ELEVEN

Tuni an sallamo Karimatu daga asibiti, domin kudin jinya ya 'kare. 'Yar wayarta tuni ta siyar da ita, da wanda 'yayanta suka tallafaa mata dasu duk sun 'kare a magani. Kamar kullum a sheme take kwance kamar shekararriyar saniyar dake jinya. Lokaci zuwa lokaci takan saki murmushin takaici, da alama dai mutuniyar taku tuna baya take yi.


Wata waya 'kirar nokia wadda akewa laqabi da rakani kashi ta 'dakko a gefan inda take kwance, tasha 'dauri da kyauro, gefe da gefe kuma an nane da super glue. Can 'k'arshen wajen chaji kuwa an nannade da salatef (seal-tape). Duk screen 'din ya faffashe kana hango cikin wayar, madannan sun goge sai da biro aka zana kowacce lamba. Dakyar ta iya gano lambar Sidiya, takira ta yafi sau goma kafin ta 'dauka dakyar,


"Toh baxan 'kara ba, sai kinzo."


Shine kawai abunda Karimatu tace, ta ajiye wayar a gefe. Can wajen bayan minti talatin sai ga Sidiya tana cika tana batsewa, kallo 'd'aya taiwa 'yan gidan ta 'dauke kanta. Hajia dake gefe ta tab'e baki kawai tana ci gaba da 'kulla alala a leda. Kamar yaki Sidiya tashiga 'dakin da Karimatu take tana wani yatsina fuska, gashi ta tsaya 'kerere akanta. Ganin ta yasanya Karimatu 'dan muskutawa ta gyara zaman ta dakyar.


"Ki zauna mana Sidiya."


"Kai gaskia a'a, kin ji wani shegen zarni dake tashi a jikin ki kuwa, kuma fa nagaya miki kidena kirana da yawa, fisabilillahi baban Gali(mijin ta) sai fad'a yakemin, nifa gaskia ba zaki kashemin aure ba Karime"


Shiru kawai Karimatu tayi, tana sauraron masifar da Karimatu ke zazzaga mata, babu ma Yaya da take kiranta a da, sai Karime gatsal. Tana cikin tunani, muryar Sidiya ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi.


"Wai me zan miki ne da tun asubahi kike dokawa waya ta kira?"


Cikin taushasshiyar murya Karimatu tace,


"Da..Da..Dama kudi zaki aramun asiyo min gurasa da..."


"Kutma.. Cab lalle ke dinnan ma, kiji da kudin lapiar ki ma a'a sai ta biyewa dad'in baki? To wallahi bani dashi, ni idan kin samu ma ki biyani dari uku na ta shekaran jia, bazan iya da cin bashin ki ba."


"To ko zaki aiko mun da abincin da ki kai?"


Kyakkyawar harara Sidiya tayiwa Karimatu, kafin ta buga zani kawai, ta fice abinta, girgiza kai Karimatu kawai ke yi, ganin yadda Sidiya ta juya mata a baya, ada itace gatanta, ta'dauke 'dawainiyar 'ya'yanta ma gaba ki d'aya. Tana cikin tuna baya, Alawiyya tashiga 'dauke da kwano sai 'kamshin man 'kuli ne ke tashi. Shinkafa ce da wake na gidan asabe mai abinci.


"Gashi inji Hajia.."


cewar Alawiyya, ta duk'a ta ajiye tafi ta.  Cikin hanzari jiki na bari Karimatu ta bude kwanon abincin, shinkafa da wake da yasha man 'kuli da yajin tafarnuwa, sai yankakken tumatir da albasa, ga maggi guda d'aya a gefe. Kamar mayunwacia haka Karimatu ta shiga 'durawa cikinta abincin, tana kad'a kai da alama yai mata dadi. Ashe Hajia duk taji yadda sukai da Sidiya, uwa mai dad'i, ta ciri dari biyu cikin kudin alalar tabawa Alawiyya ta siyo mata abincin. Ko kad'an ba tabada sigar da su Alawiyya xasu rena Karimen ba, dukkoda tarin abubuwan da ta yiyyi musu. Tana gama ci ta koma ta kwanta da 'd'ayan barin, domin 'barin hagun ta baya aiki sam. Shiysa takan sau fitsari wani lokacin a zaune idan robar fitsarin ta goce.


Gaba d'aya hakurin Khaled ya 'kare, domin duk kawaicin da yake musu yaga basa ganewa, a bashi matar sa an 'ki, tun shekaran jia aka kawota amma ko fuskarta 'kememe an haramta masa ganin ta, zaune yake akan kujerar 'dakin sa shida Saifullah dake sketching wani zane . Sake sakin tsaki Khaled yayi a karo na ba adadi kafin ya turo baki gaba cikin tausayawa yace,


"Saboda tsabar an tsaneni ba, Wannan ai rashin adalci ne."


Saifullah daya gaji da mitar Khaled ya mike yana tattara kayan sa zai bar masa 'dakin, cikin azama Khaled ya riko shi yana rausayar da kai,


"Dan Allah guy, kayi wa su Umma da Aunty magana su bani matata.."


Sakin baki Saifullah yayi yana duban sa, cikin tabe baki yace.


"Saboda mace kake mita awa da awanni dama?"


Kad'a kai Khaled yayi yana wani taune 'kasan lips 'dinsa,


"Ba zaka gane ba Guy, na shirya ne, a matse nake wallahi. Su bani ita mu tafi sunki wai sai lokacin tafiyar yayi tukun na, sai kace ba mallaki na bace.."


Yakice hannunsa Saifullah yayi, yana goge wajen da handkerchief, Ganin haka yasanya Khaled girgiza kai kawai yana murmushi,


"Toh ni meye nawa aciki?"


"So nake kayiwa Umma da Aunty magana su bani matata, hak'uri na ya 'kare. Ita kanta nasan a matse take."


"Haka tace maka?" cewar Saifullah, Yana mai dubar agogon hannun sa.


"Lapiyayyar macece fa, wallahi itama nasan ta matsu, dan iska, kai saboda yau za'a kai maka taka shiysa ai baka damu ba."


"Wa?"


"Matar ka..Islam mana"


Tabe baki Saifullah yayi yana yatsina fuska, kamar an kira sunan kashi. Cikin nuna ko ajikin sa yace.


"Kai mata suka dama.."


Mikewa tsaye Khaled yayi, yana wata y'ar iskar miqa, kafin yace.


"Tabbas mata sun dame ni wallahi, tunda ababen more rayuwa ne ku.."


Be karasa ba, Saboda wani dogon tsaki da Saifullah yayi.


"So suffocating..." ya fada yana barwa Khaled dakin gaba d'aya.


Saifullah na fita sukai kicib'is da Haj Latifa, da wasu baki dake shirin tafiya rakiyar amarya Islam. Sosa 'keya saifullah yayi, Haj Lateefa tayi murmushi kafin tace.


"Lalle Ango, shine kayi shigewar ka 'daki kana ji su Gwaggo na tambayar ka, to kayi sauri dai ka sauya kaya dan Allah.."


"Toh Aunty.."


shine kawai abunda Saifullah yace, yai gaba yana tura baki alamun shagwab'a. Dakin da yaga mahaifiyar sa tashiga 'daxu nan yayi, yayi sa'a kuwa ba kowa a dakin sai ita kadai tana shirya wasu kaya a akwatuna, tana ganinsa ta fadada murmushin ta,


"Auta..."


Da sauri ya 'karasa, yana dora kansa kan jikinta, shafa sumar sa ta shiga yi,


"Auta na.."


"First love.." ya furta cike da shagwaba.


"Auta, yanzu fa ka girma, gashi yau za'a kaika gidan ka fa. Kaga kayan amaryar ka ne nake had'awa su Fatima su tafi dashi yanzu. Ra'aki ne da kususuram"


'Daga kansa yayi yana duban akwatunan kalar hoda, guda hudu da Kit, shake da kaya harda kwando cike da turaren wuta da khumrah. Cikin murya cike da tausayawa yace,


"First love ni dai gaskia tayi zaman ta a gidan su."


Ware idanuwa Haj zuwairah tayi tana duban Saifullah, 'kin yadda yayi su had'a ido. Murmushi kawai tayi kafin tace.


"Saboda me zata zauna a gidan su? Bayan an daura aure, Duk adon mace ace tana gidan mijin ta shine auta."


"First love... Ni nufi na kowa acikin mu ya zauna a nasu gidan, If she needs anything..."


"Sai kace a garin gab'a-gab'a Auta? A'ina aka tab'a yin haka? Ayi aure miji da matar kuma kowanne na gidan iyayen sa, anyi ba ayi ba kenan."


Shiru yayi kaman zai yi kuka, Haj Zuwairah tacigaba da sha fa kansa tana bashi hak'uri,


"Kayi hak'uri Auta, haka dama rayuwar auren take. Kuma kaga naji Baban ku na cewa ma kila muma cikin shekaran nan mu dawo Abuja, Saboda yana so ya dawo da asibitin sa nan."


Cikin murna Saifullah ya d'aga kansa alamun yayi na'am. Haka dai tashiga yi masa nasiha da dabarta masa yadda ake zamantakewar aure, yadda zai rike y'ar mutane da amana, ta 'kar'kare da,


"Na bawa Abbas sak'o idan zaka je gidan naka sai ka karba. Tashi kaje ka shirya, Allah yayi muku albarka, yasanya alkhairi da farin ciki a rayuwar ku."


Kad'a kai Saifullah yayi yana goge hawayen daya zubo masa, Haj zuwairah ta dafe baki kawai tana daria,


"Ah lalle ango da kukan barin gida, Lalle auta na ya kafa tarihi."


Ta fad'a tana mai mayar da nata hawayen daya taho. Zai fita daga dakin Khaled ya tunkaro kai yana sallama, ganin Saifullah yasanya shi fad'ad'a murmushin sa,


"Iyye Angon Is.."


Harara Saifullah ya wurga masa, yana furta kalmar da ta zamar masa ta dolen fad'a.


"So...s.."


Be karasa ba Khaled ya riga shi yana


"Suffocating mutamina!"


Ficewa Saifullah yayi yana tsaki, shi kuma Khaled ya samu waje ya zauna bayan ya gayda Haj Zuwairah. Sun 'dan fara magana Fatima da Humaira suka shiga 'daukar kayan Islam na ra'aki da kususuram. Bayan sun fita dasu ne Haj zuwairah ta dubi Khaled dake sake sunkuyar dakai kasa kamar sabuwar amarya, tuni ta gano jirgin sa amma ta danne,


"Yawwa ina jinka Khaled"


"Aunty...Temako na zaki yi"


"Temako kuma?!"


"Eh aunty dan Allah wallahi ba kiji 'kirji na ba"


"Subhan'Allah Khaled baka da lapia ne?"


"Kusan hakanne Aunty, akan Fatma ne"


"Matar ka?"


"Eh ita Aunty..Dan Allah ba wanda zan iya kawo wa 'ko'kon bara na ya amsa min sai ke, ki dubi girman Allah Aunty, kiwa su Ummah magana su bani..."


"Matar ka Fatma"


Sosa 'keya yayi, yana wasa da gashin carpet. Murmushi kawai tayi kafin tace.


"Khaled kenan, gata fa akai maka, sanin kanka ne gidan da zaku zauna anan garin yanzu ake yinsa,an kammala fenti kawai yarage, abunda yasaka aka dakatar kuma kace kai ba anan zaku zauna ba sai Spain. Yanzu so kake ka 'dauki yarinyar mutane kuje hotel? Ga manya a gidah, ka naso ka janyo abun da za'aita kananan maganganu ko?"


"Aunty .. Ni fa ko fuskarta an hana na gani, k.."



"Shikenan kawai, Bari zan turo maka ita yanzu sai ku gaysa."


Dadi kashe Khaled, mikewa Haj Zuwairah tayi ta fita, mintina kad'an sai ga Fatma ta shiga tana sunkuyar da kai 'kasa. Kasa hak'uri Khaled yayi, yayi hanzari janyota jikin sa yana wani shegen murmushi. Jikin sa sai rawa yakeyi, cikin kunya fatma tace,


"Ina yini..?"


"Ya rouh.! Wane yini kin gasa ni, har ramewa nayi na rashin ganin ki"


"Jiya ne fa kawai love.."


"Say no more! Dole ki karba hukunci."


Ta shiga kiciniyar kwace jikin ta, ya riko hannun ta, yana sinsinar kamshin jikin ta, hannun sa d'aya kuma na karakaina cikin rigar ta....


  *6:30pm*


Zaune Islam take, kanta a 'kasa tana tsakiyar su Daddy (prof Khaleel) da Ya Bala, da Inna bilkisu, gefe kuma Hansa'u ce da Haj Aysa, can 'k'arshen 'kurya kuma bodara Yafendo ce, da alama dai mutuniyar taku ta nisan ta kanta don gudun abun kunya. Sosai aka shiga yiwa amarya Islam fad'an yi nayi bari na bari, kuka kawai take yi tana jan majina, Haj Aysa dake gefe lokaci zuwa lokaci itama take fakar idonsu ta goge nata hawayen. Haka ma Prof Khaleel shima idanuwansa cike suke taf da hawaye.


Haka dai kowannen su ya yiwa Islam fad'a, sosai take kuka, jikin ta har rawa yake yi. Ta rungume Daddy tana kuka yana kuka, sai da Yafendo ta raba su dakyar. Sannan aka komar da Islam sashen Haj Aysa, wanka ta 'kara yi, ta sanya wata atamfa datasha stones blue, mahaifin Haj Aysa tun na aure shi aka yafawa Islam kamar yadda Aysan ta qudura, ba'ai mata makeup ba amma ba kadan ba tayi kyau cikin royal blue shigar ta, dai-dai stairs Haj Aysa ta hango Islam, da hanzari ta sulale zata gudu don kada su hadu Islam tayi saurin rikota tana kuka, duk mutanen dake wajen sai da suka koka, domin ba kadan ba xasu baka tausayi.


Dakyar dai aka 'banbare Islam daga jikin Haj Aysa, sannan aka sanyata a mota, suka fara zuwa gidan su Haj zuwairah, gaisuwar surukai, tsabar sonta da Haj Zuwairah keyi rungumota tayi jikin ta, tana shafa bayan ta, kamar ta maida ta ciki haka take jinta, da alama dai soyayyar auta Saifullah ta fara shafar Islam. Sai gud'a ke tashi.


Motoci a convoy suka nufi unguwar Asokoro kai Islam gidan ta, Abbas ke tuka motar da Islam take, gaban motar Helwa ce, baya kuma tsakiya Islam ce, gefe da gefe kuma Hansau da Yafendo, sai sauran motoci dake 'dauke da 'kawayen amarya da 'yan uwan amarya. Yan uwa na kaita suka mata sallama suka tafi bayan sun yaba akwatunan ra'aki da kususuram da aka jere su a drawer, gidan sai tashin 'kamshin turarukhan wuta yake.


A 'dakin 'kasa aka zaunar da Islam, sai kuka takeyi, yan uwa duk sun dare, sai 'kawaye dake jiran tawagar ango, Ai kuwa ba'a jima ba abokan ango suka shiga, aka tsadance kudin siyan baki suka biya, da yawa daga ciki sun karbi nambobin juna, Riri ma taci sa'a wani ya 'kyasa ya karbi tata, sai 10 sannan suka watse, duk abun nan Saifullah na mota yana danna waya. Sai da ya mula yasha iska sannan ya fito, sanye cikin yadi kalar madarar ruwa, bai sa hula ba, kwantaccen gashin kansa ya kwanta luf, sai tashin 'kamshi yakeyi, Abbas dake gefe ya ciro wasu ledoji a bayan boot ya mik'a masa yana jaddada masa da,


"Gashi Mami(Haj Zuwairah) tace lalle na baka, nasan kuma ta sanar maka, My G Allah ya baku zaman lapia ya kawo 'kazantar 'daki."


'Kwatar ledar Saifullah yayi sai kace fada, Abbas yai murmushi kawai yaja kan motar sa ya fice, Cikin takun 'kasaita Saifullah ya shiga ciki bakin sa dauke da sallama, kamshin turarukhan wuta suka doki hancin sa, ya lumshe idanu cikeda Jin dadi. Sama ya hau, ya shiga wani 'daki da ke dauke da furnitures blue and white, murmushi yayi ganin dagaske Mami ashe ta shrya masa dakin sa tamkar na Lagos. Bandaki ya fada yayo wanka da alwala, sallar nafila yayi ya karanta alqur'ani yayi addua ya shafa. Har ya mike akan gado ya tuna ledar da akace lalle yabawa Islam. Dauka yai ya bude tafarko kaji ne da gurasar larabawa da sauce, sai ta biyu kuma yoghurts ne da drinks. Tabe baki yayi ya fita.


Dakin dake kallon inda yake ya shiga batanan, ya bude dayan na kusada corridor nan ma ba ta ciki, 'kasa ya sauka, kansa tsaye ya shiga 'parlorn kasa ya murza dakin ciki, can yahangota a gefen gado tana karanta littafin addu'oin 40Rabbana. Ga wani sihirtaccen kamshi dake tashi a cikin 'dakin. Dama fitilar dim ce saita 'karawa dakin wani annurin haske, gyaran murya yai, hakan yasanya Islam daga kai ta dube shi, sai kuma tayi 'kasa dashi tana cigaba da karatun ta.


Cikin takun sa, mai cike da samartaka da nuna isa ya 'karasa wajen ta, dadda'dan turaren sa na Hugo boss ya daki kofofin hancin ta, shima fa ana sa 'bangaren khumran jikin ta yasa shi lumshe idanuwa. Ja baya tayi, ya bita sai da suka kai 'k'arshen bangon 'dakin sannan ta tsaya tana kauda fuskarta gefe, siririn tsaki ya saki kafin ya dire ledar a gabanta yana mai nuni da ledar,


"Ga shi nan, Mami tace a baki."


Yana gama fada ya sa kai ya fice, nannauyar ajiyar zucia Islam ta sauke, tana raba idanuwa.


Nannauyar ajiyar zucia Islam ta sauke bayan fitar Saifullah. Sai raba idanuwa take yi. Dakyar ta iya jan sayyadar ta, tashiga 'bandaki, alwala tayo tayi sallah, ta bude drawer dinta da su Yakolo suka shirya mata kaya, riga da wando kakkaura ta 'dakko ta saka. Tabi lapiar gado, Don dama tayi sallah d'axu. Wayar ta, ta 'dakko ta shiga WhatsApp, messages rututu tagani ana tayata murna da Allah yasanya alkhairi. WhatsApp family group 'dinsu ma na 'Y'ar Gaya Fam Bam'  duk maganar bikin ake yi, sai na secondary school dinsu na BNA 2k14. Shima sai yad'a zancen akeyi, ita dai dariya kawai takeyi, sannan ta turawa kowanne grp emijo na love ❤. Nan aka shiga maganar 'ya amarya da yin reply,ina ango,'


"Yana gaida ku, sai da safe.."


Tacewa kowannen su, kafin ta kashe data dinta ta kwanta, ko takan reply din Lee dake cewa 'sai tazo gashin amarya da safe' bata bi ba, nannauyan bacci lokaci d'aya yai awun gaba da ita. Da asubah ta mike jin kiran sallan masallacin mak'otansu, hawaye ne ya ciko fal idanunta na ganin dagske dai tabar gidah har abada, kiran sallar ma ba 'daya bane, Ta furta aranta.


Bandaki ta fad'a, tayo wanka had'e da alwala, sallah tayi da azkhar. Kafin ta dakko littafin anatomy tashiga karantawa, haka wani baccin gajiyar ya sake awun gaba da ita akan sallayar sallan. Saifullah kuwa da kyar ya tashi yana murza idanu, bandaki ya shiga yana had'a hanya don bacci ne fal idanun sa, ya sakarwa kansa shower. Sai da ya fitar da baccin daga idanun sa, sannan ya 'dauro alwala ya fito ya zira jallabiya ya fita masallaci, ana idarwa kuwa ya shiga bakinsa dauke da adduar shiga gidah,Kamar ya shiga 'dakin da Islam take sai kuma ya fasa yana haurawa sama abunsa, wayar sa ya janyo yana duba time table d'insa, 'jogging time' shine abunda yakamata yayi a lokacin. Kayan exercise dinsa ya 'dakko yana feshesu da turare, sannan ya zura su ya fice motsa jikin daya saba. Haka yai ta jogging har takwas saura kafin ya koma a matukar gajiye, ya bude gidan don ba'a kawo musu mai gadi ba tukun.


Lokacin kuma Islam ta gama turara kayanta akan kabbasa, dinkin riga da skirt, cikin dakakkiyar atamfa Holland, pusher pink and black color, mai zanen agogo. Ta gyara 'dakin duk da ba wani datti yai ba, haka ta karkad'e ko'ina tana yaba tsarin gidan. Ba kadan ba yayi mata kyau, sosai kayan da aka zuba sun 'kara 'kayatar dashi. Simple 'dauri tayi ta fito hannunta rike da burners guda biyu da ledar magic coal, ta jona burner 'd'aya a corridor ta zuba turaren halut, a parlorn 'kasa kuma ta jona 'd'aya ta zuba 'sandal bange'. Kitchen ta nufa da ledar magic coal a hannunta tana yaba tsaruwar kalar kitchen cabinets din, domin orange and black ne, sai kitchen utensils kuma duk silver color aka zuba mata, santin komai take yi tana shi wa iyayenta albarka. Nan da nan ta kunna gas ta dora coal igniter ta kunna coal biyar aciki, suna kamawa ta zuba a kasko, tuni ta barbad'e shi da turaren wutar Hawi. Jama'a gidah dai ya tashi da 'kamshi kala kala, ba a magana kawai, Ga na jikin ta dake tashin turaren kaya dana khumrah's.


Heater ta jona, ta 'dora ruwan zafi na tea. Don taga komai akwai shi wadatacce a kitchen din, domin store dinma shak'e yake da kayan gara, tea yana tafasa ta juye a royal flask dinta ta kai kan dinning ta'ajiye. Ajiyewar ta yayi dai-dai da shigar Saifullah parlorn, bakin sa 'dauke da sallama. Amsa masa Islam tayi duk a rud'e take. Tunowa da jawabin Inna Bilkisu datai hakan yasanya ta hanzarin tsugunnawa, cikin siririyar muryar ta tace,


"Ina kwana?!"


Tabe baki Saifullah yayi, bayan yagama kalleta sama da 'kasa, ga 'kamshi na dukan hancin sa na jikin ta da turarukhan wutan, cikin turo baki gaba yace,


"Yana kwano."


"Me za'a dafa maka?" Cewar Islam, kanta a 'kasa..


Ware idanuwa Saifullah yayi, yana mata kallon renin hankali kafin yace,


"Ni zaki dafawa abinci?! Lalle ma yarinyar nan."


Yana gama fad'a ya haura sama abunsa, tab'e baki Islam tayi, ta koma kitchen, cikin minti biyar ta kammala dafa indomie d'aya had'e da soyayyen kwai guda biyu. Daki ta koma abin ta, tana ci, sannan ta koma kitchen ta wanke duk abunda ta 'bata. Ta zauna a  palor tana tunanin cakwakiyar zaman da xasuyi da Saifullah. Tana jiyo 'burin 'burin 'dinsa a kitchen din sama. Ashe coffee ya had'a a coffee machine. Sai tara dai-dai aka kawo musu abinci daga gidan su Saifullah, Fatma da Humaira ne suka kawo, sai tsokanar ta sukeyi itadai murmushi kawai take. Cikin haka kuwa Saifullah ya sakko, sanye cikin dakakkiyar shadda galila golden datasha aikin hannu milk color, hular sa a hannu milk color yana gyara karin ta, Kallo 'daya yai musu dukkan su ya maida kansa kan hular sa, Fatima yayar sa ta mike tsaye tana nufar inda yake,



"Autan mu.."


"Ya fati.."


"Na'am Auta, yauwa ga abinci can aunty tace akawo muku, naga amaryar mu ma har da wahala, tayi tea gashi can a dining."


"Tohm angode"


Cewar Saifullah, Humaira dake gefe tace,


"Ya Saif ina kwana?"


"Humaira.." abunda yace kenan kawai ya sa kai zai fice, Fatima ta riko rigar sa,


"Ina zaka ango da sanyin safiyar nan? Indan mune dawo ka zauna, yanzu zamu tafi. Dama sallama nazo muku yau zamu koma mu."


Ware idanuwa Saifullah yayi, cikin sauri yace,


"Komawa kuma?! So soon haka? Amma banda Mami ko?"


"Duk 'yan lagos yau kowa zai tafi bare ni da ke port-harcourt,k.."


Ai be jira ta gama ba ya fice cikin sauri, Islam dai duk tana jinsu bata tanka ba, nata dai murmushi ne kawai, Fatima da Humaira suka shiga hirar su, lokaci zuwa lokaci islam ke samu su baki, sam kunya take ji, haka kawai taji har Humairan take kunya, uwa uba kuma Fatima yayar Saifullah.


A 'dari Saifullah ya figi motar sa, sai gidan su, yana zuwa ya tarar kuwa yan uwa nata shirin tafiya, duk sai yake jin ba dadi, haka dai ya amsa gaisuwar kowa awajen a kunyace musanman yadda suke tsokanar sa, 'dakin Haj Zuwairah ya nufa, lokacin ta fito kenan daga kitchen hannunta rike da kofi da kunun tsamiya aciki. Fad'ada murmushin ta tayi, tana karasawa cikin dakin.


"First love.." cewar Saifullah,cikin shagwababbiyar murya.


"Auta na.. kadde kace su Fatima ba su kai muku abincin ba, yau naji shirme a wajen yaran nan."


"No sun kai.. Ni first love zuwa nai wajen ki, I love and miss you, dakyar nai bacci jia" ya karasa fada yana dora kansa a cinyar ta.


"Shine ka baro yarinyar mutane acan? Ni auta yaushe zaka san ka girma ne? Tashi ka tafi"


Make kafad'a ya shiga yi, yana jijjiga kansa alamun a'a. Cikin cuno baki yace,


"Ni fa first love kinsan inde ba siblings dina ba da ku, da sauran family i barely eat with strangers."


Salati Haj Zuwairah ta rafka tana 'daga kansa daga cinyar ta,


"Wacace stranger auta? Islam matar taka ce ta koma bare kuma? To tashi tun muna shaida juna ni da kai ka tafi gidan ka, ko na mugun sab'a maka. Akan yarinyar nan Allah auta zamu 'bata dakai, ka kasa sakin jikin ka da ita, kar dai kacemin kana mata wannan halin naka itama."


Cikin cuno baki gaba yace,


"First love, Ya Fati ce fa tace yau zaku tafi.."


"Sai akai yaya da tafiyar mu? kai fa nace ka kwantar da hankalin ka, Baban ku yace zamu dawo muma nan 'din cikin shekaran nan, to menene abun damuwa kuma uhm?"


Shiru Saifullah yayi, gaba d'aya tamkar zaiyi kuka haka fuskar sa ta koma, ganin hakan yasanya Haj Zuwairah, tausar sa, don tasan halin autan nata baya cin abinci sai ta tasa shi agaba, kamar yaro, bayason abinci, yawanci sai abu mai ruwa-ruwa, kuma bana ko'ina yake ci ba, sai na gida, Sam bayason na roadside ko na wasu restaurants din. Abincin ta zubo masa, da kunu sai da yaci sosai, sannan ta tasa 'keyar sa suka tafi, dama tayi niyar zuwa ta gano gidan daganan ta musu sallama, fal suka cika motoci uku, sukaje gidan . Lokacin itama Islam yan uwan Ammi sunzo fal na bornu suma duk yau zasu juya hakama na 'yan 'kauyen y'ar gaya. Tuni gidan ya kacame, Ita dai Islam na dakinta tana canza wani kayan, domin tayo wanka na biyu. Ta shirya cikin wani lace ja, doguwar rigar A shape, hannun kuma peplums akai masa. Ba kadan ba tayi kyau. Light makeup Lee keyi mata,


"Lam Lam ba ki labarta mun first night ba.."


Dariarta Islam ta danne, ko da hakan ta kasance ai ba zata tab'a fada ba domin Yayya Safa tace karta soma bawa kowa labarin yadda sukai auratayya da mijin ta, dama duk wani sirri dake tsakanin su, don babu kyau. Murmushi tayi kafin tace,


"Bari kawai, ba'a magana it's beyond your imagination, ki shirya hajjaju.."


Lee ta bude baki, ganin da gaske labarin da take ji akan hakan ashe gaskia ne, Yatsina fuska Lee tayi kafin tace.


"Tab zan iya yadda kuwa?"


"Da me fa" cewar Islam, cikin zakuwar abunda Lee zata fada.


"Wallahi ina gaya miki, Fahad ya matsa shi aure kwanannan, Naga abun nasa na neman zautar dashi nace yafadawa Baba sunfi kusa, shine jiya yake cemin cikin satin nan za'a kawo komai, kuma biki bayaso ya wuce nan da wata 'daya."


Cikin murna Islam tace,


"And so?! Kakki wani damu wallahi, Allah yasa hakanne yafi alkhairi, mu gwangwaje mu rak'ashe."


"Waye zai barki ki rak'ashe ki gwangwaje? Lokacin ma akwai little unborn, beside Ya Saif baze yarda ba"


Tab'e baki Islam tayi, cikin cuno baki tace,


"To y'ar ciki baki, sai ki hana ai.."


"That aside.. Ni kuwa kinji labarin cousin d'inki Saifullahi, zai fara lecturing a school namu ko, as visiting lecturer amma, shi zai 'dauki course 'din: Introduction to Humanities and community medicine"


Tabe baki Islam tayi, kafin tace,


"Lalle, Za'a sha ruwan carryovers"


Lee ta kyalkyale da daria kafin tace,


"Kiji tsoron Allah Lam-Lam, dan jinin ku bai hadu ba sai ki laqaba masa sharri, in sha Allah zamuyi passing kowanne course with flying colors.."


Islam ta mike tana kallon kanta a wani mudubi, dogo fari kal, kana kallon kanka full dnka ta ciki. Ba kadan ba ta yaba kwalliyar da Lee ta mata, ta faffesa perfumes kafin tace,


"Can ta matse muku ke da shi, yanzu dai tayani kwaso ledojin nan, Ammi tace na babbawa duk wanda sukazo zasu tafi.."


Kad'a kai Lee tayi, tana duban ledojin, atamfa ce guda d'aya, da kwalba cike da turaren wuta, sai kasko da hair dryer set a kowacce leda, kin kima sukai, suka kai parlor, Islam duk ta takure da irin shegen kallon da Saifullah ke jefanta dashi, in sun had'a ido kuma ya sakar mata harara, ita abunma daria yake bata.


'Y'ar walima dai akai na yan uwa da suka zazzo, yan bornu ne suka fara yi mata sallama suka tafi, ta bisu da ledojin su, daga nan yan Y'ar gaya suka 'daga suma, bayan sun tafi da awa d'aya su Haj Zuwairah suka fara mikewa don tafiya, Saifullah yayi rau-rau da idanuwa kamar zai yi kuka, sosai 'yan autancin suka motsa masa, sai da Haj Zuwairah ta tasa 'keyar sa 'daki, daga shi har Islam din ta sasu agaba, ta dubi Saifullah tana murmushi kafin tace,


"Haba auta, ai sai matar taka ta rena ka, 'katoto dakai zakai kuka"


Ai kuwa daria ta tahowa Islam ta gimtse ta dakyar, Nan de Haj Zuwairah ta shiga yi musu nasiha da jan hankali na yadda zasu gina rayuwar auren su, ta 'kark'are da,


"Wannan sabuwar rayuwa ce kuka shige ta, wadda ba irin ta baya bace, sai kunyi hak'uri da juriya akan komai, ga ku duk 'yan auta, ni dai auta ga amanar Islam nan, kaga itace karama dan Allah ko menene zatai maka kayi hak'uri, komai 'dan hak'uri ne, ke kuma Islam ki bishi sau da 'kafa, karki bi zugar 'kawaye ko shawarar su wurin munanta masa, yi nayi bari na bari, nasan Auta na jan ido ne sai da magani, sai kina hak'uri dashi, amma idan ki kai hak'uri zaki ga ribar sa, domin shi mutum ne mai saukin kai, Allah ya muku albarka..Duk abunda kike bukata ki gayamin kinji auta ta?"


Murmushi Islam tayi tana rufe fuska jin itama ana kiranta da auta, Mami tai daria kawai kafin tace,


"Sai maganar abinci, sai kin matsa masa bayason abinci, tun yana 'karami muke fama, ungo nan, lists ne na duk abunda yake ci." Ta karashe maganar tana mika mata wata takarda, kafin ta sake cewa,


"Kema ki dinga cin abinci kinji auta ta, duk abunda kike so kici ki girka kinji, idan an kawo miki y'ar aiki ma sai ta dinga tayaki da wasu abubuwan, Allah ya muku albarka.."


"Ameen.." suka amsa gaba ki d'aya.


Dakyar dai Saifullah ya bari su Haj Zuwairah suka tafi, har 'dan zazzabi yai, domin duk dunia yafison mahaifiyar sa, ya shaku da ita fiye da komai, bai tab'a soyayya ba, bai san ya ake yi ba, domin duk 'yammatan dake nuna suna sonsa ba ya taba basu fuska, ya 'dauki mata marassa kamin kai, aganinsa duk haka mata suke, domin yadda suke farautar zuciar sa abun har mamaki yake bashi, shiysa ya jingine kalmar So gaba d'ayanta ballantana soyayyar kanta. Shi kadai yake rayuwar sa, ko kadan bai taba sawa a zuciar sa, zai yi soyayya ba bare aure nan kusa ba ma, sai gashi rana tsaka anyi mai auren dole. Auren dolen ma da yarinyar dake rokar maza su aure ta, take kuma zubar da mutuncin ta a titi....


Haka dai rayuwar gidan *SAIFUL_ISLAM*, ta cigaba. Kowannen su harkar gaban sa yake, gwara ma Islam tana k'ok'arin saukar da hakkinta na gaisuwa dana abinci, amma sam bayako kallon dinning table, kullum sai dai ya hada porridge yasha, gashi scent din abincin ta na shiga har hanjinsa don tsabar dadi, amma saboda fadin rai da miskilanci irin na Saifullah ko kallo mai abincin da abincin basu isheshi ba..


Haka dai ta koma makaranta, haduwar su kullum sai magrib, ta gaisheshi ya amsa a dak'ile, har bikin Lee ya 'karaso, da ita aka karbi lefe da komai, aka fara shirin biki, su bridal tea party da duk sauran events da akai Islam taje, domin Ya Bala ya aiko mata da kyautar mota, tuni harta koya cikin sati biyu ta kware. Ita ta tuk'a kanta ko'ina, ita har addua take yi Allah ya kawo k'arshen wannan 'kaddararren auren nata da Saifullah, tunda ta gano baya sonta ba kuma zai tab'a son taba a cewar ta, domin shekaran jia abunda yace mata kenan, 'baya son ta ba kuma zai tab'a son ta ba'. Ta ajiye kalmomin sa a kundin zuciyar ta, sosai tai musu kyakkyawan mazauni.


Ranar lahadi aka kai Lee gidan ta dake nan garin Abujan, domin basu da nisa sosai ma da gidan Islam din, shiysa ma Islam ta 'kara jin dadi, ganin ta samu y'ar uwa kusa da gidah. Monday da sassafe Islam ta gama gyaran ko'ina na gidan lungu da sak'o, ta sassaka turarukan wuta, riga da skirt tasa na English wears ta 'dakko after dress shara-shara a hannu zata yafa, da babban mayafi wadatacce saboda yanayin zafin garin. A lokacin Saifullah ya sakko shima, sanye cikin Kaki na NYSC zai je monthly clearance, yana tafe yana taje sumar gashin sa, kallon kallo sukai ya dauke kansa, Islam ta daure ta dan rissina tana,


"Ina kwana?!"


"Lapia." Ya fada a takaice yana wani shan kunu.


Ita dai Islam kitchen tayi abinta, ta had'a kayan breakfast dinta a wata y'ar jaka, ta zuge ruf abunta, a kitchen ta zura rigar ta yafa mayafin,bakin nan ya sha jambaki ja,Ta koma parlor inda yake, daga tsayen tace masa,


"Toh ni na tafi school, and I might be late today, Saboda yanayin lectures din namu na yau."


Tana gama fada ta juya zata tafi, Don kullum idan tayi masa sallama zata tafi baya tankawa, Ita dai tana k'ok'arin binsa ne kawai,


"Ke.." ya fada yana wani yatsina fuska,


Juyawa tayi tana kallon sa.Batare daya kalleta ba yace,


"Koma ki saka hijab, ki rage wannan lip stick din yan 'kauyen da kika sa, you luk so suffocating.."


Tabe baki tayi,cikin kasa da murya ta furta,


"Latsi.."


"Kika ce mene?"


"Da kai na nake.."


Ta bashi amsa da sauri tana komawa daki,gudun karta makara, kayan gaba d'aya ta canza, zuwa wani material blue and pink, ta zura jilbab tafito, Sam ta manta da maganar janbaki, zata wuce yai taku d'aya biyu ya riko ta,tuni jikin ta ya fara rawa, siririn tsaki ya saki yana harararta,cikin isa yace,


"Wato saboda ga sa'an ki ko? Na miki magana ki goge jambaki shine kikai ignoring ko?"


Shiru Islam tayi, tana raba idanuwan wannan bakon al'amari, k'ok'arin kwatar kanta take ya hana, ta hanyar riko hannayenta ya jasu can k'arshen corridor ya jingina ta,hannun sa sakale da kugunta, kafin tayi aune sai ji tayi ya had'a bakin sa da nata ya shiga yi mata wata irin sweet and passionate sumba mai ratsa jiki, mutumin ku daga shanye jambaki ba sai ya rike lips din yarinya ba, har wani lumshe idanuwa yakeyi, Ai kuwa da karfi Islam ta ture shi, yaita maza ya hade rai, ya yagi tissue yana goge kan bakin sa, zatai magana ya rigata cikeda borin kunya yace,


"Tun ba yau ba, nake kama ki kina satar kallon lips dina, sai gashi daga gwadawa kuwa kin rike mun lips sai kace kin samu alawa, idan nace ban yafe ..."


Katse shi tayi, tana masa kallon yaushe nai haka? ! Cikin bacin rai tace,


"Ni ce na rike maka lips?"


Ko kallon ta beyi ba ya fice daga wajen corridor yana nanata kalmar,


"So suffocating"




(THE START OF SOMETHING NEW; SAIFUL_ISLAM#LOVE STORY BEGINS🚴🏼‍♀)

Comment