Hakk'in iyayena ne page 7

: Hakk'in iyayena ne😢



Na
Zainab Yakasai
(Shukrah cute).



Wattpad:Zainab Yakasai


Don't forget to vote pls.


Page7.


A main parlor Assadeeq ya Samu Mummy tana zaune,Ya durk'usa a gefenta,tana murmushi tace "Son har an dawo,ya Mamah? Ya kaga Surayyah tayi maka dai ko?" Yayi murmushin takaichi yace "Suna lafiya,Mummy Surayyahn Tana da hankali sosai da tarbiyya" Mummy ta shafa kansa tace "Masha Allah tayi dai,bari Daddy ya dawo muyi magana" Mik'ewa yayi ya k'arasa fridge ya bud'e ya d'auki bottle water ya wuce upstairs. Mik'ewa Mummy ma tayi zuwa room dinta,Wayarta ta d'auka tayi dialing number Mamah tana zama a gefen bed,ringing biyu Mamah tayi picking da fara'arta tace "Hajiya ya kuke? Sadeeq ya komo lafiya?" Mummy ma da farin ciki a muryarta tace "Lafiya lau,yace Surayyah tayi mishiq hundred percent,sai yaba kunyarta da nutsuwarta yake tunda ya dawo" Mamah with excitement tace "Masha Allah,ki masa bangajiya,sai mun sake magana" Daga nan sukayi hanging.
Room d'in Sury Mamah ta wuce daga nan ta tura bayan tayi knocking, a kwance ta sameta,ta zauna gefenta tana had'e mata gashinta daya barbaje tace "Bakya son kitso Baby,gashi nan gashi baya gaba baya baya ai" Surayyah ta tashi zaune tana turo baki tace "Da zafi fa Mamah" Mamah tace "Ba wani nan mak'iwaciya" gyara Zama tayi in a serious tone tace "Baby d'azu yayanki yazo ai" Sury tayi nodding tana kallonta,Mamah ta d'ora "Dama yaga picture d'inki ne gurin Husnah shine yace kin masa shine yazo ganinki,ya kukayi?" Sury ta kasa 6oye farin cikinta tace "Amma ni be gaya min ba,nima gaskiya yayi me kyau dashi" Mamah taja kunnenta tace "Fitsararriya ni kike gayawa ya miki?Allah Shirya,yanzu kunyi exchanging numbers ne?" Sury tace "A'a" tana komawa kwance,Mamah Tace "Shirme kenan,zan cewa Mummy ta bashi to" daga haka ta fice a room d'in,Kwanciya tayi akan bed kafin ta kunna Data ta nemo Mummy,tana online kuwa,tace mata.
  "mummynsu,sai kuma Sadeeq ya manta be kar6i number Baby ba"
Mummy ta turo imojin zare ido tace
   "Me kenan akayi Hajiya?bari in masa sending yanzu" daga haka Mamah ta sauka.


**
A 6angaren Surayyah kuwa har yau bata samu labarin Hameem Na,mistake tayi bata kar6i number sa na Senegal ba,gashi har yanzu be neme ta ba,juyi tayi had'eda jan tsaki tace a fili "Kar ka nemeni d'in ni yanzu ma na samu wanda ya fika".


Washe Gari.
Sury da Meenah na zaune a capteria wata friend d'insu tazo ta zauna tana cewa "Kunji wai anyi pesting exam timetable?" Sury tace "Haba haba yaushe ma aka fara semester d'in" Meenah ta harareta tace "Kina fashi yaushe zaki gane tafiyar semester?semester dai tayi nisa amma a ka'ida sai nan da 3weeks za'a fara exam's fa" yarinyar tace "kinsan Anata cewa za'a fara strike may be shiyasa zamuyi exams din kar strike ya rik'e mu" Meenah tace "Haka ne,Allah ya bamu sa'a" daga haka suka cigaba da hirarsu kafin suka tashi suka koma lecture hall d'insu.
Kwana ukun da aka basu kafin exam's d'in ya mugun yiwa Sury kad'an don a semester gaba d'aya babu Wani course da taci rabin karatunsa gashi courses 12 suke, gashi tayi missing test's bare tace zata iya making,wanda ta samu tayi ma ba wani abun arziki tayi ciki ba,abun ya dameta sosai har ta kasa yin karatun ma,dama Hameem ne hope d'inta da yace zai kaita skyline gashi babu shi babu labarin shi.
Ranar da zasu fara exams ta shiga tashin hankali ganin CHM 211 zasuyi,tayi tunanin da Bio zasu fara don shi ta d'an duba jiya,giving up tayi ta shiga.exam d'in ta bata wahala yadda batayi zato ba don dakyar ta samu ta answer question d'aya,gashi ba hall d'aya suke da Meenah ba duk bata San wanda aka had'a ta dasu ba.
Da kuka ta k'arasa gida, Mamah dake parlor ta tareta tana tambayarta ba'asi,cikin kuka Sury tace "Ko ba exam d'in bace ta bani wahala" Mamah ta rungumeta tana patting bayanta tace "Im so sorry my  dear,insha Allah you're going to make it indai kece" Sury ta k'ara fashewa da Kuka tace "Mamah wallahi I can't make it,ko test d'in course d'in fa banyi ba" Mamah ta d'agota tana mata kallon tuhuma tace "Garin yaya kikayi missing test din?" Gaban Sury ya fad'i bata san ma sanda bakinta ya Ku6uce ta fad'awa Mamah ba,sai tayi saurin cewa "Koba online akayi ba,Kuma ranar banida data" Mamah ta daka mata tsawa tace "Meyasa baki gaya min bakida data ba bayan kinsan kuna abubuwa online?" Sury tana wiping tears tace "ai yace zeyi mana makeup" Mamah tace "Allah ya sawwake" daga nan Sury ta wuce upstair's.


Ranar da suka gama exam's Assadeeq yazo,a main parlor suka zauna shiru tun bayan gaisuwar da tayi mishi,shikam kallonta kawai yake har a lokacin be dena mamakin irin wayonta ba da har take aikata abinda Take Mama bata gane ba,ranar har bugun cikin Husnah yayi yaji ko ansan halayenta amma sai ce masa tayi ai Sury shiru-shiru ce,kamila.


Yayi clearing throat d'insa bayan ya dawo daga tunaninsa yace "Kina wani level ne a university?" Tace a hankali "level 2" ya d'an zaro ido alamar mamaki yace "Har kin kai level2? To wani course kike?" Tayi murmushi tace "physiology" yace "Lallai kina so ki zama likita kenan?to meyasa bakiyi MBBS ba?" Murmushi ta sakeyi tace "ai shi nayi applying amma suka bani physiology,but all the same ni nama fi son Physiology d'ina" yayi dariya yace "what you get is what you'll use right?" Tayi nodding,yace "Fine! So are you ready to get married?" A ranta tace 'so early' kafin a hankali ta d'aga masa kanta,yace "Good,zanyi magana da Daddy zuwa nan da karshen shekarar nan sai ayi ko?" Ta rufe ido alamar jin kunya tace "Ai second semester muka gama yanzu,kuma 3month's ne hutun mu" yayi dariya yace "ayi yanzu kenan? Shikenan Madam yadda kika ce,zan gaya musu" ta rufe fuskarta tana dariya,shi kuma ya bita da harara yaja k'aramin tsaki can ciki.
Har bakin motarsa ta rakasa tana ta murna kamar tun da can sun saba da juna ne.tana Komawa ciki ta rungume Mamah dake k'ok'arin shiga kitchen tace "Mamah I'm getting married soon,may be a cikin hutun nan" Mamah ta d'agota tana rik'eda ha6a tace "Baby bakida kunya wallahi" k'ara rungumeta Sury tayi tana Dariya........

Comment