Search: munafinci
8 stories
NANA JAWAHEER

Labarine wanda ya kunshi soyayya da tausayi

7.1K 28 617
 AFRA

Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta buga akan speakern dan ta ga ko yana aiki. Illai kuwa sai ta ji ƙaran bugun da tayi. Murmushi ta ƙara sakar wa mutanen da duk ita suke kallo, da mamaki a idanuwansu, kafin ta buɗe baki tafara magana kamar haka." Assalamu alaikum " sai ta ɗan dakata kaɗan don su amsa mata, ba laifi wasu sun amsa mata wasu kuma sunyi ƙum da bakin su. " dama na zo ne don na nuna farinciki na game da taya abokin mu, kaninmu da yayen mu Salim murna " tace yayin da take kallon angon wanda tun tahowarta stage yake warwara ido kamar baƙin munafuki, gashi yanda zufa yake ta keto masa, zaka zata ba ac a wajen.Kau da idanunshi yayi kafin su hadu da nata. " amma kuma abin da ya sosa min rai game da wannan abin shine ni nafi chanchanta da a kira in zo in bada tarihin wanan bawan Allah. " ta ƙara dan dakatawa yayin da ta runsunar da kanta kamar mai wani tunani, sai kuma ta k'ara daga kanta ta kalle mutanen da duk suke yi mata kallon mahaukaciya wadda batasan abin da take ba.Budar bakin ta ne sai tace. " duk da dai an kira abokin ango yayi nasa bayanin barin in ɗan baku tak'aitaccen nawa "." amarya Salima " tace tana kallon amaryar da tace kwalliya a cikin doguwar riga kalar ja itama, sai dai na amaryar bai kai na wannan budurwar kyau da tsaruwa ba, dan inbaka san wacce amaryar ba sai kazata itace.Salima wacce tun da yarinyar tafara magana ta ke ta faman bankamata harara, taja wani ɗan tsaki game da sake sakarmata wani hararan.Afra , yarinyar da ta ke kan stage in ta murmusa kafin tace ." ina taya ki murnar auran munafukin namiji, azzalume wanda bai san darajar mutane ba, ina kuma ƙara tayaki murnar samun daƙiƙin na namiji wanda ban da wata shakka ƙarshen sa bazai yi kyau ba, kuma ki kasa kunan ki kiji mijinko mayaudari ne, me bin mata ne kuma zan iya rantse miki fasiƙi ne "Read and find out

71.1K 58 7.7K Full
RAYUWAR BADIYYA ✅

"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi.Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai.Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu._______Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?

254.9K 61 20.7K Full
DUKKAN TSANANI

Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi. Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi.Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min

115.4K 70 9.6K
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU**NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?*TAMBAYA:

70.7K 200 1K
Rose Evergreen

Ella vivió la guerra y la guerra vivió con ella.Una persona sin sentimientos, realmente qué es?En la vida solo hay dos polos:Frio y Calor.Cúal de ellos es Rose?

5 1 2
The Soul Psion | by Novelis

Book 1 of The Andania Series֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎֎Other than her parents, Nafissatou Cisse feels like the only one in the domed city of Asuna with a batyyn--- and that's most likely because she is. Because the Mlasere government demonizes the power as a "mutation disease," and disappears anyone with it, Nafi and her parents have been hiding their powers and living amongst the dormant civilians of the city ever since the apocalyptic Demunia took over their hometown. But when her family are discovered by the Mlasere, Nafi is forced to flee from the city and journey to the Anyato Mountains with the help of a mysterious woman and her companion. There she learns that she is part of the legendary Andania, a prophesized group of psions who can help save the Earth from wicked creatures called the Kulti. As Nafi faces the threat of not finding the rest of the Andania before the Kulti launch their greatest onslaught against humanity, she will have to find the strength in herself, and those around her, if she wants to save the ones she loves.

18 1 1