "i always wanted to study medicine amma suka bani Physiology,but shaa they're all the same kuma at long last ma sukayi withdrawing d'ina,kaico na Ya Sadeeq banyi amfani da dama ta ba" tana kaiwa nan ta fashe da kuka sosai,Sakin Hannunta Sadeeq yayi ya juyo da ita facing each other yasa finger's d'insa yana wiping mata tears na both cheeks d'inta yace "its not too late for you my Dear yanzu ma zaki iya komawa university kuma kiyi studying MBBS,kuma kin manta nace ki dena tuna fast life d'inki ko? Ai na yafe miki kuma muna sa rai ma Allah ya yafe miki tunda kinyi regretting sincerely" rungume SadeeqĀ  Surayyah tayi tace "Thank you Ya Sadeeq,you're the best husband on earth.....I so much love you" ya zameta daga jikinsa yana kallon titi yace "ki rakani naga best friend d'ina na Florida tunda na dawo banje ba har ya gaji da kirana yayi fushi fa" nodding kawai tayi masa ya fara nemar musu mota.
Super market Sadeeq yasa aka kaisu suka fita bayan ya biya suka shiga katafaren super market d'in,da ido Sury take bin ko ina don bata ta6a ganin babban supermarket me kaya da yawa kamar wannan ba,line d'in da Sadeeq yabi itama tabi yaja trolley itadai tana biye dashi,chocolate's kala-kala da biscuit's da Sweet's sai wafer Cookie's,wafer stick's da wafer cube's taga ya kwasa masu yawan gaske kafin ya juyo yana mata murmushi yace "me kike buk'ata?" d'an rolling eye ball's d'inta tayi tace "Just ice cream" yayi saurin girgiza kai yace "A'a shan sanyin ya isa haka d'azu ai munsha ki canja wani abun" pouting tayi ta d'auke kai kamar zatayi kuka,ya saki trolley ya dawo gabanta ya d'aga jaw d'inta trying to look directly into her eye's yace "Please don't be upset with my words,bana son abinda zai ta6a lafiyarki ne" d'an kallonsa tayi kafin ta zame fuskarta daga hannunsa tayi faking smile tace "is okay,thanks" d'an shiru yayi yana kallonta kafin ya janyo trolley gabanta tace "hold this and wait for me" ya juya yaje ya d'auko mata ice cream,sai sannan ta saki ranta tana tura trolley suka k'arasa counter,aka gaya masa bill ya bada suka fito hannunsu rik'e da shopping bag's.
Ā  Mota suka k'ara samu suka wuce *IVE'S ESTATE* dake *MIAMI DADE*.Suna knocking wata wadda bazata wuce Sury a shekaru da girman jiki ba tazo ta bud'e ganin Sadeeq yasata ware idanu ciked farin ciki tace "Doctor!" Sai kuma ta d'an 6ata rai tace "Munyi fushi" ya ajiye shopping bag's ya had'e hannayensa guri guda yace "I'm so sorry" durk'usawa yarinyar tayi ta kwashi bags d'in daya ajiye ta basu guri suka wuce itama a shiga.
Zama sukayi nan parlor bayan ta kawo musu ruwa da lemo tace "Sabeer ya fita d'azu da kid's d'in wai zasusha ice cream" Sadeeq ya ajiye cup d'in hannunsa yace "Allah sa bazasu dad'e ba don a hanya muke" yarinyar tana kallon Sury tace "Yanzu zasu dawo,wait! Wai ina Raheema na ganka da wata daban kuma?" Da sauri Sadeeq da Sury suka d'ago suna kallon junasu dukansu zuciyoyinsu na racing.....









Shukrah Cute.

Comment