11

*KWANTAN ƁAUNA*
         FitattuBiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*011.*

       Maimakon ya wuce gida samun kansa yayi da nufar gusset house d'in mai martaba da yake hannun sa ya shiga ya faka motar ya shiga cikin gidan, a kan kujera ya zauna yana sauke numfashi a wannan lokacin kiran Zaid ya shigo wayar sa, d'auka yayi dan yasan maganar guda d'aya ce ya ya sauka kuma daman abinda ya tambaya d'in kenan. Ajjiye wayar yayi yana kallon wani waje daban kafin ya kulle idanun sa hoton ta yana gifta masa a idanun sa.

         Tuno fuskar da aka zana masa yayi ya tuno fuskar yarinyar da ya taimakawa a bayyane yace, "Akwai kama sosai, kenan suna da relation?." Sai kuma ya dafe kansa a zuciyar sa yace, _Why Asad meyasa wannan zai dame ka?, kawai dream ne fa ba gaskiya bane, ka manta da wannan tunanin ko zaka samu peace of mind._ numfashi ya sake saukewa a bayyane yace, "but why nake ganin ta a mafarki always tana taimako na?."

        Sai kuma ya mik'e tsaye yana fad'in, "ya kamata na nemo wannan yarinyar" Sai kuma yaja ya tsaya ya kama k'ugu ya fad'a kan kujera ya zauna yana furta, "Oh Asad!" Ya dafe kansa yayi shiru yana sauke numfashi a hankali tunanin yake barin ransa ya runtse idanun sa yana goge fuskar ta mafarki da wacce aka zana masa a hankali suke barin idanun sa yana ajiyar zuciya.
Ya jima a haka sosai har magariba tayi a nan yayi sallah kafin ya mik'e ya d'auki key da wayar ya fita ya shiga mota ya fita daga gidan.

          Baiyi gida ba babban company sa ya wuce ya tarar da Hafiz yana ta kai kawo har lokacin ganin sa ya shigo ya saka shi bin bayan sa zuwa office suna zama Hafiz yake cewa, "Asad what happened?." Bai bashi amsa ba yayi shiru ya jawo laptop d'in dake kan table d'in gaban sa yana dannawa. Ganin hakan sai Hafiz ya bar shi ya fita bai jima sosai ba ya fita daga office d'in yaja motar ya fita gabad'aya.

          Gida ya wuce kai tsaye wajan Mama ya shiga kasancewar magariba ce bai same ta ba Suhaima take sanar dashi tana d'aki ya shiga wajan Hydar yana nan kamar yadda yake koda yaushe ko hannun sa baya motsawa yayi masa addu'a ya zauna a kan kujera yana kallon sa. A nan ya kwashe lokaci da yawa har i'sha tayi ya fita yayi sallah ya sake dawowa a nan ya ga Mama a wajan Hydar ya k'araso gaban ta ya tsuguna da girmamawa yace, "Barka da dare Mama."

"Ina kaje yau?" Ta tambaye shi ba tare da ta amsa ba. Kallon ta yayi sai kuma ya d'auke idanun sa wannan tun yana ganin wani abu kan tambayar nan da Mama take masa ta ina kaje, ina zaka, me zakayi in ka fita, wa ka tambaya har ya daina ma domin ya saba.

"Naje Abuja" ya bata amsa a tak'aice. Bata ce komai ba tayi jim kafin tace, "yaushe zaka je wajan Jidda kasan dai ita zaka aura ko?." Kallon Maman yayi baice komai ba tace, "in baka ce ba nasan ai ka jini, nan da lokaci kad'an za'a d'aura muku aure ta." Kai ya girgiza kafin yace, "Mamaa......" Sai kuma yayi shirun jin hakan sai tace, "kar kace min baka sonta ko baku dace ba, itace zab'ina ya zamar maka dole ka sota." Kai ya jinjina alamun gamsuwa kafin ya mik'e jikin sa a sab'ule ya fita.

      Sallama akayi aka shigo falon ana fad'in, "y'ar sarki, jikar sarki, matar sarki, babar sarki kuma k'anwar sarkin garin Kano in sha Allah." Jin muryar tasan wacece k'anwar mai martaba kenan Rabi'a kaf cikin dangin mai martaba tasu ce tazo d'aya suna shiri sosai ta juya ta kalle ta ta fad'ad'a murmushi tace, "babbar bak'uwa." Murmushi tayi mai sauti itama ta k'araso tana fad'in, "Zaman kujera ya gagare ni ni Rabi in dai har gimbiya na zaune a kai." Kan Mama ya sake fashewa izzar ta ta ninku ta saki murmushin k'asaita tace, "keda kika b'uya ko ganin ki ba'a yi."

"Yanzun ma dole ce ta saka na taso nazo domin naji abubuwa suna ta faruwa marasa dad'in ji." Mama ta sauke numfashi tace, "bari kawai Rabi'a komai yana neman lalace min lokacin da ban shirya ba."
"Shiyasa nazo ai naji ya akayi hakan take faruwa."
"Sharrin Hajiya ne, itace ta bama Asad guba a ganye yaci." Murmushi Tayi tace, "Zata aikata ai, in kince badaqalar da suke yi da waziri kare bazai ci ba. Waziri yayana ne amma bazan b'oye miki ba baya son ki baya son me son ki, kinga dashi da galadima dama kawai suke jira a kan ki su kawar da y'ay'an ki sabida a lalata maki goben ki."

     "Na sani takwara, na sani. Duk abinda suke yi a kan idanuna suke yin sa. Nan Suhail fa ya kira Suhaima yana bata wani abu wai ta bawa Asad na tsarin jiki ne, kiji rainin wayo da y'ar uwar sa yake son yin amfani yaga bayan sa." Tace, "shiyasa dana tashi tawowa na biya wajan malamin nan na karb'o garin magani da rubutu, kinga lamarin Aliyu ma wallahi saka masa hannu akayi haka Hydar ma. Asad ya gagare su ne kawai sabida ibadar sa amma shima zasu iya nasara a kansa nan gaba tunda ya kasance mai rauni ta wani fannin."

Mama tace, "ta b'angaren yarda da mutane Asad yana da rauri, ta b'angaren magana Asad yana da rauni. Amma fa wani abun kwantan b'auna yake yi kallon kowa yake kawai bar shi da rashin maganar sa. Amma wani lokacin in yayi wani abun sai ki d'auka Aliyu ne." Mama Rabi tace, "na sani, namijin duniya kenan kallon su yake yi ta wani b'angaren na san da hakan. Ga rubutun da maganin ko wanne da bayanin sa akwai na Asad akwai na Hydar dana Aliyu harda Suhaima."
Mama ta ja ledar kusa da ita tana dubawa tace, "ai yanzu ma zan tashi na shafawa Hydar nasa dan wancan lokacin rubutun da kika kawo aka shafa masa yayi amfani sosai."

"Mai martaba baya aiko da nasa?." Mama tace, "Da kansa yake zuwa ya bashi kin san gidan ya yake baya barin kowa yazo da kansa yake zuwa, shi da Asad kuma kin san ai ba'a jin sirrin su."
"Haka ne. Wai kuwa Rukayya da Sa'adatu sun zo duba Hydar kuwa?." Mama ta tabe baki tace, "Sun zo."
"Ki dai kula da Sa'adatu zata iya goga masa wani abun a hannu ko a k'afa wallahi." Murmushi tayi tace, "na sani fa rasss nake kallonta."  Mik'ewa tayi tace, "ranki ya dad'e ki shafa masa zan shiga ciki na dawo." Kai ta girgiza kawai ita kuma ta fita.

*Bayan Kwana biyu.*

Babu abinda ya ragu ta b'angaren harin da ake kawowa Asad bai kuma fasa addu'a ba mafarkin da yake kullum k'aruwa yake, tunda aka zana masa fuskar ta kuma sai ya koma ganin fuskar a mafarkin amma yak'i bari mafarkin yin tasiri a zuciyar sa yana k'ok'arin mantawa dashi koda yaushe. Fuskar ta ta zama masa tamkar hoto a idanun sa da ya kulle sai ya hango ta hakan ya saka yake jin wani iri a zuciyar sa.
Hydar na kwance har lokacin amma an samu cigaba dan zuwa lokacin yana motsawa alamun ya kusa farfad'owa kenan.

         A zaune take a babban d'akin ta wanda aka k'awata shi da kayan gado na alfarma waya na hannun ta, kamar wacce aka tunawa ta danna number Dr ta kira shi bata jima tana ringing ba ya d'auka yana fad'in, "Allah ya ja da ran Mama."
"Ka sallami yarinyar nan kuwa ko tana nan?" Bata amsa gaisuwar ba abinda ta fara tambaya kenan. D'an dabarbarcewa yayi kana yace, "Na sallame ta Mama."
"In ka min k'arya na gano gaskiya kai kasan sauran."
"Ba k'arya nake ba tun lokacin na sallame ta."
"Ka kyauta. In Hydar ya farfad'o kasan sometimes yakan manta wasu abubuwan na baya sai daga baya ya tuna in ya manta batun ta koda zai tambaye ka bana so ka sanar dashi kace komai bai faru ba ka gane ko?."

        Kamar yana gaban ta ya girgiza kai alamun to kafin yace, "zanyi in sha Allah."  Bata kuma cewa komai ba ta yanke wayar yabi wayar da kallo yana sauke numfashi. "Wannan mata masifaffiya ce, ta yaya zan iya sallamar Rauda bayan har yanzu bata ji sauk'i ba?. In kuma na barta ta gano na shiga uku."  Tsaki yaja ya mik'e ya tafi d'akin da Raudan take ya same ta a zaune tana karatun alkur'ani a bayyane. kallon ta yake da birgewa domin da wuya yazo ya same ta haka kawai bata karatu ko lazumi.

Sallama yayi ta katse karatun ta kalle shi tace, "Dr shigo mana." Umma da bacci ya fara d'aukar ta ta mik'e zaune ya k'araso ya tsaya yana kallon k'afar tata yace, "Ya k'afar?."
"K'afa da sauk'i yanzu bata min ciwo ai sai dai gajiya da zama." Ya sauke numfashi yace, "Rauda kud'in wanda ya kawo ki asibitin nan ya k'are kuma shima yana kwance babu lafiya tun zuwan sa na k'arshe nan shine na rasa yadda zanyi." Gaban Umma ya fad'i itama Raudan haka ta rufe alkur'anin tace, "To sai mu koma gida."
"Eh ko kuma ku biya kud'in."
Umma da take gefe tace, "mu biya me likita? Ina muka ga wannan halin?, gwara dai mu koma tunda Allah yayi k'afar tayi kyau."

      Jikin sa sai yayi sanyi ya sauke numfashi yace, "to in kun shirya zan saka a kai ku a mota sabida k'afar tata kafin kuje ku saka a gyara mata inda zata zauna, zan baku magungunan da zata dinga sha da abubuwan da ya kamata ta cigaba da ci in sun k'are a kuma siya. Kuyi hak'uri dan Allah na rasa yadda zanyi ne."
"Haba likita meye na bada hak'uri? Ai kayi k'ok'ari ko kaine ka buge ta ai sai haka."

Rauda ta tab'e baki tace, "Daman su y'ay'an masu kud'in nan babu abinda suka sani sai kansu, yanzu inda girmamawa ai yaci ace wani nasa yazo ya cigaba da d'aukar nauyi na tunda sune silar komai. Tunda bashi da lafiya an bar maganar daman ba gata ne dani ba sun yiwa banza. Allah wadaran wasu masu kud'in" Rauda ta fad'a a fusace.

Dr yace, "Wallahi Hydar bashi da wannan halin baki ga yadda ya tsaya akan ki ba rashin lafiya ce dashi in ta tashi sai ya kwashe sati uku a sume bai farfad'o ba, yanzu zancen da nake miki tun da yazo nan ciwon ya same sa bai tashi ba har yanzu."

Umma tace, "kai ka biye mata ai likita ai ko iya haka aka tsaya yayi k'ok'ari sosai, wanda in sun buge ka suke guduwa fa su kuma ace musu me?."
"Umma maganar da ta fad'a gaskiya ce ya kamata ace wani nasa ya tsaya, amma da zaku san waye shi ku kuma san abubuwan da suke faruwa da ku kan ku kun tausaya masa shida y'an uwan nasa."
"Allah ya kyauta" Umma ta fad'a.

A wannan lokacin aka had'a magungunan Rauda da komai nasu aka saka Rauda a ambulance Umma ma ta shiga aka wuce da ita gida. Kafin suje Inna ta gyara d'akin Umma an yiwa Rauda shinfid'a aka shigo da ita a akan gadon aka zaunar da ita aka basu maganin ta suka koma.

        Umma ta cire mayafi ta ajjiye  tace, "Daman na gaji da zaman asibitin nan, zaman asibiti sai dole." Rauda tayi shiru bata ce komai ba haka kawai take jin haushin wanda ya kad'e ta a ganin ta bai d'auki lafiyar ta da mahimmaci ba tunda ita talaka ce.
Ummulkhairi da Khalil sai dawowa sukayi suka ga su Umma a gida suka dinga murya Umma ta dawo.

      K'arfe biyu na rana Baba ya diro gidan ganin k'ofar Umma a bud'e ya saka shi ya lek'a ya gansu a zaune Rauda tace, "Baba sannu da dawowa." Kallon su yake da mamaki kafin yace, "Me kuma ya dawo daku?." Umma tace, "Kud'in wanda ya kad'e tane ya k'are a asibitin kuma bashi da lafiya shiyasa aka dawo damu gida." Baba yaja dogon tsaki yace, "Kai amma ban so hakan ta faru ba, yanzu shikenan bazan kuma ganin sa ya bani wani abun ba? Abin takaici wallahi."

      Rauda tabi mahaifin nata da kallo da mamaki kafin ta d'auke kanta Allah ya sani abinda yake yi yana bata takaici kawai dan babu yadda zatayi ne uba uba ne. Juyawa yayi ya fita yana fad'in, "To Rahma a fito." Ba musu Rahma ta fito da hijjabi ya nuna mata kular yace, "gashi nan na dubu uku ne ayi aje a dawo." Da to ta amsa ta d'auki kular ta fita ranta a b'ace.

Inna ta fito daga d'akin ta ta kalle shi tace, "Tsakani da Allah malam nima da nake goya maka baya na gaji da wannan tallan da kake d'orawa yaran nan, ka duba halin da Rauda take ciki ta dalilin talla ni na d'auka zaka saduda sabida hakan amma ko gezau bakai ba."

     Kama k'ugu yayi yace, "To uwata kama kunne na zakiyi ki fad'i maganar nafi fahimtar ki sosai." Inna ta d'auke kanta gefe yace, "in ban d'ora musu tallan ba a gida kike so su zauna naita kallon su su ba aure ba ba kuma samari ba?, meye amfanin su in basu yi tallan ba?."
"Abinda kake sakawa suna yi ba shine zai kawo musu miji ba, aure kuma ai lokaci ne in yazo kamar ba'a zauna ba."
"To bazan daina ba, tallah yanzu suka fara siyar da abinci ba ki d'auka yanzu aka fara wallahi sai sunyi. Inda Allah ya bani manyan y'ay'a maza ya za'ayi na saurare su?, haihuwar y'ay'a mata a farko ma ai asara ce."

Umma da take d'aki tace, "Haba malam, da kanka kake furta wannan maganar?, abinda Allah ya baka ne fa kake cewa asara?."
"Asara mana inda wad'anda na  aurar suke gidan mazajen su ne y'ay'ana maza da yanzu sune suke taimaka min ko d'awainiyar ku suka d'auke min ai na huta amma duka mata ne kuma suka auri talakawa ba uwar abinda nake mora, su kuma wannan da suke zaune ba miji sai na zuba musu idanu haka kawai ina ciyar dasu a banza bana k'aruwa?."

     "Daman hakkin ciyarwa a kanka yake ba kan su ba" Inna ta fad'a tana kallon sa. Yace, "wannan kuma ku kuka jiyo tallah dai yanzu na fara in kunji haushi bakwa so suyi ku dinga ciyar da kan ku kuga zan basu tallah ko bazan basu ba" yana fad'ar hakan ya fita Inna tace, "nidai na gaji da wannan dabi'ar wallahi." Umma bata kuma cewa komai ba balle kuma Rauda da take zaune.

         Ba jimawa Yaya Ummi tazo ta fara shiga d'akin Inna ta gaishe ta sannan ta shiga d'akin Umma tana fad'in, "Allah ya taimaka banje can ba kika min waya Umma." Ta fad'a tana zama Umma tace, "Shiyasa na sanar dake ai dan nasan tsaf zaki iya wucewa." Gaisawa sukayi ta kalli Rauda tace, "Sannu Rauda, kin ajjiye k'iba kinyi haske da yake babu inda kike zuwa." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba.
"Ni gwara ma da kuka dawo gidan wallahi k'afar taki ai tayi kyau da yake asibitin kud'i ne kamar ba karaya ba."
Umma tace, "haka nace nima wallahi, ai yayi k'ok'ari yaro."

         Ledar da ta shigo da ita ta bud'e ta mik'a mata tace, "karb'i kazar hausa ce kici ance ana so masu karaya suci kaza." Karb'a Rauda tayi tace, "Na gode Yaya Ummi, Umma kici." Umma tace, "ki ci k'oshi tukunna, naji dad'i ma dasu Khalil sun tafi islamiyya." Ba musu ta fara ci  suna hira sama-sama kawai sai ganin Baba sukayi kamar an cillo sa.

       Kafin suce wani abun ya saka hannu a kwanon hannun Rauda ya d'auki k'atuwar b'angare daga cikin kazar ya saka a baki yana fad'in, "Daman sai dana aiyana wani abun kika kawo kika k'unso a leda to Allah yayi da rabona, yaushe rabon da a gamu da kaza?" ya fad'a yana taunawa tare da lumshe idanun sa. Umma takaici kamar me haka take ji amma ya zatayi haka tayi tagumi tayi shiru suma haka ba wanda yace uppan ya cinye ta hannun sa ya kuma d'aukar wata yana ci.

Yace, "Ke Mamana yaushe mijin naki yayi kud'in siyo miki kaza har kika bayar?." Yaya Ummi tace, "ba shine ya siyo ba bashi na karb'o a mak'ota na na dafa mata ganin mai karaya ce, ina yaga halin da zai siyo min kaza Baba?."
Baba yana b'alla k'ashi yace, "yauwa koda naji" ya fad'a yana fita ya sha ruwa ya dauraye hannun sa ya fita. Umma tace, "Allah ya kyauta." Da amin suka amsa kafin Rauda tace, "Amma Yaya meyasa zaki karb'i bashi?."
"Ke k'arya nake ba bashi na karb'a ba wasu y'an kud'i Abban su Islam ya samu ya siyo mana guda uku yace na kawo miki guda d'aya. Kin san halin Baba ina fad'a masa hakan gobe a gidana zaiyi sallama yace masa bashi da kud'in cefane."

Dariya Rauda tayi tace, "kinyi farar dabara." Umma ma dariya tayi bata ce komai ba Yaya Ummi tace, "ke ai kece a ruwa kika auri wannan yaron Anas ai kun shiga uku da rok'on Baba wallahi." D'aure fuska tayi tace, "nifa bashi zan aura ba Allah zai kawo min miji na."
"Allah ya kawo k'anwa ta burina naga anyi auren ki. Allah ya kawo wanda ya fishing mu sha biki." Da amin suka amsa ta cigaba da cin kazar kafin ta ragewa Umma.

            *☆☆☆*

        A zaune ya same ta kamar koda yaushe ya k'arasa ya zauna a kan carpet ta kalle shi tace, "tun yaushe nace kaje gidan su Jidda?." Yayi shiru bai amsa ba ta kuma cewa, "ba magana nake maka ba?." Asad yace, "tun kwanaki."
"Sabida ban isa dakai ba ya saka baka je ba kenan ko?." Kai ya girgiza alamun a'a yace, "Tuba nake."
"To me ya hana ka zuwa?."
"Na manta ne."
"Yanzu na tuna maka ai saura ka kuma cemin ka manta. Kunyi waya da mahaifin ka?."

Kai ya d'aga tace, "yaushe zai dawo?."
"Jibi" ya bata amsa a tak'aice yana kallon k'asa. Zatayi magana Aliyu ya shigo cikin k'ananu kaya mara sa tsayi a jikin sa ya mayar da gashin fuskar sa bak'i kamar na Asad daman shine yake banbanta su sai suttura kuma. Shima k'asa ya zauna Mama ta kalle shi tace, "Lafiya na ganka haka?." Ya cize bakin sa har zai magana sai kuma yace, "babu komai."

"Kai dai ka sani" ta fad'a tana kallon Asad kafin tace, "na gama dakai zaka iya tafiya." Ba musu ya mik'e yace, "Ki tashi lafiya" ya fad'a yana fita. Aliyu ya kalle ta yace, "Allah ya taimaki Mamana maganar me naji kuna yi dashi?." Mama tace, "to wanda ya haife ni bani umarni sai na fad'a maka." "Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake. Ki tashi lafiya" ya mik'e yana girgiza kansa ya fita ta bishi da kallo cikin takaici.

         Asad yana fita mota ya hau ya tafi company dan akwai abubuwan da dole sai yaje da babu abinda zai kai shi, yana zama a office yaji kansa yayi mugun sarawa ya dafe kan da duka hannu biyu ya kulle idanun sa, "Prince lafiya?" Hafiz ya fad'a yana shigowa. D'ago kai Asad yayi ya kalli Hafiz da ya zauna ya girgiza kai kafin yace, "kaina."
"Sorry."
"Ina files d'in nan?." Hafiz ya mik'e ya kawo masa yana dubawa Hafiz yace, "akwai abinda yake damun ka deaf, tell me please." Baice komai ba ya koma ya jingina da kujera yana sauke ajiyar zuciya amma baice komai ba.

Hafiz yace, "i don't know why yanzu baka sanar dani damuwar ka." Asad yace, "no ba haka bane, babu ne" ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya d'auki key da wayar sa yace, "in ka gama ka same ni gida."
"Okay, akwai meeting da kamfanin k'asar Dubai yarjejeniyar suke so a k'ara musu tsahon lokaci."
Asad yace, "Kuyi komai" yana fad'a ya fita Hafiz ya bishi da kallon tausayi gabad'aya ya canja kamar ba shi ba.

         Bai koma gida ba yawo yayi tayi a gari bai koma gida ba sai magriba, yana shiga apartment d'in su yaga giftawar mutum kamar iska alamun rashin gaskiya ya dawo da baya ya ganta ta juya baya tana waya ya k'arasa kusa da ita ya tsaya yaji ana cewa, "na saka tun wancan lokacin har yanzu kuma yana cikin d'akin nasa." Juyo da ita taji anyi ta zaro idanu waje shima nasa idanun ya wara ganin wacece ya Bud'e baki yace "Suhaima!."

*Ba'a fara komai ba ku shirya kawai.*

Comment