MY BESTIE'S HUSBAND

*_Mbh_*



*_Oum Hairan_*



*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*_Telegram Link_*
            👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7


*_57-58_*


_______________________________
_______________________________


Miqewa shima Jamal yayi cikin sarqewar murya yace “dad da gaske kasanta Yaya a Ina kasanta meye alaqarka da ita don Allah?" Qit Ja'afar ya kashe wayar tsabar kidima da tashin hankali Ina Jamal yasan Rafi'ah dama ashe Bata mutu ba? A Ina ta boyewa ganinsa tsayin wadannan shekarun kusan antafi hudu meyesa ta kasa nemansa a halin tana raye Kuma tasan shima yana raye? Tambayoyin da yaketa jerawa kansa kenan babu amsa dole ya miqe ya fara neman lambar Mai martaba bugu biyu ya daga ya fara zayyane masa abinda ke faruwa Mai martaba yayi hamdala yace “dama da safe nakeson kiranka kome kakeyi ka bari ka taho gida abubuwa fah sun lalace Ina buqatar ganinka da gaggawa"
Saida gabansa ya fadi da Mai martaba yace dole ya taho gobe yasan wannan Kiran bashida mafuta shiyasa ya aje wayarsa ranar bai rintsaba kamar yanda Jamal ma bai rintsa ba itama Rafi'ah da batasan meye yake faruwa ba Bata rintsa din ba saboda wani azababben ciwon Kai da yayi Mata dirar mikiya tun daren take juyi har gari ya waye sannan ya qara ta'azzara har takaita ga ficewa daga hayyacinta da safen kuwa Alh Hashim ya Kira Jamal yake fada masa abinda take faruwa duk da yanda ya kwana da mutuwar jiki bai iya sharewa zuwan ba haka ya nufi gidan suka dauketa sai asibiti suna tafe yana tunanin tashin hankalin da yake tunkaroshi indai ya kasance Rafi'ah ta zama matar yayansa da gaske shi yanzu meye makomar qaunarsa gareta?"



A asibitin ma kass hassala Mata komai yayi ya hadata da wasu likitocin suka duqufa kanta shikuma ya duqufa tunani lkc zuwa lkc yana share hawaye dole ta tabbata Rafi'ah ba tasa bace kenan?" Haka ya yini a zaune ruwa ya kasa hadiya baiji sanda aka turo qofar ba saiji yayi an janye hannunsa daga tagumin da yayi ya daga Kai tare da miqewa da sauri suka rungume juna yace “duk wani Abu muhimmanci ya gaza kaiwa muhimmancin da zaka taho takanas saboda shi Amma wannan yakai tabbas da kasan hakan da tun farko kazo ka rabani da ita ba Saida zuciyata ta saba da sonta ba duk da ita bata taba Sona ba kullum Kaine abakinta Kaine take ambato Koda yake ta manta da siffarka ta zahiri Amma Bata manta da yanayinka na badini ba Yaya Ja'afar meyesa kabarni na saba da matarka da danka sabo me tsananin da nakejin bazan iya rayuwa babu suba?"



Shafa bayansa yayi ya janyesa daga jikinsa ya zaunar dashi yace “kayi hqr Jamal haka Allah ya tsara mana tunda nayi rayuwa me tsayi babu su kaima zaka Saba har Kama manta dasu Kai bakasan wace Rafi'ah ba Ni nasani inasonta da jikina da zuciyata da ruhina bazan taba amfanuwa babu itaba Kai shedane" miqewa yayi zai fice Jamal ya riqoshi yace “suna cikin asibitin nan batada lfy tun safe" daga haka suka fita suka nufi dakin da Rafi'ah take kwance aunty Bari'ah tana zaune a gefenta sukayi sallama ta amsa tare da miqewa ta dubi Ja'afar dubi Mahir daketa wasa mamaki ya kamata ta matsa ta dago Mahir tace “kayi gsky Jamal idan da Mahir bata yayi aka tsinceshi akaga yayanka yazo wuccewa a hanya zaace Masa ga danka ikon Allah kenan" murmushin yaqe Jamal yayi inda tuni Ja'afar ya wucce inda Rafi'ah ke kwance ya zubanta ido cikin tsananin tausayin kansu da gdy ga Allah daya sadasu a duniya batare da daya cikinsu ya mutu ba, hannu yasa ya shafa kanta kawai sai ya fada jikinta ya rushe da kuka me sauti yana cewa “ashe mafarkina gsky ne Rafi'ah kuna raye keda dana kika watsar dani kikaqi nemana kikaqi waiwayena nida iyayenki kika barni cikin zullumi da ciwo Mara magani Rafi'ah meyesa kikaqi nemana don Allah har yaronmu yayi girma haka?"
Ajiyar zuciya yaji taja me qarfi wacce ta sada hancinta da wani ni'imtaccen qamshi da ya fara tariyo Mata wasu abubuwa da suka faru a baya aikuwa saita miqe ta angajeshi da sauri tana fadin “wayyoh innanillahi zasu haukatani Ja'afar zasu rabani dakai Hajiya Barebari da Bestie Ja'afar riqen...." Rufe Mata baki yayi da sauri tare da rungumeta ya fara tofa Mata addu'o'i sun dauki lkc a haka tana maqale a jikinsa kafin ta janye ta bude idanunta tar a cikin nasa shidinma itan yake kallo taja ajiyar zuciya tare da daga hannu tace “Alhmdllh da wannan mummunan al'amari ya kasance mafarki" sai Kuma ta fara bin dakin da kallo kowa ita yake kallo ta shafa cikinta tare da sake kallonsa tace “Ja'afar Ina jaririna? Ina Hajiya Innah ba a dakinta nake ba meye ya dawo dani asibiti banida lfy ne?"


Matsawa yayi gabanta ya riqota daidai lkcn da Mahir ya taso ya taho ya riqe qafafunta yace “mommy Kinga Abban Nan yana kuka" juyawa sukayi ga Jamal da gaske hawayene sosai suke zuba a idanunsa kallon Ja'afar tayi tace “JM Kuna Kama da wannan mutumin wayeshi?" Da sauri aunty Bari'ah da Jamal da Alh Hisham suka kalli juna Alh Hashim yace “alhmdllh a hakan ma wato da tunanin farko ya dawo saiya kore sabon tunani ya akayi hakane wai meye ya faru?"
Nan Jamal ya qwashe komai ya fadawa su Ja'afar abinda yake faruwa da dalilin haukacewar Rafi'ah aikuwa tayi kuka sosai tana Jinjina girman abin batayi tunanin hakan ba tace “kun cuceni Hajiya keda Ni'imah bantaba tunanin rashin imaninku yakai hakaba meye na tsare muku da kuka cutar dani haka Allah kasani wlh bazan taba yafewa ba Allah kabimin haqqina da gaggawa sun rabani da mijina sun rabani da iyayena sun rabani da garina sun rabani da hankalina Allah kayi musu daidai da abinda sukayimin"




Sake kamota Ja'afar yayi ta lafe a jikinsa tana shafa bayansa tanaci gaba da kukanta tace “basu cutarmin dakai ba ko mijina Ina su Abbana da Ammy inna Hajiyata da Karimatu wayyohhhh mijina sun cutar damu nikam ko ka yafewa hajiyanka wlh bazan yafe Mata ba" shima hawayen yakeyi bai qara tabbatar da yayi missing din wani bangare na rayuwarsa ba sai yau Babu Mata Babu da kayy wadannan mutanen sun tagayyara shi ba haka sukaso ganinsa ba shima bazai yafe ba" sun dade suna koke kokensu sauran mutanen dakin suna tayasu kafin daqyar sukayi Shiru daidai lkcn da Jamal da Mai martaba da Abba suka shigo bayansu Kuma Ammi ce da Hajiya Innah tuni Rafi'ah ta saki Ja'afar ta kwasa tayi gurin Abba da gudu ta fada jikinsa ta sake rushewa da kuka Hajiya Innah ce ta kalli Hashim tace “Aa Hashim ya akayi haka dama a gurinka Rafi'ah take ya akayi banganta ba watana uku fah da zuwa gurin Yaya Rakiya nayi sati guda?" Shafa kansa yayi yace “haka Allah ya nufa Mama in zaki tuna lkcn ai nace kizo gdana kikace sai Bari'ah ta haihu sauri kikeyi da kinzo qila da tuni ba wannan zancen akeyi ba"




Nan aka rinqa mayar da magana itadai Rafi'ah tana kwance jikin Ammi tana kallon Ja'afar shima ita yakewa kallon qurillah tayi qiba tayi wani kyau alamun hankalinta a kwance yake sabanin shi da yake a kode sai tsayi da dogon hanci kawai amma duk Wanda yaganshi yasan a fukace yake
Daganan sallama aka rubuta Mata suka dunguma sai family house dinsu Alh Hashim  Nan fa akayi mayar da yanda akayi shidai Ja'afar ji yakeyi kamar yace yanason ganawa da matarsa Mahir kuwa tunda suka taho yake hannunsa yanajin qaunar dannasa tana ratsashi tare da tausayinsa duk Shirin gatan da yayiwa rayuwarsa data dansa an rushe Masa shi dansa baisanshi ba sauqin ma dake yasan qaninsa sun shaqu sosai Mahir da dan banzan surutu idan aka tambayeshi Ina abbansa sai yace da “abba baqine Abbana Amma yanzu Abba farine abbana" dariya Ja'afar yayi yace “yaro kasan gaskiya ni nasha wahalata da wannan uwar taka tun daga neman aurenta har kawo cikinka da laulayinka kawo yanzu ban hutaba qanne nawa kakeso ayi maka?" Sai ya dunqule yatsansa babba ya nuna hudu kowa dariya yakeyi suna yabawa da wayon yaron.



A daren Mai martaba yace zasu wucce Bauchi daqyar suka roqi alfarmar su bari Saida safe Bari'ah ta janye Rafi'ah suka koma gidanta shikam Ja'afar baiso hakan ba yaso ya samu kebewa da ita don dai kawai bayaso ya fito da maitarsa a fili ne, suna zuwa gidan kwanciya tayi zuciyarta wasai ita kadai a dakinta kasancewar Mahir yabi ubansa tanata juyi tare da tunanin mijin nata taji wayarta tana ring ta dauki wayar tana duba lambar duk da batada ita yanzu Amma ta fado Mata ranta tayi murmushi ta Kara a kunnenta yace “naso ace yau tare dake zan kwana na hucce gajiyata na bayyana Miki asalin halin dana shiga saboda rashinki Rafi'ah naga rayuwa fah mutanen nan sun cuceni" katseshi tayi da cewa “sa minjaye sun cucemu dai" murmushi sukayi tare yace.
So nake najiki a jikina matata don Allah bari nazo na daukeki wlh tunda naganki na kasa control din kaina na dade Ina azabtuwa saidai tayau zata bambamta da kowacce saboda kece kika harqitsani da kanki" Sarai tasan halinsa nan ta ringayi Masa magiya Amma ko a jikinsa saima ya kashe wayar ya nufi dakin Jamal  yace “bani mukullin motarka zan dan fita kallonsa yayi zaiyi mgn yace “banson tuhuma in kaso ka kulle gdanka wlh bazan iya kwana ni kadai ba yau" dariya Jamal yayi yace “a baya Kuma ya kayi?" Shima murmushi yayi yace “hqr Kuma lkcnsa ya qare"



_Comments_
_Share_
_Vote_



*_Oum Hairan_*

Comment