Hakkin iyayena ne page 16

Hakk'in Iyayena Ne😢






Na
Zainab Yakasai
(Shukrah cute)



Wattpad:Zainab Yakasai


Aslm....fan's kaina bisa wuyana pls,nayi alk'awari ban cika ba,seriously ban samu time na zauna bane....ayi hak'uri pls.
Thank you'll for considering me.



Page 16.


Two day's later....


Sury taji sauk'i sosai don haka Assadeeq yayi deciding kaita gidan Mummy da tunda su kayi auren basu ta6a zuwa tare ba.
Da fara'a Mummy ta taresu ta rungume Sury tana cewa "Amarya oyoyo",Sury ta 6oye kanta a jikinta tace "Mummy mun sameku lafiya?" Kan kujera Mummy ta kaisu suka fara gaisawa cikeda girmamawa,Sury tana kallon stair case tace "Mummy Husnah fa?" Mummy da fara'a tace "Husnah tana room d'inta tareda 'yar uwarta Zahrah" jin an ambaci sunan Zahrah yasa lokaci d'aya mood d'in Sury ya canja,tayi Shiru tana wasa da gold ring d'in hannunta,Mummy tana kallonta trying to observe something tace "Ko bazaki iya hawa ba in kira miki ita?" Yak'e Sury tayi kafin tace "A'a ina hutawa ne" still da murmushi a fuskar Mummy tace "To,Allah ya rabaku lafiya dai" Assadeeq da tun d'azu yake sauraronsu hankalinsa akan wayarsa yayi murmushi jin abinda Mummy take tunani, ba don Sury taso ba ta tashi
tabi stair's,Sadeeq ya bi bayanta da sauri,a kusan tare suka k'arasa room d'in tayi applying fake smile kan cute face d'inta ta k'arasa,Husnah ta taso ta rungumeta tana cewa "Amaryarmu,meet my favorite cousin Zahrah" ta k'arasa tana pointing Zahrah da tunda suka shigo bata ko kallesu ba tanata pressing phone d'inta,Fisge wayarta da Assadeeq yayi ne yasata d'agowa a shagwa6e tana turo baki tace "Ya Sadeeq mana!I'm Using my phone please" Sadeeq yana murmushi yaja hancinta cikin kwaikwayon muryarta yace "Zahrah mana! Nima I want to talk to you" Surayyah da taji kamar ta d'ora hannu akanta ta fasa ihu don takaici ta dinga watsa musu harara,Husnah dai tagumi tayi tanata kallon Zahrah data turo baki ta langa6ewa Sadeeq kai,yadda tayin ya mugun yi mata kyau.
Gbaamm! Sukaji k'arar k'ofa sai a sannan sukayi noticing Surayyah ta fita,da sauri itama Zahrah ta mik'e tace "Husnah barin zo in gudu" Husnah ta zaro ido ta rik'e jakarta da take k'ok'arin ratayawa tace "ha'an aiko bazaki tafi ba,keda zaki yini kuma" Husnah ma tana jan jakar tace "Next weekend insha Allah anan zan miki,yanzu sauri nake" Mik'ewa shima Sadeeq yayi suka sauko duka su ukun a tare,basuga Surayyah a,parlor kamar yadda sukayi expecting ba,sai Mummy dake kitchen ce jin motsinsu ta lek'o tace "Sai kuma ina?sarakan yawo" Sadeeq Yana shafa side burn d'insa yace "Zamu ajiye Zahrah a gida ne" tana kallon stair's kamar tana neman wani abu tace "ita Kuma Surayyah fa? Ko hutawa take?" Nodding Sadeeq yayi mata da sauri yaja hannun Zahrah suka fice don kar Mummy ta k'ara cewa komai,murmushi Mummy tayi ta zauna tana tunanin irin shak'uwar dake tsakanin Sadeeq da Zahrah though ba k'asar yake ba.


***


Sury ko dama data sauko bataga Mummy ba ficewa daga parlor tayi da sauri,sai da taje har bakin titi kafin ta samu Napep akwai ragowar kud'in data d'auka a room d'in Sadeeq da zasuje duba result,dashi tayi amfani ta tafi gida. Da gudu ta k'arasa shiga parlor ta fad'a jikin Mamah dake fitowa daga kitchen rik'eda glass cup,Mamah ta sake cup d'in ta rungume Sury with over excitement tace "Baby it's been long,ya gidan?" Ta k'arasa tana d'ago fuskar Sury trying to  look into her eye's,sai ta saketa da sauri ganin hawaye ke gangarowa daga idanunta, a rud'e tace "Baby are you okay?,talk to me please",k'ara rungumeta Sury tayi muryarta na rawa tace "Mam...Mamah bazan koma ba" Mamah tajata kan kujera tana wiping mata tears dake flowing kan fuskarta tace "Baby meyasa?har yanzu bakuyi settling issue's d'inku ba?" Sury tayi nodding tana Kwanciya a jikin Mamah tana lumshe idonta,tasan it's all her fault,and she's not ready to let Mamah know what exactly is their issue. Shiru Mamah tayi ganin haka tanata shafa bayan Sury har ta dena kukan ta dawo ajiyar zuciya,a haka bacci ya d'auketa Mamah ta zameta daga jikinta ta gyara mata kwanciyarta kan three sitter ta wuce up stair's,room d'inta ta shiga ta d'auki wayarta tana tunanin wanda zata kira,Daddy ne ko Mummyn Sadeeq,koshi Sadeeq d'in da kansa? Zagaye room d'in kawai take tana goge zufar dake keto mata da d'ayan hannunta.


***
It was a long and silent drive,don har suk'arasa gidansu Zahrah ba wanda yace komai a cikinsu kowa hankalinsa na kan phone d'insa banda Sadeeq da idonsa kekan titi,yana parking Zahrah ta fito ta nufi gate dinsu tana waving to Husnah,ta6e baki Sadeeq yayi and he drop away,a gate d'in gidan Mummy Sadeeq yayi parking ya juya yana kallon Husnah da itama take kallonsa with disturbance all over her face,sai da yayi clearing throat d'insa tunda ya dad'e beyi magana ba yace "Ki shiga gida,nima gida zan wuce" kamar zatayi kuka tace "Yaya! Aunty Surayyah fa? Baka kirata ba" ya sauke ajiyar zuciya,tun d'azu itace a ransa besan dalili ba,a hankali yace "Zan sameta a gida,you don't have to worry my dear" daga haka ta fice zuwa gate. Ya d'an jima a gurin kafin ya kunna motar ya wuce gidansa.
A parking spot d'insa yayi parking ya fito waya kare a kunnensa,ya dade yana answer wayar kafin ya Koma jikin motar,har ya bud'e sai kuma ya rufe ya koma ya murd'a handle d'in entrance door d'insu yajita a rufe gam,which means Sury bata dawo gidan ba.Dafe kansa yayi
yana fitar da Iska me zafi,motar sa ya koma ya shiga ya fita daga gidan,bashida za6in daya wuce ya tafi gidansu Sury.
Da sallama ya Shiga parlor ya tsaya yana kallon Sury dake baccinta peacefully,kujerar kusada tata ya zauna yana k'arewa fuskarta kallo a ransa yace "She's extremely Beautiful",jin takun Mamah tana saukowa stair's ya d'auke kansa daga kallon Sury,Mamah tayi faking smile tana zama,ya zamo ya gaidata,ya maida kallonsa gun Sury yana shafa kansa yace "Nazo mu tafi naga kuma tana bacci" Mamah ma ta kalleta tana kai hannu kan k'afarta tace "Ai sai ta tashi Ku tafi yamma tanayi",Tapping k'afar ta farayi,Surayyah ta tashi tana murza idanunta tana kallonsu,murmushi Sadeeq ya mata ta d'auke kai,Maamah tace "tashi ku wuce yamma yanayi" Sury ta turo baki tace "Ni bazan bishi ba" Mamah cikin lallashi tace "Meyasa to?" Sadeeq yayi saurin cewa "Bafa wani serious issue bane Ma! She's just jealous don ina wasa da cousin sister na shine ta tawo,and I come to apologize" Mamah tace "Kai Baby,ki tashi to ku koma tunda ya baki hak'uri" shiru Sury tayi not ready to talk,Assadeeq yayi k'asa da murya yace "please" Mamah ta mik'e ta ja hannunta ta d'agota tace "Kuje please", a hankali ta dinga bin bayan Sadeeq dake gaba Mamah ma na biye dasu har jikin mota,sai da suka fita ta sauke ajiyar zuciya hoping that zasuyi settling matsalarsu.
  A hanya Surayyah sai kallon Assadeeq take a ranta tana cewa 'Wannan ba k'aramin munafiki bane', ta jingina for the first time kuma taji ta fara regretting rashin rik'e mutuncinta da tayi,da ta kama kanta da duk haka bata faru ba,bata San yadda akayi ba sai jin hawaye tayi yana zuba a idanunta, a wani traveling agency Sadeeq yayi parking ya juya yana kallon Sury can ciki yace "Kinada passport?" Ta d'auke kanta batace komai ba,gajiya yayi yace "Sauko muje a yimiki to,visa zamuyi next week zan koma aiki......

Comment