SHIN ZA A IYA YIN TSARKI DA PURE WATER

*052 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*


*SHIN ZA A IYA YIN TSARKI DA PURE WATER?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, fatan alkhairi gare mu baki daya. Malam don Allah ruwan da aka sha na pure water zai iya tsarkake fitsari, bayan an sha raguwar a ledan sai a yi tsarki da shi ga yaro ko babba?

AMSA:

Ruwan da aka sha aka rage na pure water zai yi tsarki mana, saboda ruwa ne mai tsarki a karan kansa, sannan kuma mai tsarkakewa. Sharaɗin ruwan da za a yi tsarki da shi ya zama mai tsarki a karan kansa, sannan kuma mai tsrkakewa, wanda kuma pure water ya haɗa duka sharuɗɗai biyun nan.

Allah ne mafi sani.


*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

28/5/1440 h.

03/02/2019 m


Comment