MY BESTIE'S HUSBAND

*My Bestie's Husband*


_Oum Hairan_


_Bismillahir Rahamanur Rahim_


_Alhamdulillahi ala kulluhal_


_Masoya da maqiya duka Ina gaisheku kyauta wlh wlh wlh nayi muku alqawarin wannan littafin kyautane tundaga farkonsa har qarshensa._


_Tukuicin qauna qauna tabbas inasonku masoyan asali na Fadata ta Oum Hairan palace tabbas qaunarku tana firgitani har inrasa da kalmar da zan fasalta ta shiyasa nayi fitar burgu na kawo muku wannan na musamman a qarshen shekarar 2020 kasancewar mu lissafinmu na Muslumci ne Amma dai duk da haka nabaku happy new year saboda su Gebral Ostin da Mareetah da Nita da Helina  Kuma inayinku sosai bambamcin addini bazaisa naqi yaba qaunarku gareni ba Oum Hairan ta kowace Banda munafiki😍_


_Dedicated to_
_My husband Abdulqadir AGB Sidi sonso fisabilillah😘😘_


_Wattpad-realfauzahtasiu_


*_1-2_*


Yanayi ne me sanyi da kwantar da hankalin duk Wanda zuciyarsa ke cikin nutsuwa inda zai kasance matashin hankalin duk wanda nutsuwa tayi qaura cikin rayuwarsa, yaf yaf yaf ruwan yake sauka a saman manyan motoci da suka parkar a harabar Event center din da akayiwa laqabi da *Beautiful bridal*
Bude qofofin akayi a tare Kuma lkc daya wasu zafafan kyawawan yammata suka fara fitowa a jere a gefe guda Kuma sautin sassanyar iska da kida me zama a zuciya ya qawata gurin da yasamu qawatuwa da wasu kyawawan manyan flowers abindai sai Wanda yagani.
Salon kidanne ya sauya lkcn da wata arniyar mota ta samu matsuguni aka bude mawa wadanda ke cikin motar suka fito yammatane guda biyu kyawawa cikin shigar da take nuna amare ne sanye suke da farar wadding gown data karbi jikinsu, tare Kuma a lkc daya Suma angwayen suka  fito a tasu motar suka nufosu inda suke tsaye kansu a lullube.


Tahowa angwayen sukeyi inda sukuma amaren suke tsaye qiqam bude musu fuskar akayi inda duk Wanda ke gurin yayi mutuwar tsaye suka zuba musu ido dukkansu kyawawane na kwatance daya farace tas kamar bargonta zai fito inda dayar ta kasance wankan tarwada duk da hasken ya rinjayi baqin da ya sirka fatarta.
Dawowa sukayi a tare suka sauke idanunsu aka cikin na angwayen wankan tarwadar ce ta saki wani murmushi ta Kama hannun farar ta kamo hannun daya cikin angwayen ta saqala a nata ta bude Dan qaramin bakinta tace “Hml Mr Ja'afar Wakil"
Wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke tare da qoqarin tattaro nutsuwarsa ya hada guri guda ya kama hannun amaryar tasa ya janyota jikinsa har yanzu idonsa nakan na dayar budurwar ya bude bakinsa cikin sanyin yanayi yace “koda bantaba ganinki ba kamanni da siffa da yanayin sanyin halitta ya bayyanamin waceceke tabbas tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya halicci kyawawa guda biyu Kuma ya sanyasu suka zama aminan juna..."


Dariya wanda yake babban aminin angon yayi yace “Rafi'ah Nasir Darazau kenan aminiyar arziqi wannan itace remote control din matarka aduk lkcn data rikice maka to ka nemo Rafi'ah zata daidaita maka ita cikin sauqi" har yanzu idon Ja'afar akan Rafi'ah yake inda har ta fara qosawa da kallonsa ta juya ta dubi dayan tace.
“Muhseen kodai abokinka yayi ciwon makanta ne Bestie mijinki ya taba samun eyes issues ne" hannu takai zata janyota ta janye da sauri tana murmushi yayi saurin riqota yace “kinga Ni'imah qyaleta zamu rama ne danma ta samu an kalleta shine take wani jin dadi?" Muhseen ne yace “abin mamaki miskilai biyu ku mu qarasa fili nasan mu ake jira a fara program"
Takawa sukayi muhseen na gefen Ja'afar ita Kuma na gefen Ni'imah suka Isa cikin Hall din inda gurin ya kaure da tafi da sowar mutane a haka suka qarasa ango da amarya suka zauna MC ya fara aikinsa bayan kowa ya nutsane ya gabatar da Muhseen da Rafi'ah a matsayin wadanda zasu bada tarihin amarya da ango.


Rafi'ah ya fara bawa Abin mgn ta karba cikin qwarewa tayi sallama tare dayiwa kowa godiya da nuna farin cikinta da zuwan wannan rana ta farane da gabatar da kanta a matsayinta na best friend ta amarya sannan tabada tarihin amarya kamar yanda aka buqata sannan  tabada tarihin amintarsu anan ne zuciyarta ta karye hawaye ya fara zuba a idonta inda take cewa.
“Tabbas burin kowacce mace a rayuwa shine samun masoyi na haqiqa amatsayin miji duk da yau itace rana ta farko dana fara ganin Mijin Aminiyata na yaba da zabinta Kuma nayiwa Allah godiya daya kasance a matsayin mijinta Ja'afar Ina cikin wani yanayi na quncin zuciya saboda zan fara rayuwar kadaici ka rabani da bestie na  munsan dama wannan ranar zatazo amma bamu shirya yanda zamu dauketa ba inayi maka fatan nasara da addu'ar riqemin Bestie na amana don Allah bayan matsayin miji da ubangiji ya baka ka maye Mata gurbina a matsayin amini kada kabarta tayi kuka ko kewar rashina duk mace haka ta gada sai haquri haka Allah ya tsara mana mubar iyayenmu mubar yan'uwanmu da qawayenmu mu tafi sabuwar rayuwa da itace zata zamo hanyar samun tsiranmu duniya da gobe kiyama....."


Muryarta ce ta fara sarqewa da gaske tayi qoqari domin tun a harafin farko kuka yakeson qwace Mata inda gurin ya dauki kabbara da tafi a lkc daya, bawai don ta rasa abin fadaba saidon ganin qawar tata itama tana kuka yasata miqawa MC din abin mgnr  ta nufi step din zata sauka kasancewar duk wata nutsuwarta ta qaura sun dade suna kukan zuwan wannan ranar Amma Basu tabajin dacinta kamar yau datazo ba.
Jitayi an riqo hannunta ta baya ta juya da sauri idonta na shararar da hawaye ga mamakinta sai taga Mijin aminiyar tata ne murmushi ta qaqaro ta janye hannunta ta bude bakinta tace “karka damu Ja'afar bakayi laifiba hakan shine cikar gatan kowacce ya mace munsan da zuwanta rashin hankaline yasa muka kasa shiryawa zuwan nata..."
Fakar idon mutane yayi ya dora hannunsa a bakinta yana me qare Mata kallo yanajin bugun zuciyarsa daya fara tun farkon haduwarsu yana qaruwa yace “Nasani Rafi'ah amma Ina Zaki?" Janyewa ta kumayi tana saita qoqarin bashi space kasancewar qarancin taqin tsakanisu yayi yawa tace “zan zanje na sallami baqinmu ne abokan karatunmu"


Jinjina Kai yayi yace “Ni'imah tace kince idan kika kawota tafiya zakiyi why?" Shiru tayi tanaci gaba da jan zuciya yayi murmushi yana ayyana abubuwa da yawa a ransa yace “kiyi har kada ki tafi ki jira a tashi mu tafi mu tare mu kaiku gda please kada kiqi kinji?"
Daga masa Kai tayi ta juya da sauri saboda tagaji da gwama numfashi dashi binta yayi da kallo shikadai yasan me yake saqawa a ransa ya juya ya koma gurin zamansa ya kamo hannun Ni'imah yace “ta hqr daqyar qawarnan taki akwai wayo" murmushi tayi me hade da kuka tace “danma kaine tana ganin girmanka da bazata tsayaba kafaffiya ce akan ra'ayinta daqyar Dad ya rarrasheta tazo shima don ance ita zatayi history ne"
Numfashi yaja yace “tanada kyau...." Dariya Ni'imah tayi kadan tace “danma bata cikin nutsuwa ne shiyasa duk a hargitse take ko kwalliya taqiyi" da wannan akaci gaba da gabatar da dinner din duk wani motsi da Rafi'ah takeyi idon Ja'afar akanta bayako qiftawa hakanne yasa tasha jinin jikinta ta koma gefe tana caje kanta ko want abune yasa yake kallonta da bazai iya fada mataba


Ta jima tana qarewa kanta kallo a madubin motar kawai saiji tayi ance Mata “sannu" a tsorace ta juya kuma a firgice hakan yasata karo dashi tayi taga taga zata fadi yayi saurin tarota ta daidaita a qirjinsa yaja wata ajiyar zuciya tare da dora kansa saman kanta ya shaqi qamshin gashinta, jin yasa hannu ya qara shigar da ita jikinsa tayi saurin janyewa don ganin waye.
Ja tayi da baya da sauri tare da cewa “lfy?" Duk da baiji dadin tambayar ba haka ya hadiye ya shafa kansa yace “ankirani a waya na taso don amsawa kawai na hangoki so nayi tunanin kukan kikaci gaba dayi shiyasa na qaraso am sorry please na tsorataki ko?" Numfashi taja ta furzar tace “ok ka koma gurin Bestie bani bakai zata shiga damuwa"
Binta yayi da kallo yace “ke Kuma kinason zama a damuwa ko?" Wani kallo tayi masa daya sanya lakar jikinsa tsinkewa tace “ita ce yake wajibi a gurinka kayi qoqarin gusar nata da damuwa nima inada me gusarmin da tawa shi nake Shirin Kira ma yanzu kaje na gde da kulawa...."


Batayi aune ba tajita a qasansa a jikin mota yadan janye kadan yace “ni na rabaki da farin cikinki saboda haka ni zan samar Miki da wani farin cikin Rafi'ah kijira" haka kawai ya fada ya juya yana amsa waya ya koma ciki tabi bayansa da kallo tare da cewa “wannan wanne irin mutum ne?"
Tabe baki tayi ta juya taci gaba da harkokinta hakanan taji ranta yana baci batason mutum me shisshigi a rayuwarta wannan dalilin ya hanata komawa gurinsu taci gaba da sallamar baqi bayan ta gama sulale ta koma can qarshen hall din ta zauna tana chart dinta da qawayensu.
Yawanci wadanda Basu samu damar zuwa dinner din bane suketa bata hqr tare dayi musu fatan alkhairi Saida taji ankusa tashi sannan ta tashi ta koma mazauninta cikin dan zaman da  tayi dau dagowar duniya idonta a cikin na Ja'afar yake fadawa taja wani dogon tsaki da yasasu dagowa duka harda Muhseen daya lura da abinda ke faruwa tun dazu, dubanta yayi yace “yadai ammata?" Murmushi ta qaqalo tana kallon Ja'afar din tana yatsina fuska tace “saurone ya takuramin anan gurin wlh tunda ankusa tashi ku sameni a mota kawai"


Bata jira amsaba ta miqe shina Muhseen ya miqe yana tsokanarta yace “daki ai baya tashi ragaya ta zauna ba muje tunda mun sallami baqinmu mu jira ango da amarya danni wlh bacci nakeji ma" da wannan suka jera suka Isa inda motar take suka shiga suka zauna suna dan taba hirarsu.
Duk hirar akan bikinne sukeyi inda rabin hankalinta yake kan tunanin dalilin wannan mayataccen kallo da bibiya da mijin aminiyarta yafarayi Mata tundaga kallon farko, kasa jurewa tayi ta dago ta dubi Muhseen da hankalinsa yake kan danna wayarsa tace “Mr Muhseen Wlh banason kallo a rayuwata takurani yake ya hanani sakat"
Dagowa yayi ya zuba Mata ido yace “waye ya dameki da kallo?" Ajiyar zuciya taja ta kawar dakai tace ka share kawai" yariga yasan inda ta dosa fada masane bazatayi ba hakan yashi sake kallonta yace “to Rafi'ah meye laifin mutane don sunbawa ido abinci kedince Allah ya ginaki ginin gaske wlh na dade banga mace me cikar halittarki ba kinsan ba kowa yake iya gani ya dauke Kai ba kekuma gaki kamar me aljanu da mutum yace yanasonki sai ki Kama gaba dashi"


Murmushi tayi tace “wannan dalilin ne yasa banason kallo saboda nasan daga kallo saqo yake shiga zuciya nikuma na tsani ma ace anasona wlh tunda Yassar ya rasu nakejin bana sha'awar sake soyayya da kowa" tabe baki yayi yace “wanda ya tafi ya tafi kenan bazai dawo ba garama ki manta da komai ki fara sabuwar rayuwa kina ganidai ga aminiyarki yanzun bikinta akeyi ke kanki bazakiji dadin rayuwa ke dayaba ko Ina kun tare ku tashi nan ku fadi csn kwanciyar bacci ke rabaku itama in kunso"
Hadiye wani Abu tayi me ciwo tace “babu komai ana tare insha Allahu inasa ran zabi mafi kyawun kyau gurin lillahi Muhseen badagani bane zuciyata takasa karbar madadin Yassar shi na fara so shi ya huda zuciyata shiyasa madadinsa yayi wahala"
Ji sukayi ana qwanqwasa glass din gabanta ya fadi lkcn da Muhseen ya sauke glass din idanunsa akanta yace “kazo ka sata a corner me kake karanta mata?" Shafa kansa yayi ya bude masa yace “kawai nasiha nakeyi Mata itama ta fitar da miji cikin masoyanta tayi aure saboda lkc qurewa yakeyi" bai wani bawa mgnr muhimmanci ba suka shiga shida Ni'imah Muhseen yaja motar suka tafi.


Tunda suka taho babu me cewa wani qala lkcn da sukaje duk motocin sun jima da zuwa anayin parking Rafi'ah ta bude qofar tanayiwa Muhseen Saida safe ta shige cikin gidan mutane nayita yimata tsiyar saura ita itama ta fitar da miji suzo susha shagali murmushi kawai takeyi ta shige ciki ta haye saman ta fada dakin Ni'imah ta kwanta tana mayar da numfashi.
A haka Ni'imah tazo ta sameta t zauna a gefenta tace “Sweet yace kiyi hqr da laifin da yayi mki kike gudun hada inuwa dashi"
Dagowa tayi ta dubeta tace “baimin komai ba Bestie kaina kw ciwo nakeson samun relief" miqewa Ni'imah tayi ta cire kayanta tace “ke kika sani ni wanka zanyi na kwanta" itama miqewa tayi ta cire rigar jikinta ta daura zani Ni'imah na fitowa ta fada wankan tana fitowa taja bargo tare da addu'a bacci ya dauketa.
Saboda gajiyar da sukayi Basu farka ba sai da Rana ta fito shima momy ce mahaifiyar Ni'imah tazo ta tashesu suka tashi Ni'imah tayi wanka tayi sallah kasancewar sun makara ita Kuma dake ba sallar takeyi ba tayi wankan sukazo sukayi zaman shiryawa me kwalliyar ta  shigo tayi musu suna gama shiryawa aka daura auren rungume juna sukayi suka saki wani ihu daya janyo hankalin kowa dake gdan.........


Nufosu sukayi da sauri suka riqosu aka rabasu daqyar tare da zaman rarrashinsu itadai Rafi'ah zazzabi ne ya rufeta ta koma ta kwanta tana rawar sanyi angwayen da suka shigone sukaga meke faruwa Ja'afar ya Kira wani abokinsa likita yazo ya dubata yabata magunguna tasha ta kwanta yinin ranar bata iya tsinanawa kanta uwar komai ba sai bacci da takeyi har aka gama bikin da yamma ta farka anata shirye shiryen Kai amarya batare data bari kowa yaganta ba ta sulale tabar gidan bikin ta cikin saa tana fita tasamu napep ta nufi unguwarsu ta shiga gidansu babu kowa sai kishiyar mamanta mama tana wajen kai amarya.


Aunty Murja tana ganinta tasan ba lafiya ba ganin bata saurari kowa ba ta shige dakinta ta kullo yasata miqewa tabita ta tarar da ita zaune ta hade Kai da gwiwa sai kuka takeyi, zama tayi kusa da ita tace “ni bantaba ganin irin wannan rayuwa taku ta qaryaba to dawwama zakuyi babu aure yanzu da Allah yayi naki auren ita ya zatayi da sai yanzu Allah ya nufi nata? Dama kun hqr kunsawa zuciyarku hqr da salama kowacce mace wannan lkcn take jira ita ta tafi Abuja ke Kuma waye yasan inda zaki"
Shiru tayi batace komai ba sai kukanta da takeci gaba dayi ganin bajin lallashin zatayi ba yasa Anti Murja miqewa tacd idan ya isheki kyayi Shiru nikam nayi nan" tana fita wayarta tafara ring ta duba taga number Bestie ce ta mayar ta kife saboda bata buqatar wani Abu da zai qara daga Mata hankali a wannan lkcn hakance tasata tayi kwanciyarta, Ni'imah tayi Mata misscall yafi ashirin taqi dagawa qarshe ma ta kashe wayar haka tana kuka tana Kiran Bestie aka sata a mota aka nufi wani Martaba Estate dake cikin garin na Bauchi domin Kai amarya.


Saida komai ya lafa akakai amarya dakinta gdanta babba me kyau da tsari an zuba kaya Kuma ankashe kudi a gidan kasancewar iyayen Ni'imah masu haline shima kuma mijin da arziqinsa dan sarautar Azare ne Ja'afar Wakil suna tashen kudi da mulki mahaifinsa ne abokin mahaifin Ni'ima sune suka hada auren cikin wata biyu akayi komai aka gama abinka da masu data a hannunsu.
Angwayen ne zaune cikin mota Muhseen ya dubi Ja'afar yace “kai kanada matsala baka iya control din zuciyarka ba don Allah Ja'afar na roqeka kads ka soma wannan katobarar ita zuciya tausarta akeyi ba komai ake qyalets tayi abinda takeso ba kada kasa ka zamo silar yankewar wannan kyakkyawan zumunci da aka faroshi tun yarinta Ja'afar Mata basuda hankali akan wannan qaramin issue din sai hankalin kowa ya tashi koda yake inada yaqinin Rafi'ah bazata taba baka fuskaba"


Girgiza Kai yayi yace “Muhseen bakada adalci a rayuwarka 34 years muna tare dakai katabajin nace maka inason mace da aure wlh da gaske nakeson Rafi'ah tsakanin jiya da yau zuciyata tana azabtuwa da qaunarta bansan meyesa hakan ta faru ba meyesa bansanta ita kadaiba meyesa batazomin babu alaqa ba sai tazomin a matsayin aminiyar matata Muhseen kabani mafita wlh idan har banga Rafi'ah a daren nan ba bazan iya yiwa yarinyar nan komai ba Kai nifa badan lkc ya qure ba da zuwa zanyi na samu Dad na fada masa a janye na samu wacce nakeso wacce na dade Ina mafarkin samu irin matar da na dade Ina zanawa a zuciyata"
Sarai yasan halin abokin nasa iyakar gaskiyarsa yake fada shidin ba mutumne ma'abocin qarya ba kuma bai iya boye Abu a ransa ba, ji yayi ya damqesa yace “don Allah don annabi kakaini naganta wlh babu abinda zance Mata Muhseen iyakar ganine insson sanin halin da take ciki bansan hanyar gidansu ba da tuni na tafi"


Badon Muhseen yaso ba ya juya motar daga gurin da sukazo siyawa amarya kaza suka nufi unguwar su Rafi'ah a bakin get suka tarar da Abba da me gadi suna tattaunawa saboda haka Kai tsaye shi suka nufa suka gaisa yace bai ganesu ba Muhseen yace “Abba surukanka ne mijin yarkane da ka aurar yau Ni'imah shine tace muzo mu gano Mata meye ya hana Bestie dinta zuwa rakata gidan mijinta"
Dariya Abba yayi irin tasu ta manya yace “kayy Amma yaro yarone shine kums kuka dauko jiki Kuma da taya shirme hauka, bari na shiga na gano muku ita  naji uwayenta suna cewa batada lfy ma"
Shigewa yayi ciki Ja'afar ya miqe ya daga hannu sama yayi hamdala babu jimawa saiga Abba ya fito yace “ai kawai ku shiga tanacan ma amai taketa fama ita dama jinyarta amai kamar me yaron ciki" wani dadine ya cika zuciyar Ja'afar ya fadada murmushinsa Muhseen ya harareshi tare dayin qwafa kan ya ankara tuni Ja'afar yaje qofar falon suka shiga da Abba jansu Abba yayi har saman ya tura qofar ya shiga tana kwance daga ita sai dogon sikert da taja har qirjinta ko bra babu a jikinta har yanzu kuka takeyi Ammi na rarrashinta tsaki Abba yayi yace.


“Do Allah amina ku qyaleta tayita kukan gajiyane batayi ba yo naji iskanci so kike a qyaleta kuyita babare a gari ke babu aure ita babu kaji wani sakarci" sake shigewa jikin Ammi tayi ta shafa kanta tace “to bandama abin me sunan manya kema ai addu'a mukeyi Allah ya kawo mijin mu auraddake kema kije kiyi bautaTashi tayi zaune daidai lkcn da Ammi suke gaisawa dasu Muhseen idon Ja'afar akan qirjinta ya sauke numfashi tare da cewa “ya jikinki" wata uwar harara ta watsa masa ta dauki hijjab dinta ta zura ta koma can qarshen gadon ta kwanta ba Shiba hatta Abba Saida abin yabashi dariya yace “to Ja'afaru kai me laifine fa ka rabata da aminiyarta"
Murmushi yayi a ransa yace “kema very soon zan daukeki sai naga ya amintar zata kaya tunda kunayiwa dodo daya tsafi" a fili kuwa cewa yayi “kiyi hqr bansan da wannan amintar ba dana bari anyi Rana daya Kinga da duk haka bata faruba".......


_Please share_
_And_
_Comments_


*_Oum Hairan_*

Comment