*KUSKUREN DA MATA SUKE AFKAWA YAYIN 'DAUKEWAR JININ HAILA

*KUSKUREN DA MATA SUKE AFKAWA YAYIN 'DAUKEWAR JININ HAILA*
______________________


Mafi yawan mata idan jinin al'ada ya 'Dauke musu suna jinkirta wanka da niyar ko jinin zai Qara dawowa.


Wasu sukan Qara kwana 'Daya zuwa biyu bayan haila ya 'Dauke.


Wasu kuma idan suka ga alama guda 'Daya na 'Daukewar jinin, sai suce zasu jinkirta wanka domin su jira zuwan sauran alamomin. Misali: Mace taaga bushewar gaba amma bata ga Farin ruwa ba, wanda ake kiransa da larabci (قصة البيضاء), daga nan sai tace bari ta bari sai farin ruwa yazo sannan tayi wanka ta cigaba da sallah da azumi.


Duka Wannan kuskure ne babba ❌❌


Abinda yake wajibi shine: Da zarar taga jini ya tsaya ko taga alamomin Daukewar Jinin haila, toh wajibi ne tayi wanka nan take ta cigaba da ibadar ta. Qin yin wanka har lokacin sallah ya wuce babban zunubi ne.


Allaah ya tanadi Azaba mai tsanani ga masu wasa da sallah.


Allaah yace:-


" ﻓَﻮَﻳْﻞٌ ﻟِﻠْﻤُﺼَﻠِّﻴﻦَ ‏(4 ‏) ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻋَﻦْ ﺻَﻠَﺎﺗِﻬِﻢْ ﺳَﺎﻫُﻮﻥَ "
{ﺍﻟﻤﺎﻋﻮﻥ : 5-4 }


Allaah ya qara da cewa:-


" ﻓَﺨَﻠَﻒَ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِﻫِﻢْ ﺧَﻠْﻒٌ ﺃَﺿَﺎﻋُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﺍﻟﺸَّﻬَﻮَﺍﺕِ ﻓَﺴَﻮْﻑَ ﻳَﻠْﻘَﻮْﻥَ ﻏَﻴًّﺎ "
{ﻣﺮﻳﻢ : 59 }


...... Da ayoyi masu yawa cikin al-Qur'ani.


daga lokacin da jini ya 'Dauke, ibada ya wajaba ga mace.


idan mace ta jinkirta sallah toh sai ta rama su bayan tayi wanka, sannan tayi istigfarin jinkirin sallah


*_Idan kin karanta kiyi Qoqarin turawa yar uwarki musulma zaki samu lada in shaa Allaah._*


✍ Dan uwanku a musulunci da Sunnah:-
*
Dr zahradden Kano

Comment