Hakkin iyayena ne page 15

Hakk'in Iyayena NešŸ˜¢





Na
Zainab Yakasai
(Shukrah cute)




Wattpad:Zainab Yakasai.




Page15.


Da daddare bayan Sury ta gama Komai ta kwanta all exhausted at the same time so lonely wayarta ta d'auko tana missing social media sosai,lokaci kuma d'aya zuciyarta yasa tayi trying number Hameem na Nigeria dake kanta,number tasa a wayar ta kira amma a kashe,saving tayi kafin ta kunna data ta shiga play store,dan danan tayi downloading WhatsApp,twitter,IG,fb tayi installing.
Number's da sukayi appearing a WhatsApp d'inta ta fara bi, taga ta Hameem tahau,zuciyarta tace ta dubashi aiko tana bud'ewa ta ganshi online,Zumbur ta mik'e ta ajiye wayar tasa finger's dinta na duka hannu biyun ta murza idanuwanta trying to believe she isn't dreaming,d'aukar wayar ta k'ara yiĀ  ta masa sallama,kusan 5mint's tana zaune ta k'urawa wayar ido taga ya fara typing,tashi tayi daga zaunen da take ta tsuguna a kan gwuiwoyinta ta tallafe kumatu tana jiran tsammani.
_Wslm.who's this please?"_


Shine abinda taga yasa,ajiyar zuciya ta sauke kafin ta d'au wayar hannunta har rawa yake ta fara typing.


_Hameem! Why did you keep me waiting for God sake,you made me feel betrayed why pls?.....it's Surayyah"_
Karanta message d'in Kawai Hameem yake trying to recall who exactly is Surayyah to him,don shi saurin mantawa da 'yammata yake,da yaci moriyar ganga yake yarda Korenta,can yace:


_Surayyah? Pls I can't recall you,I need more light about who you are to me_


Gabanta ya bada *Dammmmm* wai ita Hameem yace bai gane ba,upon all that she did to him? She gives him everything including herself,ya ilahie! Ta dafe goshinta,she can't even type sai ta fara masa VN muryarta na rawa tace:


_Hameem,how can you said you can't recall me....I'm your Surayyah,idan ma wasa kake ka bari pls kana bani tsoro,kasan I can't do without you,I'm thinking of youĀ  with every single breath,pls don't betray me I can withstand....._ sai kuma ta fasheĀ  da kuka ta mishi sending tana kife kanta a jikin pillow,dai-dai nan Assadeeq ya bud'e k'ofar room d'in ya tsaya yana kallonta da mamaki,kukan Sury ta cigaba dayi duk kuwa da tasan Sadeeq ya shigo room d'in,Ganin she's not ready to stop yasa Sadeeq cikin muryar bacci yace "ke!lafiya kika cikamin gida da koke-koke kamar gidan mutuwa?" Banzan da tayi masa ne yasashi k'arasawa cikin d'akin yana karewa every angle kallo,jinshi a kusada gadon yasa Sury saurin janye wayarta dake gefenta zuwaĀ  pillow,akan idon Assadeeq,da sauri ya haura gadon for the first time in his life,yasa hannu ya fisgo wayar yakunna,still wayar tana kan chart d'insu da Hameem,scrolling up yayi ya koma farkon chart d'in,har yazo kan VN d'inta da Hameem yayi listening beyi replying ba,murmushin takaici yayi ya kashe wayar gaba yana sawa a side pocket yana k'arewa Sury da tunda ya d'auki wayar ta d'ago kallo,nunata yayi da yatsa yace "A gidana kike chatting da gardi Surayyah?a gida na? To wallahi you've made the great mistake of your life kuma by Allah sai nasa rayuwarnan da zame miki tamkar gidan kurkuku,sai na wulak'antaki kamar yadda kike wulak'anta min igiyar aure na,kuma daga yau bake ba waya har abada ki gayawa duk wanda zaki gayawa,jahila kawai!" Daga nan ya fice da sauri don idan ya tsaya zuciyarsa zata iya sakashi ya kasheta a yadda yakejin kansa.


Dakyar bacci 6arawo yayi gaba da Sury,she can't believe wai Hameem ya manta da ita ne....anya kuwa ba wasa yake mata ba?,da safe da zazzafan ciwon kai ta tashi,dakyar tayi wanka ta dawo ta kwanta cikin bargo sai shivering take saboda zazza6in daya rufeta tunda tayi wanka.
Sadeeq ko yana kwance parlorn downstairs yana lissafin kwanakin da suka rage masa a Nigeria,dama Annual leave ya d'auka gashi yana neman k'arewa,thought of going back with Surayyah yana zuwa masa yaji ransa yayi masifar 6aci,sai ya tuno tana karatu a nan ya saki lallausan murmushi yana shafa side burn d'insa yasan anan zai barta,inma tana tsoron zama ita d'aya sai ya d'auko mata Husnah,har 12:00pm yana gurin kwance,mik'ewa yayi ya shiga kitchen yana k'ok'arin d'ora indomie,door bell rings yaji ya ajiye knife da albasar hannunsa ya fito ya bud'e,wata budurwa ce wadda a shekaru bazata wuce Sury ba a tsaye,ya mata murmushi yana bata hanya ta shiga gidan,k'ofar kitchen ya tsaya yace mata "Sannu" tana murmushi ta zamo k'asa tana gaidashi ta d'ora da "k'awar Surayyah ce,tana nan kuwa?" 6ata fuska yayi don ya tsani duk k'awayenta don a zatonshi suke da alhakin lalacewarta,har ya bud'e baki zaice bata nan sai sukaji footsteps daga stair's,gyara tsayuwarsa yayi yana k'arewa Sury dake cikin peach jilbab kallo,ya mata kyau sosaiĀ  duk da fuskarta tayi fayau alamar ramewa,tana murmushi tazo ta zauna kusa da Meenah ta rik'o hannunta tace "K'awata ashe zakizo" Meenah da duk bataji dad'in reaction d'in Assadeeq datace ita k'awar Sury ce ba tayi yak'e tace "Aikuwa,na miki message dana ganki a WhatsApp bakiyi replying ba kuma na kira wayarki yau da safe a kashe,dama result akayi pesting nazo muje mugani" shiru Surayyah tayi tana kallon Assadeeq da har a lokacin yana tsaye yana sauraronsu,sai taga ya juya ya koma kitchen,jiki a sanyaye tace "Meenah bari na tambayo shi",daga nan ta mik'e ta bishi kitchen d'in,zama tayi kan kujera tace "Zamuje duba result" kamar bazeyi magana ba sai kuma yace "karku dad'e" murmushin jin dad'i ne ya kwace Mata don dama batasan da idon da zata kalli Meenah ba idan ya hanata,da sauri ta mik'e zata fita taji yace "akwai kud'i a bedside table d'ina",room d'insa taje ta d'auko suka fice daga parlorn.


**
A hanya Meenah ta kalli Sury da ta tafi duniyar tunani with so much care tace "Friendy....meke damunki ne? It's like bakya jin dad'in auren nan,karki 6oye min komai ki fad'amin matsalarki may be I can settle for you" murmushi Sury tayi tana wasa da gold ring dake hannunta tace "Meenah kallon kitse ashe na dinga yiwa rogo?Ashe ba yadda na d'auki aure yake ba? Idan nace miki na ta6a jin dad'i dai-dai da rana d'aya a auren nan k'arya nake wallahi" Meenah daketa kallonta with disturbance akan face d'inta ta rik'o hannunta tace "Sury a baibai kika kalli aure,ba matsala bane Sam,may be dai kuke da matsalarku,kiyi tunani sosai baku ta6a samun serious issue da Dr. ba" Maganar abortion da Assadeeq ya ta6a yi mata ce ta fad'o mata amma batajin zata iya gayawa Meenah don tanajin kunyarta Sosa I cuz Meenah k'awace ta gari kullum cikin yi mata fad'a take kan karatun ta da kula samari,sai kawai Sury ta lumshe idanunta da suka kawo kwallah ta jingina da seat.
A haka suka k'arasa School kowa da tunanin da yake a ransa,department d'insu suka wuce inda suka tarar da wasu class mate's d'insu suma suna dubawa,dake registration number ake amfani da nan suka fara neman nasu,na Meenah aka fara gani ta samu flat A, tanada First class kenan,abinda suka gani ana Sury ne ya mugun d'aga musu hankali don Surayyah Flat E ne da ita kuma sunyi withdrawing d'inta,jin Sury na k'ok'arin fad'uwa sakamakon jirin daya kwasheta yasa hankalin Student's d'in dake gurin yin kanta,rirrik'eta Meenah tayi tana mata Sannu a hankali trying to calm her down,dakyar suka k'arasa gate sukayi katarin samun me Napep suka shiga,a k'ofar gidan Sury ya saukesu still Meenah na rik'e da Sury suka danna door bell,Sadeeq da dawowarsa gidan kenan daga gidan Mummy ya tsaya yana shan ruwa downstairs yazo ya bud'e,kallonsu ya tsaya yi da mamaki kafin ya kar6i Sury daga hannun Meenah yace "Meya faru?" Shiru Meenah tayi da farko kafin tace "Jiri ne yake damunta" daga haka ta juya tace "Allah ya sawwak'e sai anjima"


Kan 2 sitter ya jasu suka zauna yana mata sannu har ta d'an fara nutsuwa sai a nan kuka yazo mata ta fashe masa kuwa dashi,Sadeeq a rud'e yake tambayarta menene ta mishi shiru,har akayi magrib suna zaune a gurin kafin kowa ya tashi yaje yayi alwala,mosque ya wuce ita kuma tayi sallah a nan parlor lokaci d'aya zazza6i yazo ya rufeta ruff,tanata duk'unk'unewa cikin hijab d'in jikinta yazo ya sameta,d'agota yayi yana k'ok'arin feeling temperature d'inta da damuwa yace "kink'i gayamin damuwarki tun d'azu ko accident kukayi?" Lokaci d'aya ta fashe masa da wani kukan tana girgiza kanta murya na rawa tace "Ko....koba withdrawing d'ina akayi a makaranta ba" saurin d'agowa yayi yana kallonta yace "meyasa bakya maida hankali a makarantar to? Ko yawon bin maza kike tafiya bakya zuwa?" Shiru tayi masa don taji ba dad'i,ya girgiza kai yace "Kin kyautawa kanki sai kizo kiyita zaman gida tunda shi kika za6a don banida kud'in enrolling d'inki a wata yanzu,amma ki sani *HAKK'IN IYAYENKI NE* yake bibiyarki,saboda sun yarda dake ke kuma kinci amanar su.

Comment