MY BESTIE'S HUSBAND

*_My Bestie's Husband_*


*_Ummuh Hairan_*


*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*[email protected]_*


*_39-40_*


_____________________________
_____________________________


Juyawa yayi fuuuu ya fice a fusace sai huci yakeyi inda suka kalli juna da Ni'imah Ni'imah tayi Mata murmushin mugunta tabi bayansa da sauri a jikin mota ta tarar dashi yanata huci ya bude Mata ta shiga shima ya shiga yaja suka fice daga asibitin sukabae Rafi'ah da sanyin jiki da faduwar gaba, sunan Allah ta rinqa ambato a hankali taji Hajiya Innah ta dafata tace.
“Ina mamakin zafin zuciyar Baban Innah shi komai nashi na fada ne ko meye abin bacin rai cikin kalaman ki sai naga kulawa ce da nuna damuwa da abokin rayuwa tasa kika damu da rashin nasa a kusa Koda yake wani abun sai anayiwa rayuwa uzuri kiyi hqr iya wuya kedin dai kece"
Sosai ta rinqa rarrashinta murmushi tayi tace “karki damu Hajiya nasan halinsa yanzu haka wani abun ne ya bata masa rai nasan fushinsa baya jimawa zuwa anjima zai sauko" ajiyar zuciya Hajiya Innah tayi sukaci gaba da tattaunawa saida tasan yanda tayi taga Rafi'ah batabar damuwar abin a ranta ba ranar a asibitin suka kwana saboda jinin da akasa Mata da magrib bai qare ba sai cikin dare.


Washegari har Tara baizoba aka sallamesu Hajiya Innah ta dauki waya ta kirasa ya daga suka gaisa ya tambayeta me jiki tace “da sauqi dama sàllamarmu akayi shine mukace ko zakazo ka daukemu" Shiru yayi na dan lkc sannan ya dago yace “aa Hajiya kawai bari na turo driver yazo ya daukeku ku wucce can fada kawai ni na danje unguwa ne idan na dawo zanzo" bataja mgnr ba ta kashe wayar ta miqe ta fara hada kayan lkcn da drivern yazo ta gama hadawa suka fita suka tafi suna Isa yana shigowa gidan ya tsaya jikin motarsa suka fito duk munafukai suna jira suka abinda zai faru qarasowa yayi ya rusuna suka gaisa da Hajiya Innah ya dago ya zuba idonsa akanta tayi wani haske ta qara ramewa yaja numfashi ya dubeta yace “ya jikin naki?"
Sunkuyar da Kai tayi tace “da sauqi" fasali ya sake ja yace ”nasa an qara gyara can bangaren muje na rakaki" kallon Hajiya Innah tayi idonta ya ciko da ruwa tayi saurin girgiza Mata Kai dole tasa ta hadiye kukan, taimako daya da Allah yayi mata tsakaninsu da Hajiya Innah babu nisa hakan tasa suka taka da qafa ya bude qofar shiga part din ya shiga itama ta shiga da Bismillah tana qarewa bangaren kallo tun daga waje zakasan ya kashe mazan kudi wajen gyarashi.
Yana tafe tana biye dashi a baya har suka shiga ya bude qofar parlourn ya shiga itama ta shiga ya mayar da qofar ya rufe ya juyo ya zubanta ido itanma shi take kallo fuskarsa a daure take sosai hakan ya tabbatar mata da babu wargi, rabashi tayi zata wucce ya riqo hannunta ta tsaya cik matsowa yayi ya riqo qugunta yana jan numfashi ya matsota sosai yace “meye yake damunki ne?" Dagowa tayi da mamaki so take tayi mgn Saidai yanda ya kafeta da ido yasa ta kasa furta komai sakinta yayi ya sanya hannu a aljihunsa ya zaro kudi masu kauri ya miqa mata yace “ki riqe saboda tsaro ki kula da kanki"


Juyawa yayi ya fice tabisa da kallo yaja Mata qofar ya rufe itakuma ta taka taje ta murda Mata key ta nufi step din shiga dakin ba bene bane Amma an daga dakunan sun danyi sama sabanin babban parlourn da take a qasa nan din ma akwai parlour Amma baida girma sosai kujera daya ce doguwa sai wani qaton kilishi 24 pillow sai TV da dispenser sai manyan flowers da aka qara qawata parlourn dashi gefe Kuma akwai qaramin dinning table me kujera biyu.
Tsarin wannan parlour yayiwa Rafi'ah tayi ajiyar zuciya ta bude daki daki daya ta shiga shima an gyarashi sosai gadone na alfarma aka saka komai yaji taja fasali ta zube kudin daya Bata ta fara rage kayanta ta fada wanka ta jima tana wankan tanajin dadin ruwan kafin ta fito ta shafa mai ta bude wardrobe din kayanta ne jere reras ta dauko wasu masu sauqin nauyi tasa ta kwanta tana hutawa ta Jima a kwance tana tunanin abubuwa da yawa sannan taji ana taba qofar ta miqe a gajiye ta fito parlourn tana tambayar waye.


Amsa Mata akayi da cewa “nice Rafi'ah Ashe kun dawo to sannu kinji" jin an ambaci sunanta yasata budewa batasanta a zahiri ba domin bata taba ganinta ba ko lkcn da aka kaita bangaren fuskarta a rufe take, Hajiya Kaltume ce ta kawar da shirun da shiga parlourn tace “tubarkallah Masha Allah guri yayi kyau to ai haka yafi Amma da duk ya debeku ya tareku guri guda don shirme musamman ma ke da kike buqatar kulawa yanzu sannu kinji"
Sunkuyar dakai tayi ta durqushe da niyyar gaisheta tayi saurin Dagota da cewa “subhanallah kula kada kiyi barna haba yarnan keda ba lfy ta isheki ba ai bakya tsugunna ba zauna abinki ni uwarki ce banason ki takurawa kanki da jikana" tana mgnr tana zaunar da ita a kujera tace “to ya jikin jiya munji mugun labari Koda yake Allah ya taqaita wahala


A kunyace ta amsa Hajiya Kursum ta rinqa janta da Hira harda guzurin agwalumarta ta kawo Mata ta miqa Mata tace “kinsan abinki da me wannan Abu da son tsami tsami shiyasa na bayar aka siyo miki" kamar tayiwa Rafi'ah kyautar aljanna haka taji sukayita yar hirarsu tanata nuna kulawarta tare da bata shawarwari kamar gaske, shigowar Hajiya Innah ne yasata miqewa suka kalli juna Hajiya Kaltume ta harari Hajiya Innah tace “to Rafi'ah ki kula da kanki kinsan gdan namu gidan yawa bakasan cikin wani biyune ba saiya lashe maka kurwa" itadai bata tanka ba Hajiya Innah ta zauna tace “Allah ya kyauta" Shiru ce ta dan ratsa kafin Hajiya Innah ta bude kular da tazo da ita tace “dambu nayi Miki da fatan yakuwa ko Zaki iyaci naga duk kin fige wannan jika yana wahalarmin dake"
Kunyace ta kamata tayi murmushi tace “bantaba ganin yar da take kunyar uwata ba saike tashi kici abinci" xuba Mata tayi ta zage taci dambun sosai don ta dade tanason sa tunda ta samu ciki dashi da tuwo bata taba daina kwadayinsu ba sosai taci sauran ta ajiye tace taci da dare a kalamai baa bayyane ba Hajiya Innah take nunawa Rafi'ah tayi hankali da mutanen gdan fada gidan makirci ne kowa da abinda yake zuciyarsa, sosai ta shiga taitayinta ta qara Mata da cewa idan kadaici ya dameta tana gama abinda take ta taho bangarenta, Jinjina Kai tayi ta qara da cewa mutane da yawa sunayi maka dariya Amma basa qaunarka munafikinka yafi maqiyinka illa domin maqiyi baya zama kusa dakai balle ya samu damar cutar dakai Koda kuwa zai cuta maka saidai yabi ta gurin munafikinka da hausawa kance gadon bacciñka so kibi a sannu dariya ba so bace wata dariyar tafi sukar wuqa ciwo"
Maganganun sun shigeta ta nutsu kuwa tana nazarinsu lkcn da sukayi sallama tace “ki kulle bangarenki kiyi kwanciyarki ki huta surukarki batanan tace Damagaran balle kice zakije gaisheta" tana fita ta kulle part din ta shiga kitchen ta ajiye kayan abincin ta dawo ta dan gyara gurin data zauna



Sake Shirin kwanciya tayi tabi lfyr gado ta kwanta tana dan chat dinta bacci taji ya fara sumamarta yasata miqewa ta dauro alwala ta dawo ta sake kwanciya tare da qarawa a.c qarfi bacci ya dauketa cike da kewar mijinta ko a waya bai nemeta ba ita Kuma yanayinsa yasa ta dan tsorata ta kasa kiransa da wannan tunanin tayi bacci wajen biyun dare ta farka ta sauka a gadon ta nufi bathroom ta dauro alwala wannan sabonta ne tun batasan kanta ba Amminta ta sabar Mata da tashin tsakiyar dare ko bata sallah saita tashi tayi alwala tayi tulawar qur'ani tare da istigfari hadi da addu'o'in da suka sauwaqa harma jikinta ya saba da zaran lkcn yayi saita tashi.
Ta Jima tana jero nafilfilinta sannan ta shiga jerawa Allah kirari tare da neman albarkar aurenta da zuri'a ta gari tare da roqa musu dawwamar zaman lfy da fahimtar juna ta dade sosai tanawa mijin nasu addu'ar samun budi da kariyar Ubangiji a duk inda yake.
Bata koma ta kwanta ba Saida aka Kira asuba nanma tayi ta Jima tana azkar hakanan sai ta rinqajin gabanta yana faduwa ta roqi Allah ya sassauta Mata duk wani Abu da yake tunkarota yabata wuyan dauka tare da addu'ar kada Allah ya bata ikon juyawa mijinta baya a kowanne hali, saida Rana ta fito sannan ta kwanta takuwa Jima tana bacci ba ita ta tashi ba sai 12:00pm wanka tayi ta shirya cikin wata baqar doguwar riga ta zura hijjab dinta qato sannan ta dauki wayarta har yanzu gabanta faduwa yakeyi tayi Bismillah ta Kira lambar JM Kira daya ya daga muryarsa wasai yace.
“Maman Twins kin tashi lfy?" Murmushi tayi ta sanyaya muryarta tace “har naji sanyin dadi ya ratsa zuciyata dana tabbatar da cewa Daddyn twins ya tashi lfy" dariya yayi ya dubi Ni'imah da ta wani hade rai yace “tun jiya zuciyata tana gurinku keda BBY na yar'uwarki ta riqeni ta hanani zuwa naganku" abinka da kishi da bashi da kadan sai taji zuciyarta ta sosu dake tana da wayo sai tayi murmushinta da tasan yana kashe Masa jiki tace.


“Allah Sarki mijina nasan muna qasan ruhinka kada ka damu kabata lkc sosai ai ta cancanta am dama nace idan babu damuwa inason shiga cikin gida mu gaisa jiya duk sun shigo harda Hajiya Babba" gabansa ne ya fadi yace “hajiya babba kuma? Me tace Miki?" Ajiyar zuciya tayi tace “babu komai kawai dai ta kawomin agwaluma ne Best Kai dan gatane kowa tattalin unborn dinka yakeyi"
Ajiyar  numfashi yayi yace “ok kije Amma ki kula da kanki nifa don Mai martaba ya dage ne hankalina bai kwanta da zamanki a gidannan ba Rafi'atuh zuciyata taqi nutsuwa" fasali taja ita kanta bataji tata zuciyar ta yarda ba Amma saboda burinta kullum qarfafa masa gwiwa sai tace “karka damu insha Allahu zamu kasance cikin tsaro da kariyar Ubangiji" wani gwauron numfashi yaja yace “banajinki Amma ki jirani ganinan zanzo saina rakaki ko Ina"
Yana fadin haka ya miqe ya fice yabar Ni'imah da sakakken baki cike da mamaki  mota ya shiga zuciyarsa na ayyana Masa abubuwa da yawa game da Rafi'ah yana murmushi gabadaya jinsa yake kamar Wanda ya rasa wani bangare na jikinsa iyakar kwana biyu da yayi ba tare da ita ba musamman daren jiya daya kasa rintsawa tunda yake baitabajin irin yanayin daya kasance jiyan ba wani bangare na zuciyarsa yayi masa nauyi yanajin wani Abu daya kasa tantancewa idan ya rufe idonsa Rafi'ansa yake hangowa cikin wani yanayi na tashin hankali hakanan zai zabura ya miqe ya sake kwanciya sai ya ganta dauke da wani kyakkyawan farin yaro me kama dashi cikin  wata rijiya me zurfi ga wani duhu yana mamaye rijiyar tun yana jiyo ihunsu da salatinta tana Kiran sunansa har yakar da yadaina ganinsu da jinsu gashi an Tara mutane anyi anyi à daukosu ankasa shikuma sai hanqoron binsu yakeyi Hajiya Fatsum da Ni'imah sun daddaure shi wani abin haushi ya kasa qwacewa sai hanqoro yake da ihu Amma ya kasa samun mafita


Can nesa ya hango Hajiya Kaltume ta nufo rijiyar gadan² da wani ice yanaci da wuta ta cilla a ciki inda kafin ya dira qasa ita Kuma Hajiya Innah tayi tsalle ta fada rijiyar ta cafo itacen tayo sama dashi ta jefi sarqar da aka daureshi da ita take sarqar ta tsinke ya kwace da gudu ya nufi rijiyar..... A daidai nan ya farka yayo alwala ya tada sallah domin mafarkin ya tsoratashi firgigit yayi saboda horn din da yaji anata doka Masa dubawa yayi yaga ashe tsayawa yayi a tsakiyar titi numfashi ya sauke yaja motar ya qara gaba.
Shiga fadar sarkin qofar bangaren nasa ya bude Masa ya shiga yayi parking ya bude motar ya fito taka qafar da zaiyi yaji kansa ya sara gabansa ya yanke ya fadi take yaji zuciyarsa tana tafasa “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un" ya rinqa karantawa har ya murda qofar ya shiga ko Ina na gdan qamshi yakeyi yanason Rafi'ah komai da yakeso a cikin watanni hudun ta gama karanceshi tsaf baiji fitowarta ba saiji yayi ta rungumeshi ta baya tana yar qaramar dariyarta me sanyashi nutsuwa tace “Ur are welcome My life...." Ajiyar zuciya yayi yana shaqar qamshinta ya juyota yayi kissing kumatunta yace “inasonki fatan kina lfy" qasa tayi da kanta tace “ina lfy kamar Kai" kalmar ta bashi dariya yace “haba yarinya da wannan dumar da ta fara girma a tumbinki zakiyi lfy kamar tawa?"



Dagansa Kai tayi tana shafa mararsa yanajin wani irin yanayi ta dago ta dubeshi ya wani lumshe ido tace “zuciyar Rafi'ah da alama kanajin yunwa me kakeson ci na sama maka banson zaman gwarzon maza da yunw...." Bata qarasa ba ya hade bakinsu guri daya suka zube a kujera tasan yau ta ballowa kanta ruwa da alamun dama kadan yake jira daqyar ta qwaci kanta shima Saida ya samu nutsuwa tayi luf a jikinsa son mijinta takeji a hankali yana mamaye duk wani gurbi na qiyayyarsa na baya Ashe takusa ta cuci kanta da ta yarda son farin cikin wata ya hanata karbar nata farin cikin.
Dagota yayi yace “me kike tunani?" Murmushi tayi tace “son mijina nake fasaltawa a zuciyata nakasa gane yanayin girmansa da matsayinsa na yarda na mutu dakai mijina kaifa?"  Farin cikine ya cika masa ruhi ya rungumeta yace “na dade da yarda da hakan Rafi'ah tun kafin kisoni nasoki Kuma zan mutu da soyayyarki" luf tayi a jikinsa sun jima a haka Bai zaci zata sake magana ba yaji tace “kayimin uzuri a duk lkcn da na bata maka mijina bazan taba furta ko aikata abinda zai taba farin cikinka a halin Ina sani ba" sanyi jikinsa yayi ya sunsuna sumarta yace “Insha Allah" miqewa tayi tana takansa rawa yayi murmushi komanta dabanne ya dagata cak suka shiga ciki wanka yayi ita ta qara gyara jikinta ya fito ya canza kaya suka fita bangaren Hajiya kaltume suka shiga tana parlon tana ganinsu ta miqe tana washe baki tace “tun dazu naso zuwa naga lfyrki Dije tace baki tashi ba to sannu kinji yarnan Magaji meyesa baka kirani nazo mun gaisa ba me ciki batason yawo balle ita da ba lfy ce ta isheta ba" dadi yaji sosai a ransa ya zauna yace “hakane Hajiya shima motsa jikin yana da amfani" zama tayi suka gaisa ta miqe tace “bari na kawo miki wani Abu nasan jikalle na zai soshi"



Kitchen ta shiga bata jima ba ta fito dauke da wata kula ta bude wata lafiyayyiyar gurasa ce ta alkama da aka mulketa da Zuma sai kunun tsamiya sai zuba qamshi yakeyi" kwantar da kanta tayi a jikinsa ya dago kanta yaga yanda take hadiyar yawu sukayi dariya shida Hajiya Kaltume yace “ta koma kamar mayya komai tagani tanaso tunda mukaje Mexico take sani barnar kudi a Rana sai tace tanason abu kusan kala talatin"
Zaro ido tayi sukayi dari dukansu Hajiya Kaltume ta kirawo Jakadiya Indo tace “ki dauki wannan kayan ki kai bangaren magaji" gdy Rafi'ah tayi Hajiya Kaltume tayi murmushi tace “Ah haba babu komai ai dole mu kula dake haqqi ne akanmu am don Allah Ja'afar duk abinda ya faru baya a manta dashi ya wucce har abada Rafi'ah duk abinda kikeso ki aiko a karba Miki bani da wani amfani sai hidimarku"



Jinjina Kai Ja'afar yayi yanajin dadi a ransa idan aka nuna anason Rafi'ah da cikin jikinta ji yàke kamar yayiwa mutum kyautar duniya, miqewa yayi ya kamo hannunta yace “bari mu qarasa ciki mun gode da kulawa" fita sukayi tanata zubawa Rafi'ah sannu" suna fita ta kwashe da dariya tace “zakuci ubanku waikai ne Mata ita Kuma me ciki har wani godiya kakemin kamar ka mantani nice dai Ummu kursumu yar mage baki dadin goyo sai baqin naci har wani proud akeyi Wai batada sabo tunda ta samu kwadayayyen ciki ai dole ta saba dani zan shekara yi Mata hidima domin Rana daya tak yahudu tuba babu hhhhhhhh" ta qara kwashewa da dariya.
Bangaren Hajiya Innah suka shiga anan ya tafi yabarta saboda Hajiya Fatsum batanan anan ta kusan yini ita da Karimah qanwarsa yar wajen Hajiya Innah sunata hirarsu dake dama basufi sa'anni ba sai yammaci ta tafi bangarenta ta shiga hadimai sai hidimarsu sukeyi tayi wanka ta baje a qaramin parlour Dija ta kawo Mata kunun da gurasar tayi Bismillah taci tayi hani'an sauran tasa a freegde tayi alwala tayi sallar magrib ta kunna kallo anan yazo ya isheta shima yabiyeta sunata hirarsu abin da yakebashi tsoro da mamaki idan baya tare da ita sai kewa da tunaninta ya damesa Amma idan yazo sai ysji duk ya gundura duk wani motsi da zatayi maimakon birgeshi da yakeyi da yanzu haushi yake bashi,



Sai darema da sukaje kwanciya yini yayi yana feeling nata Amma yanzu sai yaji duk haushinta yakeji gashi shi baiga wani laifi da tayi masa ba balle yayi fada yaji dadi duk wani Abu da tasan zai sanyashi farin ciki shi takeyi, itakam batajin komai a ranta kawai dai yanayinss ne yake bata mamaki sai ya kwanta ya tashi ya sake kwanciya ya tashi Saida yayi haka sau uku tanajinsa batace komai ba taji ya miqe itama saita tashi ta rungume pillow a qirjinta yakai ya kawoya tsaya a gabanta yace “na rass meye yake damuna wani haushinki nakeji Rafi'ah Kuma wlh bakiyi min komai ba" Allah sarki sai kawai tayi murmushi ta miqe ta dauki qur'ani ta dawo ta rusuna ta miqa Masa yasa hannu ya karba tace “a duk lkcn da najini a irin wannan yanayin nakan bar duniya da abinda yake cikinta ta na koma ga Allah ta hanyar ambaton sunayensa tsarkaka da Kuma karanta zancensa me dadi da sawa zuciya haske mijina kaima kayi haka nasan zakaji sauqin abinda kakeji...."
Ajiye qur'ani yayi ya matso gabanta yana huci kamar wacce ta zagi uwarsa ya dago kanta kawai saiji tayi  dauketa da Mari ya hankadata a gado ya hau bala'i yana cewa “wato saboda kin rainani harni zaki fadawa yanda zanyi idan Ina cikin yanayi ai ba duniya ce tayimin zafi ba kece kikayimin Kuma wama yace Miki banayin karatun qur'ani ko yau da asuba saida nayi nifa banson kirsa waike ta Allah to fadamin wanda yake bautar ubanki..." Fuuuu ya fice daga dakin yana cewa haba nima da jarabata in Banda qaddara ma mezanyi dake nifa baa hakicceni domin wahala ba ke kika rasa ba yar iskar da zata doramin hawan ruwa sakarya kawai" miqewa tayi da sauri ta leqa ta window jin tashin motarsa agogo ta duba 1:49am kawai saita dora hannu a ka ta rushe da kuka ita ba cin mutuncin ne ya bata Mata raiba aa fitarsa a wannan lkcn gashi gda basu kadai ba kowa da abinda zai fassara ta jima tana kuka ganin bazai kaita ba ta tashi tayi alwala ita ta rungumi qur'anin da aka mareta dominshi tana karatun tana hawaye tunda take baa taba wulaqantata irin wannan wulaqancin ba harda zagin ubanta wai JM da bakinsa yake ce Mata yar iska, sake rushewa tayi da kuka tare da daukar wayarta ta fara kiransa Kira daya tayi masa ya daga shassheqar kukanta yasashi saurin cewa “kinga don Allah kiyi Shiru wlh bazan iya kwana a gidannan ba zuciyata tafasa takeyi kaina kamar zai tarwatse Rafi'ah bansan meye yake damuna ba na kasa jurewa idan na cika takurawa cutuwa zanyi"........




_More Comments_
_More Typing_





*_Ummuh Hairan_*

Comment