Hakkin iyayena ne page 17

✨: Hakk'in Iyayena Ne😢



Na
Zainab Yakasai
(Shukrah Cute)




Wattpad:Zainab Yakasai




Page 17


Cikin lokacin da bai wuce 2 hour's ba suka gama da traveling agency,Suka kama hanyar gida,Sury daketa kumbure-kumbure ta fice daga motar yana parking,gaba d'aya batajin tafiyar nan kawai hankalinta bai kwanta ba,room d'inta ta wuce directly ta ajiye veil d'inta hadeda zame gown d'in jikinta,tana k'ok'arin Shiga toilet Assadeeq ya turo k'ofarta,tayi still tana kallon yadda ya tsaya yana kallonta from head to toe,sai tayi saurin sunkuyawa ta dunk'ule guri d'aya ganin a inda ya tsayar da idanunsa,murmushin takaici yayi ya fara takowa cikin room d'in,Sury batasan yadda akayi ba kawai dai ganinta tayi a cikin toilet ta jingina da k'ofar,ta juyo tayi saurin saka key,tana jin sanda ya murd'a handle yajita a rufe,sai da taji fitarsa daga room d'in ta sauke ajiyar zuciya ta sakarwa kanta shower.
Fita Assadeeq yayi ya cigaba da musu processing visa har bayan magrib kafin ya kammala,a Albaik chickens dake Zoo road ya tsaya ya musu order fried rice kafin ya tafi gidan,be ganta downstairs ba sai ya haura sama,suka kusa cin karo a k'ofar kitchen zata fito,yayi mata murmushi yace "Ashe zakiyi girki naje na siyo mana abinci" ta masa kallo d'aya ta d'auke kai ta fara tafiya kafin tace "Ba girki nake ba,tea zansha" yayi saurin dawo da ita gabansa yana watsa mata harara yace "Zan baki mamaki idan ina miki magana kina tafiya wallahi" batace komai ba illa d'auke kai da tayi tana shirin sa kuka,ya dinga bin fuskarta da kallo,bayajin ze iya gajiya da kallonta saboda tanada kyau bana wasa ba,sun dad'e a haka kafin ya rik'o hannunta zuwa room d'insa,a gefen bed ya zaunar da ita ya ajiye polythene bag d'in hannunsa ya fice a room d'in,ta bishi da harara kafin ta cigaba da k'arewa room d'in kallo wannan ne shigowarta na biyu,room d'in kuma yayi mata kyau don sam ba Hayaniya kamar d'akin Mata,jin Shigowarsa yasata juyowa,be kulata ba ya zauna yana bud'e ledar daya ajiye ya dire mata park d'aya a gabanta bayan ya bud'e yasa spoon d'in daya d'auko a kitchen,sai da ya fara ci kafin itama taci,kusan rabi taci kafin ta ture tana k'ok'arin komawa kan bed ta zauna,ya tsareta da ido kafin yace "In cinye nawa in k'arashe naki kike nufi?" Ta turo baki tana girgiza kanta,yace "to k'arasa kar kimin asara malama" badon taso ba ta koma ta cigaba da cin abincin da sam be mata dad'i ba a matsayinta na caterer.


2 day's later....
Lokacin saura 2day's su tafi Assadeeq da Sury sukaje suka yiwa Mummy Sallama,Mummy Kayan kamshi da kala-kalar yaji ta bawa Sury a matsayin tsaraba daga nan kuma gidan Mamah suka wuce,a parlor suka sameta tare da Daddy suka zauna suna gaidasu kawunansu a k'asa,Daddy daya dad'e bega Sury ba ya dinga binta da kallo ganin ta sauya gaba d'aya tayi sanyi kamar ba rigimammiyar yarinyarsa ba,yana murmushi yace "Aure me sa mutum nutsuwa kalli yadda baby ta koma Hajiya" Mamah da duk bataji dad'in ganin Sury a wannan yanayin ba tayi yak'e kafin tace "Aifa,Allah dai ya basu zaman lafiya" Daddy ya answer da Amen kafin ya mik'e yana cewa "Doctor bari na fita na dawo ai yini zakuyi anan ko?" Sadeeq yana shafa side burn d'insa yace "A'a Daddy sauri muke dama sallama muka zo muku jibi zamu wuce Florida zanyi resuming aiki na" Daddy ya koma ya zauna yana kallonsa da mamaki yace "Karatun Babyn fa?ko transfer kukayi?" Assadeeq ya saci kallon Sury da kanta ke k'asa wondering why she didn't inform her parent about her been withdrawn from university yace "Abbah na nemi transfer d'in ban samu ba so I decide to enroll her a Medical university dake cikin asibitin danake aiki kawai" Mamah ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah yasa haka ne mafi alheri" Daddy ya answer da "Ameen...amma da kayi magana ma in the first place dana kar6a mata transfer d'in,amma ba matsala tunda ta yarda ta koma bayan" shiru ne ya biyo baya har sai da wayar Daddy tayi ringing,ya mik'e Yana cewa "Safe flight Baby....zamuyi waya kinji" daga haka ya fice,Mamah ta mik'e zuwa sama bata dad'e ba ta sauko da k'atuwar polythene bag cikeda turaruka ta ajiye tana kallon Surayyah tace "Baby ga tsaraba na,Allah ya kiyaye hanya" bata jira answer ba ta wuce kitchen,bata dad'e ba nan ma ta fito da babbar plastic container  tace "Ga dambun nama ko a hanya kwaci" Mik'ewa Sadeeq yayi yana cewa "Thank you Ma! Bari mu wuce we're yet to park our luggage's" daga haka suka fice Mamah ta musu rakiya har jikin motarsu.


Washe gari basu fita ba kayayyakin da zasu buk'ata kowa ya had'a a room d'insa,sai yamma Assadeeq ya fita sallama da friend's d'insa kuma after isha ya dawo saboda flight d'in 8:00am zasu bi zuwa Florida,take away daya tawo musu ya tafi da room d'in Surayyah,jin motsinta a toilet da alama wanka take yasashi ajiye mata kan side drawer ya fice.
Washe gari 7:00am suka fice daga gidan zuwa airport.sanda jirginsu ya sauka fita suka daga airport d'in,a bakin gurin suka samu me mota,Gidansa dake Jasmine estate a pasco yayi wa me motar describing,cikin mintunan da basu wuce 40 ba suka k'arasa,ya sauko batare da ya ko kalli side d'in da Sury take ba ya kar6i account number me motar ya mishi transfer for ba kud'i a hannunsa,Sury da ta sauko ta cake a gefe tanata kalle kalle taja trolley ta ganin yana k'ok'arin shiga gate d'in estate d'in be kulata,Wani entrance door yayi knocking wata matashiya da bazata wuceta ba ta bud'e,rungumeshi tayi with over excitement kafin ta sake shi tayi kissing both Cheek's d'insa,ya rik'o hannunta shima yayi kissing,Sury dake d'an nesa dasu taji kamar ta tafi da gudu ta shak'e yarinyar,ta dai daure ta juya musu baya bata Iya jin me suke cewa amma data juyo bataga yarinyar ba shikuma yana tsaye hannayensa cikin side pockets d'insa,can kuma yarinyar ta dawo ta mik'a masa key ya kar6a yana mata murmushi ya nufi next door,bud'ewa yayi ya shige without minding her standing with her loads a compound d'in, da farko k'in shiga tayi ganin bashida niyar fitowa ya kirata yasa ta d'auki handbag d'inta taja trolley zuwa entrance,a parlor ta ajiye kayan ta zauna kan 1sitter tana k'arewa had'adden parlorn da kusan komai na gidan a ciki yake don tana iya ganin book shelf me shape d'in triangle da alama nan ne study spot d'insa,sai kuma k'atuwar woredrobe mara murfi me raws da columbs da yawa,daga right hand side d'inta kuma kitchen ne shima doorless sai counter's da suka zagaye shi,bedroom d'aya ne da alama don door d'aya ta gani,da yake da glasses aka zagaye parlorn tana iya hango oval shaped swimming pool a k'asan varender sai balcony a k'arshe da aka zuba masa lafiyayyan kujeru guda 2 da study table a jikinsa kuma cage ne da bird d'in da batasan ko menene ba,ta shagala da kallon Sosai har batasan Assadeeq ya fito ba sai ji tayi ya yarfa mata ruwan hannunsa ta tsorata ta mik'e da sauri wanda hakan yasashi murmushi yace "jirana dama kike in shigar miki da luggage d'inki na miki wankan?" Ta girgiza masa kanta,yana pointing wata k'ofa yace "There....is my bedroom you can take your trolley akwai toilet,you have your shower,I'm going out" kamar zatayi kuka tace "Bazaka tafi dani ba?" Ya harareta yace "saceki za'ayi inna barki?" Tayi shiru tana kallon rug,shikuma ya juya ya fita,trolley taja zuwa room d'in ta tsaya a tsakiyarsa tana k'are masa kallo tace "tabarakallah ahsanil kaliqin" saboda iya tsaruwa ya tsaru few abubuwa ne cikinsa,daga wani k'aramin royal bed sai side drawer's da mirror dogo sai plasma da wall clock,sai d'an table da kujeru biyu da flower vases guda 2 akai,k'arasa toilet d'in tayi nanma tasha kallon don Wani irin jacuzzi tub da bata ta6a gani ba ta gani da mat a gabansa,sai mirror da wani had'adden sink a gefe sai drawer da ake ajiye towel's.
Kayan ta ta cire ta ninke ta saka a drawer kafin ta shige jacuzzi tub ta fara wanka da had'adden sabulun da ta gani ciki,ta dad'e tana wankan kafin ta fito ta nufi trolley ta fito da gown peach color ta saka ta sa hula black color ta kwanta kan lafiyayyen gadon Assadeeq and before she knows it bacci ya d'auketa.
  Bazata iya tantance awannin data d'auka tana baccin ba amma data farka ta k'arasa jikin glass d'in daya zagaye room d'in tana kallon waje ta gane d'arene,toilet ta wuce ta d'auro alwala tazo ta fara rama sallolin da tayi missing,data idar had'e kanta da jikin bed tayi jin cikinta na kukan yunwa,ganin ba sarki sai Allah yasata mik'ewa ta wuce kitchen Dake parlor,kwata kwata bataga wani abu da zata iya ci ba don haka ta dawo parlor ta samu fresh milk a fridge ta fara sha, kan kujera wani baccin ya d'auketa,bata farka ba sai kusan 7:00am na agogon su,alwala tayo ta dawo parlor tana wondering inda Assadeeq ya shiga ganin babu alamar ya dawo gidan gaba d'aya.
Zama tayi bayan tayi sallah tana jiran dawowarsa,wasa wasa har 6:00pm shiru,fita tayi ta tsaya a k'ofar yarinyar da Sadeeq ya kar6i key gurin ta jiya tana son knocking ta tambayeta Sadeeq d'in amma gabanta sai fad'uwa yake ba dalili........




how's the chapter pls???

Comment