MY BESTIE'S HUSBAND

*_Mbh_*


*_Ummuh Hairan_*


*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*_Telegram Link_*
            👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7


*_55-56_*


______________________________________
______________________________________


Hakan ce ta kasance kamar yanda Jamal ya fada Mata ranar litinin dakansa yazo ya dauketa zuwa asibitin da safe tare da bata takardun daukar aikin ta cike tabashi duk da baa bata wani bangare ba, tunda suka shiga asibitin gabanta ke faduwa har suka shiga reception din tanabin hotunan da aka maqale a reception din da kallo tana sauke ajiyar zuciya batakai ga gama kallon hotunan ba taji murya a bayanta ance Mata “sannu" gabanta ne ya sake bada wani dam har saida tayi kamar zata fadi yayi saurin Kai hannu ya riqota taja wata wawuyar ajiyar zuciya tare da zuba idanunta kan fuskarsa,
Murmushi ya sakar mata yace “wa kike tunani haka" numfashi ta sauke tare da janyewa daga jikinsa tace “ka tsoratani Jamal sainaji muryarka kamar ta JM dina" da sauri ya kalleta yace “waye shi?" Dago kanta tayi tace “Baban Mahir dina wani lkcn Ina tuna wasu abubuwa game dashi amma fah Raina yana fadamin ko ganinsa nayi bazan ganesa ba" saurin zama Jamal yayi saboda cikin kwanakin nan kalamanta suna sanyashi cikin tunani to Amma Alh Hashim yace itan qanwar matarsa ce to meyesa kalamanta suke Kama da wacce wani abunta ya Bata ne? Kullum tana saba lambobi idan an tambayeta sai tace JM dinta ya mutu Kuma idan tazauna sai take kalamin da suke nuna wani Abu sabanin haka.
Zuba idanunsa yayi akan hoton Ja'afar dake maqale qato a reception din ya zubawa Mahir ido yana nazarin wani abu hakanan yaji zuciyarsa na raya Masa wasu abubuwa duk da ya dade yana qoqarin bijirar dasu Anna sunqi barinsa miqewa yayi ya dubeta ga mamakinsa itama hoton ta kafe da ido ko qiftawa batayi Kama hannunta yayi yace “kinsanshi ne?" Numfashi ta sauke me qarfi tayi murmushin yaqe tace “aa kawai Dana kalli hotonsa sai naga yanamin yanayi da wani dana sani shekarun baya Amma fah nakasa tuna inda nasanshi qila ma a hanya na taba ganinsa"


Sake shiga rudani yayi bayan ya rakata office dinta ya koma nasa cike da tunani mamaki gamida zulumi wannan abin Yana bashi ciwon kai, wayarsa ya dauka ya lalubo number yayansa ya danna Masa Kira ring biyu ya daga muryarsa a kasalce yace “meye Kuma yake faruwa Jamal?" Ajiyar zuciya ya sauke yace “abubuwa da dama suna faruwa fah Prince kayi qoqari kazo 9ja gda ya rikice gefe Kuma da wani rikitaccen Abu da yake sani tunani da shiga zulumi" tashi yayi daga kwanciyar da yayi yace “jikin Barebarin ne ko kuwa wani abu ne daban?"
Shiru yayi na dan lkc kafin ya dago yace “Mai martaba ya matsamin nayi aure har yana iqirarin idan ban kawo ba zai zabomin so nikuma wacce nakeso taqi bani dama a qarshe ma ta dasamin kokwanto Yaya inasonta sosai Amma nafijin tausayinta tayi loosing memory dinta gabadaya bata iya tuna abinda ya faru da ita shekara uku baya saidai wani lkcn takan so tuna wani Abu Amma Bata samun dama a farko Ina dauka kamace kawai kakeyi da Mahir Amma yanzu na fara tantamar hakan inaji a Raina kamar ba Kama bace jinine Yaya don Allah kazo ka ganta ko ka ciremin kokwanto nima na samu salama"
Shiru Ja'afar yayi kamar bazaice komai ba sannan ya magantu da cewa “bana marmarin sake shigowa 9ja har qarshen rayuwata Jamal banida wani Abu da yayimin saura da zan kalla naji dadi komai na kalla damuwa yake qaramin am kaga ka manta da lamarin yarinyar ka nemi wata ka aura...." katseshi yayi da cewa “nifa ba hakanne damuwata ba damuwa ta  ka bani dama na gabatar maka da ita..." Katseshi yayi da cewa “dakata dallah malam idan ka gabatarmin da ita me zanyi Mata Kaine hakan ya Kama saboda Kai kake nema a gurinta ni bana shiga sharafin wani kayi naka nayi nawa kawai" qit ya kashe wayar cike da takaici.
Shima Jamal ransa ya baci sosai yana mamakin baqar kafiyar Ja'afar da gaske duk yamai dakansa majanuni  duk wani abu me amfani idan akazo Masa dashi sai ya Kama fada kamar ance masa shiga wuta"


Tun daga wannan ranar Jamal ya mayar da hankalinsa wajen bincike bisa lamarin Rafi'ah da kalamanta inda a gefe guda Kuma yake qoqarin samo wani Abu da zai tabbatar masa da zarginsa, yaudai tsoro ya cire kasantuwar asabar ce Rafi'ah batada aiki yasashi shiryawa ya nufi gdansu ya kuwa ishesu a parlour tanata tsokanar Bari'ah da cikinta ya fara girma Alh Hisham shima yana tayata.
Kasantuwar Jamal ya zama dan gda yasashi zama kusa da Rafi'ah yana duban Bari'ah yace “auntynmu ya nauyin jiki Kuma" harararsa tayi tace “gulmamme yaushe rabonka da kazo ka dubani" shafa kansa yayi yace “wlh abubuwa sukayimin yawa so banada lkcn kaina ko hajiyata?" Harararsa tayi yayi murmushi tare da kwantar da kansa a kafadarta yace “dan qara hararata kinji" dariya sukayi inda ita Kuma tayi murmushi kawai ya hadasu ita dashi da Mahir ya daukesu hoto yayi ajiyar zuciya yace “zuwa zanyi a wankeminshi nake kallonsa tunda kinqi aure na"
Itadai batace komai ba ta miqe ta shige dakinta zuwa yanzun tausayin Jamal yana neman yima zuciyarta illa kwanciya tayi ranta babu dadi ta rasa meye yakesata damuwa kwanakin Nan tanajin kewar mutane da yawa Kuma sunayi Mata gizo a idonta saidai takasa tuna su waye idan abin ya dameta sai tasa kuka kawai haka iyayen riqon nata zasuyita rarrashinta harsai tayi shiru to yauma duniyar data tafi kenan ganin kanta ya fara ciwo yasata tashi ta dauro alwalar La'asar tayi sallah taci gaba da lazuminta zuwa wani lkc me tsayi sannan ta tashi ta nufi kitchen ta dora musu abinci.


Sai bayan magrib ta gama girkin ta jera a dinning sannan ta koma dakinta tana duba wani littafi tanajin nishadin karatunsa wayarta tayi ring Saida ta katse sannan ta janyota aka sake Kira ta dauka taga number dake yawa àkan sensor din taja tsaki abokin Alh Hisham ne Alh Hassan ya takura Mata ya hanata sakat yo bandama abinsa taqi amsar saurayi saishi me Mata harda yara.
Kashe wayarta tayi gabadaya ta kwanta tanaci gaba da bincikenta bayan ta gama ta miqe tayi Isha ta fito parlour ta zuba abinci ta koma taci a dakinta sannan ta gyara kwanciya tana mamakin kanta a wannan kwanakin abubuwa sun cunkushewa kwanyarta da zuciyarta ta kasa Samo mafita sai addu'a da takeyi Allah ya kawo Mata mafita cikin rayuwarta.


********


Tunda asuba Hajiya Fatsum ta tashi jikinta da sauqi saidai surutan da har yanzu taqi ta barsu tana kulle a dakin da akabar Mata duk gidan babu me zuwa gurinta hatta yaranta Mata sunce bazasu iya ba sai Hajiya Innah da Jamal idan yana gari zuwa yanzu abubuwa ne suke damun zuciyar kowa da yake makusancinta musamman Jamal da subadadin surutun mahaifiyar tasa yake neman zautar da tunaninsa.
To yau dinma kuka takeyi tana Kiran sunan Bilkisu tana gunji tana cewa “nice na rabata da danta Kuma nasa aka kasheta a asibiti nice na rabashi da matarsa da dansa na haukatata ta shiga duniya mota tayi gori akansu nice, nice komai nice Amma bansan waye yayi masa farraqu damu ba bansan ya akayi ya daina Sona da tausayina ba Ja'afar kazo na fede maka biri....."
Rufe Mata baki Hajiya Innah takanyi tace “zafin ciwo ne yakesata surutu shidai Jamal yashiga chakwakiyar tashin hankali domin kuwa yasan banza bata Kai zomo kasuwa tabbas inkaji gangami da lbr to yaudinma hakance ta faru tunda ta tashi take Kiran Bilkisu Ja'afar Rafi'ah kowa mamaki yakeyi to wace Kuma Bilkisu?"


Sai bayan sun gama gyarats sun fita Jamal ya dubi Hajiya Innah yace “wai wace Bilkisun da Barebari ke yawan kirane?" Numfashi ta sauke tace “bansanta ba kafin zuwana gidannan akayita ance ta  haihune ta haifi ya mace kwana uku da haihuwar aka shiga dakinta akaga tanata fitar da dafara alamun wani Abu ya faru nan akayi da ita asibiti ana zuwa asibiti aka gano guba aka bata a kunun kanwa so a wannan Rana dai Bilkisu Bata kwana ba shikuma Mai martaba lkcn yana tsakiyar gwasake Bai iya daukar mataki ba da akaso tsawaita bincike ma hanawa yayi shine aka dauki yarinyar aka bawa Hajiya Fatsum lkcn itama ta haifi Ja'afar don dama Rana daya aka haifi Ja'afar da yayarku Nafisa wannan dalilin yasa suka taso tare iyakar abinda na sani kenan"
Jinjina Kai yayi ya fice daga gidan Kai tsaye gidansa ya nufa yayi wanka yayi sallah ya dauki waya ya fara danne dannensa cikin saa kuwa ya tarar da yayan nasa a online suka gaisa ya tambayeshi mutanen gida Shiru ta dan ratsa dabara ce ta fadowa Jamal ya lalubo hotunansa da Rafi'ah ya turawa Ja'afar yace _“yaya ga surukarka kasa Mata albarka inajin yarinyar nan ko Bata amince ba zan aureta indai zata zauna dani"_ cikin Ja'afar ne ya kada ya miqe zaune da sauri cikin tsananin tashin hankali da mamaki ya Kira wayar Jamal ya daga yace “ina ka samu hoton Rafi'ah ta?"


_Kuyi hqr da abinda kuka gani yau_


_Comments_
_Share_
_Vote_


*_Ummuh Hairan_*

Comment