EIGHT

Gyaren murya Ya Bala yayi, yana mai nuni da su Haj Karimatu. Da yatsan sa na biyu dake hannun daman sa, cikin muryar fushi dake tattare da damuwa yace,


"Hakika kun bani mamaki, yadda na 'dauke ku, ashe kun xarta hakan, wannan wacce irin musibace? Shin kuna tunanin duk abunda kuke yi Allah baxai kama ku da laifi ba ne ko kuwa? Wane irin haukan kishi ku ke yi ne ? Da ya xarta tunani? Ni da ku, shekarun baya na ja muku kunne, had'e da tausasa zuciyar Khaleel, ya hakura ya dawo da ku 'dakunan ku, dukkoda yadda kuka 'kulla sharri akan yarinyar da batada masaniya akan hakan, daga ni sai ku, sai su Khaleel, aka rufe maganar ba'a bari tafi to ba. Sai daga baya na gane ba kishi bane, tsantsar mugun tace.. Tirr! Da hali irin naku wallahi."


Shiru yayi, gaba d'aya ya rasa mai zai sake cewa, ganin haka, yasanya Inna Bilkisu dake gefe cewa,


"Duk dan akan kishi kuke hakan ko? Shinma menene kishi? Tunda naga kamar bakusan ma'anar sa ba, da yadda ake yinsa. Shi kishi wani yanayi ne na soย  da kauna da burin kare abun da ake son daga kamuwa da cuta. Ana kishin kasa kuma ana kishin sana'a da abokan zama.. Duk inda akwai kishi mutane na ganin cewa akwai so, har ma wasu kan ce "kishi so ne". Duk dan Adam bai cika mutum ba sai ya kasance yana da kishi. Ko dai ya kasance yana kishin kansa, kishin iyalinsa da dai makamantansu.,


"Hausawa na cewa "kishi kumallon mata." Amma a zahiri ba mata kadai ke da kishi ba, har mazan ma suna da shi. Mutane da dama na ganin cewa maza sun fi mata kishi, kawai dai matan sun fi nunawa ne. Wannan abu ne da za a iya muhawara a kai. In har hakan ne, akwai abubuwa da dama da ke silar hakan. A addinin musulunci da kuma al'adar mutanen Afirka da yankuna da dama, maza ne suke auren mace fiye da daya. Su kuma mata miji daya kadai suke aure. Wannan shi ke sa mata su yi ta jin tsoron kawo musu abokiyar zama wadda ake kira kishiya. Kalmar kishiya kanta bai dace ana fadar ta ba, kasancewa zama aka zo yi tare da miji daya ba wai wasa ba. Ita kalmar ke kara wa mata da dama tsoro cikin zukatansu da zarar an furta ta. Sannan kuma maza da dama sukan fara wulakanta uwargida idan amarya ta zo. Ita da 'ya 'yanta su zama ko oho. Su ma amaren su yi ta jin dadi cewa ana wulakanta uwargida, ba sa tunanin cewa su ma idan aka yi sabuwa, haka za a yi masu. Hakan na matukar tsoratar da mafi yawancin mata, har ma ka ji suna cewa "ba kishiyar ake tsoro ba sai sharrin ta,


"Yarda da amincewa na da matukar muhimmanci a dukkan tarayya, musamman ma ta aure. Da zarar babu yarda a cikin zaman aure, zargi zai shigo ciki kuma ba za a taba samun zaman lafiya ba. Ya kamata mu rika gina aure bisa yarda da amincewar juna, don hakika su ne gishirin zaman aure. Rashin yarda ne ke kawo rashin jituwa har ta kai ga rikici, a wasu lokutan ma har da kisa,


"Kusani cewa, Kishi wata dabi'a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A'isha tana cewa : "Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, duk da cewa ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi s.a.w yana ambatonta" Bukhari 1388, Kishi mai tsafta, shi ne : kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, Akwai Jahilci : ta yadda mata da yawa suka jahilci, hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni a kara aure, kamar;rage yawan zawarawa da 'yammata, da kuma yawaita zurriyar Annabi S.A.W.,domin da za su kalli wannan da kishinsu ya ragu. Mummunan zato, yawanci uwar gida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwar gida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima.Amma idan da ace kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba'a samu matsala ba.,


"Rashin adalci daga wajen namiji, yawanci maza su kan karkata zuwa amarya, wannan sai ya haddasa fitina, saboda uwar gida za ta ce ba ta yarda ba. Amma idan kuka duba anan zaku ga cewa, shi maigidan ku sam ba haka yake ba, hakika yana k'ok'arin adalci a tsakanin ku, Saidai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne : babu yadda za'a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya, Annabi s.a.w. ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A'isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, sukan 'kirkidi ranakun da yake dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, saidai abin da sharia ta hana shi ne, rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum. Wanda ku Kan ku kunsan maigidan ku na kamanta adalci a tsakanin ku, sannan akwai Munafukai, masu cece-kuce, idan da ace kishiyoyi za su daina daukar guzuri-zoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli. Amma ku duk kunyi fatali da wannan idanuwan ku sun rufe, kun 'dauki zugar shed'an kun d'orawa zuciyar ku, kuna aikata shirka, domin wallahi had'a Allah da wanin sa shirka ne, zuwa wajen duba, da yan tsibbu suna gaya muku 'karya da gaskia, kuna zama akai, kun cusa mummunar 'dabi'a aranku, kun 'dau wani qudri na ganin kunyi mai yiwuwa kun fidda wasun ku daga gidan, to ku gayamin da ta tada rigima kar a auro ku, Allah ba za'a yin ba, dandai bakusan k'ok'arin da baiwar Allahn nan tai muku bane da har ta bari aka auro ku,


"Dan ni 'dinnan da kuke gani, ca nai sam a'a, kada ya 'kara aure, Aysa ta isheshi zaman dunia da 'yan 'yayan su, yace rufa muku asiri zai yi, barin ke Karimatu" inna bilkisu tafadi hakan tana mai nuna da Karimatu, Kafin tace,


"Bazawara ce ke, mijin ki ya miki duka ya sakeki, Allah ya temaka babu rabon 'yaya a tsakin ku, kawun ki ya samu Khaleel da zancen ki, ya rufa miki asiri ya aure ki, Ke kuwa Amina(Yafendo), ta tallan nonon shanu, Allah yai auren ku zai had'u, ta sanadiyyar kad'e 'kanin ki da drivern sa yayi, yaji tausayi bayan an kammala komai, yace xai aure ki ya temakawa Baffan ki da hidimar ku, ganin kunyi yawa awajen sa, amma duk hakan bai isheku yin hankali, kun zauna da abokan zaman ku lapia ba, Sai tada fitina da neman yadda zaku fiddasu daga gidan, Ku na jifansu da sharri da sihiri kala-kala, wanda duk daga 'k'arshe idan da zakuyi nazari kan ku yake dawowa, kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa. Ko kunsan,


"Hukuncin sihiri, da bokanci da abunda suka 'kunsa? To ku sani baya halatta ga ko marar lapia ya je wajan bokaye da suke ikirarin sanin abubuwan da ke boye, wai don ya gano masa rashin lafiyansa, kamar yadda baya halatta ya gasganta su cikin abinda su ka bayar da labarin sa ba, domin su suna maganine ko kuma su kirawo aljanu domin su taimaka mu su akan abinda su ke so, to wadannan hukuncinsu shi ne 'kafirci' idan sun yi ikirarin โ€“ ilimin gaibi, hakika Muslim ya ruwaito cikin ingantaccan littafinsa, lallai Annabi โ€“ tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce;


((ู…ู† ุฃุชู‰ ุนุฑุงูุง ูุณุฃู„ู‡ ุนู† ุดูŠุก ู„ู… ุชู‚ุจู„ ู„ู‡ ุตู„ุงุฉ ุฃุฑุจุนูŠู† ูŠูˆู…ุง))


Ma'ana: "Duk Wanda ya je wajan dan'duba sai ya tambaye shi wani abu to ba za'a karbi sallar sa ba ta kwana arba'in". Kuma daga Abuhuraira Allah ya kara masa yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:


((ู…ู† ุฃุชู‰ ูƒุงู‡ู†ุง ูุตุฏู‚ู‡ ุจู…ุง ูŠู‚ูˆู„ ูู‚ุฏ ูƒูุฑ ุจู…ุง ุฃู†ุฒู„ ุนู„ู‰ ู…ุญู…ุฏ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…)).


ุฑูˆุงู‡ ุฃุจูˆ ุฏุงูˆุฏ ูˆุฎุฑู‡ ุฃู‡ู„ ุงู„ุณู†ู† ูˆุตุญุญู‡ ุงู„ุญุงูƒู… ุนู† ุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ุจู„ูุธ ((ู…ู† ุฃุชู‰ ุนุฑุงูุง ุฃูˆ ูƒุงู‡ู†ุง ูุตุฏู‚ู‡ ุจู…ุง ูŠู‚ูˆู„ ูู‚ุฏ ูƒูุฑ ุจู…ุง ุฃู†ุฒู„ ุนู„ู‰ ู…ุญู…ุฏ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…)).


"Ma'ana: "Duk wanda ya je wajan boka sai kuma ya gasganta abinda ya ke cewa, to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi". Abu dawud ya ruwaito shi kuma ma'abota littattafan sunnah hudu sun fitar da shi, kuma Hakim ya ingantashi daga Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi da lafazin:


"Duk wanda ya je wuri dan'duba ko boka sai ya gaskanta abinda yake cewa to hakika โ€“ ya karficewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi".


Kuma daga Imran dan Husaini Allah ya karama sa yarda ya ce: Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:


((ู„ูŠุณ ู…ู†ุง ู…ู† ุชุทูŠุฑ ุฃูˆ ุชุทูŠุฑ ู„ู‡ ุฃูˆ ุชูƒู‡ู† ุฃูˆ ุชูƒู‡ู† ู„ู‡ ุฃูˆ ุณุญุฑ ุฃูˆ ุณุญุฑ ู„ู‡ุŒ ูˆู…ู† ุฃุชู‰ ูƒุงู‡ู†ุง ูุตุฏู‚ู‡ ุจู…ุง ูŠู‚ูˆู„ ูู‚ุฏ ูƒูุฑ ุจู…ุง ุฃู†ุฒู„ ุนู„ู‰ ู…ุญู…ุฏ


๏ทบโ€ฌ)). ุฑูˆุงู‡ ุงู„ุจุฒุงุฑ ุจุฅุณู†ุงุฏ ุฌูŠุฏ


"Ma'ana: "Baya cikimmu duk wanda ya ke yin camfi ko a ke yi masa camfi ko ya yi bokanci ko ake yi ma sa bokanci, ko ya yi sihiri, ko ya sa ayi mishi sihirin, duk kuma wanda ya je wajan boka sai ya gaskantashi a aduk abinda yake cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi". Bazzar ne ya ruwaito shi da Isnadi mai kyau.


" saboda haka ku sani, A cikin wadan nan hadisai masu girma akwai hani game da zuwa wajan 'yan'duba da bokaye da masu sihiri (asiri) da makamantansu, da kuma hukuncin tambayarsu da kuma hukuncin gasganta su da bayanin narkon azaba akan haka. Domin hakika manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hani akan zuwa wajan su da kuma tambayar su da gaskanta su, domin abinda ke cikin haka na muni maigirma da hatsarin da ya ke babba da mumunar makoma kuma domin lallai su makaryatane fajirai, kamar yadda ya ke cikin wad'annan hadisai dana baku, wadannan Hadisai dalili ne cewa boka kafirine da mai sihiri domin su biyun basu cimma manufar su sai ta hanyan yi wa aljanu hidma da bauta musu koma bayan Allah kuma wannan kafurcewa Allah ne da kuma yi masa tarayya โ€“ tsarkakken sarki,


"Kuma mai gasganta su cikin abinda su ke cewa na sanin gaibu ya kasance kaman su ne, kuma dukkan wanda ya karbi wadannan al'amura na abinda su ke bayarwa to hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya barranta da shi, kuma baya halatta ga musulmi ya yarda da abinda su ke rayawa cewa magani ne. Domin lallai wannan yana daga cikin bokanci da rudar da mutane, kuma wanda ya yarda da hakan to hakika ya taimaka musu akan barnarsu da kafircin su,


Hakanan kuma baya halatta ga wani mutum musulmi ya jewajansu โ€“ domin ya tambayesu gameda wanda. Zai aurar da dansa ko wani makusancinsa ko kuma abunda ke iya kasancewa tsakanin ma auratan biyu da danginsu na soyayya da cika alkawari ko kuma kiyayya da rabuwa da makamantan haka;domin wannan yana daga cikin gaibi wanda babu wanda yasansu sai Allah tsarkakke mada'au kaki.


"Kuma sihiri yana daga cikin abubuwa haramtattu na kafirci kamar yanda Allah mai girma dad'au kaka yace cikin sha'anin mala'I kunnan biyu cikin suratul Bakarah: ๏ดฟูˆูŽูฑุชู‘ูŽุจูŽุนููˆุงู’ ู…ูŽุง ุชูŽุชู„ููˆุงู’ ูฑู„ุดู‘ูŽูŠูŽุทููŠู†ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูู„ูƒู ุณูู„ูŽูŠู…ูŽู†ูŽ ูˆูŽู…ูŽุง ูƒูŽููŽุฑูŽ ุณูู„ูŽูŠู…ูŽู†ู ูˆูŽู„ูŽูƒูู†ู‘ูŽ ูฑู„ุดู‘ูŽูŠูŽุทููŠู†ูŽ ูƒูŽููŽุฑููˆุงู’ ูŠูุนูŽู„ู‘ูู…ููˆู†ูŽ ูฑู„ู†ู‘ูŽุงุณูŽ ูฑู„ุณู‘ูุญุฑูŽ ูˆูŽู…ูŽุง ุฃูู†ุฒูู„ูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ูฑู„ู…ูŽู„ูŽูƒูŽูŠู†ู ุจูุจูŽุงุจูู„ูŽ ู‡ูŽุฑููˆุชูŽ ูˆูŽู…ูŽุฑููˆุชูŽ ูˆูŽู…ูŽุง ูŠูุนูŽู„ู‘ูู…ูŽุงู†ู ู…ูู† ุฃูŽุญูŽุฏู ุญูŽุชู‘ูŽู‰ ูŠูŽู‚ููˆู„ูŽุง ุฅูู†ู‘ูŽู…ูŽุง ู†ูŽุญู†ู ููุชู†ูŽุฉ ููŽู„ูŽุง ุชูŽูƒููุฑ ููŽูŠูŽุชูŽุนูŽู„ู‘ูŽู…ููˆู†ูŽ ู…ูู†ู‡ูู…ูŽุง ู…ูŽุง ูŠูููŽุฑู‘ูู‚ููˆู†ูŽ ุจูู‡ู ุจูŽูŠู†ูŽ ูฑู„ู…ูŽุฑุกู ูˆูŽุฒูŽูˆุฌูู‡ู ูˆูŽู…ูŽุง ู‡ูู… ุจูุถูŽุงุฑู‘ููŠู†ูŽ ุจูู‡ู ู…ูู† ุฃูŽุญูŽุฏู ุฅูู„ู‘ูŽุง ุจูุฅูุฐู†ู ูฑู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูˆูŽูŠูŽุชูŽุนูŽู„ู‘ูŽู…ููˆู†ูŽ ู…ูŽุง ูŠูŽุถูุฑู‘ูู‡ูู… ูˆูŽู„ูŽุง ูŠูŽู†ููŽุนูู‡ูู… ูˆูŽู„ูŽู‚ูŽุฏ ุนูŽู„ูู…ููˆุงู’ ู„ูŽู…ูŽู†ู ูฑุดุชูŽุฑูŽู‰ู‡ู ู…ูŽุง ู„ูŽู‡ู ูููŠ ูฑู„ุฃุฎูุฑูŽุฉู ู…ูู† ุฎูŽู„ูŽู‚ ูˆูŽู„ูŽุจูุฆุณูŽ ู…ูŽุง ุดูŽุฑูŽูˆุงู’ ุจูู‡ู ุฃูŽู†ููุณูŽู‡ูู… ู„ูŽูˆ ูƒูŽุงู†ููˆุงู’ ูŠูŽุนู„ูŽู…ููˆู†ูŽูกู ูข๏ดพ


Ma'ana: "Kuma basu sanar da kowa ba balle suce: mu fitina kawai ne, saboda haka ka kafirta," balle har suke rarrabwa tsakanin mutum da matarsa dashi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) basu zama masu cutar da kowa da shiba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma baya amfaninsu, kuma lallai ne, sun sani tabbas wanda ya saye shi, baya da wani rabo lahira. Kuma tir da abinda Suka sauar da raukansu da shi, da sun kasance suna sani)). Suratul Bakara, aya ta: 102,


"Sai kuma waccan ayar maigirma da ta yi nuni akan cewa lallai masu sihiri suna raba tsakanin mutum da matarsa. Kamar yadda ta yi nuni kuma cewa lallai sihiri baya tasiri don karan kansa ta fuskar amfanarwa ko cutaruwa, sai dai yana tasiri ne da iznin Allah wan ya riga ya kaddara kuma ya kasantar, domin lallai Allah tsarkakke madaukaki shi ne ya halcci alkhairi da sharri, hakika cutar ta yi girma kuma zaluncin ya yi tsanani ga wadannan masu kirkirar, wadanda su ka gaji wadan nan ilimomi daga mushrikai su ka zo suka rikita masu raunin kwakwale da su, lallai mu daga Allah mu ke kuma lalle mu gare shi zamu koma, Allah ya isar mana kuma madalla da wakili wanda yake shi ne Allah.,


"Ma'aikin Allah ๏ทบโ€ฌ Ya sake cewa kuma


((ู…ู† ุฃุชู‰ ุนุฑุงูุง ุฃูˆ ูƒุงู‡ู†ุง ูุตุฏู‚ู‡ ุจู…ุง ูŠู‚ูˆู„ ูู‚ุฏ ูƒูุฑ ุจู…ุง ุฃู†ุฒู„ ุนู„ู‰ ู…ุญู…ุฏ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…)).


"Ma'ana: "Duk wanda ya je wajan danduba ko boka sai ya gaskanta shi da abinda ya ke cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukar wa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi".


"Anan zan dakata, ku sani duk wannan ayoyi da hadisai na kawo su ne domin ku, saboda ku tabbatar abunda kukeyi ba mai kyau bane, babban shirka ne, ko da nan gaba hakan zai zamto silar shiryuwar ku, Ta haka har Allah yasa ku janyo ra'ayin masu hali irin naku, zuwa turbar gaskia. Abunda na fada dai-dai Allah yabamu ladan, kura-kuren dake ciki rabbi yayafe min."


"Ameen..." suka had'a baki d'aya wajen cewar hakan.


Ya Bala da Dr Khaleel ne suka ce da Inna Bilkisu,


"Toh! Inna Allah ya saka da alkhairi, mun 'karu muma gaskia.."


Sannan Ya Bala ya 'kark'are da,


"Toh Karimatu da Aminatu yanzu zamu ji daga bakin shi mai gidan naku kan wane hukunci ya yanke abisa hakan. Domin a zahirin gaskia ni na cire hannuna a harkar ku, babu ruwana, baxan dinga tilastashi ya hakura ba, akan yadda kuke cutar dashi. Saboda haka Khaleel ka yanke hukuncin ka kawai, bansan Inna ba dai, amma ni duk hukuncin da ka yanke, Ina bayan ka, domin sun cancanci kome kayi musu wallahi."


Dr Khaleel ya 'daga kai yana kallon su, Dan murmushin takaici yayi, kafin yace,


"Toh inna ni da na yanke hukuncin sallarmar su kawai, domin baxan iya xama suna cutar da ni da ahali na ba, nan gaba bamusan mai zasu aikata ba."


Wata gigicacciyar 'kara suka saki, cikin zabura Karimatu ta fara sumbatu, Yafendo kuwa rarrafawa tayi ta 'riko 'kafar Inna Bilkisu,


"Inna kiyi hak'uri, mun tuba, ba zamu sake ba wallahi, ni de.. Ni.. dai dama Yaya ce ke sa ni aikata duk wani mummunan aiki, tace idan ba haka ba zata fiddani daga gidan.."


ashar Karimatu ta lailayo ta 'dura mata, kafin kace me? Tuni duk sun to nawa kansu asiri, baram-baram sukai da junan su, kowanne yana kwashe wa 'dan uwan sa albarka. To dama ance komai nisan dare gari zai waye, Allah zai bayyana mai gaskia, a ranar dai gaba d'aya duk wani b'oyayyen al'amari sai da suka bayyana shi, har da yanda aka qullawa Safa makirci. Duk kansu sai suka koma suna hararar junan. Dama haka ne rana dubu ta 'barawo ce, d'aya kuma dal ta mai kaya.


Inna Bilkisu tai hanzarin girgiza kai, kafin cikin dattako tace,


"Kar kai haka Khaleel, nasan kayi hak'uri, kana kanyi ma, karka zamto sauran maza masu saurin yanke hukunci Khaleel, kayi hak'uri ka dubi girman Allah, ka sauqaqa hukuncin da za kai musu, su ci darajar 'ya'yan dake tsakanin ka dasu. Kayi hak'uri Khaleel, mata sunyi yawa yawa agari, yan mata da zawarawa, hakika duk sanda akai saki, al'arshin ubangiji girgiza take, kaga kuwa ba 'karamin abu bane. Kayi hak'uri Khaleelu, Allah ya dubi hakurin da kai, ya cika maka burikan ka, dunia da lahira, Allah ya muku albarka, ya tsare ku ya 'kara kareku daga sharrin ma sharranta."


Sam Dr Khaleel bai so ba, amma ya xaiyi? Hakika zab'in iyaye shine zab'i nagari ba son rai ba. Cikin taushasshiyar murya yace,


"Ameen Inna. Sun ci darajar ki, da wallahi hukuncin da na 'dauka shine sawwake zaman mu dasu tare, Allah yasa zab'in da kikai shine mafificin alkhairi, na janye qudurina, amma zamana dasu a Abuja ya 'kare Inna. Ita Karimatu zan mayar da ita can Bauchi inda gidan gona ta yake, ita kuma Amina zata koma jigawa, saboda zan fara part time lecturing acan. Ina ga idan akai haka, komai zai yi sauki, tunda zama waje 'd'aya shine yakawo had'uwar kan su, dama cusa mummunan ra'ayi a zukatan su."


Jinjina kai Inna Bilkisu da Ya Bala sukai, alamun sun amince da hakan, Karimatu da Yafendo kuwa sun 'danji sauki a ransu. A washe-gari kuma aka 'dakko su Hafsat daga kano, hade da Hidaya dake Zaria. Sosai sun canxa tamkar basu ba, dukkan su, suka rankaya gidan Haj Aysa, takanas daga umarnin Inna Bilkisu wacce ke jagorancin tafiyar. Hak'uri sosai suka shiga bata, tamkar basu Karimatu ba, duk sunyi laushi, fadakarwar da Inna Bilkisu tayi musu, ta matukar canza su, sai dai duk da haka Karimatu da Yafendo sun 'dau mummunar gaba a tsakanin su, Dan ko d'aya na magana, d'aya bata saka baki. Haka suka dawo gidah, suka kara neman gafarar, Dr Khaleel. Ganin hakanne yasanya Inna Bilkisu baiwa Dr Khaleel shawarar ya 'dan saiwa su Hafsa da Hidaya matsakaicin gidah kowacce a garin da take aure, saboda zama waje 'd'aya da kishiya babu dadi. Hakan kuwa akayi, da sati ya zagayo kuma kowacce cikin matan biyu, wato Karimatu da Yafendo, ta koma sabon gidan ta, Karimatu a bauchi. Yafendo kuma a Dutse/Jigawa.


LAGOS IDIROKO.


Bikin Fatima, yayar Saifullah aka yi, aka kaita gidan ta dake port-harcourt. Da sati ya zagayo kuma Islam ta koma Abuja, Don fara lectures din first semester na MBBS.


*USA ๐Ÿ‡บ๐Ÿ‡ธ *


Harvard University(Cambridge)


Sosai convocation hall ya cika da students ,parents da kuma teachers. Kowa ka gani da graduation gown a jikin sa, can na hango Saifullah. Sanye cikin graduation gown, tayi matukar amsar jikin sa, ba kadan ba, kyakkyawa r fuskar sa ta kamala ta 'kara cika da annushuwa. Chancellor 'din makarantar ne ya kirashi, nan aka bashi award na, best student of the year. Da kuma first call student na department of Architecture. Awards dai kala-kala haka aka dinga kiran sa ana bashi, Muslim student society of Cambridge ma sai da suka bashi award na, Mufti of the year. Kai abun sai sam barka kawai, ba'a cewa komai.


Saifullah faruk muhammad, saurayi ne 'dan shekara ashirin da takwas a dunia, ya kammala senior secondary certificate d'insa anan Lagos, inda ya tsallaka nahiyar turai ya karanci fannin architecture a first degree d'insa (Bsc. Architecture), bai dawo ba ya 'dora da degree na biyu a matakin harkar kasuwanci, wato master of business administration (MBA) .


Fari ne, amma ba irin dau 'dinnan ba, kallo d'aya xakai masa kasan Allah yayi kyakkyawar halitta, dogo ne sosai, sannan ba shida jiki, sannan bai cika rama ba, zamu iya kiransa moderate. Yanada yalwataccen gashin kai dana gira, domin girarsa ta kusa had'ewa ma, tsabar cikar ta. Yana da kwantaccen saje a gefan fuskar sa, wanda turawa ke kira sideburns. Idanuwan sa dara-dara ne TubarkAllah. Hancinsa kuwa tamkar shiya zana shi dan tsawo, bakinsa dan 'karami ne jawur dasu kamar ya shafa jambaki. Kai bayyana yadda saifullah yake tamkar bata Lokaci ne, sai dai muce TubarkAllah kawai. Allah yayi halitta.


Yana karbar certificate d'insa yai apartment d'insa, ko takan friends d'insa dake kiran sa bai-biba, domin bayason hayaniya. Shiysa yace su Baba(Uncle Faruk) ba sai sunxo ba ya yafe, burjik ya tadda gifts boxes kala-kala da kati, duk na tayashi murna,


Girgiza kai yayi, shi sam mata suna bashi mamaki, yadda suke gaya masa suna sonshi, ko su rubuto masa wasik'a, yawancin gifts dinma duk sunan 'yammata ne akai. Ko takan su bai-biba ya tattake wanda suka tokare mai bakin 'kofa yai wucewar sa ciki, bakin sa 'dauke da sallama, jefar da gown din yayi a kan sofa, yana sakin siririn tsaki, kafin yace.


"So uncomfortable...!"


Gidan sa na da dasu Karimatu suka tashi, Dr Khaleel ya k'ara gyara shi ya koma tamkar sabo, aka rushe wasu sashen aka mai dashi sashe biyar kawai, b'angaren sa, dana Haj Aysa da Helwa uku kenan. Sai na Inna Bilkisu da b'angaren baki. Tamkar wasu amare haka ya mai dawa kowacce apartment d'inta, Royal furnitures sababbi fil aka sanyawa kowane sashe, amma na b'angaren Inna Bilkisu yafi kowan ne tsada tun farko haka suka saba yi komai nata yafi na matansu tsada, ko atamfa ce tata super ce, su kuma Holland domin iyaye ba abin wasa bane musamman ita da ta tashi tsaye da addu'oi, dan ganin Allah ya cika musu burikan su tun suna k'anana.


Sosai su Islam suka fara lectures, gaba d'aya bata da lokacin komai, dan da asubah malam yake zuwa yayi mata tahfiz da safe kuma take tafia lectures sai yamma ta dawo da daddare kuma lesson teacher d'inta yake zuwa, sam bata da wani spare time kullum she's busy, har time-table tayi na yadda xata dinga gudanar da ayyukan ta na yau da kullum. Cikin lokacin ne kuma aka sanya bikin Fatma Bichi dake kano, event d'aya Islam da Lee suka samu zuwa saboda school, gashi class d'insu d'aya kuma. Can Middle-East aka kai Fatima k'asar Qatar ko d'igon hawaye ba tayi ba domin tana matuk'ar son mijin nata, ko makaranta tace ita baxa cigaba ba ta yadda zata yi ABU mai labule.


****


Zaune suke a parlor Haj Aysa da Yakolo, wannan karan harda k'arin Yaburra(Zainab) 'yar gidan Aunty d'in Haj Aysaa dake Bornu. Shirye-shiryen auren Yakolo suke yi sai kace auren budurwa, dawowar Islam kenan daga school a matukar gajiye take, gaishe su tayi ta haura sama abunta, mai aiki ta bita da abinci. Wanka tayi kawai tayi sallah ta kwanta bacci. Can k'asa kuwa suna list na kayan gidah. Yaburra da tun d'azu zancen ke cinta ta kasa ajiye shi a zuciarta sai dai ta daure tace,


"Ni wai Yayya Islam har yanzu shiru? Ba wani a k'asa ne?"


Haj Aysa dake gefe ta sauke nannauyar ajiyar zucia kawai bata ce komai ba. Yakolo ce ta dank'arawa Yaburra harara kafin tace.


"Sai akai yaya? Wai ke bakisan aure lokaci bane? Ko kuwa duk dangin mu da sun tasa aure suke yi? Haba mana, ni fa bana son k'ananan maganganu da gutsiri tsoma, sai inci..."


Hanzarin katseta Yaburra tayi da sauri tace.


"Kai! Wallahi ni ba da wani abu na fad'i haka ba, kawai dai naga ina 'yar ya Fanna ta Askira? To itama kusan hakan ne issue d'in, sai da abu yai tsamari aka gane wai ashe jinnul-Ashiq ne."


Dogon tsaki Yakolo taja tana maida d'ankwalinta kanta, kyakkyawar harara ta k'ara bankawa Yaburra kafin tace,


"Duk naji, Toh kina nufin kice Islam aljanine a jikin ta ko me?"


Girgiza kai Yaburra tayi, tana k'ok'arin wayarwa Yakolo kai, wadda sam tak'i yadda, ganin hayaniyar tasu na neman caza mata kai ya sanya Haj Aysa dakatar dasu cikin sanyi tace,


"Ku bar zancen dan Allah! Allah ne kad'ai masanin gaibu, ke kuma Yaburra tunda kin kawo suggestion ki kirawoshi ya mata tambayoyi idan sune Allah ya mata maganin su, idan kuma basu bane Allah ya gaggauta kawo mata mafita ita da duk masu matsala irin tata."


"Ameeeen!"


Suka amsa gaba d'aya. Bugu biyu kuwa Ustaz Aliyu ya d'aga wayar, zaiyane masa komai Yaburra tayi cikin harshen kanuri, ya shaida mata gashi nan Insha Allah bada jimawa ba don dama basu dad'e da dawowa daga tafiya ba shida amaryar sa Jiddah. Ba'a d'au lokaci ba kuwa sai gashi duk sun gaggaysa dashi kafin a kira Islam dake sama tana bacci, sai data watsa ruwa kafin ta sakko sanye cikin hijabi. Gaishe shi tayi ya amsa cike da fara'a, ya d'anyi naxarin ta na d'an wasu lokuta kafin yayi addu'a yafara magana cikin sanyayyar muryar sa.


"Idan aka ce Jinnul Ashiq, ana nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji. Akwai kuma Ashiq dake bibiyar 'yan mata ta hanyar ture (sihiri) ko kuma sun yi wasarere ya shiga jikin su. Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma k'ok'arin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga k'ok'arin kashe mata shi. Su na kuma k'ok'arin hana mace samun ciki ko kuma in ta samu cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa ya zamo tun daga haifar sa za a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau'in Aljani shi muke kira...JINNUL ASHIQ ๏บŸ๏ปฆ ๏บ๏ปŸ๏ปŒ๏บŽ๏บท๏ป–,


"Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne, alamomin shafar aljana mace ta b'angaren maza sune; rashin sha'awar aure ko jima'i sam-sam, k'in mikewar gaba sanda kai nufin yin jima'i alhali kuma haka kawai ma yana tashi, k'in fitowar ruwa yayin jima'i, domin Aljanin yana iya zama a cikin marainan mutum, saurin gajiya yayin jima'i da rashin iya komawa, jin motsi kamar tafiyar wani abu a ga6o6in haihuwa yayin jima'i, rashin cimma bukatar jima'i in ka yi nufin yin jima'i sai bacci ya d'aukeka, da ka yi niyyar yin jima'i kawai sai ka ji ka kawo tun kafin ka fara, komawar gaba da maraina su shige ciki, yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili,


"fad'uwar gaba da dai sauran su, haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka, yawan mafarki kana saduwa da wata matat, yawan samun matsaloli a duk inda ka je neman aure sai maganar ta lalace, Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai, Matsananciyar sha'awa da tsoron mata da dai sauransu.,


_YADDA MACE ZATA GANE ALJANI YA AURETA_


"Yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi a cikin, a duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al'adarta bane, jin zafi yayin jima'i da rashin samun wata fa'ida, suna gama jima'i sai maniyyin da mijinta ya zuba ma ta ya dinga dawowa ba zai shiga mahaifar ta ba, matsanancin ciwon baya ko kwankwaso, kin yarda da jima'i za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban, yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da taron suna, ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa a cikinki ya fizgo wani abu,


"Musamman idan kina da ciki, yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen dalili ba. yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke, jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yana dad'a girma amma in likitoci suka auna za su ce ba su ga komai ba, rashin son yin magana da kowa da jin haushin mutane haka kawai, tsanar mai gida haka kawai alhali za ki ji kina sha'awar wasu mazan,


"Jin wari mara dad'i yana fito miki ko kaykayin gaba da kurajen gaba Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba. Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi, In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suyi mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fad'ar cewa wance kwarjini take musu, za ta dinga yawan zama a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane, Idan yarinya tana zuwa makaranta za'a ga k'ok'arin ta yana raguwa kuma tana ramewa, yawan ciwon kai da yin jiri, fad'uwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa. Idan mace ta fara bacci sai ta ji an zungureta ta farka. Da dai alamomi da yawa. Ya k'ark'are da cewa,


"Mafita shi ne ka ziyarci mai Rukiyya don ya d'ora ki akan tsarin maganin da ya dace da ke. Kuma ki dinga zama da alwala da addu'o'in safiya da maraice. Idan kuma wannan matsala tayi karfi, to dole sai an yiwa mutum rukiyyah, an nemi Aljanin an kona shi ko kuma a had'a magungunan da za su kashe shi. Ko'a sami garin harmal, ad'ebi cikin karamin cokali d'aya azuba a cikin ruwa babban kofi d'aya, sai a tofa ayoyin ruqiya ciki a dinga sha sau uku ayini. sannan a had'a man zaitun, man habbatussauda, man hulba, man gelo, man tafarnuwa, man na'ana'a, man Khisdil Hindi, Turaren za'afaran,


"Turaren miski, turaren wardi, Garin khaltit. Sai a had'a su duk awaje d'aya, a tofa ayoyin ruqya aciki, ana shafawa sefe da kuma dab magriba. Insha Allah za'a dace"


Daganan ya shiga yiwa Islam tambayoyi ko zai gano alamun ko ta kamu da shafar jinnul Ashiq, amma kemad'agas ko alamu babu. Ta amsa komai tiryan-tiryan babu matsala, hamdala yayi, kafin yace ta samo biro ya babbata wasu addu'oi, Daganan yace ta koma sama abunta, ruwan da aka ajiye agabansa yasha kafin yace.


"Toh hajia Alhamdulillah domin gaskia 'yarku bata da matsalar Ashiq, kawai jinkiri ne da zai zamto alkhairi Insha Allahu, tunda yadda na d'auka ma ashe ba hakan bane, domin yarinya ce har yanzun, Insha Allahu zata samu abunda ake buk'ata da yardar Allah, kawai dai shine ta rike addu'oi, azkhar na safiya da maraice dana kwanciya bacci. Kullum ta zamto cikin alwala, lalle ne kuma ya zama wajib idan zatai bacci ta kwanta da alwala, ta kuma dinga yin addu'o'in dana bata sannan ni zan mata wani tofi a ruwan zam-zam Allah yasa mu dace."


"Ameen.." suka fad'a baki d'aya. Fuskar Haj Aysa fad'ad'e da murmushi.


Zungurar Yaburra Haj Aysa tayi da k'afa tana mata alamun nawa za'a bashi? Murmushi Yaburra tayi kafin tace,


"Malam Aliyu, Toh mahaifiyar Islam d'ince ke tambayar nawa za'a bayar na lada dana zam-zam d'in?"


Murmushi Aliyu yayi yana mikewa tsaye, hannunsa d'auke da ragowar ruwan sa, cikin muryar sa mai dad'in sauraro yace,


"Haba Yaburra. Ladan addu'a fa kikace? Haba Allah ya kiyaye, ni dan Allah nayi batun zam-zam kuma idan nagama yi zan aiko a kawo, fatanmu koma menenen ya warware cikin sauqi, ballantana ma k'alau take, kada kusa komai a ranku wallahi lokaci ne kawai bai yi ba, Allah yana sane da komai, ba kuma wai dan baya sonta ba, sam ba haka bane, wani lokacin ma jarabawa ce daga gareshi ya gani shin zata iya cinyewa ko kuwa? Toh Allah ya bata ikon cinye jarabawar ita da duk masu jinkiri irin nata"


"Ameen.." suka fad'a baki dayan su.


Har bakin k'ofa Yaburra ta rakashi kafin ta dawo ciki, Haj Aysa tai mata godia itada Yakolo. Nan suka sake zaman hirar Aliyun da irin kirkin sa, har maganar matan sa ta shiga ciki, Yaburra tace.


"Wallahi matan sa biyu, Maimuna itace uwargidan sai Jiddah ta biyun, amma naji ance yana neman ta uku a kano."


"Haba?" Cewar Yakolo da Haj Aysa.


Jinjina kai Yaburra tayi cikin gasgata abun da take fada tace,


"Haka naji, kai dagaske nema domin yace min da kansa yana neman ta uku a kano, wai kinji sunan ta 'Miss xoxo' shine nickname d'inta, yace wai ta WhatsApp suka had'u a group d'insa na ilimi-haske ne. Ya ma sunan ta na gaskiyar..? Yawwa Nana-Hafsatu."๐Ÿšด๐Ÿผโ€โ™€


"Allah sarki, Allah ya basu zaman lapia, ya sanya alkhairi."


"Ameen" cewar Yaburra.


Basu tashi daga wajen ba sai da suka gama list d'in komai na biki, da sati ya zagayo kuma a ka raqashe bikin Yakolo, kamar wata 'yar budurwa, rana d'aya akai wushe-wushe a farfajiyar gidan su Helwa ne akan komai. Aka kai amarya nan gidan ta dake unguwar Asokoro.


*LAGOS*


Tunda Saifullah ya dawo, ya fara shirye-shryen tafiya bautar k'asa (NYSC), ya gama komai. Jira kawai yake yaga inda za'a tura shi, ranar Monday da safe kuwa Mail ya shigo masa na anturashi 3weeks camp a Abuja. Sam bai so haka ba, domin yaso kudu aka kaishi, aganin sa wai zaifi samun life experience. Kwana biyu nayi ya d'aga zuwa Abuja bisa jagorancin Khaled, wanda vissa d'insa zata fito nan bada jimawa ba. Camp ya shiga, yanayin yadda 'yan mata ke rushing d'insa ya sashi kasa zama, sannan shi mutum ne mai son tsafta, amma yanayin band'akin camp d'in sam bayi masa ba, beside gurin ma gaba d'aya is too noisy acewar sa. Nan yai ciku-cikun sa yai exeat from camp. Yakoma gidan su Khaled yana jiran fitowar 'yan camp d'in don ganin shin za'a canza masa gari(relocation) ko kuwa?.


ย ย  Sanyayyar safiyar asabar ce ya fito da damuna, garin yai luf-luf dashi, Sam ba hayaniya korayen bishiyu sunyi shar dasu ni'ima na busawa ta ko'ina. Da kyar ya fita daga gida domin daily exercise d'in daya saba. Yana tafe yana d'an had'awa da gudu ya rufe kansa da hular sanyi. Yanayin na matukar ratsashi sosai yake jin dad'in yadda yake motsa jikin nasa.


A lokacin ne kuma Islam tafito daga gida itama, don yin exercise, aganinta saboda yana da kyau yana gyare jiki musamman kuma don ta rage yanayin jikinta dan sam bata san yadda mutane ke bin jikinta da kallo, shi yasa a school kullum cikin hijabs/jilbabs ko Abaya take. Tafe take tana tafiya tana had'awa da gudu. Riga da wando ne a jikinta kasancewar da sassafe ne ba wanda ya fito tunda weekend ce, kuma d'ai-d'ai kune ke fita exercise din. Ba kowane zai ganeta ba, amma ta yane kanta da mayafin abaya, kunnuwanta saqale da earpiece tana sauraren karatun alqur'ani mai girma na k'ira'ar shureim. Medicated glasses d'inta kalar kayan jikin ta, ta bayan gidan su ta fara zuwa gaban layin su.


K'ok'arin rage volume take yi lokacin data shawo kwanar gidan su Humaira, kanta a akan wayar ta sam bata kallon gaban ta, hakama Saifullah dake tafiya da baya-baya, wai shi kwarewa cikin rashin sani ji kake garau, goshin su ya had'u dana juna. Tuni wayar hannun ta, ta sulale tafad'i a k'asa cikin azabar zafi Islam ta dafe goshin ta tana fad'in.


"Ouch! Ya Salam!"


Saifullah dake rik'e da nasa goshin yana mulmulawa ya sakar mata wata uwar harara, yana fad'in,


"What the fuck... hey watch it."


Dago dara-daran idanuwanta tai tana duban mai fad'ar haka, ya bigetan sannan ya fad'a mata haka? Ba ko ban hak'uri. Dake blurred take ganin fuskar mai maganar sam batasan ya kalar sa take ba. Girgiza kai kawai tayi ta duk'a k'asa tana d'aukar wayar ta. Ko takansa bata biba tai wucewar ta gidah cike da haushin arrogant fellow d'in da suka had'u yanzu. Har ta wuce wa ganinsa yana bin bayanta da harara tamkar tana ganin sa. Cikin shagwababbiyar muryarsa yace,


"Annoying piece of shit...!"

Comment