Search: rayakasafar
8 stories
KWANTAN ƁAUNA

Izza, mulki, k'asaita sun tattara a gare ta ita kad'ai. Y'ar sarki ce, jikar sarki, matar sarki. Bata k'aunar talaka bata son had'a hanya da talauci, burin ta d'aya tak ya rage a duniya shi ne d'an ta ya zama sarki ta zama babar sarki kuma kakar sarki ta gobe; Sai dai kash! Y'ay'anta maza har guda uku masu matuk'ar kama da juna sun kasance babu wanda yake da qualities d'in rik'e ragamar Al'umma. Na farko shaye-shaye, na biyu kurma ne, na uku ba ya da lafiyar k'wak'walwa. A Lokacin da burinta ke gab da cika kwatsam Y'ar talakawa, bak'a, gurguwa mai tallan abinci ta shigo rayuwar samarin 'ya'yan nata guda biyu, gurgurwar da ta zama silar girgizawar duniyarta da burinta, gurgurwar da ta haddasa mata raunin da bata da shi, gurguwar da ta zamar mata inuwar dodo...shin me zai faru? Ta wacce hanya gurguwa ta kutso cikin rayuwar wad'annan sarakunan...? Waye zai zama sarki cikin su ukun duk da kasnacewar su masu kama d'aya......? ina alwashin da ta ɗauka na ganin cewar sai taga bayan duk wanda ya nemi ya ruguza lissafinta?, ina alwashinta na cewar sai ta kassara rayuwar wanda ya kawo kutsen hana ɗanta zama sarkin gari....? Zai cika ko A'a?.*KWANTAN ƁAUNA*

3.3K 27 145 Full
Dil Jaanta Hai

This story continues from when Ram leaves the police station after hearing that Priya is pregnant with Krish's child. And a 5 year leap takes place.

4.3K 6 231
Bade Achhe Lagte Hain 2 OS

Featuring Nakkul Mehta and Disha Parmar as Ram & Priya respectively. Refreshing takes on their married life as what I would love to watch. It has no drama just RaYa and their friends in day to day life.

33.3K 16 1.6K
WASA DA RAI

Ga rayuwar da yawa daga cikin ƴan Adam sukan iya fakewa da ƙaddara ko ruɗin shaiɗan. Sai dai a rayuwar wasu duka babu ɗayan da ke kasancewa daga cikin biyun da na lissafa, ciki kuwa har da ni kaina. Na tsammaci shiga gidaje masu manyan benaye da zama a cikin su kan iya mantar da kai wani mataki kake a yanzu?Haka na iyakance adadin motocin da zuciya ke muradin hawa. Ga irin rayuwar da nake gudanarwa na tasamma ware nau'ikan ababen cimaka don gudun gamuwa da wata lalurar, ko da kuwa jariri ce. Duk wata kusafa da na san zan iya gamuwa da talaka ko mai matacciyar zuciya da baya ɗauke da buri, ina iya kokarin don ka da mu gamu.A lokacin da lamarin zai soma ne duniya tamin atishar tsaki ta yadda komai da komai da ya wanzu a cikin rayuwa ta sai da ya zama ya disashe tamkar bai faru ba, hatta lafiyar da nake ganin ta jima tana walankeluwa dani wuri guda, yo i mana. Duk sa'adda wannan lamarin ke wakana ciwon kai banyi, sai dai a yau cutar dake tare dani, ko kuma ince cutuka, baza su zamo silar kai ni ƙas ba, sai dai lamarin da ya haɗoni da komai tunda fari ya zame min sanadi.

639 22 48
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU**NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?*TAMBAYA:

69.9K 200 990
BAƘIN RUHI

400 Century Masarautar Hawariyya dake arewacin India babbar masarauta ce da duniya tasan da zamanta wadda take wanzuwa ƙarƙashin jagorancin Sarki Ulumul Hawzar Sarki Ulumul Hawzar ya kasance matsafin gaske sadaukin jarumi da duniya ke tsoron kaidinsaSarki Ulumul Hawzar da Talakawansa sun kasance suna bautar wani ƙwarangwal wanda sukayi imani cewa wanzajje ne kuma buwayayye sunyi manna cewa wannan ƙwarangwal shike basu kariya kuma shike basu nasara akan abokan gaba sun jima da yarda wannan ƙwarangwal shine Abin dogaransu.Sarki Ulumul Hawzar yana da ƴa guda ɗaya Tal daya ɗauki son duniya ya ɗorawa wato Gimbiya Ayshuwar kenan mace me ƙuwwa Izza da taƙama da ƙarfin Iko.Nasruddeen ya bayyana a da wata ƙasaitacciyar siffa wadda ta sanya kowa yake gudunsa inda ya kasance ita kuma Gimbiya Ayshuwar shi take nema domin ta daɗe yana zuwar mata cikin baccinta cikin tunaninta da mafarkinta.Tabbas ta gasƙata shine suka taɓa rayuwa dashi shekarun baya kafin su shuɗe a sake halittar su tabbas shine masoyin da suka sadaukarwa da juna jininsu domin gujewa rabasun da iyayensu sukeson yi a wancan zamani.Shin kun aminta kamar yanda jama'ar Birnin Hawar suka aminta bayan mutum ya mutu ana sake halittar sa bayan ƙarni ɗaya 1 Century wato shekara ɗari?Wannan amsar sai kun kasance da Uwar Hairan yar gidan Tasiu jikar Umar ƴar Mutan Rano.Tsafi Sihiri mulki Rikicin SarautaZazzafar soyayya me salon ban tausayi da karya zuciyaRikicin Addini Cukumurɗa turka² Kudai kuyi maza ku rugo da gudu ku kwamushi naku akan 500 ku biya ta wannan account ɗin 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241

301 2 10
Sanadin Gata

~~Kanta dauke yake da farantin talla wanda aka kasa mata dafaffen rogo da gyada kulli kulli, taci damara sai kace wadda za tayi dambe tana tafe tana rera wakar ta"iye nanaye ayye yaraye nanaye carmama, ina tafiya ta jirgin goro zaya kade ni, jirgin goro kar ka kadeni, jirgin goro zan maka sako, sakon goro ko na turare in kaje kace da uwata, in kaje kace da ubana jirgi yai bari, jirgi yai bari da madaurin aurena, iye nanaye ayye ya raye nanaye carmama, da inna da baba an kawo kudin toshina cacas cas suna kirgawa, sun ganni suna boyewa in kun so kubar boyewa, auren fari sai na zaba sai na zabi wanda na ke so koda soja ko dan sanda, koda kuku koda boyi, koda jinjiri sha mama sai yaci tuwon kwanona sai yasha ruwan kwanona sai na kai ruwa sai nakai ruwa ban daki yai wanka, iye nanaye ayye yaraye nanaye carma....kuluwa, kuluwa kawo rogon, muryar wasu maza masu sai da ruwa ne ya hana kuluwa karasa baitin wakar da take rerawa, cikin sauri ta nufi wurin da suke, tana zuwa ta sauke farantin da ke kanta ta fara kukkulla musu kamar yadda suka saba siya, nan da nan aka warwashe ta dauki farantin ta cikin hanzari bayan ta kirga kudinta ta hada Kansu naira dari biyu cif cif, sauri take sosai dan tasan yanzu iyatu tana nan tana jiran zuwanta.

172 4 9