MY BESTIE'S HUSBAND

*_My Bestie's husband_*


*_Ummuh Hairan_*


*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*_Free book_*


*_7-8_*


_Masu Bina suna cewa na turo musu daga farko kuyi hqr bazan iya bane duk groups din da kukaganshi to ku tambaya zaku samu abun zaimin yawa nayi typing nayi Post sannan nazo na rinqa binku one by one Ina tura muku please kada wata tace banida da mutunci wlh ko kin bini bazan turaba Amma fah kuyimin uzuri nima inada uzurirrika na na qashin kaina sannan wannan book din kyautane sadaukawa ga duk wani masoyina dake fadin duniya nasan addu'ar ku ke samamin kariya gurin Ubangiji Kuma Allah ya kareku daga bakin duniya😘_


____________________________
____________________________


Batare da yayi aune ba ko ya zata yaji saukar yatsun hannunta akan kyakkyawar fuskarsa me cike da saje abinda ya haddasa masa cin wani uban birki ji kaki qiiiiiiy! Abinda yasasu wata girgiza hakan baisa Rafi'ah ta daina tsumar da takeyi ba idanunta har yanzu na kansa ya saki baki yana kallonta rabon da asa hannu a mareshi har ya manta.
Bude qofar takai hannu zatayi yayi saurin danna pin din ta juyo cikin bala'i tace "zanci kutumar ubanka Ja'afar zan yaga alfarmarka da mutuncinka matuqar baka budemin motarnan ba...." hannu ya sa ya toshe kunnensa ta sake daga murya cikin qaraji tace "ka budemin mota nace stupid man kawa...." Bata rufe bakinta ba ya cafki bakinta da nasa ai baigama Kama harshenta ba ta gasa masa cizo a harshe dake cikkaken dan air ne ido kawai ya rintse ya sake tura harshen nasa cikin bakinta yana qoqarin sanya qarfi ya janyota jikinsa ta cure jikinta ta banqara ta kwace ta zame daga kujerar ta rushe da kuka tace "nashiga uku ni Rafi'ah wannan wacce irin baqar ranace Jama'a meye yake faruwa danine...." Bude motar yayi ya dube fiddausi yace "jeki little jirani...." Kafin ya ankara Rafi'ah ta bude qofar ta dire waje kamar wata mahaukaciya ta kwasa da gudun bala'i ta runtuma cikin daji.


Cikin tashin hankali ya fito yabi bayanta a guje dake dogone ita Kuma tsayin ba sosai ba sai gashi yacin Mata da taimakon bishiyar da tayi karo da ita ta caki goshinta tayi baya taga taga zata fadi ya tareta ta fada hannunsa ga matsanancin mamakinsa sai yaga ta fado hannunsa sumammiya abinda ya qara fitar dashi a hayyacinsa ya dagakai ya kalli Fiddausi data dafe qirji tanason mgn Amma tsoron jizginsa ya hanata yace "meye hakan Fiddausi saboda nace inasonta shine harta suma"
Cije lebe tayi tace "yaya abinda girma ka taimaketa ka kaiyi Mata urgent treatment" sabarta yayi a kafadarsa ya sata a mota ya shiga cikin garin Kai tsaye wani asibintinsa ya nufa sabone bai dade da budeshi ba ya dauketa kamar beby ya shiga da ita har dakin da zai dubata ya cire babbar rigarsa duk likitocin dake asibitin ya hanasu tabata dakansa yayi treet nata ya cire Mata iccen daya shiga goshinta ya wanke gurin da magani, yana tsaka da dressing din gurin wayarsa ta fara ring ya daga ganin number Ni'imah ya danna ok Bai bata damar mgn ba yace "naje cikin Bauchi ne inada wani petiant bama lallai tafiyar nan yau ba saboda yanada muhimmanci a gurina" yana Shirin kashe wayar yaji tace "sweet kaje gurin Bestie kace nace tabani abin dadi" duk da damuwar dake cinsa Saida yayi murmushi yace "insha Allah zanyi qoqari" yana fadin haka ya kashe wayarsa yaci gaba da abinda yakeyi.


Yana gama dressing din ta farka ganinta daure da drip yasata miqewa ta fincike allurar ta watsar juyowar da zaiyi yaganta tana daye dressing din da yayi mata ya nufota a guje yana cewa "kewai meye hakanne baki da hankali ne jibi yanda kika jiwa kanki ciwo kina tunanin hakanne zaisa na janye qudurina" wani matsiyacin kallo tayi masa ta nufi qofa ya nufota da niyyar hanata fita ta juyo tace "wlh tallahi ka qara matsata sai nayimaka ihu na tona maka asiri fajiri maci amanar qauna ka dauka ni yar iskace da zakazomin da wannan games din to kayi gaggawar lashe amanka kafin ka fuskanci qasqanci a gurina Ja'afar bana zama inuwa daya da maci amana maha'inci dan uwan shaidan me burin shiga tsakanin qauna,
Sakin baki yayi tare da rungume hannunsa a qirjinsa shi masifar tata ma burgeshi takeyi baitaba ganin mutumin da yake fada yana kyau ba sai ita yana wannan tunanin ta fice da sauri cikin saa tana fita ta fada napep ta fada masa inda zai kaita Koda ya fito baiga alamarta ba ya tambaya akace tahau napep kafin yaje ya dauko rigarsa ya nemo Fiddausi har takai school tana zuwa ta nufi hostel tanata wucce mutane bata gane su waye har ta Isa dakin ta fada gado ta rushe da kuka tana furta " Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allahummah ajirni fih musibati wa'akalifni khairin minha" ta jima tana kuka me dafa zuciya bata taba shiga tashin hankali irin na yauba ji tayi anzauna a gefenta ta tashi firgigit.
Ajiyar zuciya tayi ganin Nina ce tace "meye Kuma pretty?" Kukanta ta qarawa qarfi tanasa tisue tana tsane jinin da Bai daina zuba a ciwon ba Nina ce ta dauko wani dan qaramin akwati ta bude ta dauko auduga da magani tayi Mata dress na gurin tace "yanzu Mutuminnan na jiya yazo yabani magunguna yace na kawo miki garinyaya kikaji ciwo?" Dora Mata magungunan tayi a cinyarta tayi watsi dasu tace "kije kice masa banaso bana buqata ki hada masa da kayansa na jiya duka banaso ya fadi meye yakeso bayan wannan na fadawa abbana ya biyashi nidai roqona ya janye furucinsa, kwanciya tayi tace "Nina meye yasa mutane basusan girman aminta ba meyesa basusan darajar alaqa ba ? Meyesa Ja'afar zaiyimana haka wlh bantaba zatoba Koda wasa nayi tunanin duk abinda yakeyimin saboda Bestie na yakeyi min meyesa zaiyimin haka me yake nufi dani Nina ya cutar dani ko iya haka kalamansa suka tsaya na rantse da Ubangijin da yake rayani bayan ya kasheni a kowanne lkc nayi bacci bantaba jin tsanar wani mutum araina ba sai yau naji tsanar Ja'afar Wakil ta darsu a qoqon zuciyata natsani mutum maci amana"


Ta qarashe maganar tana shigewa jikin Nina tace "ko iya haka da wanne ido zan kalli Bestie mijinta yace yana Sona har ya hada bakinsa da nawa innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Hasbunallahu wani'imal wakil wannan masifa dame tayi Kama nikam na shiga ukuna Nina qaddarorina sunada wahala"
Miqewa tayi kamar zararriya ta kalli gabas tama manta da ciwon dake goshinta tayi sujjada tace "Allah inhar ka qaddara yankewar alaqata da Ni'imah alaqar daka sardata tun bamusan kanmu ba Allah kada ka yanketa ta wannan hanyar ka karbi rayuwata na tafi na barta da mijinta abin qaunarta farin cikinta Allah nafi kowa sanin cewa Bestie na tanason mijinta Allah kada kabashi ikon cutar da ita Allah ka cire masa so da sha'awar duk wata ya mace a ransa bama niba ya Allah idan kayimin haka ka gamamin koma...."


Ji tayi an rufe Mata baki ta dago Nina tace "meyesa kike roqon farin cikin wata har kike roqon Allah ya kasheki akan farin cikinta?" Share hawayenta tayi tace "ba wata bace Bestie nace wlh tafi gaban haka a gurina zan iya bata rayuwata matuqar zata rayu cikin farin ciki meyesa mijinta zaice yanasona Nina meye bambamcina da Ni'imah mutane suna cewa saboda aminta Kama mukeyi toshi meye yasa yakeson raba amintarmu?"
Murmushi Nina tayi tace "ai jiya dana fada Miki baki yarda ba Rafi'ah tun ranar bikin da kika gayyacemu na fahimci sinadarin dake fita a idonsa sone da zallar qauna Amma wanne mataki kika dauka?" Shiru tayi nadan lkc kafin ta dago tace "zan yanke mu'amala da matarsa na dan lkc idan burinsa kenan" girgiza Mata Kai tayi tace "kada ki fara hakan zaisa ta zargeki kici gaba da mu'amala da ita shikuma ki take Masa dogon burki kiyi duk meyuwuwa kiga kinsa masa tsanarki ta yanda dakansa zai janye Rafi'ah jiya dana fada Miki haushina kikaji har kina cewa bazai yuwuba to gashi dai kin gasqatani" Jinjina Kai tayi ta miqe ta fada bathroom tayi wanka ta dawo ta kwanta ranar duk wata lecture batayi ba tanajin wayarta tana ring taqi ko dubawa balle ta daga Nina ce ta zauna tanata rarrashinta tare da nuna màta bafa wani Abu bane latsine irin na mazan zamani yanzu haka ma bazai qara mgn ba tunda ta nuna masa batada mutunci,


Da wannan ta dan samu kanta harta dauki wayarta ta fara duba kiraye kirayen kiransa yafi hamsin da layin data sani saina dayan daya rinqa turo Mata saqo jiya Wanda shima yakai talatin saqonni kuwa sunyi ashirin batako dubaba tayi delete all ta watsa layukan a black list kiran Ni'imah ta gani har hudu tayi kamar ta share sai Kuma taga rashin dacewar hakan yau gabadaya basuji junaba zatayi tunanin ko ba Lau ba hakance tasata kiranta dagawa tayi cikin muryar kuka tace "inata Kiran wayarki kinqi dagawa Bestie kinsan Kuma bana samun nutsuwa idan banjiki ba har na fara tunanin ko wani abune ya sameki na kiraki sosai da wayar Sweet ma baki dagawa I hope fine dai?"
Ajiyar zuciya tayi tace "banji dadi bane Bestie kaina na ciwo sosai Amma nasha magani na samu relief Ina fatan kina lfy Ina unborn dina?" Dariya tayi tace "waye yace Miki inada ciki wlh banida komai yanzuma period nakeyi in fada Miki jiyama Saida mukayi fada da sweet wai saina bashi nutsuwa Wai Ashe akwai yanda akewa namiji ya samu nutsuwa ko ana halin haila?" Dariya Rafi'ah tayi tace "matsalace dake babba Bestie Ina littafin dana zauna na rubuta na baki harfa buga mikishi nayi saboda kinsan rubutunmu na likitoci ba kowa ke ganewa ba, idan kika duba book din Zaki samu komai har addu'o'in da zaki samu daukaka da soyayyar mijinki nabaki sannan ki cire ganda Bestie ki tallafi mijinki namiji da kike ganinsa bashida tabbas don Allah kada kibani kunya wlh a shirye nake na baki taimako ta kowanne bangare indai akan mijinki ne inason Kuma Ina burin ki zama tauraruwa a gurin mijinta"


Tabe baki Ni'imah tayi tace "ke nifa duk dare fada mukeyi dashi banason nacinsa shiyasa naso kizo kinqi zuwa wlh idan ya fara baya gajiya a dare sai yayi sau biy....." Katseta tayi da cewa "sheeet! Bestie banson ji don Allah haramun ne sirrinki ne ke dashi ki daina fada mijinki nakine ke kadai kiyi Masa komai babu komai Bestie your are educated meyesa kike Abu kamar tashin qauye duk wani farin ciki fa yana tare da aure duk da cewa aure ba dadi gareshi ba tsanani ne Kuma kinsa dama ita aljanna samunta ba abune me sauqi ba Ashe kuwa hanyar samunta bazata zama me dadi da sauqin biba please ki cire ganda Bestie don Allah ki tarairayi mijinki kinji?"
Numfashi Ni'imah ta sauke tace "nifa na rasa meye yasa wlh banason wahala kinsan ban sababa shi ya cika tsurfa wai bazaici abincin kuku ba saidai nayi masa Kuma idan nayi sai yace yaji ko yace magi yayi yawa shi komai baayi masa gwaninta ga izza da Isa kamar wani sarki Bestie Ja'afar fah inaga kamar ma yafi Muhammad Wakil Izza" murmushi tayi tace "haka zakiyi hqr baki bishi inda zaku daidaita bane komai yakeso bakiyi bakya dauke buqatarsa a bed baki kashe masa yunwar cikinsa baki zama kuyi Hira dasshi kina fama da waya Ina gani fah 24 hours datarki a bude kina online da anyi Miki mgn ki amsa why Ni'imah why da bazaki raba lkcnki ba kibawa mijinki kaso mafi rinjaye Ni'imah namiji zuciyar jariri gareshi Wanda yaje tattalinsa yake kula dashi dashi yake sabawa dashi yake tashi kibi a sannu ki fahimci mijinki ki haqura da chat matuqar kina tare dashi sannan ki fahimci dandanon mijinki ki daina cika masa magi da yaji a abinci kinji tawan?"


Jinjina Kai Ni'imah tayi tace "na gde Bestie ba komai zan iyaba Amma zanyi qoqari kinsan mazan ne sai a hankali Ja'afar ko kallo idan baqatarsa ce ta tashi ba ban isheshi ba yanzu ma yake tambayata wai dama kin iya ashar shine nace masa nidai bantabaji ba don ko wani yayi nasiha kikeyi masa ya Kuma cemin Amma ke masifaffiyace nace sanyinki yafi na ruwan freezer ko lkcn yarinta ni nake tare Miki fada ke mgn ma bata dameki ba don wani lkcn idan na dameki da surutu har kuka kikeyi hawayenki yafi komai arha shine yace yanason mace me saurin kuka nace to aikuwa ke sannu ma kuka sakesaki"
Haushine ya cika Rafi'ah tace "kewai bakida hankali ne kike yabon mace a gaban mijinki?" Dariya Ni'imah tayi tace "haba ai mace kikace ke kuwa jini daya nakejinmu nasanma bazaiji komai ba yasan ni dake Abu dayane balle wannan dan girman kan idanfa ya tambayeni na bashi amsa sai ya tabe baki yace meyesa ban zama kamr ke ba sai nace bansani ba kawai sai yace Allah ya kyauta yaci gaba da danna system dinsa" murmushin takaici tayi tace "ok ki daina ko Yusrah ki daina yabo a gaban mijinki ki rinqa yabon kanki kinsan zuciya tsokace batada qashi kinji Bestie na ki kiyaye harshenki don Allah ni zan kwanta kije ki shirya ki dauki littafin nan Zaki samu yanda zakiyi dashi a daren nan"


Ajiye wayarta tayi tana mamakin hali irinna aminiyar tata dole aiki ya sameta zatayi qoqari Koda bataje inda takeba take bata gudummawa domin da alamun da gaske tana buqatar kulawa so takeyi dole ta qarfi kamar yanda Ummanta take juya gidansu itama saita juya gidanta Wanda samun hakan da alamun zaiyi wahala.
Wata baquwar number taga an kirata da ita ko kusa ko alama batayi tunanin komai ba ta daga jin ajiyar zuciyar yasata kasa kunne domin sauraron jin dawa take mgn, a sanyaye cikin muryarsa me cike da kwarjini da qasaita yace "bestie meye ribarki don kinyi block mijinki kinajin na dameki ne? Ashe dai duk halinku daya da qawarki?"
Wani dogon tsaki taja ta kashe wayarta yakira yafi so goma taqi dagawa qarshe ma ta kasheta don da gaske ta fahimci akwai alamun tabuwar qwaqwalwa ga mijin aminiyar tata, washegari ta fice da wuri daga Hostel din ta nufi Venue dinsu ta zauna tana nazarin wani littafin biology taji an tsaya akanta bata dago ba da farko saboda tunaninta Nina ce dan dago idonta tayi ta cikin farin glass din dake sanye a idon nata ganin takalmi sawu ciki yasata dagowa tunaninta Taheer ne abokin karatunta da yake nacin sonta.



Annurin fuskarta ne ya dauke ganin JM ne tsaye sanye yake da alqabba irin tasu ta sarakai hannunsa zure cikin aljihun alqabbar sai baza qanshin wani tsadaddan turare yakeyi me kwantar da hankali fuskarsa dauke da murmushin daya fito da siririyar wushiryarsa, sake tsuke fuska tayi ta fara tattare kayan karatunta zata fice ya ya dora qafarsa ya tare hanyar tare da cewa.
"Bestie kin tashi lfy?" Rafi'ah akwai Dara daran idanu hakan yasa harara bata Mata wuya aikuwa ta jefeshi da wata zazzafa da tasa zuciyarsa harbawa yayi qasa da idonsa tare da zama, zare glass din idonsa yayi yace "zauna muyi mgn don Allah meye kikejin tsoro ne nidai nasan babu macen data Isa tace batasona saboda duk inda namiji yake nakai please ki tsaya mu fahimci juna Rafi'ah muyi auren qauna kada wani qaramin dalili yasa ki bijirewa hukuncin Ubangiji to waima ni meye laifina ne da har kika daga hannu kika mareni kinsan jiya Marin nan ya hanani bacc...." Dafe kuncinsa yayi a karo na biyu data daukeshi da mari ya dade dafe da kuncinsa yanabin Hall din da kallo ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya ganin dagashi sai ita a hall din ta sake maida hankalinta a tattare kayanta kawai taji an ruqo weast dinta ta baya.


Ya dora hannunsa a saitin ask dinta duka biyun ya miqe lkcn da tayi mutuwar tsaye ya hada gabansa da bayanta qirjinsa yana gugar bayanta ya matseta tare da Dora kansa saman nata yaja fasali tare da sakin wata qaqqarfar ajiyar zuciya, sai lkcn ta samu damar dawowa nutsuwarta ta sanya hannunta domin bambare nasa Amma saima ya qara matseta ya janyo hannunsa sama daidai tushen qirjinta ya Kama sosai ya riqe yanda yasan duk qarfinta bazata iya motsi ba saboda wata matsiyaciyar kasala daya saka Mata ta bazata ya bude bakinsa muryarsa na shaking yace "ko kasheni zakiyi bazan fasa cewa inasonki ba Rafi'ah I really love you wlh tallahi ko zan mutu saina aureki"


Yanayin da takeji tasa ta kasa ko daga hannunta sai tafasa da zuciyarta takeyi dumin hawayenta da yaji a hannunsa yasashi juyota ganin yanda ta rintse idonta Zara zaran eyes lasher's dinta suka sauka kan beauty face dinta da hawaye yake wankewa yasashi cika da sauqi baisan sanda yakai bakinsa ya fara tande hawayen ba kawai sai shima yaji zuciyarsa ta karye daqyar ya daure ya hadiye nasa hawayen yanajin bugun zuciyarsa na qaruwa tunda yake baitaba ganin masifa irin wannan ba shekara da shekaru anaso ya nuna waccce yakeso ya kasa lkcn da Allah ya nuna masa abinda ya dade yana nema Kuma sai abin yazo musu a baibai tabbas akwai sarqaqiya cikin lamarin shidai duk juyin da duniya zatayi bazai janye qudurinsa ba saboda yasan hakan shine kawai zai dawwamar da zuciyarsa cikin fayyataccen farin ciki,
Janyewa tayi daqyar daga jikinsa ta durqusa a qasa ta kama qafarsa cikin kuka tace "don Allahu huwar Rahamanu Ja'afar Wakil ka daina bibiyata ka janye wannan mugun nufin naka akaina wlh ka dauko hanyar ruguzamin rayuwata ne please Ja'afar nayi maka alqawarin ko wani lapse kega Bestie na wlh da qarfin buwayar Ubangiji zata gyara nidai ka rabu dani Allah matuqar ace babu wani namiji bayankai daya saura a duniya to zan aminta na gama rayuwata babu aure...." Murmushi yayi ya durqusa ya sanya hannu ya Kama hancinta yana murmushi yace "nikuma ko duk duniya matane yanzu ke kadai nake muradi matsayin Mata wlh tallahi matuqar baki amsamin buqatata ba to kuwa zakiyiwa Bestienki asarar igiyar aurenta......."



_Vote_
_Share_
_Comments_
_Please_



*_Ummuh Hairan_*

Comment